Showing 54001 words to 57000 words out of 149977 words

Chapter 19 - IDON NERA BY MAMUHGEE CMPLT.txt

25 Nov 2024

6521

kawo hardashi a wannan zaman?


Koma menene batada alaqa ko wani hadi dasu Dan Haka Babu amfanin tabari ya ganta,..


Rawa zuciyarta da jikinta ke dauka tareda wani irin sanyi na shekaru data Dade batajiba,


Rintse idanuwanta tayi cikin wani irin nauyi da zuciyarta ke sauka Mai qarfi,


Bata so ko buqatan sake kallonsa a yanda takeji zuciyarta na bubbugawa da da sauri da karfi.....


Tsanananta tarinta yayi Wanda ya Hadu da bugun zuciyarta dayake qarfi da sauri....take tafara neman fita hayyacinta.


Da sauri uncle Lulu ya Kamata suka miqe sbd Dole zaman ya wargaje sbd gabaki daya ta fara fita hayyacinta idanuwanta tini sukai jajir hannuwanta sai rawa sukeyi.


Kai tsaye aka miqawa lauyoyinta bayanan matsayar zancen da aka Kai Wanda akaso karantawa gaban kowa a zaman Wanda take nuqatar saka hannun amincewa Dan Haka tunda zaman ya lalace sbd zuwan tsautsayin sai aka bawa lauyoyinta daga baya ta karanta su saka hannu itada Lulu lauyyinsu su dawo dashi a miqa kotun shikenan.


AQEEL ASAD Wanda ya kasa dagowa ya kallesu sbd ba halayyarsa bace yawan kallon bare Kuma ga mace irin wannan dayaji Ana fada,


Yanada kiyaye ganinsa akan abubuwan da kallonsu zasu damu Kansa da zuciyarsa shiyasa duk abinda yasan baida mahummanci kokuma zai taba Masa nutsuwar Kansa baya kalla sbd kaucewa damuwa da ciwon kai.


Koda IDON NERA tayi nata bayanin kwata kwata Bai dagoba hakama jinsa ba sosai yake akantaba...


Miqewa sukai Lulu na gefenta Barr Salahudeen na dayan gefen da handbag dinta a hannunsa sai sannu suke jera Mata tana dafe da kirjinta dake zafi da nauyi matuqar gaske kamar zai fado...


Tana gap da kaiwa kofar ficewa data matsu tabar dakin sbd suffocating takeji....


"MAMI"


Taji Nutsatsiyar muryarsa ta sauka akan kunnuwan duka Wanda yake dakin..


Babu Wanda yajuya ya kallesa sbd tunanin waya yakeyi
Itakuma datasan menene Bata juyoba ta wucewarta Kai tsaye batareda ta nuna alamar Jin sunan ba..


Motarta ta nufa har lokacin hannuwanta da kirjinta rawa sukeyi Kuma tarin ya sarqi makoshinta sosai ta yanda ko magana Bazata iyaba.




Kasa yarda da idanuwansa yayi alokacinda ya dago yaga matar da batada bambamcin kamanni da Maminsa,


Baisan lokacinda bakinsa ya furta kalmar Mamin ba,
To Amma meyasa ta dakata alokacinda ya Kira sunan kafin daga baya ta wucewarta Bata juyoba....




Miqewa yayi da sauri ya nufi kofar yabi bayanta da sauri Kansa na daukan wani irin zafi da juyawa,


Yana gap da Ida jikin motarta Yana kallo tace aja motar awuce.




Maminah ce wannan da gaske?
Maminah ce nake gani?
Am i hallucinating?


Dafe Kansa yayi daya Wani irin sarawa Yana sake daukan zafi...


Morarsa ya nufa kai tsaye da drivernsa harya bude Masa.


Yana Shiga cikin wata shaqaqqiyar murya yace,


"Muje office yanzu Nan.


Jan motar Rabiu driver yayi cikin Dan speed sbd ganin yanda Mai gidan nasa yake kamar a zafafe.


Wayarsa ya daga ya saka Kiran PA dinsa Kuma na hannun damarsa Al-Amin tajudden.


Al-Amin na daukan wayar Kai tsaye yace,


"Ina son bayanan komai da hoton Idon Nera yanzu Nan..


