Showing 78001 words to 81000 words out of 149977 words

Chapter 27 - IDON NERA BY MAMUHGEE CMPLT.txt

25 Nov 2024

6529

Lulu dasuma ita din suke kalla,


Zancen Bai razanata sosaiba sbd tasan bamai yiyuwa bane abinda take tunanin taji din?


Ba ita Amal din ba sbd abune da bazai taba yiyuwaba mommyn su aurar da ita bada sanintaba Kuma aurenma na Dole da Wanda sukasan kota Yaya bazata yarda ta taba aurensaba.


Qin kallonsa tayi ta qaraso ahankali gabansu mommyn tana sake kallonta da kyau kafin ta bude Baki tace,


Mommy wace Amal ake magana akai?


Wane auren Kuma aka daura?


Dakuma waye aka daura auren??


Siddi ma cikin mamakin ta qaraso tana kallon Mommyn tasu Amsarta suke jiran ji Dan itama tashiga rudani da mamaki Mai girma idan har Amal dinsu ake nufi,


Mezai hada Amal da auren bazata, auren Dole, auren rashin sani??


Rintse idanuwa Haj Zainab tayi hawayen dake ciki suka Kuma gangarowa kan fuskarta datake ta jiqewa da hawaye tunda suka dawo din.


Kasa kallon Amal tayi sbd tasan baa kyauta Mata Dan Koda zaayi Mata auren bazata da dolen yakamata a sanar Mata


To Amma ya zatayi AQEEL itama yasha gabanta ya zartar da wannan danyan hukuncin da batasan ya zatayi ba bare Amal,


Girman kaunarda takewa AQEEL wata halittace da Allah ya halitta Mata cikin ranta da bazata taba iya cirewaba ko fincikewa,


Tasan kaman yanda yafada tafi kowa saninsa a duniyarsa baya magana ya janye tun Bai kawo yanzu dinba bare yanzu daya sake zama mutum tsayayye,


Wlh tasan bazai saki wannan aurenba a yanzu gashi tayi rokon harta galabaita Babu alamar Wasa ko sauyin raayi a tattarre dashi,


Me zata cewa Amal?


Tayaya zata kalleta tace Mata aurenta aka daura ayau batareda saninta ko Jin raayinta ba.


Innalillahi wainna ilayhi rajiun"


Kan daya daga kujerun palon ta zube dabas tana dafe kanta hawayenta na tsananta gudu..


Siddi ce ta qaraso kusada ita da sauri ta zauna tana sake shiga mamaki da firgici Dan kuwa alamun sun nuna dai kila Amal dinsu ake magana akai..


Dafata tayi cikin kulawa Mai tsanani da damuwar ganin halinda take ciki sanyaye tace,


"Mommy Dan Allah ki kwantar da hankalinki ki dawo daidai bamason ganinki hakan


Koma menene matsalar zata wuce zamu fuskanceta mu maganceta kaman yanda muka Saba tsayawa da juna,Amma Kuma mommy wace Amal din aka daurawa auren ayau??


Dago jajayen idanuwanta tayi ta kalli inda Amal ke tsaye tana jiran amsar da zataji tabawa Siddin.


Ahankali ta iya bude Baki murya a shaqe tace,


"Amal wannan da muke da ita guda daya gatanan.....


Kaman siddi batasan wacece Amal din ba ta waiwayo cikeda dinbin mamaki ta kalli Amal din zatayi magana Amal ta katseta da cewa,


"Aure fa kuke magana MommyΒΏ


As in aure aure irin na kowa da ake Masa???


Maida kallonta kan uncle Lulu tayi cikeda mamaki tana sake kasa gasgata abinda aka fada din tace,


"Uncle meyasa kayi magana Dan Allah Mana.


AQEEL ASAD daga inda yake Bai waiwayo ba ya nufi kofa hankalinsa kwance ya fice yabarsu sbd bayajin akwai sauran bayanin da Bata ganeba idanma Bata gane dinba zasu Mata bayanin dazaisa ta gane din.


Bayansa uncle Lulu yabi da kallo fuska a Dan yamutse da tunanin Yaya Kuma zai tafi ya barsu da bayani baya shine yayi Aika aikar gabaki daya.


