Showing 126001 words to 129000 words out of 149977 words

Chapter 43 - IDON NERA BY MAMUHGEE CMPLT.txt

25 Nov 2024

6515

da kanta.


Dif taji ya kashe wayar batareda yace komaiba itama wurgi tayi da wayar tana sake tsiyayo hawaye fuskarta.


Kaman a mafarki batafi mintina arbain da jefar da wayarba mommynta ta shigo dakin tana kallonta ko saukowa gadonta batayiba idanuwanta sunyi jajir alaman kukan datasha.


Cikin sanyi mommyn ta qaraso gadon ta zauna tana cewa,


"AQEEL yazo Yana jiranki inaga tun 10 din Bata qarasa ba zaku wuce.


Rintse idanuwanta tayi sbd harga Allah Bata buqatan zuwa koina ta kanta din takeyi,
Hakama batasan menene wannan tafiyan take nufiba.


Haj Zainab data dauka tsananin rashin son tafiyar ne yasa Amal din wannan halin duk sai jikinta yayi sanyi Amma Kuma tunda bama qasar zasu bariba yace cross River ne zasu ita wannan lamarin batasan wane irin likatane zaa iya ganiba acan,


Dan Haka tabar zancen Akan idanma sunje yanzu itama idan zata gaskia zata tafi gurin nata liktan da Amal din zata sake zuwa.


Shafa Fuskarta tayi tareda Kiran sunanta ahankali tana rarrashinta akan tayi hakuri taje din ba komai bane idan taje taga wannan likitan insha Allah Suma idan zasu nasu bazai hanaba zai barta suje gaba dayansu.


Kasa magana tayi bare motsawa tayi shiru kanta na sake sarawa,


Jin takeyi inama Bata tareda abinda take ganinsa kaman abin kunya data kwanta jikin mommynta taji sanyi Amma yanzu ita kanta kunya da takaicin kanta takeyi da bazata iya dogayen motsiba ganin takeyi kaman zaa gane metake dauke dashi.


Mommy da kanta ta tayar da ita tasata tayi wanka jikinta a sanyaye ta shirya Suka fito siddi ce ta fidda Mata kayanta suna fitowa Bata gansaba yariga ya fice sbd bayason Yana ganinta a yanayin datake agaban mutane coz a yanda yake jinta dinnan zai iya rungumeta gabansu Kuma yasan bazataso hakan ba.


Tea kawai tasha sama sama har lokacin batada walwala ko kadan
Ita kanta mommyn zuwa yanzu tanason Amal din taje taga likitan tunda ya buqata hakan
Daga nasa likitan har nasu basusan Ina Saar samun lafiyar takeba.


Mommyn daga na palon tayi bankwana da ita Takoma sama sbd batasan rakiyar me zatayi Mata har waje ba.


Siddi ma daga kofa ta tsaya ta Dan rungumeta tareda Mata sallama ta juya tana cewa,


"Amal Dan Allah ki Dan sake Masa fuska kafin kudawo.


Batada energy na iya amsawa zancen siddin Dan Haka ta shareta kawai kafin tayi wani motsin tajisa a bayanta ya qaraso cikin nutsuwa.


Juyowa tayi ta kallesa da idanuwanta dasukai jajir take taji jikinta yasake mutuwa da wani irin damuwar halinda ya sakata a yanzu.


Hannunta ya Kama ahankali batareda yace komaiba ya nufi mota da ita tana tafiya kaman Mara lafiya ba kuzari ko kadan,
Tun kafin su qaraso Ahmed yabude masu mota
Shine yafara shigar da ita ya rufe Mata kafin ya zagaya ya shiga nasa bangaren Ahmed ya rufe Masa.


Suna barin harabar gidan Kai tsaye airport suka nufa duk da akwai sauran 1 hour kafin tashin kirjinsu.
#MAMUH#






*_ZAFAFA BIYAR_*


*RUMBUN K'AYA*🔥
Hafsat Rano


*DAUDAR GORA*🔥
Billyn Abdul


*IDON NERA*🔥
Mamuhgee


*A RUBUCE TAKE*🔥
Safiya huguma


*KI KULANI*🔥
Miss xoxo


Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200


ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN


0022419171
Maryam sani
Access bank


Shedarka ta 09033181070


MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN


09166221261


🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*


+22799643131


Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA


*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*🔥


66


*_Arewabook@Mamuhgee_*


66


Koda suka Isa Al-Amin na airport din tareda tickets da sauran abubuwan nasu na tafiya da alama taredashi zsuyi tafiyar wadda Daman akwai abinda zasuyi acan zuwa jibi Amma AQEEL ASAD ya zabi tafiyar da wuri kawai.