Ok done Sir" Al-Amin din yace Yana janyo Apple tab dinsa dake gefensa yafara dubawa kafin ya saka Kiran Wanda zai Basu sauran bayanan komai da bazai samu a internet ba.


AQEEL ASAD da yagama fita gabaki daya tinaninsa akan lamarin dayake kamar kyaftawar ido a mafarki ace yaga Maminsa,


Maminsa fa yake tunanin yagani...


Shi gabaki daya bayama kawo a matsayin datake din idanma mamin tasa ce,
Sam zancen wata karuwa ko karuwai ya fita Kansa shidai fata da buqatan sanin itace 'dince kokuwa.


Motarsa na parking cikin harabar babban gidansa ya fito ya nufi sashen mahaifiyarsa Kai tsaye kaman yanda ya Saba duk ya dawo saiya fara zuwa ya gaidata yake Isa nasa sashen sbd ba lallai ta sake ganinsaba sai gobe Kuma Daman a wuni kafin ya fita yake zuwa su gaisa sai Kuma idan ya dawo.


Wayarsa ce tayi ringing Yana gap da Isa palon ummansa
Ya daga wayar cikin nutsuwa..,


"Sir I just forwarded you all the informations.


Kashe wayar yayi tareda bude sakon,


Hotonta yakeson gani kawai kafin sauran informations din..


Yana saka qafarsa ta dama a palon Haj Maryamah dake zaune ta zuba Masa ido tana jiran shigowarsa adaidai lokacin hoton Zainab ya bude fes akan screen din tsadaddiyar wayarsa..cak ya tsaya batareda ya qarasa saka qafarsa cikin palon ba.


Wayar ya zubawa fararen idanuwansa dasuka sauya atake,


Komai nasa tsayawa yayi cak idanuwansa suna qara sauyawa,


Kasa motsawa yai sbd gabobinsa da zuciyarsa da suka tsaya cak na wucin gadi...


Kallonsa Haj Maryamah takeyi cikeda mamaki tana ambatar sunanta ganin yanda yayi kamar Wanda yaga matacce yadawo duniya...


Bayajin komai bare yaji sunansa da umman ke Kira...


Miqewa tsaye tayi cikeda tsoron daya cika zuciyarta itama na ganinsa a wannan halin zuciyarta da jikinta na sanyi ta nufosa....


Bata qarasaba ya juya ya koma hanyar daya shigo ta fita idanuwansa na kadawa jajir..


Cak ta tsaya itama daga inda take batareda ta qarasa inda ya Bari dinba jikinta na wani irin sanyi zuciyarta na Shiga tsoro Haka kawai.


Jamilu driver na kokarin Isa gate gurin securities yana juyowa ya hango Mai gidan nasa tafe
da sauri ya juya ya Isa motar ya bude Masa Yana bude Baki zaiyi magana AQEEL ASAD ya katsesa Kai tsaye da cewa,


"Ikeja GRA right now..


Ok Shaykh.


Rufe kofar yayi ya zagaya da sauri ya shiga tareda tayarwa ba Bata lokaci da ribas ya fita gidan suka hau titi da wani irin gudu suka Kama hanyar ikeja GRA Kamar yanda Al-Amin ya turo Masa address din.


Hotonta ne yake yawo cikin Kansa da idanuwansa,


Rintse kyawawan idanuwansa dasukai jajir yai wani daci dake zuciyarsa Yana gauraya bakinsa tareda qafar da yawunsa dasukai daci.


Babu yanda Maminsa zata koma a duniya ya kasa ganeta,
Shekarun da sukai a rabe bazasu taba goge masa asalin kamannintaba dasuke Zane a zuciyarsa da rayuwarsa duk canji da sauyawar da zatayi.






****Haj Zainab kuwa suna baro gurin Kai tsaye gida suka nufa zuciyarta na sake daukan nauyi da wani irin 'daci data manta yanda yake a zuciya.


Lulu daya shiga damuwar halinda ta Shiga din ya kalleta Yana sake tambayarta ko zasu tafi asibitin ne.


Ahankali ta girgiza Masa Kai tana kokarin dawowa hayyacinta sbd ganin yanda ya damu saidai Amon muryar AQEEL ASAD ya daki zuciyarta mugun dukanda takasa daidaita kanta.