Dawo da kallonsa yayi kan Amal Yana Dan Jin tausayin abinda zai fada Matan, cikeda kulawa da tausasa harshe yace,


"Baby Aurenki AQEEL ASAD yayi ayau,


Kudin aljihunsa ya cire tareda kamo hannunta zai Dora Mata ta zame tana kallonsa da idanuwanta dake cikowa da hawayen tashin hankali,mamaki da baqin ciki tareda firgita.


"Wannan shine sadakinki Amal" uncle Lulu yafada Yana kallon idanuwanta dake kokarin cika da hawayen baqin ciki da zafi zai tsanani,


"Sweetie kiyi hakuri....


Uncle aure fa kace?


Auren Dole kukai mun?


Kallon Mommy tayi sai kawai takasa cewa komai ta juya ta fice dakin da sbd zuciyarta harbawa takeyi da qarfi da ciwo..


Kai tsaye dakinta ta nufa tana kokarin rufewa mommynta ta tare kofar tareda shigowa idanuwanta cikeda rauni da tausayin 'yarta takasa magana sai rungumeta datayi Tana cewa,


"Kiyi hakuri Amal,


Bada niya ko cutatarwa akai Miki hakan ba Nima fin qarfina akai Akan hakan Amma ban taba tunanin yimiki auren Dole ba ko irin wannan na rashin tsammanin, I'm so sorry sweetie....


Kasa rike kukan dayake cin zuciyarta Amal tayi sbd duk yanda taso daurewa sbd takasa yarda da abinda suke fada din takasa daurewa, zuciyarta takasa riqewa Dan Haka ta saki wani irin silent kuka ajikin mommyn tana girgiza kai alamar bazata iyaba,bazata iya karban wannan abinda suke fada din ba.


Tausayintane yasake cika zuciyar mahaifiyarta ta sake rungumeta zuciya a karye tana cewa,


"Kiyi hakuri Amal Dina Zaki iya,


Zaki iya insha Allah,


Allah zai kawo mafita sbd Shi kadaine yasan dalilin hakan,


Shine ya qaddara hakan,


Please sweetie karkiyi irin wannan kukan Zaki sake karyamun zuciya.


Amal bazata iya magana ba sbd kuka takeyi sosai Wanda takeson abinda ya danne maqoshi da zuciyarta ya fada tukuna tasamu damar borewa wannan auren dasuke magana Dan bazata taba iyawaba,


Bazata Yi wannan aurenba dasuke magana,


Bazata taba son aurenba bare wainda suke cikin rayuwar auren,


AQEEL ASAD fa suke magana,


Mata ne dashi harda budurwar 'ya,


Mutuminda mahaifiyarsa tayiwa tata mahaifiyar tsanarda ko kafiri batawa irinta.


Kokarin tsayar da kukan dayaci qarfinta takeyi ta dago da idanuwanta dasukai jajir harma da fuskarta ta kalli mommyn muryarta a shaqe tace,


"Mommy wallahi bazan iyaba,


Kisaka ya sakeni batareda min wahalarda juna dukanmuba,


Bazan iyaba Mommy,


Wannan ba aure bane fitinace aka hada kawai,


Wlh bana sonsa ko kadan nidai ko kallonsa bazan iyayiba a matsayin mijina sbd ban taba fatan auren me mataba kinsani bare shi da mahaifiyarsa bazata taba karbanaba kaman yanda bazan karba dantaba.


Mommy kisa ya sakeni banason auren indai dashine..


Rintse idanuwa Haj Zainab tayi tana girgiza kai ahankali murya a sanyaye tace,


"Kiyi hakuri Amal bazan iyaba,


AQEEL nada iko fiyeda yanda kike tunani akanki,


AQEEL shine Wanda ya daukeki a duniya ya rada Miki asalin sunanki,.shine Wanda yakesonki fiyeda yanda kowa yakesonki a duniya bayan Ni Dana haifeki,


Bazan iya tirsasaba sbd yayi iko akanki,


Ya zartar da wannan hukuncin ne sbd ya tabbatarda Babu Wanda zai iya yin hakan akanki bayan shi,


I'm sorry my princess Amma Nima duk yanda nake qin wannan auren nasan bazan sauya komaiba tunda yariga ya rataya Miki igiyoyin aurensa akanki.