Ahmed na parking din motar dakyau ya bude ya fito yabar gurin gabaki daya Dan Basu guri yabi Al-Amin dashima baiso tafiyar tasu yanzuba yaso sai jibin.


Juyowa yayi yana Mata wani irin kallon da baisan wane iri bane,


Zuciyarsa tariga tagama dadewa da ita manne acikinta har bazaice ga lokacinba.,


Tazama Kamar itace rauninsa da qarfinsa tareda kuzarinsa da akalarsa Amma sam ita bata gane hakanba,


Ayau yatashi da azumi ne na nunawa ubangijinsa tsananin godiyarsa da babban arzikin dayayi Masa na abinda Dr tayo ta sanar dashi jiyan,


Yashiga wani yanayi ne Mai hadeda shock da zallan wani yanayi Mai tsananin girma a cikin zuciyarsa alokacinda kalmar Amal din na daukesa cikinsa ajikinta ta shiga kunnesa,


Ya Dade zaune shiru cikin nutsuwa alokacin da Dr tayo take cigaba da Koro Masa bayanin Yana sake kokarin kame Kai daga shiga firgicin zancen Dan arzikin daga Allah ne daya basa a lokacinda Bai taba tsammanin wannan kyautarba Dan kuwa Amal tagama basa duk wani abun a duniya dayake buqata bayan gamawa lafiyada cikawa da Imani.


Idan Bai samu ya dauketa yaje inda zai dauki lokaci Yana Jinta da cikinsaba to duk yanda yake biya Mata gurin Hana kowa ganesu dan kada ranta ya baci tashiga damuwan kunya to tabbas idan bai bar Nan da itaba komai bayyanuwa zaiyi Dan tsakanin jiya zuwa yau din daqyar yake controlling Yana nutsar da Kansa akanta,


Buqatan rungumeta yakeyi ajikinsa ya sauke Ajiyar zuciya ya shaqi qamshinta Da numfashinta dake fitowa da 'dansa ko 'yarsa ajikinta.


Hannuwanta ya riqo cikin nasa ya sarke ahankali tareda sauke ajiyar zuciya ya kalleta itakuma har lokacin taqi kallonsa daga zuciyarta har jikinta ba Dadi.


Bazai iya shigar da ita jikinta ya shaqi qamshinta ba sbd azuminsa Dan Haka hannunta kawai yakai bakinsa yayi kissing sai alokacin ta juyo ta kallesa batareda tace komaiba.


Shima kallon nata yakeyi da idanuwansa dake neman qarasa rikitata ahankali cikin wata murya Mai sanyi da Dadi tareda nutsuwa yace,


"Congratulations Mrs AQEEL ASAD...


Wani kallo tayi Masa jikinta na qarasa mutuwa da mummunan halinda takejin tana ciki tareda mamakinsa Akan ta tabbata dai Dr tayo ta sanar dashi tana daukeda ciki,


Meyasa zaiyi congratulating nata bayan ko a kallo ya kalleta yana iya hango mummunan tashin hankalin datake ciki,


Idan yasani to meyasa zai dauketa suje ganin wani likitan?


Akan me zasu ganin liktan?


Fuskarta ya shafa kadan Yana sake cewa,


"Idan kina mun wannan kallon Zaki karyamun azumi fa.


Juyar da kanta tayi ahankali tana rintse Ido cikin damuwar data dameta.


Al-Amin ne ya iso ya sanar dasu su fito lokacin tafiyan yayi.


Hannunta cikin nasa a riqe yake tafiya da ita ahankali ba gaggawa ba garaje cikin nutsuwa da kwanciyar hankali Al-Amin ne janyeda kayansu.


