Showing 147001 words to 149977 words out of 149977 words
cikin daya qwallafa Rai suna tsanantawa rasashi zasuyi,hausawa sukace da Babu gwara ba Dadi, Dan Haka dasu rasashi duka gwara su lallaba a zauna lafiya.
Zaune yau a Palo habiba nayiwa Amal din gashin qafafunta dasuka Dan fara kumbura kadan wayarta ce a hannunta tana chatting da siddi ba zato taji qamshin turarensa.
Ajiye wayar tayi ta juya tana kallon kofar shigowa ga mamakinta ganinsa tayi tsaye Yana kallonta cikin wasu navy blue Cartier wears yayi wani irin kyau da haske na kwanciyar hankali da hutu harda wani kyakkyawan qasumba ya Tara daya qara Masa wani sanyin kyau da nutsuwa.
Murmushi ne dauke a fuskarsa Yana kallota cikin wani madaukakin sonta da kaunar abinda yake cikinta Wanda ya qara girma sosai.
Kallonsa takeyi sbd kasa dogon motsin datayi,
Ahankali ta sauke ajiyar zuciya tana lumshe fararen idanuwanta ahankali.
Da ido yayi mata" Hi love"
Sake sauke ajiyar zuciya tayi tareda janye kafafunta daga hannun habiba da Basu lura dashiba Dan tun farko sallamarsa Babu Wanda yaji
Itama qamshinsa dayake haddace cikin kanta da zuciyarta yasata dagowa ta kalli kofar.
Miqewa tsaye tayi ta nufesa ahankali tana kallonsa cikin tsananin farin ciki da sonsa Mai tsanani da kewarsa data Gama dawainiya da ita.
Bata qarasaba ya tako yashigo gabaki daya Yana sake kallonta da cikinta cikin kewarsu shima..
Gabansa ta tsaya tana kallon cikin idonsa ya bude Baki zaiyi magana ta daqa qafafunta ahankali takai fuskarta ta Dora bakinta kan nasa tafara kissing dinsa ahankali cikin sanyi.
Rungumeta yayi tareda Kama bakinta da nasa din yakarbi kissing din sbd sanyi da nutsuwar Wanda take Masa zai iya zautashi a gurin.
Tsotsan bakinta yayi tsawon minti daya da seconds kafin ya saketa ahankali Yana kallon fuskarta datake bayyanarda galabaituwan datayi da sonsa da kewansa.
Juyawa sukai palon habiba ta Dade da barin palon a rikice Kai aqasa
Haj Maryamah Daman tana daki tana fitowa tun bataga me sukeyiba ganinsu a jone yasata juyawa qafafunta na rawa tareda mamakin dawowar tasa.
Umman Cameroon kuwa qyam tayi a palon zaune abunta tareda qurawa tv Ido batareda tana fahimtar komaiba sbd duk ta rikice da wannan diban albarkar dasukai musu a palon.
Hannunta cikin nasa ta riqe cikin farin ciki suka qaraso tana Masa shagwaban ya dawo ba sanarwa.
Duk neman susucesa takeyi daqyar yake kamo nutsuwarsa da kamewarsa Yana gaisawa dasu umma dasuke Masa barka da dawowa Suma cikin kulawa da farin cikin ganinsa Amma duk Amal din tagama susutasa dauriya kawai yakeyi Yana amsa musu suna cigaba da magana.
Hararar duniya umman Cameroon tayiwa Amal akan ta sakesa karya rude da abinda yake fada Amma Amal ta fuske a gefensa taqi kallon umman Dan Jin takeyi duk ta narke da ganinsa kawai.
Daqyar tabarsa dasu umman ta nufi kitchen sbd girkin dataketa sake koya a gurin habiba sbd Idan ya dawo din.
Sharp sharp Suka hada Masa simple abinci Suka jera da komai ba kunya taje Tai wanka ta shirya cikin doguwar Leyla A casual gown mara nauyi ta fito tana qamshi lokacin ya tafi sallar laasar.
