Showing 138001 words to 141000 words out of 149977 words

Chapter 47 - IDON NERA BY MAMUHGEE CMPLT.txt

25 Nov 2024

6535

shiga duk ya shigesu musamman mommy da ahalin Idon Nera din dukkaninsu ita kanta Haj Maryamah da umma tashin hankali suka shiga


Yau kowa yasan da cikin Kuma ace yau idin zai bare,Babu Wanda zaiso hakan,.shi Mai cikin ko maganarsa baayi Dan Haka Bai tsaya jiran kowaba ya dauketa Kai tsaye Yan nufi mota da ita tun kafin yaqaraso Al-Amin ya bude Masa yashige da ita a jikinsa


Wani mugun ribas Al-Amin yayi dashi ya fita gate din gidan kafin ya juya yahau titi da mugun gudu suka nufi asibiti.


Uncle Lulu da Ransa yagama mummunan baci fiyeda yanda ake tunani Kai tsaye Yan SARS yakirawa Bilkees da 'yarta tsabar baqin ciki da takaici.


Ita kanta Haj Zainab Bata damu da matakin da uncle Lulu din yadaukaba kafin suyi wani motsi saiga ya Media din data Kira sun iso kofar gidan tareda shigowa harabar datake bude sbd masifar data afku.


Daga ita har mufeeda sun Dan bugu Amma bawani ciwo sukaji ba fitowa mota sukayi tana bude Idon inda zataga Amal Dan batasan AQEEL yazo ya dauketaba Dan Saida kanta ya dawo daidai daga buguwar da yayi Suka iya fitowa motar.


SARS office na kusan kusa da Anguwarsu Dan Haka kafin kace me Suma sun iso ba wata wata suka cafketa Yan media kuwa abin yaqara musu armashi take guri yacika aka wuce da ita abin baqin ciki su haj Maryamah na kallo rayuwar dansu da Mai mutunci da qima da girma a idanuwan mutane tazama abar daukan media da Allah wadai sbd rashin matar albarka.


Asibiti Haj Zainab dasu Siddi da hankalinsu ya tashi Akan Amal Suka nufa itama Haj Maryamah asibitin Suka nufa itada umma a motar da umma tazo da ita


Har lokacin umma Bata Gama dawowa hannyacintaba daidai Bayan ajiyar zuciya akai akai Babu abinda takeyi sbd ta girgiza ta firgita matuqar gaske,


Duk haukar dasuke Kiran Bilkees da ita Bata dauka Dagaske dai batada hankalinba sai ayau data kusa hadata da malaikun azaba Dan kuwa kafin ta hadu da malaikun rahama ta tabbatarda azabar markadar da motar zatayi Mata ita zata fara Sha kafin ranta ya fice.


Kalma daya takasa fitowa daga bakinta sbd Bata Gama fitowa daga shock ba,


Sai yau sukasan asalin yanda shock yake ba irin Wanda Suka Saba shigaba na bacin Rai Ashe.


Ita kanta Haj Maryamah yau ta dandani asalin shock in gaske data hangi mahaifiyarta zaa niqata da mota da tsufanta Bilkees taso gana Mata azabar da ko a labari ba Dadi.


Koda suka Isa asibiti Kai tsaye har Amal na labour room su Dr tayo na kanta Ana dubata Dan cikin Kam ya zuba.


Har Suka zo Suka tsaya taredashi a office din Dr tayo suka zazzauna jigum jigum Babu Wanda ya iya cewa komai sai Satan kallonsa sukeyi sbd yanda gabaki daya Babu Wani rahama ko fuskar da wani zai iya magana a gurin sai kallon kallo kawa sukeyi gasu aguri daya yau din Amma Babu damar fada da juna Dan yau duk Wanda yai fadama kila AQEEL yafesa zaiyi tunda sunkoma kaman sune 'yayan shine uban sbd rashin tinaninsu.