Hakuri zakiyi mu rungumi wannan sabuwar qaddarar muga inda zata kaimu tukuna kafin Allah yakawo Mana mafitarta..


Sake fashewa da wani sabon kuka Mai tsananin qona Rai da zafin zuci datake Jin kamar zuciyarta zata Kama da wuta.


Kallonta Haj Zainab takeyi idanuwanta na kokarin tsayar da nata hawayen ta sake kamota zatayi magana AMAL din ta girgiza kai ahankali tana kokarin tsayar da nata hawayen itama tace,


"Mommy bazaki iya Bata Masa ba ko quntata Masa shiyasa bazaki iya cewa ya sakar Miki 'yarkiba??


Wane matsayi ne yakedashi Acikin zuciyarki Wanda yafi na ni 'yarki da Kika Haifa,


Shi din fa 'dan maqiyanki ne wainda Basu taba sonki ba bare kaunarki....


Cikin tsawa da Hana bayyanarda zafin maganar tata ta katseta da cewa,


"Shut up Amal,


Hankalinki zai Bata ne sbd auren Dole yafara akanki ne?


Bakece farkoba bakuma Zaki zama qarsheba,


AQEEL ya aureki ne sbd ya Isa dake,


Koni dana haifekin bazan iya hanasa ba bare ke da aka Haifa din,


Idan inada ikon warware auren zakima San anyi ne?da tun lokacinda aka daura Zan sa a warware din,


Karki Bari bacin rai yasa Naga laifinki sweetie kiyi hakuri nasan tako Ina Babu inda aka kyauta Miki Amma AQEEL nada matsayi da girma a rayuwata da zuciyata da ba ke ba koni ya aurar wa wani bazan iya bijirewa duk tsanata kuwa da abin bare ke,


Nace Miki komai zai daidaita


Zan samo Mana mafita Akan lamarin Amma ba irin wannan da kike tunani ba...


Sassauta muryarta tayi cikin sanyi da kulawa tareda kauna da soyayyar 'yarta tana kallon yanda Amal din ke kallonta kamar yau tafara ganinta cikeda mamaki da tsoron irin kaunar AQEEL ASAD Mai tsananin girma datake hangowa Acikin idanuwa da kalaman mahaifiyarta,


Wace irin kaunace wannan Mai tattareda mamaki da tsoro da baqin ciki tareda kishi take ganin mahaifiyarta nawa 'dan matarda tasan a duniya tafi kaunar masifa da hasara akan Zainab din.


Kasa cewa komai tayi sbd sanyi da jikinta yayi na ganin abinda yake neman shallake tunaninta,


Ahankali ta saka bayan hannunta ta share hawayenta dake gudu sun kasa tsayawa ta bude Baki a hankali tace,


"Mommy meyasa kike sonsa da yawa Haka?


Rufe Ido tayi ta bude tareda miqewa ta nufi kofa ta fice sbd tasan Amal bazata taba yarda da komaiba cikin sauki bare su nutsu su samo ganin inda hanyar bullewa take garesu da wannan auren Kamar yanda tasan mutuwarta dolece tasan umma da umman AQEEL din Koda zasu rasa lafiyarsu bazasu yarda da wannan aurenba bare har ayi tinanin mafita a natse,


Masiface kwance a qasa tasani,


Zasu tashi tsaye da kyau su tabbatarda wannan auren Bai 'daga daga inda yakeba,


Koda zasu rasa komai bazasu taba karban 'yarta amatsayin matar AQEEL ASAD ba,


They can go to Any length to Make sure Amal Idon Nera tabar rayuwar AQEEL ASAD a wulaqance Wanda itama Koda zata rasa komai da kowa bazata yarda su lalata rayuwar 'yarta ba kamar yanda suka tabbatarda tata tagama lalacewa tako wane bangare har Saida taqare a titi gidan karuwai Acikin karuwai da prison cikin masu manyan laifukanda ko labari Bata taba ji ba,


Idan har bazai warware aurenba to itama bazata yarda 'yarta tabar gabanta ba taje koinaba sai taga yanda iyayensa suka tarba auren tukuna,


