Showing 123001 words to 126000 words out of 149977 words
gabar
da abinda Bata taba kawo tinaninsa akantaba ko a
mafarki yahau kanta,
Innalillahi me zatayi?
Ya zatayi?
Me zatace?
Ko yanda ake cire ciki da inda ake zuwa acre din Bata taba saniba tayaya zata fara fuskantar wannan tashin hankalin daya girmi tinaninta.
Tafiya sukeyi batareda Ahmed yasan Ina suka nufaba sai yawon gari da bulayi yakeyi dasu.
Wani masifaffen nauyi kanta ya dauka tareda zafi ta rasa Ina zata saka kanta,
Wayarta taciro a karo na farko data Nemo numbernsa dakanta batareda Tama saniba ta saka kiransa cikin sa'a a daidai lokacin suke fitowa daga airport malam
Rabiu ya daukosa tareda Al-Amin.
Ganin Kiran nata shima a wavarsa a karo na farko yasashi sauke numfashi Mai sanyi sd vasan Dole akwai wani babban abin ne.Daukan wayar yayi tareda dorawa kunnensa kafin yayi magana ta sakar Masa wani kasalallan kuka tana rintse idanuwanta dasukai jajir ta.
Ahmed na Jin hakan ya nema guri Mai kyau yayi parking ya bude motar yafito yabata guri.
AQEEL najin sautin kukanta ya sake sauke wani nannauyan numfashin Kansa na daukan dumi ya kalli
Al-Amin da Idanuwansa dasuka Dan sauya take ahankali yace,
"Kira Ahmed kaji inda suke muje can yanzun Nan.
"Okay Sir" yace Yana Nemo numbern Ahmed cikin rashin Bata lokaci ya saka kiransa,Ahmed dake wajen motar daga can gefe Yana ganin
Kiran Al-Amin ya dauka da sauri cikin girmamawa kafima yayi magana A -Amin ya katsesa da jeho Masa tambayar inda suke,
Shima Ahmed din cikin rashin Bata lokacin yafada ta guraren dasuke
malam Rabiu na Jin inda Ahmed ya fada ya sake taka motar yana qara Mata speed.
Har Suka iso gurin bayan tafiya Mai Dan tsayi ba sosai ba Bai kashe wayartaba tana kunnensa Yana sauraran kukan datakeyi Masa ahankali takasa cewa komai itama.
Suna parking Al-Amin ya fito daga gaban motar zai bude Masa Bai tsaya jiransaba harya bude ya fito ahankali cikin nutsuwa bazaka iya gane abinda zuciyarsa da Ransa suke cikiba na yanayinda yashiga jin kukanta.Ahmed ma da sauri ya garasa motar ya bude Masa bayan motar inda take zaune daga dayan bangaren
Yana Masa barka da dawowa amma Bai sakaran
Yama jisa ba.
Yana shiga Ahmed ya rufe Al-Amin ya kalli malam
Rabiu yace sutafi ya ajesa gida yaje ya maida motar.
Yana Shiga motar ta dago jajayen idanuwanta ta kallesa tana sake fashe Masa da kuka Mara garfi
ahankali ya janyota jikinsa ya rungume Yana kokarin
Hana Kansa rikicewar gangar jiki gabaki daya Dan yariga yashiga rikicewar zuci da ruhi daga lokacinda
•vail kukanta vasauka cikin kunnensa ta wavar
Kuka take Masa sosai ahankali harda shesheka
Baice komaiba sai sake shigar da ita jikinsa yay Yana shata bayanta bugun zuciyarsa na wani irin tsananta sauya bugawa sbd ita din.Kiran Ahmed yayi yazo ya jata motar Suka nufa hanyar gidan karatunsa Yana kallon time sai alokacin
5 na yamma tayl.
Har suka Isa Bata Dena kukanba harta gaji jikinta yayi sanyi hawaye kawai takeyi.