Suna Isa gida tayi bedroom dinta da sauri ta rufe kanta tana dafe zuciyarta dake zafi da radadi.


Siddi ce dake zaune palon ta miqe tabita tana Kiran sunanta cikeda so da kulawa tana cewa,


"Mommy are you ok??
Mommy meya sameki?
Mommy please meyake faruwa?
Bakida lafiya ne?


Kasa magana Haj Zainab tayi sai kokarin hana kanta shiga shock takeyi.


Amal ce tashigo dakin itama tana kallon mommyn sbd tana shigowa Bilkisu ta sanar da ita kamar mommyn ba lafiya taji siddi na daga murya.


Qarasowa tayi ta zauna gefen mommyn ta riqo hannayenta biyu tana kallon siddi tace,


"Meya sameta?
Mommyn menene?
Wani abin ya faru ne?


Rintse idanuwanta dasuka fara kokarin sauyawa tayi tana tunanin Meye hadinta dasu AQEEL din da zata damu Kuma?
Ai rayuwarta batada wani Hadi Koda amafarkine bare a zahiri,


'yayanta da 'dan uwanta Lulu sune kadai jininta Kuma abinda ya Kamata ta damu akansa...


Ta manta tayi alqawarin rufe babin rayuwar Zainab Yar malam adamu,
Yanzu Haj Zainab IDON NERA ce wannan.


Bude idanuwanta tayi tareda sauke numfashi Mai sanyi ta dafe goshinsa tareda kallon 'yayan nata dasuka daga hankalinsu gabaki daya.


Wani kyakkyawan murmushi tasaki tana kallon idanuwansu musamman AMAL datake jiran bayanin komai..


Zame hannunta tayi daga na AMAL ta shafa Fuskar Siddi da tafi AMAL rauni tace,


"Babyna ahakan Zaki zama uwar da muketa fata da burin ki zama
Kina komawa kamar baby daga Kinga mommynki cikin ciwo.


Dawo da kallonta tayi kan kyakkwar Fuskar AMAL mai daukan hankali tana murmushi tace,


"Am ok sweetie and everything is fine karki damu,


Wani case mukaje da uncle dinku suka Bata Mana Rai Amma ankai karshen matsalar komai yazama tarihi Babu abinda zai taba sauya Mana rayuwar farin cikinmu da kwanciyar hankalinmu.


Ajiyar zuciya suka sauke dukkaninsu Amal na cewa,


"I love you Mom.


Kallonsu tayi itama tana dariya tace,


"I love you both.


Uncle Lulu ne yashigo tareda Dr tayo daya Kira Dan yakasa nutsuwa da yanayin Zainab din.


Ganinsu ahakan yasashi sauke numfashin samun nutsuwa suka dawo palon dukkaninsu Dr tayo ya dubata yace jininta ne kawai ya Dan hau shima ba wani abin damuwa bane.


Dr tayo na tafiya AMAL ta miqe ta nufi bedroom dinta ta tube ta Shiga toilet.


Wanka tai ta fito ta Sanya doguwar Riga Mara hannu Kamar yanda ta Saba ire irensu ne kayan datafi sakawa idan tana gida.


Qaramar hula ce da Bata Gama rufe kanta ba a kanta sai slippers data saka ta fito taci abinci tana miqewa tsaye zata nufi sama inda su mommyn suke Bilkisu ta tareta da cewa,


"Anty AMAL Pelo yakira wai mommy tayi baqo.


Bata tsayaba tace,


Zan fada Mata.


Sama ta wuce ta tadda mommyn tana waya Mai mahummanci Dan Haka ta dawo qasan tace kice musu yajira tana waya.


AMAL na sake Hawa sama ko zama batayiba wayarta tayi ringing tana dagawa Bata Gama sauraron abinda ake fadaba tace,


"Waye AQEEL ASAD din?.....


Haj Zainab dake waya da sauri ta waiwayo gefen AMAL din tana cewa,


"Wake magana a wayar??


Kashe wayar Amal Tai tace,


"Daga gate ne Wai AQEEL ASAD na gidan Kuma gurinki yazo.


Itama Haj Zainab kashe tata wayar tayi batareda damuwa ko wani shock ba tace,


"Ina fama da ciwon kai inaga suce banajin Dadi bazan samu saukowaba.