Saita Gama ganin kalar haukar data shigesu akan auren sbd suna taba Mata yarinya wannan karon rigimar da ake neman magancewarce zata Gama girmama ta zama wani abin Kuma,


Ita Bata da damuwar duk yanda duniya zataji sunanta ya lalace sbd Daman qaurin sunan ne da ita


AQEEL ASAD din kawai takeji kada duniyarsa takoma abar bugawa a jarida Koda yaushe Amma tunda kusan hakan kowa ya zaba bazata quntata rayuwarta ta quntata ta 'yartaba


Aure dai an daura to zata zuba Ido taga abinda zai biyo baya daga garesu.


Ficewa tai dakin tabar Amal wadda itama kukanta ya tsaya sbd abinda ya tsaya ya danne Mata zuciya akan yanda mommyn ta zabi kasa baqanta ran AQEEL ASAD akan nata,


Bazata sake maganar komai Akan aurenba tunda batama yarda da aurenba Dan Haka suda suka daura Saji da maganar Amma Babu Wani aure da zata dorawa kanta.


Bayan fitar mommyn kasa taurin ran tayi wani sabon kukan ya yunquro Mata ahankali sbd anrigda anyi Mata wata irin cuta da illa a rayuwa Koda an warware sbd har abadanta AQEEL ASAD shine Wanda akasan yafara aurenta.


Kuka takeyi ahankali jikinta koina Yana daukan zafi da mutuwar jikin.


Mommy na fita Kai tsaye Palo ta sama uncle Lulu daketa amsa wayoyin Taya murna Babu qaqqautawa daga mutanenda duk sai daga baya suke samun labarin daurin auren Wanda Babu Wanda ya taba Tunanin zasu iya samun Saar mutum irin AQEEL ASAD ba ya shigo cikin ahalinsu ya zama sirikinsu ba sbd Shi din dasu Kamar doya da manja ne rayuwarsu tayi hannun Riga data juna nesa ba kusaba.


Wasu kuwa Kiran dasukeyi Dan tabbatarda labaran ne cewan Dagaske AQEEL ASAD ne yayi nasarar aure Amal Idon NERAr dasukaita burin auraba Dan cike burinsu na mallakarta ta zama tasu sbd son da kusan duk suke Mata da shaawar aurenta.


##MAMUH#


#LOVE/ROMANCE/MARRIAGE


#SISTERSLIFE


*_ZAFAFA BIYAR_*


*RUMBUN K'AYA*πŸ”₯


Hafsat Rano


*DAUDAR GORA*πŸ”₯


Billyn Abdul


*IDON NERA*πŸ”₯


Mamuhgee


*A RUBUCE TAKE*πŸ”₯


Safiya huguma


*KI KULANI*πŸ”₯


Miss xoxo


Littafi daya---400


Biyu---600


Uku----800


Hudu-----1k


Biyar din duka----1200


ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN


0022419171


Maryam sani


Access bank


Shedarka ta 09033181070


MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN


09166221261


πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ


*Ina yan uwa 'yan nijer?*


*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*


+22799643131


Littafi daya---450CFA


biyu---650CFA


uku----850CFA


hudu----1050 CFA


Biyar----1250CFA


*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*


*Thanks for choosing us*πŸ”₯


41


Kumun uzuri tafiya nayi sai a Daren Nan nasamu kainaπŸ™πŸ™πŸ™


Amma insha Allah har weekend zan bakuπŸ₯°


*_Arewabooks@Mamuhgee_*


41


SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!


Makarantar Lafiya dake garin Kazaure (Kazaure school of health technology) tana farincikin sanardaku cewa ta Kawo wani sabon tsarin karatu a saukake na part-time Degree da Diploma a wasu kwasakwasai domin ma'aikata masuson karin karatu da 'yan Kasuwa wanda basu da isasshen lokaci.