Daukota yayi da Kansa daga motar ya kawota har
Palo ya ajiye ya zauna tareda janyota ya zaunar gefensa tareda rigo hannayenta duka biyun cikin nasa Yana kallon idanuwanta dasuka sauya sod kukan ya sauke Ajiyar zuciya da numfashi a lokaci daya ya Ciro handkerchief dinsa Mai gamshi ya fara share Mata hawayen ya sake kallonta cikin wata irin kasalalliyar murya data Gama kashe Masa jiki da halinda ya ganta aciki yace,
"Kuka va lsa Haka,
Tell me meya faru?
Menene kikewa wannan kuka?Jikin naki ne?
Dr tayo Bata zo bane.
Girgiza Kai tayi ahankali hawayenta na sake saukowa cikin qunci Mai tsanani da damuwa.
"Mami ta gano kina kwana watara baa gidan bane??
Was hawaven masu zafine Suka Kuma gangaro
Mata ta rintse Ido tana Jin Ya zatayi da rayuwarta.
Sake sarke hannayenta Acikin nasa yay yana kallonta cikeda kulawa yace,
"Menene?
Hakan ne?
Mami ce???
Uncle ne ko su Anty Fareedah?
Waye ya gano? Meyasa Zaki damu idanma hakan ne a gurin Mijinki kike kwana waye baisan me ake nufiba da matsayin mili da aure acikinsu??
Girgiza Masa Kai tayi tana Nemo kuzari da qarfin halin dazata iya sanar dashi abinda yake faruwa din amma
bazatama iya furta kalman ciki ne ajikintaba.
Shirunta yasashi yin shirun shima sai kawai yaci gaba da rarrashinta Yana taba goshinta zuwa wuyanta yaji temperature dinta is normal sbd masifar data kunno
Mata ta warke zazzabinta take.
Qarfe 6 ta nace akan gida zata ta fito da Kansa yakaita har gate saidai ta hanasa shiga sbd mommy na gida ta hango motarta a harabar gidan.
Bayason bata ranta musamman yanzu datake cikin wannan halin Dan Haka sai kawai ya juya din ya tafi bayan ta shige.
Yana juyawa Kai tsaye Al-Amin yakira ya tambayesa
Dr tayo batazo ta duba Amal din bane?
Tazo" ya basa amsa Kai tsaye Yana sake basa
tabbacin zuwanta sbd tace saisunie asibiti da Amal
din ma amma batace komaiba Bayan hakan.
Kashe wayarsa yayi ya ajiye tareda taka motar da
speed Mai Dan garfi ya dauki hanyar asibitin sbd
bazai iva Bata lokacin nemanta a wayaba zai sameta
yaji abinda ya samu matarsa.
Itama tana shiga ba kowa a gasa suna sama
acan dinma tana hawowa ta samu duk suna Palo
kowannensu zuba Mata idanuwa sukai sbd yanayinta
daya nuna Batada lafiya da Kuma Jan da idanuwanta sukal.
Mommy kafeta da idanuwa tayi sbd takasa gane kan
Amal din gabaki daya kwanakin,
Komai nata ya sauya yanzu Kuma ciwo yaqi ci yagi
cinyewa ga jan Ido Kuma yau.Kiranta mommyn tayi tareda cewa tazo.
Dakatawa tayi daga inda take tsaye tana kasa hada
Ido da mommyn ahankali tace,
"Mommy daga asibiti nake banajin Dadi sosai please abari na Dan nutsu sai nazo Dan Allah Mommy."
Qarasa zancen tayi idanuwanta na cikowa da hawayen data kasa riqewa.
Tashi hankalin Hai Zainab da siddi yay ta taso ta nufota tana rigo hannuwanta tace,
"Meyake damunki ne Amal?
Meyasa kikaje asibitin ke kadai ai nace nice Zan kaiki sod musan Meye wanna sabuwar matsalar data bullo,
Me akace a asibitin to?Me aka gano Yana damunki???
Hawayen dake ciko idanuwanta ne suka gangaro takasa cewa komai sai kawai tace,
"Ciwon maratane ya taso shiyasa naje,
Yanzuma ciwo nakeji sosai mommy inason na kwanta.
