Showing 66001 words to 69000 words out of 149977 words

Chapter 23 - IDON NERA BY MAMUHGEE CMPLT.txt

25 Nov 2024

6514

ya kwaso najasarsu,


Bazata taba yarda wannan karon 'danta Mai tsarki tsarkakakke ya kusanci inda sukeba,


Kome zatai zatayi Amma wlh Zainab bazata dawo rayuwar 'dantaba itada 'yarta,
Wannan karon kome na dukiyarta zata watsar akan 'danta ya tsaya gurinta bazai sake kallon zainab bama bare wata 'yarta wadda itama take baqin cikin fadar sunanta da aka sakawa 'yar gashinan ta qare a rayuwa irinta uwarta,


Sake kallon AQEEL din tayi idanuwanta da zuciyarta na sake daukan zafi da ciwo,


A natse cikin kamewa yagama tabbatarda Babu wata matsala zasu iya tafiya da umman gida.


Bilkees data gap da faduwa sbd tiririn da zuciyarta take ciki itada mufeeda,


Bata tafi gidaba itama saida aka duba bp dinta daya kusan haura 200 daqyar akai Mata controlling dinsa tayo gida a gigice saidai cikin rashin saa tana isowa akace AQEEL din yabi jirgin dare ya wuce Abuja.


Cikin tashin hankali ta kalli umma wadda itace ta matsa Masa akan ya tafi din taji sauki sbd tanada buqatan barinsa a garin na kwana biyu Dan tabbatarda abinda tasani,


Zainab tazama masifar rayuwarsu itada ummanta da 'danta,


Tayaya zata fuskanci wannan tashin hankalin dayake dawowa musu???


Bilkees data kasa gane kan umman ta qaraso gabanta hankali baa kwanceba tana jiran Jin ta bakin umman tukuna tasan ta inda zata fara da lamarin.


"Idon Nera" duk sunan ya fado a ransu sai anrasa tsakanin zuciyar haj Maryamah data Balkees wacce tafi girgiza dashiga mummunan yanayi,


Tashin hankali da rikicewar Balkees a zahirin bayyane yake ga duk Wanda ya ganta yasan tayi kololuwar fita hayyaci da tsananin kishi da tashin hankali akan lamarin tun lokacinda idonta ya kyallo jaridar,


Ga AQEEL ASAD din yaqi tanka kalma ko daya akan lamarin bare a bude zancen komai Susan matsayarsa saima kaman harda bayason zancen yasashi tafiya a Daren,


Idan AQEEL ASAD baiyi niyar magana akan abu ba Sam ko fuskar a tayarda zancen baya bayarwa Amma wannan ma yafi kowanne yanayin qin bada damar saima wata irin tsananin rashin bada Dama ko fuskar da zatai tashin hankali da aibata Idon nera,


Haj Maryamah kuwa sake juya zancen takeyi a ce Zainab idon Nera, qanwar mahaifiyarsa wadda itace yakewa kallon uwa sbd itace tasan wahala da dawainiya dashi tun Yana cikin mahaifiyarsa take dawainiya da wahala dasu harya fito duniya ta renesa tamkar itace ta haifesa haryayi girman dasuka rabu,


Itace macen da a duniyarsa mahaifiyarsa data haifesace kawai tafita haqqi akansa Amma shaquwa da kaunar zahirima tafi girma a tsakaninsa da ita,
ta sadaukar da rayuwarta da kuruciyarta gabaki daya gurin kulawa dashi,


babban abin firgicin shine 'yarta daya a duniya itace wadda yakejin kamar yayi failing malaminsa akan rashinta,


Ko a cikin mafarki ne kunya,baqin ciki, takaici da qyamar fadan tasan Zainab ma zatayi bare a zahiri,


Duka wannan bayanin idan duniya taji mutuncin AQEEL dintane zai zube,
Tayaya zata Bari asan alaqarsa da Zainab Idon Nera,
Bazata yardaba.


Kwanan baqin ciki da zullumin tunani sukai aranar wadda sukaga safiya daqyar.