Kwasakwasan kamar haka:


DIPLOMA


1.Dental surgery Technician


2.Medical X-ray Technician


3.Health Information Technician


4.National Diploma in Biomedical Engineering


5.Public Health Technician


6. Community Health Extension Worker (Re-trainee)


7.Junior community Health Extension Worker (JCHEW)


DEGREE


1. Health Information Management


2.Public Health


3.English Language


4.Public Administration


5.Business Administration


6. Economics


7. Accounting


8.Computer Science


9.Mass Communication


10.Agricultural Economics


Domin karin bayani a tuntubi wannan Lambobin:08035298851, 07066542055 ko Azo haraban makaranta dake No 3 Emir's Palace road off Kano-Daura road Kazaure a jihar Jigawan Nijeriya.


********


Uncle Lulu kallon Haj Zainab yayi wadda ta zauna kusada Siddi ta kalleta tace,


"Ki kula da Yar uwarki tana cikin damuwa da zafin zuciya sosai


Ki rarrasheta kada ta sakawa kanta damuwa tajawa kanta ciwo


Insha Allah komai zai koma daidai.


Ajiyar zuciya siddi ta sauke ahankali tareda kallon Mommyn tace,


"Ok mommy Amma please kada ku takurata akan komai na maganar auren yanzu Kuma ni nakasa gane meyake faruwa gabaki daya Kamar nayi shekara bana taredaku nadawo na tadda wannan rikicikin da shigowar AQEEL ASAD rayuwarmu Kai tsaye,


Mommy akwai abinda ya Kamata na sani??


Girgiza Mata Kai tayi tareda cewa,


"Baby Babu abinda yafi kulawa da Yar uwarki yanzu sbd tana buqatanku keda Fareedah kune abokan shawararta Dan Haka kuyi kokarin Dan tausanta kada ta sakawa kanta damuwar da zata sakata wani halin I can't take that Nima wani halin Zan shiga.


Ajiyar zuciya siddi tasake saukewa tana cewa,


"Ok mommy Amma Kuma please kuyi abinda yakamata Kar a sake kawo maganar komai for now abari tagama ji da maganar auren tukuna Dan Allah.


Gyada Mata kai kawai Haj Zainab tayi sbd bazata iya doguwar maganaba sbd kanta dake neman juyewa sbd tsananin azabar ciwon dayake mata,


Komai ya cakude Mata a Rana tsaka batamasan Yaya zatayiba,


Batada wani sauran tunani daya wuce ta watsar da zancen itama tayita kanta da 'yarta sbd neman juyewa da kansu keyi Akan wannan sabon lamarin ba tsammani.


Tana buqatan nutsuwa itama tadawo kanta Dan tanaji hawan jini ma kawai ya Isa ya Gama da ita idan Bata koyi nutsar da kanta akan masifar su umma ba tinda qarfi da yaji sundawo rayuwar juna.


Shi kansa uncle Lulu ganin zasu dorawa kansu ciwo abanza suzo ayi biyu Babu gwara su nutsu subi komai ahankali kamar yanda Shi uban gayyar Babu ta inda ya damar da Kansa ya tattara kowa da wahalarsa ya zuba musu Ido,


To Suma zasu zuba Idon Amma dai Babu maganar wani tarewar Amal gidansa a ayanxu Koda yai magana shine maganar da Haj Zainab ta tsaya akai kawai.


Likita aka Kira Mata tazo gida ta dubata sbd kanta ya tsananta ciwo sosai.


Magani da drip aka daura Mata take bacci ya dauketa Mai qarfin gaske sbd shine kawai zai saukar da nauyin kanta da ciwonsa.


***Siddi da Anty Fareedah duk yanda sukaso Amal ta bari su zauna suyi magana da ita rufe dakinta tayi Bata buqatan kowa


Kadaicewa kawai take buqata sbd kukan datasha Mai tsananin gaske Wanda sai daga baya taji haushin kanta ma data tsaya rufe kanta a daki tana kuka akan Wanda ya nuna Babu abinda ya damesa da duk halinda kowa zai shiga akan lamarin.,


Tashi tayi ta nufi toilet ta tube Tai wankan da duk wunin ranar batayiba sbd yanda ranar tazo Mana a juye.


Wanka tayo tafito a nutsuwarta sanyeda bathrobe ash ta nufi gaban mirror ta zauna tareda qurawa fuskarta Acikin madubin Ido tana kallon yanda fuskarta tayi jajir sbd kuka gata fara Dan Haka sai tayi ja koina idanuwa Kuma sun kumbura kamar ba itaba data tsani kumburin fuska Koda na barci ne.