Kallon Hai Zainab siddi tayi cikin kulawa da tausayawa tace,
"Mommy abarta ta huta da alama tanajin jikin please,
Idan ta tashi ta huta ciwon ya Dan fada anima sai kiyi maganar da ita.
Kyaleta Haj Zainab din tayi ta wuce dakinta ganin da gaske din da alamar Jin jiki atareda ita.Tana Shiga dakinta zubewa bakin gadonta tayi tareda sake sabon kuka Mara sauti tana rinse idanuwanta dake radadin kukan datasha.
A dakin sai data Jima tana kukanta kafin ta tashi tashiga toilet tasake wanka tayo alwala tayi sallar magrib tayi karatun Qur'an kadan tasamu zuciyarta ta
Dan sake tasamu qwarin gwiwar fitowa tana Dan nuna dauriyar samun sakewa Acikin familynta.
Abinci sukaci Banda ita da fruits kawai Tasha ganin
Mommy na kallonta sai ta Dan sakura abincin tana basarwa.
Fira sukai a Palo dukkaninsu kaman yanda Suka Saba
Amma ita tana gefe kwance tareda Fahat suna firarsu kaman vanda Suka Saba Amma shine Mai surutun yau sauraronsa kawai takeyi.
Suna zaune suna firar saishi Bilkisu ta bude Masa kofar dayayi knocking Yana shigowa dukkaninsu Suka gaidasa Banda Amal datake neman rikicewa bd idanuwansa daya kafe akanta batareda damuwa da
Maminsa da sauran jamaar gidan nagurin ba.
Jin idanuwansa har lokacin akanta yasata dago nata da Basu koma daidaiba har lokacin ta Dan saci kallonsa sai gashi idanuwansu yashiga cikin na juna ta janye nata tana kallonsu Anty Fareedah da hankalinsu ke kan zancen dasukeyi na wani kayan da
zasu siya a waya.
Gurin mommy da uncle ta maida kallonta sukuma magana sukeyi dashi bilhaqqi batareda sun lura da idanuwansa na kanta ba.
Sake kallonsa tayi ganin kallon nasa kusan ya banbanta dana koyaushe..Wani tunani ne yashigeta na ko Dr tayo tayi magana dashi take gabanta yay wani irin mummunan faduwa jikinta ya dauki rawa a boye tasake kallonsa taga irin kallon dayake binta dashi idan Bata bar gurinba zai iya tasowa ya dawo gurinta agaban kowa Dan Haka ta janye Fahat daga jikinta ahankali tareda miqewa tsaye tana gin sake kallon gefensa ta daga gafafu a sanyaye cikin toro da fargaba ta nufi stairs zata
Haye..
"MARYAMAH" ya ambaci sunanta cikin wata irin nutsuwa hankali kwance Wanda fadan sunan yasa dukkaninsu kowa ya juvo Yana kallonsa sbd Babu
Wanda ya taba kiranta da sunan sun ma manta da ance sunan nata na asali MARYAMAH ne Dan har lokacin Hai Zainab Bata fadar sunan a bakinta Koda na wanine daban ta yafe fadarsa.
Ita kanta cak ta tsaya bugun zuciyarta na wata irin tsananta take idanuwanta suka ciko hawaye matugar ya bude Baki yayi maganar data danganci abinda take boyewa to zata iya yanke jiki agurin tsabar tashin hankali da mummunar kunyar duniya.Fatanta da adduarta a lokacin shine ya kasance baiyi magana da Dr tayo ba Dan kuwa tsabar tashin hankalin data Shiga yasa ta manta Bata fadawa Dr tayo din karta sanar da kowaba.
•Ha Zainab kallonsa tayi lokacinda ya dawo da fararen idanuwansa dasukai wani irin sanyi akanta Yana kallonta Kai tsaye yace,
"Amal zataje gain likitan da nay alqawarin zataje akan matsalarta,
Ta shirya gobe da safe zamu wuce Zan kaita da kaina...