****
Haj Maryam kusan tafi Balkees shiga qunci da damuwa tareda baqin cikin bayyanuwar wannan Al'amarin sbd kaman 'dacin zuciyarta tun na quruciya ne yake Shirin dawowa idan bata datse wannan alqar tasuba da wuri,


Idanma 'yar Zainab dince IDON NERA duk baqin cikin daya ne sbd girman Zainab a zuciyan aqeel ganin takeyi ya wuce nata itada ta haifesa saidai batajin har abada zata iya karban Zainab da itace qurjin zuciyarta,


Aqeel tsarkakakke ne itakuma yanzu najaza ce abar qyama daga ita har 'yarta....
Babu ya yanda AQEEL zai iya ko kallon Zainab din bare dawo da matsayinta na uwa a zuciyarsa matuqar itace IDON NERA din
Koda 'yarta ce IDON NERA AQEEL saiya qyamacesu..


Qarin abin kunya da baqin cikin da zubewar mutunci da darajarsu zai fara ne daga lokacinda duniya tasan ita din yayar Idon nera dince,
Jininsu daya,
Mutum daya ya haifesu..


Haka zalika girman MUHAMMAD AQEEL ASADULLAH a duniya zai rangwanta a idon mutane idan sukaji Karuwar da kowa yasani IDON NERA qanwar mahaifiyarsa ce,
Jininsa ce,
Marikiqiyarsa ce wadda yake Kira da uwa.


Babban tashin hankali da tsoronta yace zaiyi yunqurin dawo da Zainab rayuwarsu wadda AMAL IDON NERA itakuma itace babbar tashin hankali da masifar datake girgiza bilkees da duniyarta gabaki daya sbd daga lokacinda tasamu damar ganin hotunan IDON NERAs din a Media kiris ya hanata samun shanyewar rabin jiki badan mufeeda tayi gaggawar taimaka mataba.




Abinda ya sumar da Balkees shine bayan gama qarewa hotunan haj IDON NERA kallo shine Ido biyu da hoton AMAL Idon Nera wadda duniya ta shedar da mutuwar so datakewa mahaifiyarta haj Zainab Idon Nera.


Ganin Amal yasa bilkees daga kwanciyar hankalin gidan gabaki daya akan lamarin sbd son sanin asalin meke faruwa...


Haka zalika batajin ko gida jaridar daya wallafa wannan jaridar zata qyalesu mataki zata dauka tako Ina sbd ko wannan qazamtaccen zancen Adena yadawa bare wani abin ya biyo baya,


Dan Koda zata rasa komai da kowa a duniyarta bazata taba yarda asake hada sunan tsarkakken sunan mijintaba da sunan IDON NERA Koda uwar Koda 'yar.
##MAMUH#


ZAFAFA BIYAR 2023


*RUMBUN K'AYA*πŸ”₯


*DAUDAR GORA*πŸ”₯


*IDON NERA*πŸ”₯


*A RUBUCE TAKE*πŸ”₯


*KI KULANI*πŸ”₯


*_uhmmmm_*😊😊😊😊😊😊😊😊😊😊


*Nasan zakuce ya da murmushi haka?*


*Wanda bai shigo ba bazai gane ba*


*Sai kin shigo daga ciki zaki gane me nake nufi*☺️☺️


*KE DAGA JIN SUNAYEN LITATTAFAN MA KADAI KASAN CEWA AKWAI WANI BABBAN ABU MAI MATUQAR JAN HAKALI TATTARE DASU*


*KINA NEMAN INDA ZAKI HUTAR DA KWANYARKI?*


*KI SAMU ZUNZURUTUN NISHADI DA ILIMI?*


Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200


*ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN KI ANTAYA JIRGIN FITON ZAFAFA BIYAR*πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯


0022419171
Maryam sani
Access bank


*MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN*


09166221261


πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*


+22799643131


Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA


*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*SIYAN NA GARI KUMA MAIDA KUDI GIDA!*
*_Arewabooke@Mamuhgee_*
34
Wayar umma Haj Maryamah ta Kira
Saida takusa katsewa umman ta dauka,


Wani irin kukan da Bata taba fashewa dashiba ta fashewa umman dashi zuciyarta na tafarfasar da kunci da bacin Rai harma da baqin ciki.,


Zaune umma ta tashi daga kwacen datake akan doguwar kujerar dakinta ta hutawa hankalinta na tashi Dan Bata taba jin kukan Maryamah dinta ba tun bayan rasuwar Mijinta na farko,
Ko mijita na biyun daya rasu batai wani kukaba saidai hawaye Amma yau din lamari ya girmama,


Maryamah??
Lafiya?
Waye ya rasu?
Ina AQEEL lafiyansa kalau kuwa?
Ya matarsa da 'yarsa Suma lfy dai??
Meyene ya faru gayamun kafin hawan jinina yayi sama.