A jirgi ma Haka ya zaunar da ita da Kansa kafin ya zauna Yana kallon yanda duk tayi sanyi batada walwala ko kuzari ko kadan.


Ajiyar zuciya kawai ya sauke Yana Hana Kansa yimata rarrashin dayake buqata sbd azuminsa,


Ayanda yake jinta Acikin Ransa Dole Yana buqatan janyewa da nesanta Kansa da ita aduk lokacinda zaiyi ibada irin wannan ta azumi.


Ciki ba ruwansa da damuwa Dan Haka suna tashi wani bacci Mai dadi da Dan nauyi ya kwanshe hannunsa daya Yana manne da nata.


Bayan isarsu Kai tsaye beach Villa resort aka kaisu Kai tsaye dakinsu yakaita Wanda yake kusan zagaye da ruwa da abubuwan hutawa da asalin iskan ruwa Mai dadi.


Al-Amin gabaki daya baa resort din nasa masaukin yakeba Dan Haka shi juyawa akai aka wuce dashi nasa masaukin dayake kusa ba nesa sosaiba.


Bakin manyan windows din dasuke kaman kofofi ta tsaya tana shaqan iskan dake kadawa Mai sanyi da rashin hayaniya.


Ajiyar zuciya ta sauke ahankali tana kokarin barin kanta ya warware yasamu salama ko zata Samu sassaucin komai.


Waya yakeyi Mai mahummanci Sosai tunda Suka shigo makeken dakin dayake daukeda komai na tsadaddiyar luxury rayuwan Jin Dadi da kwanciyar hankali da hutawa.


Tunda yake wayar idanuwansa akanta suke Yana kallon sauyinta na haske data qara da wani irin kyau Mai sanyi saidai daga hankalinta datayi a jiyan zuwan yau din yasa duk ta Dan rame.


Gurin cikinta dake cikin doguwar Rigar jikinta ya zubawa Idanuwansa Yana cigaba da wayarsa.


Koda ya Gama tashige toilet tayo alwala ta tana fitowa yasa ta jirasa ba musu ta jirasa din Yana fitowa sukai sallan tare,


Da Kansa yayi Mata order na abinci kusan kala uku da drinks marasa sanyi aka kawo,.


Kaman yanda yasabar Mata idan har suna tare zataci abinci shine yake Bata abaki,


Haka ya janyota ya zaunar gabansa yabata abincin taci sosai ba laifi sbd yinwar da cikinta yake ciki gashi kwanakin sosai takecin abinci dama Ashe da dalili.


Tana Gama cin abincin Takoma ta zauna ta rafka tagumi tana sake shiga tunani Mai zurfi daga Nan Bata jimaba bacci ya dauketa Mai qarfi.


Tanayin baccin ya dauketa yakai tsakiyar lafiyayyan gadon dakin ya kwantar da ita ya zare Mata doguwar abayan jikinta yabarta da leggings da qaramar singlet din dake jikinta ya rufe ta da lallausan duvet me taushi ya fice daga dakin Yana nufi makeken qaton corridor dinsu budadde Yana cigaba da amsa wayoyi sbd abubuwan dasuka danganci aiki da wasu mahimman abubuwan daya baro sbd tafiyar ta Babu tsammaninta kusa.


Bacci sosai tayi sai yamma ta farka ta sauko gadon ahankali tana kallon cikinta dayake kukan yunwa.


Toilet ta nufa ta tadda tuni an kawo duka abubuwan dayasan tana amfani dasu an jere a toilet din,


Brush tasake Yi tayo alwala tafito ta saka abayan tayi sallar laasar tana idarwa Yana shigowa sanyeda qananun Calvin Klein's isowa yayi gabanta tareda miqar da ita Yana cewa,


"Barka da tashi Yar Mommy.


Juyawa tayi ta kalli abincin datake hangowa jere a lafiyayyan 2seat dinning din dake dakin.


Gurin abincin ya nufa da ita still shine yasake feeding nata Yana tarairayarta dan mantar da ita damuwarta wadda tarasa Ina mafitar take.


Yana gama Bata abinci ko dining din basu dagaba lokacin Shan ruwansa yayi,


Kai tsaye yace Mata ta zuba Masa tea ya nufi toilet Dan yin alwala.