Daga Hai Zainab harsu siddi da Anty Fareedah da uncle Lulu kallonsa sukai
Ita kanta Amal din juyowa tayi ta kallesa cikin yanayi biyu sod tariga ta saddakar maganar cikin jikinta zaiyi saikuma taji wanna zancen Wanda shima ta tabbatarda idan akaje duk likitan da zata gani take zai tabbatar da cewa akwai ciki ajikinta.•Hai Zainab kuwa Dadi da akasinsa ne tareda mamakin Yaya Amal zataje taga likita Babu kowa atareda ita saishi Kuma bawani sabo ko magana sukeyi da junaba babu yanda tafiyar zata yiyu a hakan
Dole saidai idan ta shirya ta bisu kokuma Fareedah ko
Siddi.
Magana zatayi uncle ya dakatar da ita da cewa,
"Amal dawo zo.
•juyowa tayi ahankali jikinta na sake mutuwa da wannan abubuwan wani bayan wani datake shiga,
Shikuma uncle ko ya taba ganinsu ne kila shiyasa shima yace tadawo.
Innalillahi wanna ilayhi rajiun" tafada cikin ranta hannuwanta na rawa ta saci kallon AQEEL dayake kallonta Kansa tsaye da alamar yariga yagama magana takuma sani tafiyar Nan sai Allah idan baayita ba Amma itama batason zuwa koina yanzu ta cikin jikinta take tukuna.
##MAMUH#
* ZAFAFA BIYAR *
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
65
Kasa qarasowa sosai tayi tsakiyar palon ta tsaya daga gefenda su Anty Fareedah suke tana Dan sauke kanta qasa,abinda yasake bawa kowa mamaki kenan ganin kanta a qasa
Abinda Basu taba ganiba kenan,
Haj Zainab AQEEL ta maida idanuwanta akansa ta kalla sbd Shiga mamakin wannan halin na Amal datake tunanin da ace sunada kusancin da juna da tabbas zatace akwai saka hannunsa a sauyin da aka samu na wannan dabiar da zaa iya sakawa cikin kyawawan dabiu saukar da Kai gaban manya.
Shi kansa uncle Lulu hakan datayi sai yasashi manta ma mezai fada cikin Dan mamaki yace,
"Amal Yaya dai?
Akwai matsalane??
Dagowa tayi jikinta na sanyi da tambayarsa ta kasa kallonsa shima tace, "lafiya kalau"
Shirun da AQEEL ASAD yayi musu tareda zuba musu Ido Yana jiran abinda sukeson fada suke zagaye zagaye yasa dukkaninsu Dan rudewa da rashin sanin yanda zasu Masa bayanin yabari zuwa ko qarshen watan Nan ne sai Amal din tareda Siddi mommyn tasake kaisu.
Haj Zainab dince tayi karfin halin kallonsa Kai tsaye tana cewa,
"Qarshen watan Nan zamu koma da siddi insha Allah inaga abari lokacin yayi mutafi taren kawai.
Cikin sanyi da nutsuwa tareda girmamawa harma da kulawa yace,
"Ai Mami ba likita daya zasu ganiba,
Wanda MARYAMAH din zata gani daban ne so inaga ba amfanin jiran ta shirya goben insha Allah.
Ajiyar zuciya Haj Zainab ta sake sbd har cikin ranta batason zuwan yanzu sbd wancan likita taso Amal din tagani musamman yanzu da period din ya canja yayi latti da wuri takeson sanin menene wannan sabuwar sauyin da aka samu duk da ba dabiarta bace daddigin yaranta Dan ta yarda da abinta kawai dai ita kanta yagama juyewa yanzu Bata gane komai sosai.
Kan Amal dataqi sake kallon gefensa yayi cikin nutsuwa da kulawa yace,
"Ki Gama shirinki kafin 10....
Kallonsa ta juyo tayi tareda Dan juyawa ta kalli su Anty Fareedah harma da mommyn dake jiran ta watsar da zancensa a gurin ta wucewarta kaman yanda ta Saba har umman na fargaban yanda Amal zata karbi zancen Dan Daman ita harda sanin Amal din bazata yardaba yasata kame Kamen yabar tafiyar su saisu tafi da ita sbd abune Mai wuya Amal ta Amince tafiya dashi din tunda haryanxu taqi kallonsa a matsayin Mijinta.