Kasa magana Haj Maryamah tayi sabd takasa riqe kukanta akan Zainab datake riqewa shekaru,
Yau tasamu abinda yake makoshinta akanta ya fashe shiyasa kukan yakasa tsayuwa.


Kukane takeyi dayake fitowa can qasan zuciyarta da ranta,


Umma daga zaunen qarasa miqewa tsaye tayi tana sake ambatar sunan maryamah din hankalinta na tashi.


Saida tasamu ta danne zuciyarta ta cusawa kanta dauriya da taurin Rai kafin ta share hawatenta da tissue ta sauke ajiyar zuciya ahankali tukuna ta bude baki tareda Dan gyara muryanta datayi nauyi takoma daidai
ranta na quna tace,


"Umma Zainab tadawo rayuwar AQEEL,
AQEEL yaga Zainab da 'yarta,
Zasu Bata suna da mutuncinsa a Idon duniya,
Zainab magajiyan k.....umma Ni bama Zan iya fadan qazantaccen sunan da bakina Mai tsafta ba..


Umma AQEEL zai koma gurinta ya sake juyamun baya,


Me nayiwa Zainab data zabi shiga tsakaninsa da rabani da 'dana daya danake dashi a duniya??


Umma wannan karon wlh bazan iya daukaba......


Zama umma tayi a hankali tana shiga nata mamaki da tashin hankalin itama sbd abune da Bata taba kawo tunanin shine zaa fada ba wato dawowar Zainab rayuwarsu,


Tun tana qaramar karuwarta sun samu sun yakiceta sun rabu da ita rayuwarsu ta huta sai yanzu zata dawo rayuwar 'dansu tana shahararriyar karuwa,
Me take nufi da hakan?


Rayuwar ta bare Mata ne kokuwa?


Cin mutuncinsu da barnar suna zatai musu kome?


Baqin ciki da damuwa zata dawo musu dashi bayan sun samu nutsuwa da salama tareda dangana ya shiga AQEEL ASAD baya rashinta shine yanzu tunda ya zama babban mutum Mai fada aji zata bullo Dan tozartasu da kawo musu sabuwar masifa...


Wani 'daci ta hadiye a makoshinta bayan Haj Maryamah ta zayyana Mata komai na bayyanar Zainab harma da yarta..


IDON NERA??" itama ta mamaita sunan a bakinta tana Jin ranta na tsananta soyuwa da bacin Rai da tashin hankali...


Tashin hankali dasuke gujewa na tsayuwar AQEEL akan zance daya ne idan ya tsaya ya tsaya kenan baya magana biyu,


Idan har yace ya yarda da zainab da rayuwar karuwancinta Babu me sauya Masa hakan,


Kafin ya yarda da hakan sukuma bazasu taba yarda tadawo rayuwar tasaba tinda ba ita Maryamah ta haifawa 'dan ba..


Cikin damuwa da takaici umma tace,


"Maryamah ba kuka Zaki tsaya kiyiba tufkar zakiyiwa hanci tun lamarin Bai fita hannuba,
Karki tsaya sanyar Dama zaasan ita din jininki ce Dan kuwa Babu wani sauran mutunci da girman da zakuyi a Idon mutane idan akaji kinma Santa bare Kun hada uba daya tunda ita nata sunan qaurarre ne,


Karki jira komai ki nema inda take Ina hanya zuwa gobe inshallah Zan biyo jirgi
Kafin AQEEL din yadawo daga tafiyarsa zamu tabbatarda tabar rayuwarsa wannan karon har abada tunda ba fin karfinmu taiba,


Maza ki Dena yiwa kowa kuka,.
AQEEL Dan ki Babu Wanda ya haifar Miki shi,
Kece Kika haifesa kece kikeda iko da Isa akansa fiyeda kowa,


Tasan hakan tunda itama tanada 'yayan ta Haifa da Yar halak data banza dan Haka tasan me ake nufi da 'da yanzu.