Kai tsaye Amal din ta isar da sakon ta waya tareda fada musu karsu Kuma kiranta itama batason damuwa.
##MAMUH#






*_ZAFAFA BIYAR_*


*RUMBUN K'AYA*πŸ”₯
Hafsat Rano


*DAUDAR GORA*πŸ”₯
Billyn Abdul


*IDON NERA*πŸ”₯
Mamuhgee


*A RUBUCE TAKE*πŸ”₯
Safiya huguma


*KI KULANI*πŸ”₯
Miss xoxo


Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200


ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN


0022419171
Maryam sani
Access bank


Shedarka ta 09033181070


MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN


09166221261


πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*


+22799643131


Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA


*A DADE ANAYI SAI GA
SKIYA!*
*Thanks for choosing us*πŸ”₯
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
29
Wayarta ta dauka taci gaba dayi duk da Rabin hankalinta na kan sunan baqon da akace yazo gurinta,


MUHAMMAD AQEEL ASAD Wanda tasani a baya kokuwa wani AQEEL ASAD din ne daban,


Koma wanne daga ciki batajin tanada himmar ganinsa ko magana dashi,
Kamar yanda alaqarsu ta yanke to hakama batada abinyi ko tattaunawa dashi.


Fincike zancen gabaki daya tayi a ranta tareda cigaba da wayarta hankali kwance harta Gama ta maido hankalinta kansu Amal suka cigaba da fira cikin Jin Dadi da kwanciyar hankali.


AQEEL ASAD dayake kofar babban gate din gidan hankalinsa yagama tashi ya fita nutsuwarsa gabaki daya


IDON NERA kawai yakeson gani a gabansa Dan da idonsa ya tabbatarda Maminsa ce IDON NERAr da ake fada,


Idon NERAr datayi mummunan suna a duniyar da bama zai iya fadaba,


Maminsa ce matarda akewa kirari da sunan da tambarin uwar karuwai?
Maminsa ce me aurarrakin da basa kirguwa.....


Ina Little MARYAMAH dinsa???


Su waye yayan nata biyu da ake fada?
Waye MARYAMAH din Baba sandan sa aciki??
Waye Mai aure aure acikinsu Kuma waye Hayat yakeso acikinsu???


Rintse idanuwansa yayi suna wani irin radadin Jan dasukai
Kansa juyawa yakeyi Yana Sara Masa tako Ina...


Wannan Idon Nera din kawai yakeson gani shi,
Ganinta kawai a gabansa zai tabbatar Masa da waye ita,Maminsa kokuwa wata dabanΒΏ




Baisan lokacinda suka daukaba a gurin suna jiran abasu damar shiga gidan kokuma ta fito din Amma Babu alamar ko daya,


Tun Rabiu driver na jiran fitowar sako daga ciki harya bude motar ya fito yabawa maigidan nasa guri sbd ganin mummunan yanayin dayake ciki,


Gurin securities na gate din Rabiu yazo ya sake magana tareda Yar magiyar asake isarda sakon zuwansu ga hajiyar..


Suna Kira Kai tsaye ta sanar dasu bazataga kowaba ayau din batajin Dadi.


Daqyar malam Rabiu ya dawo motar ganin har yamma tayi suna gurin ya shigo motar ya rufe tareda Dan waiwayowa kadan cikin girmamawa yace,


"Shaykh Ansake Kira Dan isar da zuwan naka
hajiya Idon Nera din batajin Dadi akace,
ko zaa kaika gida ka huta kafin asake dawowar???


Rintse idanuwansa yayi Yana Hana rauninsa bayyanuwa a fili ya gyada Kai Kawai sbd yasan malam Rabiu din Dole zai gashi duk da tsawon awannin dasukai agurin motars kunne take sbd AC dan bazai iya zama cikin zafi ba.


Hanyar gida suka nufa Yana Jin damuwarsa da tashin hankalin dake cikeda Ransa Yana qaruwa,


Meyasa taqi ganinsa,
Da gaske batada lafiya dinne?


Innalillahi wainna ilayhi rajiun,
Maminsa fa ake maganar shugaba Kuma uwa da gatan Karuwai....