Ajiyar zuciya ta sauke ahankali sbd batada zabin daya wuce yin abinda yace din,


Tea din tafara zuba Masa tareda janye plates daya gama abinci ta gyara table din Dan samun space yanda yakamata Dan abincin kusan gab da magrib din aka kawosu aka jera.


Yana fitowa tablet din yake kalla da mamaki ganin ta gyara komai tana janye wainda suka Bata da farko.


Zaunawa yayi ahankali ya Dan sha fruits da tea din kafin yamiqe sukai sallan magriba a tare suna idarwa ya jata da Kansa yace shima itace zatayi feeding dinsa.


Zamewa takeyi tana neman kaucewa Amma Bai Bata Daman hakanba ya dauketa cak ya nufi dining din suka zauna tana jikinsa ya gyara Mata zama jikinsa Yana shinshinata idanuwansa dasukai tsananin kewanta a jikinsa da qamshinta suna lumshewa,


Sake zagayeta yayi dakyau Yana zira Kansa cikin wuyanta ya sake shaqo qamshinta Yana shafa wuyanta da fuskarsa.


Ita kanta lumshe fararen idanuwanta tayi tana dan motsawa tsikan jikinta dayake neman tayarwa da fuskarsa dake shafan fatan wuyanta wuwa kirjinta.


Fuskarta ya tsayar da tasa a saiti Yana shaqan iskan numfashinta dake sauka akan fuskarsa ya kalli cikin idanuwanta da itama ta dago tana kallonsa,


Harshensa yakai kan lips dinta ya laso yasake lasowa ya lumshe Ido Yana sauke ajiyar zuciya kafin ya Dora bakinsa akan nata din gaba daya ya kamo harshenta da nasa yayi nasa wata irin kyakkwar tsotsa Mai sanyi da nutsuwa kafin ya Ciro bakinsa ya dago ya sake kallon fuskarta cikin matsanancin sanyin sonta dake riqe da dukkanin zuciyarsa da wata kasalalliyar murya qara qasa yace,


"I Love you MARYAMAH Amal Sanda,


Nagode da wannan farin cikin da Zaki bani na zamowa uba.


Kasa motsawa tayi sai idanuwanta dasuka narke data zuba Masa tana mantawa da halinda ma take ciki da damuwa.


Sakinta yayi Yana gyara Mata zama a jikinsa yafara cin abincin Yana tsokanarta Akan ta basa da hannunta Amma taqi.


Gabaki daya din abincin da shirirta aka gamasa sbd qamshinta da jinta jikinsa yasa yakasa bawa abincin mahummanci Sosai,


Itama kanta tasan bawani cin abincin yayiba sbd hannayensa dasuka kasa zama guri daya.


Yana gamawa kafin yayi yunqurin komai Yana saka hannuwansa cikin rigarta Kiran Al-Amin yashigo wayarsa


Wani silent numfashi ya sauke Yana kallon wayar da idanuwansa dasukai ciki kamar Mara lfy,


Yasan abinda yasa Al-Amin yakirasa Dan Haka yakai hannu ya dauki wayar ahankali yakai kunnensa yaji abinda Al-Amin yafada ya kashe wayar tareda ajiyewa ya sauke ajiyar zuciya tareda kwantar da Kansa akan kirjinta ya sake dawo da nutsuwarsa daidai.


Dagowa yayi ya kalleta ya zura hannunsa cikin singlet dinta yayiwa cikinta wata irin shafa Mai sanyi..


Dafe hannunsa tayi ahankali tana kasa kallonsa sbd yanda yake shafar cikin Yana kallonta yasata kunyar tunawa da cikin dake jikinta.


Kunnenta yakai bakinsa ya lasa fatarta tareda wani kiss me sanyi murya a shaqe yace,


"Zamuje Al-Amin zai kaimu gurin likita inason adubamun Matata dakuma ganin Babyna.


Juyowa tayi ta kallesa ahankali maganarsa na shigar Mata kai da zuciya Dan saitake tinawa da ashefa babyn nasane ba nataba a zancensa.


Bata motsaba ta bude bakinta tana Dan rage kallonta akansa cikin sanyin da muryarta tayi tace,


"Menene Dr tayo ta fada maka?