Kallon mommynta tayi da Uncle Lulu ta bude Baki cikin Dan matse fuska tace bata buqatan zuwa koina yanzu abarta kawai.
Tanajin idanuwansa akanta lokacinda tayi maganar.
Jin wannan maganar yasashi miqewa batareda yasake cewa komaiba akan maganar yayiwa Maminsa da itama takeson ya tsaya ayi maganar dalla dalla asan abinda zai yiyu acikinta Dan tafi kowa sanin rigimar Amal din, Saida safe yamasu tareda uncle ya fice daga palon Yana Hana Kansa janyo matarsa a gurin ya rungumeta ko zai dawo cikakkiya nutsuwarsa daya rasa na Abinda Dr tayo ta sanar Masa.
Yana ficewa Haj Zainab ta kalli Amal data Gama kasheta da mamaki tace,
"Kinji abinda ya fada ai,
Ki bude Baki kiyi magana ki roka yabari sai lokacinda zamu din kiga wancan likitan Amma kin tsaya wani Sumi Sumi,Wai Ni mema ya sameki ne da wannan dabiar??
Meya samu duka Baki da kuzarin naki be Wai?
Siddi data kasa rike nata mamakinta Kai tsaye tace,
"Mommy shakkarsa takeyi fa,
Kina ganin AQEEL ASAD dinnan bafa Wasa ko fuskar Wasa a lamuransa,
Gashinan karfi da yaji yaso hanata karutu Allah yasa ya sassauto yanzu gashi tsakanin gaskia da gaskia ya hanata driving da kanta saidai driver duk inda zata kaman tsohuwar mace,
Mami kema fa kina Dan shakkar wannan fuskewar ta 'dan ki bare mu,
Nidai gaskia karma asani tafiya binsu bazan iya binsa ba Kinga ko kallon Mata bayayi itama datake matarsa Baga Yana kallonta bare,
Saidai ko Anty Fareedah zataje Ni Abuja ma zankoma satin Nan.
Amal datayi nisa a tinani batama San gardamar dasukeyi ba Dan kuwa Anty Fareedah ma duk da tanason zuwa ko Dan taga likitan itama haihuwar takeso tasake ko dayace kamar me Amma itama hakanan take shakkar tafiyar Dan zaiyi wuyama yaje da kowa tunda iya Amal din yace.
Itama dai zuqewa din tayi ta nuna gaskia bazata iya zuwaba Suje Ana fada bazata iya komai akai ba sbd tasani Sarai Amal zafin Kai zata nuna Masa shima nasa zafin kan ya shanye na kowa da alama, gwara ta Kama kanta bazataba gaskia.
Shiru mommy tayi sbd itama ba iya zuwan zatayiba a gabanta Amal ta ringa Masa abinda taga dama takasa hanata yaga rashin mutunci da kaman rashin tarbiya a tareda ita.
Uncle Lulu kuwa Kai tsaye yabada shawarar abari suje din idan Amal taga ba kowa zata iya Dan sassauta fushi da zafin auren idan har zata samu lafiya ai komai Mai sauki ne bare a tinaninsa AQEEL din dawowa zaiyi idan ya kaita Dan bazai iya zama acan ba tsawon lokaci tunda akwai ayyuka na office Dana mutanensa daya Bari.
Amal Suka kalla ganin tayi nisa a tinani sbd tana cikin wani matsanancin Hali na rashin qaqanikayi akan abinda yake tareda ita,babban tunani da wasi wasinta shine idan AQEEL ASAD din yasan da cikin?
Tana tsoron ace yasan da maganar Dan bataga dalilin wata tafiya zuwa ganin likita ba yanzu bayan shi da ita sunsan ba lallai ta sake ciwon marar ba Idan harda gaskene bazaka sake ciwon mara ba sosai after first sex zuwa uku haka,ita da bama zata iya cewa so nawa hakan ya faru da itaba.