Wannan wata babbar jarabtace da Allah yakewa imaninsa,


A rayuwarsa sunan karuwanci da Karuwai Bai taba Hawa harshensa bama bare ya taba ganinsu harma ace gashi ga su,


Idan ta tabbata Maminsa ce IDON NERAr datayi suna da shahara a wannan sunan dayake baqin ciki da Jin ciwon ambata Yaya zai iya kallonta,
Tayaya zai kalli MARYAMAH wadda yayi alqawarin inganta rayuwarta da zama gatanta tako Ina ya cike gurbin uba,Yaya,Kuma dangin uba agareta.


Har suka kusa Isa gida bai fita cikin tashin hankali da firgicin dayake cikiba,


Bazai iya Isa gidansa a yanayin dayake cikiba Dan Haka a hankali ya bude Baki cikin shaqaqqiyar murya yace akaisa gidan hutu da karatunsa.


Juya kan motar malam Rabiu yayi ya nufi can din batareda yace komaiba saima zallan tunanin dashima ya shiga na Abinda yakai Mai daraja da mutunci kamarsa gidan IDON NERA wadda yau da anganesa kokuma aka samu labarin mutum kamarsa yazo gidan takanas take zaa yada shima yafada tarkon IDON NERA yashiga sahun mazan datake juyawa sbd yayanta dandai ita din ta matsa girma.


Parking malam Rabiu yayi batareda yace komaiba yafito zai bude Masa motar AQEEL ASAD din ya girgiza Masa Kai ahankali yace,


Thank you,
Ka tafi kawai idan nagama zanyi driving din kaina zuwa gida.


Wucewa ciki yayi malam Rabiu din ya bisa da key na motar har bakin kofar Shiga kafin yamiqa Masa yayi Masa Saida safe ya juya ya nufi gate ya gaisa da masu gadin gidan ya wuce Dan neman abin Hawa sbd saiyayi tafiya sosai kafin ya fita anguwar yasamu abun Hawa Dan abin Hawa na haya basa shigowa anguwar.


Bai zaunaba zuciyarsa da jikinsa Babu wani wani ya wuce zuwa bedroom dinsa na gidan ya wuce toilet Kai tsaye yayo alwala yafito.


Masallacin gidan ya wuce Wanda suke gap da tayarda sallah,


Yana Shiga suna tayarwa yabi sahu tareda tayarda sallan.


Bai baro masallacin ba Saida yai sallar ishai ya fito Kai tsaye yau bazai zaunaba Dan bazai iya Aiko ko karatun komaiba yadauki key din motar Yakuma fitowa.


Kai tsaye ikeja GRA Yakuma nufa gidan IDON NERA sbd bayajin zai iya bacci ko samun nutsuwa Koda yaje gida batareda ya gantaba.


Zuwansa Kai tsaye gate din ya nufa yayiwa securities din horn.


Tasowa sukayi zasu gaidasa tareda Jin abinda ya sake dawo dashi.


Suna gaidasa suka sanar Masa Haj Zainab ta fita yanzu bada jimawaba tareda uncle Lulu.


Rufe idanuwansa yai Yana Jin nauyin zuciyarsa na qaruwa sbd rashin ganinta zai iya zauta tinaninsa..


Hannu yakai ya saukar da glass din motar ahankali
Take wani irin daddadan kamshi Mai sanyi da nutsuwa ya daki fuskokinsu...


Kwarjinin dake cikeda kyakkyawar fuskarsa yasasu da sauke idanuwansu daga kallonsa Kai tsaye suna sake bayyanarda girmamawarsu garesa.


Saida yasake sauke nutsatsen numfashi a boye kafin yace,


"MARYAMAH fa????


Shiru sukai cikin Dan tinani da mamaki kafin dayan yace,


"Sir babu Maryamah a gidan,
Kwata kwata yau Haj madam batayi baqi ba so Babu kowa su Ms AMAL ne kawai sai Mrs Lulu da 'dayan 'yar Haj madam din Ms siddi sai masu aiki kawai,
Babu Maryamah aciki batazo Nan ba Sir.....


Shiru yayi Yana sake shiga rudani da tinani,
Babu Maryamah?
Ina Maryamah din take?


Meyasa bazai hadu da IDON NERA dinba ne sai Kansa da zuciyarsa sun kusa bugawa.