Dr tayo Allah yabasu nasarar Hana cikin zubewa Ya tsaya saidai zuban dayayi kawai Dan Haka Dr tayo tace Gaskia zata riqeta a asibiti sai tasamu qarfi sosai Dan ta fahimci akwai rigimar da akeyi a gidan.


Jin ansamu daga Amal din har cikin suna lfy yasa Suka samu damar fitowa kurmanci wucin gadin dasuka shiga Amma still dai Babu Wanda ya iya yiwa AQEEL magana sbd shima dai baicewa kowa komaiba.


Uncle Lulu da aketa kira sbd zancen kamun Bilkees din daya fara fita sunan AQEEL na neman baci aciki yasa yaje da Kansa SARS aka saketa ta hau motan haya ta nufi gida da yarta datasha kuka har idanuwanta basa gani,


Suna zaman zamansu ta rasa meya jawo musu wannan wagararriyar rayuwarba.


Tsoronta abinda daddynta zai musu idan yaji wannan abin da umminta takusa aikatawa.


Gashi kusan kila kowa yaji abinda sukayi tunda a Media din dasuka Kira sun hada hardasu sun dauki rahoton sun hada da Wanda Suka Basu.


Suna Isa gida ba kowa har lokacin su umma suna asibiti tareda AQEEL dayake cikin wani irin Hali na qunci da bacin Rai tareda baqin cikin rayuwar dake gudana a familynsa,


Kobai fadaba dukkaninsu sunga halinda yake ciki Kuma sun tabbatarda Yana cikin qunci Mai tsanani,


Bayan daidaituwar Amal shi kansa saida Dr tayo Suka dubasa tareda Dr Abdulsamad salees yayan Dr Inayah A majeed sbd kirjinsa dake ciwo Wanda alamu ne dake nuni da gap yake da kamuwa da ciwon zuciya koma zuciyar ta buga kowama ya huta sai suci kansu.


Haj Maryamah da umma da Zainab dasuka ji wannan mummunan labarin hankalinsu tashi yayi


Umman Cameroon datafi kowa saurin kuka fasa kuka tayi tana tsinewa zuriarda Bilkees ta fito tana tsinewa aurenta dabai qaresu da komaiba bayan haihuwa daya.


Haj Maryamah ma kuwa kasa cewa komai tayi Dan tunanin Mijinta ne yadawo Mata matuqar wani Abu yasamu AQEEL ya bar Mata duniyar to me zata zauna tayi.,


Ita rayuwarta a qunci ta taso a qunci tayi rayuwa gashi haryanxu a qunci take takasa samun farin cikin rayuwa sbd balai da masifar abinda yake zuciyoyinsu.


Haj Zainab ma sanyi jikinta yayi da 'yayan nata suke cikin wannan masifun daga wannan sai wannan gashi yazo ya Hadu da mahaukaciyar Mata ya aura zata kashesu taja Masa masifa sukuma ta kashesu lokacinsu Bai qarasa yiba,


Son zuciyarsu umma yakaisu ga kwaso Masa masifa gashinan masifar harsu tana neman gagararsu.


Sai dare suka tattara suka koma gidajensu gabaki dayansu aka bar Anty mommyn a asibiti tareda Siddi sune zasu kwana da Amal.


Shi kansa shawara likitoci suka basa na ya kwana anan asibiti taredasu su samu su qara duba yanayinsa Dan Allah ne kawai ya tsaresa ya Hana zuciyarsa bugawa a yau din.


Umma dasuka Isa gida taji su Bilkees din sun dawo suna gida Jin tayi kaman hankalinta zai tashi sbd yanzu Bata yarda da Bilkees ba


Tanada tabbacin zata iya Cinna musu wuta da daddare a wayi gari sun gama soyewa tas dan Haka fir taqi yadda su kwana gidan Acikin Daren Suka koma gidan karatunsa acan umma tasamu nutsuwa dayake dame aikinsu sukaje Dole a Daren tayi musu abincin Basu wani ci ba sbd Haj Maryamah datakejin wani nauyi a zuciyarta gameda halinda akace 'danta na ciki.


Haka Suka kwana cikin damuwa da sanyin jiki.