Wani kyakkyawan murmushi ya sake mara sauti komai nata na taba Kansa,


Rashin maganarta yasa duk lokacinda ta bude Baki tayi Masa magana yakejin kaman tana kunce Masa Kai,


Kama fuskarta yasakeyi ya Dora bakinsa Akan nata Yana tsotsan bakinta tsawon minti daya kafin ya saketa Yana miqewa tsaye da ita yace,


"Tafadamun dararrakun rashin bacciba ladansu ya bayyana......


Mamakin maganganunsa yakasa sakinta akoda yaushe idan yai irin wannan zancen masu tinatar da ita shine yagama samunta ciki da waje gashi yanzu yasata a tsaka Mai wuya,


Babban damuwarta takasa tunanin cire cikin kwata kwata batama kawo wannan tunanin.


Itama qatuwar sweatshirt fara ta Fendi da wandonsu Mai Fadi shima ta saka Suka da mayafinta dayayi Mata rolling da Kansa suka fito Yana riqeda hannunta Suka nufi motar da Al'amin yazo da ita daga inda ya karbo suna shiga Kai tsaye wani babban private specialist Suka nufa inda suna zuwa Babu Bata lokaci aka sake yimata scanning daga ita harshi suna kallon screen din


Bayani likita tasake yimasa akan lafiyan cikin kalau kaman yanda itama Amal din take lafiya kalau.


Magunan data kasa tsayawa gurin Dr tayo ta amsa su aka Basu Suka fito Yana binta wani mayen kallonsa yanajin bazai iya barinta ba kuwa a gidan Maminsa Yana buqatan matarsa a inda yake.


##MAMUH#


*_ZAFAFA BIYAR_*


*RUMBUN K'AYA*🔥


Hafsat Rano


*DAUDAR GORA*🔥


Billyn Abdul


*IDON NERA*🔥


Mamuhgee


*A RUBUCE TAKE*🔥


Safiya huguma


*KI KULANI*🔥


Miss xoxo


Littafi daya---400


Biyu---600


Uku----800


Hudu-----1k


Biyar din duka----1200


ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN


0022419171


Maryam sani


Access bank


Shedarka ta 09033181070


MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN


09166221261


🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪


*Ina yan uwa 'yan nijer?*


*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*


+22799643131


Littafi daya---450CFA


biyu---650CFA


uku----850CFA


hudu----1050 CFA


Biyar----1250CFA


*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*


*Thanks for choosing us*🔥


67


*_Arewabooks@Mamuhgee_*


67


Suna dawowa sallah Suka fara Yi kafin ya sake musu ordern abinci sbd take ya lura da abinci takeci akai akai sbd cikin.


Koda abincin yazo tafara bacci sama sama,


Dagota yayi tareda zare Mata hijabin sallarta Yana kallon yanda ta Dan bude idanuwanta dake nuna baccin dasuke ji,


Ahankali ya janyota cikinsa Yana sake miqar da ita Yana cewa,


"Ni fa ba raggo bane tayaya babyna zaisa ki zama wannan raguwan haka¿


Kamata yai kuzarina dake cikinki yasa ki zama Mai kuzarin gaske.


Kallonsa tayi tana Dan Bata fuska tana lafewa jikinsa daya janyota.


Ganin Bata buqatan abincin a lokacin saiya qyaleta ya zauna a kujerar Yana sake gyara Mata kwanciyarta ajikinsa.


Da mahaifiyarsa yake waya tana tambayarsa ya hanya dakuma son tabbatarda shi kadaine yayi tafiyar Dan hankalinta kwata kwata ya dena kwanciya da duk tafiyan da zaiyi yanzu tunda Zainab ta canja salon tura masa 'yarta tana daukan hankalinsa tunda ya sameta a budurwa shikenan suna neman maida abin 'dan kullum,ko kunya Zainab din bataji tana amfani da 'yarta gurin mallake AQEEL din sbd shegen kwadayinta yafi Mata 'yarta.