Baki sake su umma Suke kallon ikon Allah harta Gama wayoyinya dasu Mommy ta sanar musu da isowarsa.
##MAMUH#
77
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
77
LAST PAGE
Yana dawowa daga masallaci su umma Suka shige dakunansu sbd kaucewa ganin abinda Bai Kamataba Dan yanda Amal ke narke Masa suna gudun ta sakasa kunya a gabansu,
Dukkaninsu mamakinsa ma sukeyi Dan su ba Haka sukasan AQEEL ASAD dinsuba,
Mutum Mai kunya da kamewa zama cikin zuriar Idon Nera ta fedare musu shi.
Babu kowa a palon daga ita sai shi ta jasa dining ta zaunar dashi sai janyota yakeyi Yana shinshinawa kaman Wanda zai cinyeta.
Kaucewa ta ringa Yi tana zuba Masa abinci Wanda tana Gama zubawa ya janyota kan qafafunsa Yana da shafa cikinta Yana kokarin cusa Kansa cikin wuyanta ta Dan janye tana kama fuskarsa tayi kissing bakinsa tana cewa,
"Girkina ne wannan fa,nice nayi maka.
Murmushi yayi Yana kallon abincin yace,
"Mmmmn really??
Gyada Kai tayi tana murmushi tareda miqewa daga kafafunsa ta fara debowa ta Kai bakinsa.
Itace tayi Masa Bismillah tareda saka Masa cikin Baki.
Jinjin Kai yayi Yana cewa,
"Thank God Matata ta iya abinci.
Qara Masa tayi Yana basa ahankali Yanaci Yana shaqan qamshinta dayayi masifaffen missing.
Lokaci Mai tsayi suka Bata kafin Gama cin abincin Suka dawo palon Suka zauna tana Masa fira da sakalci daban daban tareda mantawa dasu umma na daki makure.
Sai magrib ya fice zuwa sallah.
Bai dawoba sai Bayan ishi lokacin Dole itace tabarsa ya gana dasu mahaifiyarsa.
Abinda Bata taba zaunawa tayi da danta bane sukayi a yau din wato fira cikin kauna da kulawa da sakewa ba kaman baya da iyakacinsu magana cikin girmamawa da da'a kawai Babu sakewa Babu zama free.
Daqyar ya iya barinta a sashen ta kwana bayan sun Gama shiriricewa a palon tana Masa shagwaba da narkewa iri iri duk yabi ya birkice Haka yaso lallabata suje sashensa Amma taqi Dan har cikin ranta zafin kishinta bazai barta ta bisa can bangaren daya gama rayuwar komaima da matarsa.
Ko bayan datazo ta kwanta Hana umman Cameroon bacci tayi da waya dashi akai akai daqyar umman taga safiya tayi ta baro Mata dakin.
Da safe suna kallo ta ringa neman Dama Masa lissafi da sakalcinta har harya fice gidan.
Akwai ayyukan dake jiransa Dan Haka can ya wuce Bai samu zuwa gurin Maminsa ba har yamma ya dawo ya huta tukuna ya fito zuwa sashensu umman.
Bayan sallar magrib sai ga Yan gidansu sunzo gabaki daya yimasa barka da dawowa harda uncle Lulu Wanda duk lokacinda Haj Maryamah zata gaisa dashi saita Jinjina yau itace ahali daya hardasu Dan daudu.,
Ita Siddi dasuka San yanda aka sameta tun suna duba lamarin qarfi da yaji dai Suma sun saje yanxu har mantawa sukeyi da yanda take shiyasa wani lokacin suke mamakin Wanda yake rayuwa free Bayan yasan yanada abin fada to ya yake rayuwar?
Ashe abin daka barwa Allah ka watsar shikenan mantawama kakeyi.
Gashinan yanzu Suma mantawar sukeyi da waye siddi,
Waye Lulu hakama waye Zainab wadda zuwa yanzu sun fara manta zancen sunan karuwancin dasuka santa dashi batareda anfada musu gaskiyartaba sbd AQEEL daya zabi su kaunace yanzu a yanda take sbd Allah ba Dan anfada musu ba abinda suke tinani bane idan sun sani daga baya shikenan dai.