Sake danne zafin zuciyarta Haj Maryamah tayi tana cewa,


"Umma ko Baki fadaba walh bazan taba barin 'dana ya kusanci rayuwar Zainab data haramtacciyar zuriarta ba kome zaayi bazan yardaba Koda hakan na nufin AQEEL din zai zabi daya ko Ni ko zainab din.


Zuciyoyinsu Babu Dadi Sam sai bacin rai da tashin hankali suka Gama wayar da Shirin isowar umman a gobe wadda takejin kamar tayiwa Zainab tsinuwar da zata bita tabi duniya ta bace daga rayuwar 'yarta da jikanta har abada,
Hada jini da Zainab ko masifa da balai.




*********
Haj Zainab da AMAL harma da Uncle Lulu dake jiran zuwan AQEEL ASAD a ranarda jaridar ta bullo Bai samu yazoba saidai yayiwa Mamin tasa waya akan tafiya ta kamasa ta gaggawa saiya dawo zaizo.


Juyar da Kai AMAL tayi cikin Dan takaicin sakon nasa sbd taso yazo din Mommy ta Kai karshen alaqarta dashi,
Har cikin ranta Bata kaunar kusancinsa da mahaifiyarta,
Babu alamar alkhairi a tarensa da mommynta tunda hakan ya fara bullowa,


Duk wani Abu dayake taba Mata mommynta tsanarsa takeyi da gaske shiyasa aurenta da SSG har abada bazai taba faruwaba Koda ta rasa Mijin.


Bedroom dinta Takoma ta zare kayan jikinta ta shige toilet.


Wanka tayo tareda alwala ta fito lafiyayyan farar fatarta na daukan Ido.


Sama sama ta shafa body cream da turaruka marasa karfi
Fuskarta bata shafa komaiba Bayan Mai kadan ta miqe ta nufi kayanta ta saka Malaysian Riga da skirt marasa nauyi rigarma as usual batada hannu sai Dan qarami siriri.


Abaya ta saka tayi sallar magrib tana idarwa ta Dan Yi waya da Siddi da sai alokacin tasan meyake faruwa ta Kira mommyn tana cewa zata dawo zuwa next week.


Harta fito cin abinci waya takeyi da siddin wadda taji kamar ta dawo a ranar Amma Dole zata Bari zuwa next week idan Mijinta yayi tafiya zata dawowarta.


Baya sun Gama cin abinci Bata tsaya fira ba ta shigewarta sbd kanta yau ciwon Yar hargitsin data Shiga yakeyi akan lamarin.


Baya shigewarta Haj Zainab ta kalli uncle Lulu cikin tabbacin abinda zai iya faruwa tace,


"Matuqar zancen Nan ya Isa kunnen dangin AQEEL ASAD inada tabbacin bayyanarsu gareni saidai Kuma bazasu taba iya sako kafarsu muhallinaba sbd tabbatarda qyamarsu gareni.


Qayataccen murmurshi yasake Yana cewa,


"Ta duk inda zasu bayyana dabararsu ce,
Abu dayane anan
Shine bazasu taba bayyana sirrin Siddi Yar da Kika Haifa a bariki bace.


Qaramin numfashi ta sauke ahankali tana ajiye wayar dake hannunta tace,


"Siddina ce kawai damuwata,
Itace Bazanso su tona wani sirrin dazaisa tasan ita waceceba shiyasa nace tabari sai zuwa next week idan Mijinta yayi tafiya ta dawo Dan inada tabbacin zuciyarsu bazata dannesu sukai har wannan lokacin ba Basu bayyana ba sai idan basa Raye a duniyar ne to.


Sun Jima suna tattauna zancen harkokinsu kafin suka shige.




****Bilkees kuwa daqyar taga safiya ta waye ta daga wayarta tafara da Kiran Nafee tayi Mata tatas akan Bata nemetaba Bayan tanada tabbacin tagani Kuma taji abinda yake faruwa IDON NERA na neman dawowa kan Mijinta.


Fuskewa tareda marairaicewa Nafee tayi tace bata saniba sbd itama SSG yaqi sauraronta
Neman hanyar gyaran aurenta takeyi.