Itama Haj Zainab a asibitin damuwar take ciki wadda tasata Tina lokacinda AQEEL din Yana qaraminsa yanda take tarairayarsa idan baida lafiya kaman itace ta dauki cikinsa ta haifesa.,


Idan har sbd damuwarsu da quncin halinda suke sakasa ne sbd qiyayyarsu da juna yake neman Shiga wani mugun halin ita ta zubarda nata makaman yaqin,


Zata dauke Ido daga duk abinda su Haj Maryamah da umma zasu Mata idan har ba cutatar Mata da 'ya zasuyiba zata dauke kai tunda Daman bazasu zauna su tsufaba suna Abu daya Dole wani zai saki Dan Haka ita tasaki


Suda suka Saba wahalar suyita yi har ranarda suma Suka gaji Suka aje.


Ita kanta bilkees a zaune ta kwana cikin tinani da tashin hankali da baqin ciki tareda qunci kala kala,


Batasan meya shiga kanta aikata abinda ta aikata dinba Amma Kuma duk da hakan Bata datasanin abinda tayi tasoma ace tahau kanta da motar cikin ya zube anyi duk abinda zaayi shikenan.


Baqin ciki da takaicin mufeeda data hanata yasa tunda Suka dawo ko kallon mufeedan batayiba gashi tabi ta isheta da kukan abinda daddynta zaiyi idan yaji abinda sukayi din.


Koda gari ya waye babban abinda suka tashi dashi shine yaduwar AQEEL yasha nono daya da matarda take daukeda cikinda ake tinanin nasa ne Koba nasa bane.


A lokacinda AQEEL yasamu labarin rufe idanuwansa yayi ahankali tareda fara karanto adduoain sanyaya zuciya daga fushinda zai iya Kai mutum ga aikata babbar barna.


Shi kansa Al-Amin dayayita fama da ya media akan dakatarda yaduwar labarin koina Kansa ya masifan daukan zafi tareda Allah wadai da Mata irin Bilkees sbd Babu Bata lokaci bare wahalarda Kai Suka gano Bilkees ce da aikin.


Familyn Idon Nera basuyi wani mamaki ba sbd zuwa wannan lokacin sun San komai familyn AQEEL ASAD zasu iya aikatawa dan Haka wannan ma qaramin aikinsu ne,


Kawai dai abinda ya Sosa ransu shine alaqarda cikin Amal dinsu yakedashi a labarin Wanda zai iya saka a sheganta Mata baby Dan Haka uncle Lulu ya tashi tsaye shima ya soke labarin tako Ina shida Al-Amin harma dasu Barr Salahudeen Dan AQEEL Saida akai da gaske kirjinsa ya Dena radadin ciwo.


Wunin ranar Haka duka families din biyu suka yisa cikin damuwa da bacin Rai Kuma har wannan lokacin Babu Wanda yasaka Bilkees ko yarta a Ido.


Su kansu su umma a asibitin Suka wuni cikin baqin ciki da jimamin wannan sabon kuma abin daya Kuma bullowa


Bilkees Tasha tsinuwa da munanan alkabai daga bakin umma.


Amal ma tunda ta warware tasamu sauki takeson ganin Mijinta Amma ba Dama sbd su mommynta dake dawainiya da ita da tarairayarta kaman ba itace ake fushi da itaba a jiyan.


Sai yamma aka sallameta shima sai alokacin sukaga juna daya shigo dakin ya fita da ita da Kansa a motarsa ya dauketa su mommy Kuma a motan uncle Lulu


Su umma ma a tasu motar.


Hanyar gidan karatunsa Al-Amin ya nufa dasu ta juyo da fuskarta ahankali ta kallesa shima ita ya kalla din tareda riqo hannunta yakai bakinsa yayi kissing ahankali batareda ya iya cewa komaiba itama Kuma Batai Masa maganarba sbd lura da tsananin bacin ran dayake qasan Ransa kwance bayason magana sai kawai ta lafe jikinsa Yana zagayeta da hannayensa.