Tayi murnar zuwansu Haka shima yayi farin cikin zuwan Mamin nasa Nan Suka zauna aka gaggaisa A mutunce.
Anty Fareedah da Amal daki Suka shige
Shikuma dasu Mamin da uncle Lulu harma dasu umman akai maganar tarewan Amal din da zatayi jibi.
Anan sukai dinner tareda mutan gidan Kai waye,
Haj Zainab da uncle Lulu da Anty Fareedah harma da Amal kansu a waye yake sosai shiyasa sukeda sakewa Dan Haka a waye ba damuwa Suka sakewarsu musamman uban gayyar shi Daman a sakensa yake indai Amal na kusa dashi.
Haj Maryamah da umma dasuka ga suna komawa kaman Yan kallo
umma Cameroon tasake rutsawa tana nuna Suma a wayen suke tunda sunyi yawon kasashe.
Murmushi kawai Haj Zainab tayi sbd tsakaninta dasu Babu wannan sakewar ta Yan uwan jini saidai girmamawa kawai irin ta sirikai Dan yanzu sabuwa alaqa ce aka kulla Basu dawo data Bayan ba tukuna kila sai gaba kokuma wannan sabuwar alaqar ta auren 'yayansu itace ta kamacesu Kuma itace zata zama sabuwar alaqarsu sbd ta Bayan Allah baiyi itace zata doreba.
Da zasu tafi Dole tareda Amal Suka tattara suka tafi gida sbd daga can ne zata tare gidanta.
Bayan tafiyarsu saiga su umma da kewan Amal da cikinta sbd tanada sanyi da nutsuwar da Basu taba tsammanin samu daga garetaba,
Ko makaranta datake zuwa kullum Ahmed yakaita ya dawo da ita Babu inda take qara zuwa idan ba gidan mommynta ba itama sai jifa jifa sbd AQEEL din da bayason yawo,
Habiba kuwa dasukai sabo fiyeda kowa Jin Tayi ta matsu Amal ta tare takoma gidanta dan tace da ita zata.
Haj Zainab ba qaramin dadin barinsu tafiya da Amal dinba dayayi taji Dan harga Allah tanason takai yarta dakinta da kanta.
Itama Amal tayi farin cikin dawowa gida duk da kwana biyu ne zatayi ta tare din.
Washe gari Haj zainab bata tsaya bata lokaciba tafara shirya yarta duk da babu daman manyan shiri sbd ciki dan haka aka fara yimata na skin da sauransu,
Gidan karatunsa dama key na hannunsu tun wancan lokacin da aka gama gyara aka Zuba sababbin luxury furnitures da komai
Dayake kusan komai shine ya zuba a gidan sai sukuma sukai Kayan kitchen masu shegiyar tsada da aji da sauran abubuwan da baa rasaba.
Siddi ma dole tadawo sbd kar ayi hiduman yar uwarta batanan,
Tunda tadawo gida tayi busy mommynta ta hanata ko saukowa shima yayi busy sosai sbd ayyukansa daya Bari hakama akwai wata tafiyar gabansa amma tareda matarsa zaije dan Haka saiya bawa su Mamin daman yanda takeso baijeba bare hankalin Maminsa ya tashi da ganinsa Dan ya lura yanzu idan yaje gidan ta dinga rarraba ido kenan Dan kada yayi wani Abu gidan da Amal tunda ba sanin inda Suka Saba kebewa suka samu ciki ba tayi.
Cikin kwana biyun Idon Nera Suka Gama shirye shiryensu na komai tareda hada family walima iya su kawai sai familyn AQEEL din.
A Nan gidan suka hada liyafar Dan Haka Dole su Haj Maryamah sune Suka taho gidan tareda AQEEL iya su hudu kawai sai Al-Amin na biyar.