Bilkees data Gama quluwa tako Ina cewa tayi,


"To gwara ki Dage da neman mafita kuwa Dan wlh Ina Nan koro IDON NERA tadawo asalin inda tafara sbd Babu gurinta a rayuwar Mijina.


Kashe wayar Tai ta wurgar zuciyarta na tafasa,


Umma taqi cemata komai haryanxu akan zancen,
AQEEL ASAD dinma yaqi lokacinta bare tayi Masa zancen,


Mufeeda ma tana cikin baqin ciki da kuncin lamarin bare su taru suyita tsinewa dangin kaf ahalin IDON NERA ta uwa ta uba,


Koma dai menene ita tinda Babu gurin Wanda zataji cikakken bayanin abinda yake faruwa zata tinkari inda ya Kamata taji Dan bazata zauna ta haukaceba sbd gap take da bugawa idan ba bayanin komai tajiba.


Zatai maganin matsalarta tareda takawa matsalar kyakkyawan burki kafinma tayi tunanin shigowa gonarta.




Da yamma umma ta iso driver yaje airport ya daukota tareda Fatima jikar yayanta sbd manyanci sosai yasa Dole yanzu tafiya Saida Dan rakiya.


Koda suka iso Babu Mai walwala ko farin ciki a gidan musamman Bilkees wadda tashin hankali dake cinta a fili yake bayyane,


Haj Maryamah ta danne nata sbd basa son kowa ya fahimci ko abu dayane dazai iya nuna alamar alaqarsu da Zainab ciki kuwa harda Bilkees wadda itama kanta bazasu yarda tasan matsayin Idon Nera agunsuba.


Tunda umma tazo ko abincin kirki kasa sakawa cikinta tayi
Ita Haj Maryamah kuwa Daman tun jiyan duk wani qunci da baqin ciki yagama cike Mata ciki
Daurewa kawai sukeyi sbd Hana kowa fahimtar abinda suke fama dashi.


Shi kansa AQEEL Babu Wanda ya sanar Masa da zuwan umman Dan kuwa Yana Jin zuwanta zai fahimci meyake Shirin faruwa Dan Haka basuda masaniyar yaushema zai dawo kowannensu yaqi yin waya dashi Dan isarda kudirinsu batareda yasaniba dagasu har Bilkees da 'yarta.






*****Washe gari karfe goma na safiya Al-Amin yagama korowa umman bayanin komai akan Idon Nera da offices dinsu da gidansu harma lokacinda take gida da lokacinda office zaa sameta.


Kallonsa Haj Maryamah tayi tace ya tafi Kuma karya sanarda AQEEL ASAD bayanin Idon Nera dasuka saka ya Nemo musu.


Yana fita haj Maryamah tace,


"Bazan taba saka kafata inda Zainab takeba sbd zuwa gabanta shine mafi qanqantar da zanyi a rayuwa,


Kafafuba bazasu taba taka haramtaccen gurinta ba......


Wani numfashi umma ta sauke tana kallon haj Maryamah din da zafin dayake cikin ranta tace,


"Kinada wani zabi ne Bayan takawa kije gabanta ki Kai karshen matsalar rayuwarki?


Rashin zuwan naki kina saneda masifa da baqin cikin dazai kawo daga baya alokacinda ta sake mallake Miki 'dan,


Bakida wani zabi Maryamah baya zuwa Inda take din sbd shine kawai mafita batareda AQEEL din ya dawo yamasan meya faruba,


Zuwanki Dole ne sbd mugama magance damuwar nakoma basaima AQEEL din ya sameniba yayi zargin wani abun tunda munkoma mune mukejin shakkarsa duk akan Zainab,


Wlh malam ya auro Mana irin masifa gashinan an haife Mana anbarmu da kuka da baqin tareda kame kame.


Idan bamuje ba kina tunanin yanda ta riqa a rayuwar datakeyi zatazo ne Ida munkirata,


Da ita tazo takawo dauda tsaftataccen gidanku ba gwara mu mujeba idan munfito mayi istigfar mu goge daudar.


Wani yawun bakin ciki da 'daci Haj Maryamah ta sauke tanajin saitin zuciyarta na ciwo da radadin akaro na farko da Zainab tayi galaba akanta tasakata zuwa gabanta a ta sameta duk akan 'dan da natane ita ta haifi abinta da wani shegen ya haifar Mata ba.