Ahankali ta sauke numfashi har lokacin idonta akan fuskarta datake Mata zafin kalla,


Yanzu itace ke yiwa namiji kuka Haka ta fita hayyacinta a wuni daya???


AQEEL ASAD duk zafin kanka da Jin kanka zaka iya mallakan Amal Idon Nera kake ganin?


Me kake daukan kanka?


Kanada komai da zaka mallaka macen da kaga Dama kake gani?.


Amal Sanda ba irin taka bace sbd nice nake juya namiji bashine ya Isa ya juyaniba da har zaka doramun aurenka batareda sanina ko yardataba.


Mai ta dauka ahankali tafara shafawa jikinta tana dauke kallonta daga kan fuskarta.


Tana gamawa Riga da wando ta saka ta Dora doguwar jilbaab akai tayi sallar azahar data wuceta tana idarwa bata bar gurinba akai sallar laasar ta miqe tayi.


Bayan tagama sallah jiki ba qwari ta zare jilbaab din ta maida tadawo ta zauna kan sofa tareda janyo wayarta data kashe ta kunna.


Sakonnin da Bata Gama budewaba dazun ta sake cin karo dasu Acikin notifications dinta.


Deleting nasu tayi gabaki daya batareda ta budesuba.


Kokarin Hana kanta shiga kowane gurinda zataci karo da zancen tayi ta shiga WhatsApp dinta inda acan tafara cin karo da sakonnin Taya murna da neman shiga daga yawan course mates nata maza da Mata daketa mamakin auren nata...


Sarai sunsan waye mahaifiyarta da sunanta akan harkarta Kuma sunsan kuma waye AQEEL ASAD Dan Haka suke mamakin yanda akai wannan hadin combination din duk da sunsan AQEEL ASAD Yana cikin wainda sune kawai zasu nema auren Amal Idon Nera Yar Zainab Idon Nera.


Babu Wanda ta amsa sakonsa sai kawai takuma kashe wayar tareda jefarwa akan gadonta ta zame ta lafe jikin sofar tana kokarin Hana kanta zubarda hawayen dake gangarowa kan fuskarta.


Bata fitoba har dare tana dakinta saidai Bilkisu takawo Mata abinci Mara nauyi Wanda shima Bataci ba Haka ta wuni tana yaqi da zuciyarta daketa karyewa da kuka Wanda take Hana kanta sbd qin yarda itace a qasan.


Haka ta kwanta batareda kowa yagantaba


Su siddi da Anty Fareedah sunyi magiya da rarrashi akan ta sauraresuma Amma Sam ta nuna Bata buqatan ko kalma daya data danganci auren Dole suka barta ta sauko tukuna.


Haj Zainab ma Bata farkaba sai dare zuwa lokacin Kuma kanta ya Dan sake sosai tadawo hayyacinta yanda ya Kamata Dan Haka itama wankan da bataiba a ranar tashiga tayi tareda alwala tafito tayi sallolinta


Siddi ce da kanta takawo Mata abinci cikin kulawa taci Tasha magani ta tambaya Amal ta sanar da ita Tana lafiya Amma dai tana buqatan space shiyasa kowa yabarta ta sauka tukana batareda an takura Mata.


Ajiyar zuciya Haj Zainab din ta sauke tana fatan kan Amal dinta ya sake kamar yanda nata ya sake Mata take jinsa yanzu Babu Wani 'daga hankali da tashin hankali,zasubi komai a tsanake Babu daga sakawa Kai ciwon kai tasan suna zaune su umma zasuyi abinda zasuyi su kashe maganar sai kowa ya huta shikenan.


****AQEEL ASAD daga asibiti very late ya Isa gidansa batareda yaje ya dubo umma ba yashigewarsa sbd kusan komai ummansa ke akai umman ce jagorar ko wace irin aikin rashin lurarta,


Securities din gabaki daya a Dan kame batareda zaqewaba sukai congratulating nasa akan auren da yayi sbd lura dasukai auren da alama Yana tafe da hargitsi duk da suna tunanin ko madam din tasa ba lallai tasaniba dan kila itama ta some kamarsu Haj

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login