Suma Idon NERA's basuda yawa Amma soyayya da kaunar dasuke wa junansa yasa Haj Maryamah zubarda hawaye lokacinda Uncle Lulu yayiwa Amal fadan aure tareda fara zayyano asalin tarihinsu komai ya fadawa su Haj Maryamah sbd fatan su kaunaci Amal da abinda zata Haifa musu da zuciya daya sbd basuda illa ko laifi.
Haj Maryamah da umma har mufeeda hawaye sukeyi sbd jin kaf Yan idon Nera din Bayan Amal datake Yar Zainab data haifa da kanta kaf dinsu basuda alaqan jini da juna Amma tsananin son dasukewa juna Babu Wanda zaice su din ba jini bane,Kuma ahakan Allah ya albarkacesu duk bakin mutane da fatan mutane Bai tarwatsasuba.
Basu sake Shiga kunyar kansuba saida siddi ta sako hawaye masu zafi daga idanuwanta tana rungume mommynta tareda fashewa da kuka Jin asalin ba mommy ce ta haifeta Amma Kuma ciwo da radadin dayayi breaking zuciyarta bekai Jin nutsuwa da qarfin zuciyar samun Haj Zainab amatsayin gurbin mahaifiyarta Dan Haka addua zata ringawa mahaifiyarta data haifeta daga yanzu har ta mutu Amma Kuma har tabar duniya mommynta itace mommynta batada tamkarta hakama familynta bakuma zata saka kanta tunani ko wata damuwar ba uwarta daya da Amal ba hakama Uncle dinta.
Qarfin zuciyarta da imaninta akan lamarin hattada AQEEL Saida ya jinjinwa hankalinta sbd kuka ko wani daga hankali Babu abinda zai sauya koya dawo dashi,
Duniya a 'yar Zainab Idon Nera ta Santa Dan Haka ko yanzu ahakan take Kuma harsu mutu a hakan sunke.
Mufeeda dataji wadda tafiya rashin asali mai kyau ta rungumi qaddararta batareda damuwaba ko sakawa Kai abinda bazaka iya magancewa kankaba sai Allah daya qaddaro maka hakan,duk saitaji jikinta yayi sanyi sbd tunda nata asalin ya fito ta tsangwama kanta ta tsani Amal tana neman illata rayuwarta da kunci da baqin ciki sbd umminta dake sake dorawa akan tsnaar Amal kullum a waya.
Umma dasuka kasa riqe Zainab din Bayan tana matsayin jininsu Kuma Yar halak dasuka shedar da halak ce ya haifeta Amma gata ta rungumi Yar da batada Hadi da ita Kuma ba Yar halak din ba a matsayin tata,
Ta amsa sunan uwa da duk abinda zaa fada akanta ga Siddin gashinan suna rayuwa cikin nutsuwa da kwanciyar hankali batareda damuwa da bakin kowaba sbd sunsan tsakaninsu da ubangijinsu gashi yayanta sunfi tasu Yar tarbiya da 'da'a.
Jiki mace ba qwari Suka Gama liyafar anan sukai sallar magrib da ishai sai dare dukkaninsu suka Kai Amal gidanta Anan ne Haj Maryamah tasake tabbatarda irin girman son da AQEEL yakewa 'yar Zainab take ta qarasa yarda ta karbi qaddararta cewan kaunar dake tsakanin Zainab da AQEEL daga Allah ne,
Kaunar dayakewa Zainab ce ya shafi 'yarta yagama kamuwa da son Amal ta sheda hakan sheda Mai tsanani,
Sannan yanzu ga cikinta Nan shima tun baizo duniyaba aka sheda girman son dayake Masa Dan Haka soyayyar jinin Zainab har abada bazata gogu agunsaba duk Wanda ya dage wahala ce rabonsa,
Tunda dai Babu Wanda ya goge matsayinta na mahaifinsa a zuciyarsa,hakama tata soyayya da kaunar tana gani yanzu data kwantar da hankali tagano girman nata son da matsayin dan Haka Alhamdllh tana godewa Allah.