Gyara parking din morarsa yayi a gurin batareda ya juya ba sbd zai jirata anan din har saita dawo.




Securities na gidan Basu sansanba sai mutum daya daga cikinsu ya ganesa shima sbd ya taba zama security a daya daga cikin kamfunansa Kuma shima so daya ya taba ganinsa dayayi wani zuwan..


Sauran yafadawa kuma Suma Daman suna ganinsa suka shedar da babban Alhajin Nera ne irin wainda hajiya madam dinsu take buqata da girmamawa, amma Kuma abin mamaki wannan din gashi tako Ina yakai harya wuce yanda akeso Amma yaqi ganinsa da alama Kuma tana sane.






Har karfe goma Sha biyu saura Yana kofar gidan Yana jiran dawowar Idon Nera cikin morarsa,


Qarfe goma Sha biyu na bugawa Dole yabar gurin yakoma gida sbd kaf rayuwarsa idan ba tafiya yaiba Bai taba Kai irin wannan lokacinba a waje.


Juya kan morarsa yayi zai bar gurin ya hau titi da speed mai qarfi yabi hanya.


Yana Isa gida parking yayi ya fito Kai tsaye ya nufi bangarensa sbd sanin kowa ya Isa yin bacci
Haka shima bayason takura ko qarin damuwa.


Yana shiga palonsa yasan Bilkees na Nan sbd ita mace ce da ake gane tana guri sbd kayanta da koina tasamu ajiyewa takeyi.


Dankwalin kayanta yagani a lafiyayyan palon nasa sai Kuma wayarta.


Kai tsaye hanyar bedroom dinsa ya nufa ya Murda kofar ya shiga.


Kallo daya yayiwa gadon nasa datake kwance akai tana bacci cikin doguwar Rigar bacci har qasa Mai kauri.


Wani irin sanyayyan numfashi ya sauke Yana qarasawa closet dinsa ya fara zare kayan jikinsa.


Yana Gama zarewa toilet ya shige Yana sake sauke numfashin kokarin daidaita nutsuwa da Kansa sbd Kansa dake neman bugawa.


Brush yayi kafin wanka da ruwa marasa sanyi ya fito daureda ash towel a qugu jikinsa na fitarda qamshin Aesop bath cream.


Goge jikinsa yayi ya Dan fesa Hugo boss body spray kadan ya koma closet ya saka pyjamas masu Dan kauri da qaramar socks sbd tafin kafarsa da bayason komai Yana tabawa.


Pineapple drink yasha kadan Mara sanyi shima sbd Kansa dake sarawa sosai yanason Shan magani yashasa.


Yana gamawa ya kwanta tareda rufe idanuwansa ahankali Yana Shiga tinani.




Idan har Maminsa ce Idon Nera yasan wuyar rayuwar ta sanyasu Shiga wannan rayuwar,


To meyasa zata bar gida tashiga irin wannan halin?


Umma ta basa tabbaci da rantsuwar cewa da kanta Dan raayinta tabar gida,


Data bar gidan meyasa Bata tafi kota tsaya inda idan yadawo zai sametaba,


Tasan cewan rayuwarsa gabaki daya ta sauya Babu farin ciki aciki daga ranarda ya dawo ya samu bata ba MARYAMAHΒΏ


Duka tsawon wannan lokacin rashinsu,
Da rashin sanin halinda suke ciki shine qunci da farin cikin daya rasa a rayuwarsa duk da Yana tareda mahaifiyarsa da matarsa da 'yarsa Amma farin ciki yakasa walwala a rayuwarsa,


Su din amanarsace,
Su din haqqine dayayi alqawarin ya ratayawa Kansa bayan baba malam sanda dinsa daya rataya masa amanarsu,


Ta Ina? Tayaya zai kalli tsakiyar Idon Maminsa da ake Kira da shahara a wannan rayuwar Mai muni da radadin fada a Baki.


Amma koma menene a yanzu tabbacin itadin Maminsa ce yakeso sbd bayyanarsu garesa shine mafi girman nutsuwa da farin cikin dazai samu.






***Da safe qarfe Tara ya fito a shirye qamshinsa Mai Dadi da sanyi Yana tashi.


Cikin kulawa Bilkees ta riqo hannunsa tana cewa,


"Daddyn mufeeda please kayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login