Ganin damuwa sosai atareda ita sai Haj Zainab din ta sauke ajiyar zuciya tana tunanin damuwa da quncin tafiyar ne Dan Haka ta Dan rarrasheta tabata qwarin gwiwar tafiyar tareda yimata fadan kada Tai Masa abubuwan da Basu Kamataba ta lallaba ta danne zuciyarta da duk fushi da zafin datakeji akan auren a Nemo Mata lafiyarta datafi komai.
Amal har lokacin bata wani gane maganganunsu sbd abinda yake cikin kanta ta rasa nutsuwa harma da hankalinta takeji,
Qafafunta ba kuzarin komai ta ja kanta ta Isa dakinta tana Shiga ta zauna bakin gado tareda tallafe kanta dake sarawa Mai tsanani tana rintse idanuwanta.
Ta Jima ahakan saiga siddi da Anty Fareedah sun shigo suna Dan kokarin tsokanarta da Wasa da cewan sune zasu hada Mata kayan tafiyar farko da miji.
Siddi datafi kowa yanko zance cewa tayi da itace bazata dawoba saita sakashi ya San ita din mace ce ba kaman matarsaba Dan kuwa ita tun Randa taga matarsa ta Renata batajin matar tasan abinda takeyi sbd alfahrinta yasa take tunanin Yar matsiyata ce yake aure.
Anty Fareedah ma zancen ta karba sunayi da Siddi
Amal din dai takasa ko motsawa Bare tankawa qarshe zamewa tayi ta kwanta a kife tareda rintse idanuwanta tanajin ciwon kanta na qaruwa.
Bata San lokacinda Suka Gama yamutsa Mata daki da sunan hada Mata kayanta ba suka fice.
Da asuba daqyar ta iya bude idanuwanta ta tashi jiki ba qwari ta nufi toilet tayi brush da alwala ta fito tayi sallah Takoma ta kwanta har lokacin da ciwon kai atareda da ita.
Bata samu Takoma bacci ba sbd tinani da damuwa Mai tsananin gaske,
Ta rasa tinanin yi ko Wanda zata fadawa ta rage nauyin zuciyarta akan cikin dake jikinta,
Idan da gaske AQEEL ASAD yasan da cikin me zatayi Dan batajin zata iya kallon mommynta dasu Uncle da cikin nanba idan suka sani,
Mezatace musu?
Yaushe?Ina? Tayaya? Duk a wane lokacin hakan ta faru zasu tambaya
Amsar da itama batasan me zataceba.
Hawaye ne suka gangaro Mata daga idanuwanta dasuka kasa komawa daidai daga lokacinda tasan tanada cikin har yanzu.
Hawaye taci gaba da tsiyayar daga kwance tana Jin zuciyarta na nauyi Dan batada makamar wannan lamarin,
Ita ko tunanin Ana zubarwa Bai zo kanta da tinanintaba Dan batasanma ta inda ake zuwa a zubda dinba.
Wayarta ce tafara ringing a hankali ta da bude idanuwanta ta kalli inda wayar ke ajiye gefen pillow dinta.
Tana ganin shine Mai Kiran sbd zuwa yanzu ta haddace numbernsa Amma batai saving ba,
Jin tayi jikinta ya dauki sanyi da zafi lokaci daya Kuma taba buqatan Wanda zatayi maganan dashi kafin kanta da zuciyarta su buga.
Daukan wayar tayi tareda dorawa kan kunnenta tayi shiru hawayenta na gudu.
Shima shiru yayi ahankali Yana sauraran yanda sautin numfashinta dayake bayyanarda kuka takeyi ahankali Mara sauti.
Wani nannauyan numfashin Mai sanyi da nutsuwa ya saki tareda Dan rufe idonsa ya bude cikin sanyi ahankali yace,
"Wannan kukan zai sakaki ciwon kai fa,
Ki shirya yanzu basai 10 dinba ganinan zuwa na daukeki bazan iya wannan jiranba,kukan Nan naki is driving me nuts..
Kawai sake Masa sabon kuka Mai qaramin sauti tayi batareda ta saniba tana cewa,
"Banason zuwa koina,
Ni kaina ma fashewa zaiyi, zuciyana ma ciwo takeyi komaima banaso Ni.......fashewa tayi da sabon kuka tana rasa yanda zatayi