Al-Amin ya sallama qarshe kafin ya shigo ya rufe koina ya nufi hanyar bedroom dinta ya bude kofar yashiga Yana lumshe idanuwansa sbd qamshinta daya yadu a dakin kaman sunsan susucewan dayake suka fesa harda Turarenta a dakin.
Qarasowa yayi Yana kallonta zaune a sofa da mayafinta akai Amma Babu wani rufe fuska.
Cikinta ya kalla Yana godewa Allah daya samu cikin Nan tintini da yanzu a Daren yau dinne zai samesa kila.
Zaman yayi kusa da ita ta juyo tana kallonsa cikin Yar shagwaba zatayi magana ya kamo bakinta yayi Masa wata irin tsotsa tsawon mintina kafin ya saketa ya sauke Ajiyar zuciya Yana godewa Allah.
Janta yayi Suka sake nafilar godewa Allah kafin ya janyota jikinsa Yana shinshinawa idanuwansa dasuka fara sauyawa a rufe Yana Jin yau gabaki daya tagama rabasa da nutsuwar da Kansa gabaki daya.
Yau wasa da Romance din masu ciki sukayi sbd zaunar da ita yayi yaringa binta da wasu irin kisses a koina Yana lashewa.
Rabata da numfashinta yakusa Yi da wasanninsa tana biye Masa da nata abubuwan dake gigitasa kafin ya dauketa suka qarasa tsakiyar gadonsa suna shaaninsu.
Washe gari a shagwabe ta tashi ta wuni tana narke Masa da shagwaba sbd galabaitar datayi a hannunsa,
Abincin safe Dana Rana Dana dare Haka aka kawo daga gida umman da gidan mommy.
Bata kowane aiki bayan gyaran dakinsa sbd gatan da ake Nuna Mata
Nata dakin ba habiba ce takeyi sbd ankawo Mata ita.
Basufi sati uku da tarewar ba ya bawa Al-Amin auren Mufeeda wadda gabaki daya ta sauya rayuwarta takoma kaman wadda baqin ciki zai kashe tarasa walwala da farin ciki gabaki daya sbd Bilkees daketa binta a waya tana cusa Mata banzayen halayenta,
Fahimtar hakan yasa ya yanke hukuncin bada ita ga Al-Amin tareda bada Dama aka daura auren cikin dan lokaci ya siya musu babban gida Mai kyau ya zuba musu komai tareda bawa Al-Amin Amanar Yar tasa.
Anyi hidima sosai a auren anyi Mata aure na 'yayan gata masu gata sosai
Kuma Bilkees tazo saidai da kanta ta silale ta koma inda ta fito batareda an gantaba ganin lamarin yafi qarfinta batada guri.
Bayan auren da sati biyu suka tafiya zuwa UAE itada AQEEL dinta
Shima Al-Amin da auren ya samesa daga sama daukan mufeedan yayi sukai tafiya dan su samu fuskantar juna da kyau kafin su dawo.
Tunda sukayi tafiya AQEEL ASAD ya tattara kamun Kansa ya watsar shida matarsa Suka ringa zuba rayuwar soyayya da Jin Dadi.
Watansu daya Suka dawo
Suna dawowa ko sati biyu batayiba cikinta ya Shiga wata Tara
Before EDD dinta ta haihu sbd barnar da cikin Kesha agurin iyayensa.
Lokacinda aka miqowa AQEEL ASAD 'yaya biyu duka maza lokaci daya Amal dinsa ta Haifa Masa wani irin numfashi ma sanyi ya sauke tareda ajiyar zuciya ya lumshe idanuwansa yana miqa dukkanin godiyarsa ga Allah.
Haj Maryamah data karbi yayan hawaye tafara tsiyayowa Dan ba qaramar kuruwa tayiba da rabon 'yayan Nan ya kasheta itada ummanta.
ASADULLAH AQEEL ASAD da UMAR AQEEL ASAD aka sakawa yaran Wanda suke Kira da Ayan da Adeel.
Mommy Kam duk abin AQEEL karbe Amal din tayi sbd tasan ba yarda zaiyiba idan tayi Sanya.