Mommy na ganin inda ya dosa ta sauke numfashi Mai nauyi sbd tasan dama zaa rina bazai Bari Amal din Takoma gidaba.


Rakasu sukai har gidan Dan Haka motocinsu uku a gidan suka shiga gabaki daya ko Gama fitowa mota basuyiba saiga motar gidansa daya tasake shigowa gidan suna ganin Bilkees aciki mommy dasu Siddi Suka nufi Amal Suka tsaya Mata Dan kuwa yau tayi gangancin taba Amal dukan mutuwa zasuyi Mata sai Mijin nata yasaka ganeta.


Amal data kallesa shima ita ya kalla tareda lumshe Mata Ido alaman ko da wasa kada ta daga hankalinta bare wani Abu ya Samu ita ko babynta.


Ganinsu gabaki daya a gidan yasa hankalin Bilkees tashi Dan Bata dauka zata samesu a gidan ba gurinsu umma tazo taji qiyayyar dasuke Mata Meye dalili.


Umma na ganinta ta tareta tareda nesantata da inda take nufa gurin AQEEL dasu Amal tace,


"Ke tsaya,


Yo daga Nan ki tsaya kiji sakamakonki Dan idan natina AQEEL yafada Miki ranarda zancen maganar Shan nono ta fita daga gurinki a iyakar Aurenki.


##MAMUH#


*_ZAFAFA BIYAR_*


*RUMBUN K'AYA*🔥


Hafsat Rano


*DAUDAR GORA*🔥


Billyn Abdul


*IDON NERA*🔥


Mamuhgee


*A RUBUCE TAKE*🔥


Safiya huguma


*KI KULANI*🔥


Miss xoxo


Littafi daya---400


Biyu---600


Uku----800


Hudu-----1k


Biyar din duka----1200


ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN


0022419171


Maryam sani


Access bank


Shedarka ta 09033181070


MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN


09166221261


🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪


*Ina yan uwa 'yan nijer?*


*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*


+22799643131


Littafi daya---450CFA


biyu---650CFA


uku----850CFA


hudu----1050 CFA


Biyar----1250CFA


*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*


*Thanks for choosing us*🔥


73


*_Arewabooks@Mamuhgee_*


73


Wani numfashi Bilkees din ta sauke Mai zafi tanajin kaman ta shaqe umman Cameroon ta sumar da ita Dan neman haukatata takeyi,


Duk balai da masifar data sameta a bakin umman Cameroon take fara jinta.


AQEEL ta kalla zatayi magana ya juya ya kalli Maminsa ahankali cikin nutsuwa yace,


"Mami kije gida da ita zanzo na dauketa daga baya Amma abar Nan da ita yanzu.


Daman Haka su mommyn keso Dan Haka Suka fara kokarin barin gurin da Amal Dan su basa buqatan kallon tashin hankalin da zaayi a gidan.


Da Babu saduda ko nadama a tareda Bilkees din.


Kallon Umma yayi da dukansu abinda zai fada suke jira Dan baya buqatan dogon hayaniya tunda kowa yayi son Ransa ya gama.


Bilkees ya maida idanuwansa akanta Kai tsaye ya furta Mata kalman saki tareda kallon Al-Amin dayake gefe yayi shiru shima Dan yasan shirun maigidansa ba kyau.


"Kasiya Mata ticket yau.....


Kallonsa Bilkees keyi idanuwanta na sauyawa jajira muryarta na wata irin rawa kanta na daukan hayaqin kalman sakin daya furta Mata gabaki daya zafi da tiriti zuciyarta keyi tace,


"Akan cikin da bakada tabbacin nakane zaka sakeni kokuma Akan yanzu kasamu 'dan kanka shine Ni zaka sakeni bayan kaima din ai ba haihuwar kakeyiba Dan Haka wlh cikin Nan ba naka bane.,


Kan Amal dasuke dap da Shigewa mota tayi zata shaqurota Kusan daga shi har Al-Amin dasu Siddi tareta sukai


Ta qwace da qarfi tana cewa,


"Wlh ba cikinsa bane tunda shima bata yarda Yana haihuwaba Kama yanda akace batayi.