Harya gama wayar da ummansa hankalinta na kan motsin dazata jiyo daga bangarensa Amma Bata samu taji komaiba Kuma Bata iya tambayarsa sbd har ranar yau din Koda Ido dagasu har shi kowa yaqi nuna ya Tina da abinda ya faru a wancan lokacinda Suka samesa a gidan karatun.


Bayan gamawarsa wayar baccinta yariga yai nisa hankalinta kwance kaman ba wadda ke cikin damuwar yanda zatayiba idan cikinta ya bayyana.


Kissing din gashinta yayi ahankali Yana sake gyara Mata kwanciyar


Itama tasake Shigewa jikinsa cikin baccin tana sauke ajiyar zuciya Mai sanyi.


Da Bilkees wadda keta kashe Masa murya tana Masa kalaman soyayya yayi waya suna gamawa mufeeda ma takirasa tayi Masa barka da hanya kafin yakira Maminsa wadda itama Kai tsaye suna Gama gaisawa Amal ta tambaya.


Fuskar Amal din yakalla yana Kai hannunsa cikin rigarta ya shafi cikinta ya sauke Ajiyar zuciya ahankali Dan yasan da a farke take data fara narke Masa idanuwanta tasashi fadan zancenda takeso akan boyewa Mamin komai.


Koda Bata farke bazaiso fadan abinda idan ta tashiba zata Shiga damuwa Dan Haka Kai tsaye yace,


"Ni inda dakina Amma ita tayi bacci sbd gajiya.


Dan ajiyar zuciya ta sauke a boye sbd Jin da alaman Basu samu Yar hayaniya ba kila,tsoronta Amal taje ta ringa Masa Kai tsayen data saba ta ringa qin abinda zai ringa cewa,


sake Masa sannu da hanya tayi Suka Dan Yi magana sama sama tanason tambayarsa Amal din dai Bata fara halin nata ba Amma Kuma tunda baiyi complain ba duk da tasan bazaiyi dinba saitayi shiru kawai sukai maganganunsu sukai sallama.


Daga kanta ya kashe wayarsa sbd Yana buqatan hutawan shima,


Wanka yakeson yi Amma baccinta dayayi Mata Dadi da alama yasa yakasa tayar da ita saiya lumshe idanuwansa ahakan yana samun nutsuwa.


Ahakan shima bacci ya dan daukesa Bai Jima yanayiba Sama sama yajita ta fara motsawa alaman zata farka


Ya bude idanuwansa yana kallonta areda kokarin gyara Mata kwanciyar sai gashi ta bude idanuwanta tana Dan lumshewa kaman baby ajikinsa.


Yunwa ce ta Dan tadata Dan Haka ta tashi zaune ahankali tana kallonsa kaman wata yarinya Qarama ta juya ta kalli inda zai nuna Mata table na abinci taga komai a jere har lokacin.


Shima kallon inda ta kalla yai tareda dawo da idonsa kanta ya kalleta cikin kulawa ya shafa cikinta dayasata Dan lumshe Ido yace,


"Zakici abinci ne?


Gyada Masa Kai tayi Kai tsaye tana jiran yakaita da Kansa gurin abincin.


Tayar da ita yayi daga jikinsa yana miqewa tsaye ya Kamata suka fara nufan toilet ya tayata wanke bakinta Suka fito Kai tsaye table din Suka nufa ya zaunar da ita yana duba abinda zai Bata taci.


Abincin ba zafi Dan Haka ya juya zai sake cewa akawo mata wani saita dakatar dashi da cewan zata ci wannan din tafison Mara zafi.


Macaroni salad taci sosai yabata ruwan dumi Tasha shima ya Dan sha ruwan dumin da snacks.


Sai dataci snacks din kadan itama kafin suka miqe Kai tsaye toilet ta nufa tanason Dan watsa ruwa sbd batayi wankaba baccin ya dauketa da kayanta data fita dasu.


Tana tsaye qarqashin shower ruwa na sauka jikinta idanuwanta a lumshe tanajin nutsuwa na Dan shigarta ta shafa cikinta tana Jin yanda mararta tayi Dan tauri,


bataji motsin shigowarsa ba saidai taji an rungumeta ta baya tareda zagayowa da hannuwansa ya Dora kan cikinta shima ya shafa ahankali Yana lumshe fararen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login