A gidan umma ta zauna sai baya suna yabari Mamin ta karbesu Suka tafi gidanta.
A gidan mommy kulawa suke samu tako Ina,
Shi kansa indai Yana gari kusan kullum Yana gidan daqyar sukai 60 days Suka koma.
Da zata koma Dole da Bilkisu aka hada Mata ta hada da Bilkisun da habiba sbd rigimace da yaran sosai.
Su Ayan basufi 9month ba tafara service dinta Dan Haka take Dan Shan wahala sosai,
Tana gap da gamawa tasamu wani cikin murnar zata yayesu Ayan din yasa batama shiga damuwar samun wani cikin da wuri ba Dan Haka aka tattarasu aka maida gida umma sbd mommy Bata zama sosai tana zuwa office saidai duk da hakan tana biyawa kusan duk bayan kwana biyu ta dubo jikokinta.
Samun cikinta na biyu yasa mommy tasake dagewa gurin yawon kasashe da Siddi sbd tanason siddinta ta haihu itama.
Amal na Gama service Suka tattara da Mijinta sukai tafiya wani aikin da zashi Greece.
Bayan tafiyarsu cikin ikon Allah siddi tasamu ciki
Murna a Idon NERA's baa magana Dan Haka Dole mommy taje Abuja tayi zaman jinyar siddin sbd tanajin jiki sosai.
Qarshe gida mommy tadawo da ita anan suka ringa lallaba cikin Anata fama harya fara tsufa.
Amal acan ta haihu tasake samun Yan uku biyu Mata sai mace daya,
Kusan zarewa AQEEL ASAD yayi a wannan haihuwar Tata Dan hakama yace bazasu dawoba sai yaran sun qwari.
Mommy da uncle Lulu da Anty Fareedah harma da Siddi cikin Dace Suka samu visa ba Bata time sosai Dan Haka Suka taho Dan bazasu iya jiran harsai sun dawoba.
Suna can su umma suka iso itada mufeeda da Al-Amin dasu Ayan da Adeel Banda umman Cameroon datace bazata iya Doguwar tafiya ba qafafu na Dan damunta kwanakin.
Wannan karon Ummu rumanah da Ummu sulaim ya saka sai Muhammad Ashraf.
Dasu mommy zasu dawo gabaki dayansu umma ta basa umarni suka dawo da yaran.
Suna dawowa wannan karon gidanta ta zauna bataje wankaba koina tinda ma haihuwar ta kwana biyu.
Sabuwar babin rayuwar so da kauna juna ahalin guda biyu suka bude cikeda mutunta juna da sanin haqqin juna,
Siddi ta haihu itama namiji ta Haifa mahaifinsa ya saka Masa Abubakar siddeq.
Data Gama wanka zata koma harda Amal aka rakata da mommy sai Anty Fareedah,
Yaranma bataje dasuba a gurin umma aka kaisu su Rumanah kawai taje dasu da Bilkisu me tayata hidimarsu.
Daga wannan haihuwar tsayar da haihuwa tayi kwata kwata Dan batajin zata qara
Koda yayi fadan a qara din ba kusa zata qaraba gaskia.
##MAMUH#
ALHAMDLLH
ANAN NAZO KARSHEN LABARIN IDON NERA INSHA ALLAH.
INA FATAN ALLAH YA YAFE MANA KURA KUREN CIKI GABAKI DAYANMU.
ABINDA NA MANTA BAN SAKABA A DAUKESA AMATSAYIN MANTUWA KO AJIZANCI NA DAN ADAM AMUN UZURI.
DAN ALLAH KAR KUCE YAYI KADAN KO YA YANKE SBD BANSAN YA ZAN JASABA KUMA,
HAKAN SHINE IYAKARSA GAKUMA AZUMI YA KARATO DAN HAKA AYI HAKURI IDAN BAIYIBA,ALLAH YA HADAMU A LITTAFI NA GABA AMIN YA ALLAH.
THANK YOU πππ
NAGODE SOSAI ALLAH YABAR TAREππ―π―