Amal tsayawa tayi cak tareda juyowa tana kallon AQEEL da jikinsa ke wata irin rawar bacin Rai da baqin ciki Mai tsanani Amma bazai iya daga hannunsa ya shararawa Bilkees mariba Dan a yanzu kallon Mara lafiya sosai yake Mata.


Kallon Amal yayi kafin ya kalli Mami dasuma duk shock na zancen Bilkees yasa Suka rude yace su wuce kawai.


Mota Suka shiga suka bar harabar gidan sai a lokacin ya kalli Bilkees da mufeeda ta riqeta tana Kiran sunanta da qarfi sbd itama zuwa yanzu ta yarda da kalman dasu umman Cameroon ke fadawa umminta batada lafiyar qwaqwalwa.


Hawaye mufeeda takeyi tana riqe Bilkees din Dan kuwa ta tabbata kan mahaifiyarta ya juye tunda tana fadan maganganun dake Kama da juyewar Kai.


Haj Maryamah mutuwar tsaye tayi Saida umma tajita tsit ta girgiza ta tana Kiran sunanta duk da itama ta shiga shock din Amma Kuma ai Basu fahimci me Bilkees din ke nufiba dan da alama kanta yagama juyewa dai daga qarshe.


Ciki suka dunguma Bilkees ko ganin gabanta batayi tabiyo bayansu mufeeda na rirriqeta tana kukan auren iyayenta daya rabu dana kan mahaifiyarta data yarda da itama ya juye.


Suna shiga Haj Maryamah taja ta tsaya cak tareda kallon AQEEL da dukkanin idanuwanta dasukai jajir Dan kuwa ta Jima itama Bata nuna Masa ikonta na uwar data haifesaba Amma zancen Bilkees ya girgizata fiyeda zato Dan Haka Kai tsaye muryarta da kirjinta na nauyin idan da gaske Bilkees take fadan baya haihuwa Ina ya samu mufeeda Kuma cikin Amal din kenan shima ba nasa bane.


A yanayin muryarta ya fahimci bacin Rai da nauyin zuciyarta tareda girmanta na uwa data fidda Nuna sosai Dan Haka ya rintse idanuwansa ahankali ya bude danshi mufeeda kome ta zama 'yarsace Kuma Bilkees ce ta Bata Masa tarbiyarta da rayuwarta Dan Haka baiso zancen ita ba jininsu bane ya fita dinba Dan zai hadata da duka 'yayan dazai Haifa ya riqesu a matsayi daya duk itama tsaf zata fuskanci hukuncinta Akan haukar uwarta datake dauka.


Bilkees dataga zuciyar Haj Maryamah na bugawa da sauri sama sama tasan zance daya zai buga zuciyarta Dan Haka ta kalleta Kai tsaye tace,


Bana haihuwa baya haihuwa mufeeda ba 'yarmu bace,ba jininmu bace,


Bamu muka haifetaba,Bai taba haihuwaba,baida 'da ko daya a duniya, adopting nata mukayi Dan Haka ko yanzu cikin da ake magana yanzu ba nasa ban....... ahankali taji saukar wani lafiyayyan Marin daya dauke jinta da ganinta atake Dan kuwa dif tayi ta tsaya cak wani qara na amsa kuwa cikin kunnenta da kanta.


Hannunta ya Kama ya fito da ita har cikin mota ya sakata yacewa Al-Amin yakaita gida ta dauki abinda zata dauka yakaita airport kada yabar gidan saiya tabbatarda yakaita airport.


Haj Maryamah ma kuwa da umma kaman yansa Bilkees din taso AQEEL Suka zubawa Idanuwa Babu Mai iya Jan numfashi daidai


Ahankali ya kalli mahaifiyarsa yafada Mata adopting mufeeda sukai da gaske Amma maganar cikin Amal ba nasa bane karma Wanda yafara wannan tinanin.