Qarfe hudu na yamma da mintina suka fito cikin shigar alfarmar dasuka Saba da ita suka shiga 'daya daga cikin manyan motocin Haj Maryamah din driver ya jasa suka fito harabar gidan.


Bilkees Kuma qarfe hudu da rabi ta fito tareda mufeeda suka shiga motarta
yau itace zatai tuqin da kanta sbd a sirrance takeson aikatar da nata aikin...
Gidan IDON NERA ta nufa Kai tsaye.






*******Qarfe Biyar saura aka wangalewa motarsu Haj Maryamah babban gate din gidan IDON NERA sbd motar dakeda lambar motocin AQEEL ASAD Wanda zuwa lokacin securities sungama sanin yanada matsayi a gidan shiyasa suka budewa motar gate Kai tsaye.


Suna parking Mai aikin gidan Bilkisu data fito daga sashen Anty Fareedah ta tsaya ta gaishesu cikeda girmamawa saidai Babu Wanda ya iya amsata Kai tsaye Zainab suka baqaci gani.


Jagora Bilkisu din Tai musu saidai a daidai palon farko Haj Maryamah ta tsaya sbd numfashinta dake siqewa da duk taku daya datakeyi Acikin gidan...


Kasa cigaba da shiga tayi ta tsaya cak tana Jin bazata iyaba zuciyarta fashewa zatayi Dan Haka kai tsaye ta juya gwara Takoma gidanta AQEEL yazo ya zaba ko ita ko Zainab da 'yarta.


Juyawarta idanuwanta cikeda baqin ciki da zafi Mai tsanani yasa umma biyo bayanta tana kiranta itama zuciyarta na tafarfasa Dan kuwa Zainab taci amanarsu tako Ina ta cucesu data sanyasu zuwa Inda take ba shiri ba tinani Allah ya isansu wlh sunkai kofa kenan ta daga qafa zata fitar
Daddadar muryar Zainab ta sauka a kunnunwansu kamar saukan ganga.




"Su waye a gurin?"


Rintse jajayen idanuwanta dasuka sauya Haj Maryamah tayi sbd yankar zuciyarta da muryar tayi tareda kalmomin dasukai Kama dana kamar ankamasu.


Umma ma zancen ya daketa sosai Dan Haka ta juyo cikin mamaki,baqin ciki da takaicin zuwansu gidan mace kamarta.


Saukowa takeyi a staircase na palon tana sake zuba musu kyawawan idanuwanta Babu alamar ta sansu ko gane daga inda suka fito.


Umma jininta ne yafara Hawa ahankali ahankali Yana sama,


Yau take qara yarda da Zainab a rayuwarsu masifa ce babba Dan kuwa jininta take yafara hayewa sama daya ganin wannan macen ace itace Zainab....


Haj Maryamah data kusan hadiye zuciyarta juyowa tayi ahankali daidai qarasa saukowar zainab din tana kallonsu Kai tsaye fuska ba alamar sani.


Wani abune dayafi dutsi tauri ya Danni zuciyarta lokaci daya saidai bazata iya barin quncinta fita gaban zainab ba.


Kallon kallo sukewa juna cikin wani yanayi dayafi Kama da kowa ta cikinsa na ciki.


Ahankali haj Zainab din ta dauke Kai tana maida kallonta kan umma dake kokawa da kirjinta Amma tana daurewa sbd kada subawa Zainab din damar ganin tashin hankalinsu.


Bude baki tayi zatayi magana AMAL ta fito daga sama tareda fara saukowa stairs ahankali sanye cikin Riga Qarama Mara nauyi da tsayi tana waya hankalinta kwance.


Ganinsu yasata kashe wayarta tana kallon mommynta da itama ita din ta waiwayo tana kallo sbd bazaso Susan waye Amal dinba Dan suna sani AQEEL zai iya sani
Shikuma idan yasani zai iya karbanta Wanda tana Tina alqawarinta akan shine ikonta tunda shine amanarta tashiga hannunsa tun Bata fito duniya ba daga mahaifinta.
##MAMUH#
#HOTLOVE#AQEEL ASAD#






*_ZAFAFA BIYAR_*


*RUMBUN

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login