Heart attack ne ya Kama Haj Maryamah agurin ta yanke jiki ta Fadi umma na ganin yarta ta zube itama Daman zuciyarta takusa bugawa da shock din take itama ta silale qasa.


Mufeeda kuwa kasa motsi tayi a inda take tsaye har aka kwashi su umma akai asibiti dasu Bata motsaba sai daga baya itama ta yanke jiki a gurin ta Fadi saidai mai aikinsu umma tayi kanta tazuba Mata ruwa Dan batada zabin daya wuce hakan.


A asibiti kuwa suna Isa wannan karon ummansa jikin yafi nako yaushe Dan kuwa Kaman sashenta ne yake neman shanyewa Amma dai likitoci nata kokarinsu.


Umman ma Saida ta kwana ta wuni kafin aka samu ta farfado tanaji tana gani wannan karon ko bakin tsinuwar batadashi ya mutu.


Mufeeda na gida tayi kuka tai ihun tayi suman ta farka Amma Babu kowa daga ita sai masu aiki a gida daddynta Yana asibiti taredasu umma idan yadawo gida da daddare samansa yake Shigewa baya buqatan ganin kowa.


Gabaki daya Kansa da zuciyarsa neman bugawa sukeyi shiyasa kosu Maminsa kwana biyun Bai iya zuwa gurinsuba Dan yasan Amal da babyn suna lafiya tunda suna tareda Maminsa hakama Al-Amin ya sauya musu securities masu tsananin gaske da tsaro.


Halinda yake ciki yasa dukkaninsu Yan gidan IDON NERA din Suka shirya Suka ziyarci su Haj Maryamah din a asibiti Kuma sun tausayawa Haj Maryamah sosai ganin yanda take kwance kaman ba wadda Rai yake jikintaba.


Umma ma taji sauko Amma Kam Bata iya ko doguwar magana idan ba ganin tayi 'yarta ta farfado ba.


Amal da aka barta a dakin Haj Maryamah din daga ita sai shi kowa ya fice Amma takasa ficewa tabarsa suna Gama ficewa siddi datayi na qarshe ta rufe musu dakin.


Ahankali ta Isa gurinsa ganin irin kallon dayake Mata idanuwansa sunyi wani irin laushi kaman ba AQEEL ASAD dintaba.


Zama tayi a kusa dashi tareda Kai hannunta kan nasa ta sarke hannuwansu ahankali tace,


"Insha Allah zata samu sauki ta warke.


Kallonta yayi tareda kissing hannunta ya janyota jikinsa ya cusa Kansa cikin wuyanta ya shaqi qamshinta ya sauke Ajiyar zuciya kafin ya sake matseta jikinsa Yana shafa cikinta ahankali yace,


"Nayi missing naku.


Lafewa tayi jikinsa tana cewa,


"We miss you too".


Wani qayataccen murmushi ya sake Yana kissing lips dinta kadan yace,


Kina cin abinci sosai yanzu?


Gyada Masa Kai tayi tana qarawa da cewa Amma ba sosaiba.


Shafa wuyanta yayi Yana cewa,


Meyasa??


Kallonsa tayi tana Dan narkewa tace,


"Bazan iyaba.


Bakinta ya Kama ya tsotsa Yana shinshina qamshinta da yayi masifar kewa yace Takoma gida kafin yayi loosing control na Kansa akanta.


Koda suka fito su mommy sun wuce sun barta da Haka suka komawarsu Suka cigaba da abubuwansu yabita duk ya tsotse sai yamma Suka dawo gida ya kawota da Kansa har palons sama Dan su mommyn na can.


Suna shiga ta zame hannunta a nasa tareda nufar guri ta zauna tana kallon mommy dataqi nuna taga hannunta acikin na AQEEL din.


Ganin ya zauna yasa itada Siddi Suka koma dakinta Siddi na tsokanarta Akan taga rigarta duk ta yamutse.


Banza tayi Mata sbd batajin zata iya biyewa iskancinta.


Fira yayi sosai da Maminsa har dare Yana gidan da zasuyi dinner qiri qiri

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login