Showing 87001 words to 90000 words out of 149977 words
ko neman izinin AQEEL ASAD din Akan tafiyar saidai ta hakura da zuwa ganin likitan gabaki daya.
Su mommy sallah sukai Bayan sunyi wanka kafin suka fito cin abinci lokacin itama Anty Fareedah ta shigo tareda Fahat Wanda yayi gurin Amal da gudu Ya rungumeta Yana cewa yayi missing dinta yau ba itace ta daukosa makaranta ba.
Wani kyakkyawan murmushi Tai Masa wanda ta Jima batayiba a kwanakin
Ta ja hannunsa suka nufi dining tana cewa itama tayi kewarsa.
Abinci sukaci suna Gama suka kwasa suka koma sama bakuma lallai wani daga cikinsu Yakuma saukowaba sai safe.
Anty Fareedah ma tanada aiki Dan Haka Bata wani tsaya firaba Takoma bangarensu tabarwa Amal Fahat dayace gurinta zai kwana sbd kaf ahalin nasu itace sukafi shaquwa da juna sosai sbd tanada son yara qanana sosai shiyasa duk suka qagara Siddi ta samu ciki ta haihu.
Washe gari da safe batayi wahalar tashi da wuri ba sbd sanin sabuwar dokar mommy Dan bazatace ta AQEEL ASAD dinba Dan mommynta tafada ne kawai ta dakata da zuwan makaranta.
Cikin bacci siddi tashigo bedroom dinta sanyeda doguwar Rigar bacci ta tadata tace mommy tace ta shirya zatace makaranta.
Batai wani murna ba sbd indai wannan ne duk zaa gaji da Mata Wasa da hankali a Dena.
Baa lokacin ta tashiba saida tagama juye juyenta kafin ta sauko gadonta ta nufi toilet tayi brush da wanka ta fito a natse ta shirya cikin Riga da skirt na atampa da qaramin gyale sai handbag da key din motarta.
Dakin mommy tafara zuwa saidai Bata ciki tana qasa sai kawai ta sauko.
Dukkaninsu suna Palo harda Anty Fareedah da siddi
Mommyn ta gaida tawuce dining sama sama ta Danci chips da doyar da aka soya tadawo gurinsu tana cewa zata wuce.
Kallon key din dayake hannunta mommy tayi tace,
"Bada motarki zakiba
Akwai mota a waje da AQEEL ya Aiko akaiki din.
Dakatawa tayi tareda juyowa ta kalli mommyn zatayi magana
Haj Zainab din ta rigata da cewa,
"Idan bazaki ba dawo ki zauna bazan iyaba Wlh
Kuna neman juyar min da Kai tsakanin ke da AQEEL din.
Kai tsaye kuwa ta juyo ta dawo din da bazata tafinba ta fasa ta hakura indai shine zaisa aringa kaita din Ana daukota...
Siddi da Anty Fareedah ne sukai saurin tareda Siddi na cewa,
"Yi hakuri ki tafi
Kada kice kin fasa ko hakura da karatun,
Idanma fa kika fasa ko hakura shi baida damuwa baida haushi..
Please Amal kiyi hakuri kije tunda bama shine zai kaiki dinba driver ne aka Aiko.
##MAMUH#
#LOVE#MARRIAGE#ROMANCE
#AQEEL ASAD
*_ZAFAFA BIYAR_*
*RUMBUN K'AYA*π₯
Hafsat Rano
*DAUDAR GORA*π₯
Billyn Abdul
*IDON NERA*π₯
Mamuhgee
*A RUBUCE TAKE*π₯
Safiya huguma
*KI KULANI*π₯
Miss xoxo
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200
ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN
0022419171
Maryam sani
Access bank
Shedarka ta 09033181070
MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN
09166221261
π³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺ
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*
+22799643131
Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA
*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*π₯
45
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
45
Dakinta takoma tareda wurgi da komai dake hannunta ta nema guri ta zauna idanuwanta na cikowa da hawaye.
Kokarin hadiyesu tayi tana hanasu saukowa sbd alqawarin datayiwa kanta na qin sake yiwa duk abinda ya shafesa kuka.
Danne fushinta da zuciyarta tayi tareda tubewa ta saka Kaya marasa nauyi tayi kwanciyarta.
Suma can su mommyn Babu Wanda ya biyota tunda sun San ba zuwan zatayiba Dan Haka aka kyaleta din.
Driver Kuma dayake sbd ita din kawai aka aikosa sai yaci gaba da zaman jira batareda kosawa ko damuwa ba tunda aikinsa ne.
Bata fito ba Saida takuma bacci har Rana kafin ta sake wanka ta fito fuskarta ba yabo ba fallasa.
Abinci taci tadawo gurinda suke suna sake tattauna maganar tafiyar tasu.
Kallonta Haj Zainab tayi cikin kulawa da Dan rarrashi tace,
"Amal ki sauko daga fushin Nan Haka Mana,
Yanzu gashi maganar tafiyar Nan Ni kaina na rasa ta yanda zanfara Masa bayanin dake zaayita sbd kiga likitan kema,
Idan ma nayi Masa Dole kina buqatan kema ki nutsu ki sake fada Masa sbd tafiyar barin qasa ce,
Dan Allah kada ki bani ciwon kai akan hakan maganar nan musamu mutafi batareda bacin Rai ba.
Kallon Mommyn tayi tana ajiye wayarta data Gama duba sako tace,
Mommy idan kin fada Masa yabari din shikenan ai.
Murmushi siddi tayi tana kallonta tace,
"Mommy kinsan fa Amal dinmu zinariya ce sai mun jawa 'danki ajinmu sbd bazai yiyu yasamemu a saukiba bayan tarin masu nemanta sannan kawai yazo Yana Mana iko sbd kawai yaga shi din Mai kyau da aji ne,
Mommy Kamata yayi aringa lallabata
Ita fa akaiwa lefi..
Murmushi Haj Zainab tayi tana kallon Amal data qi cewa komai sai wani kallon haushi data jefa Siddi dashi.
Dole siddi da mommyn suka sakata Dan sakewa ta biye musu suna fira Amma maganar tafiyar na ranta sbd bazata iya Masa maganar wani rokonsaba tafison ta hakura da tafiyar duk tsananin kaunar kuwa datakewa zuwa ganin likitan sbd ciwon marar nata ita kadai tasan azaba mai tsananin datake ji,
Har tsoro da fargaba takeyi duk wata yakusa qarewa
tuno azabar kawai damuwa yake sata Mai tsanani gashi ta saka hope akan wannan tafiyar.
Harsu Gama fira kowa yashige ya kwanta baizoba Kamar yanda ya Saba
Haj Zainab ce kawai ta Dan shiga tunanin rashin zuwan nasa tunda ya Saba din tunda yadawo rayuwarsu kullum sai yazo ya gaidata safe da dare,
Wayarsa ta Kira duk da dare yayi lokacin Amma sbd tunanin lafiyarsa yasata Kiran.
Daidai lokacin Yana tareda Al-Amin Akan tafiyar da zaiyi washe garin ranar.
A natse ya dauki wayar ganin sunan Maminsa da muryarsa Mai sanyi nutsuwa ya gaidata Yana Bata hakurin rashin zuwan nasa.
Itama jinsa lafiya yasata sallama dashi tareda Masa fatan sauka lafiya akan tafiyar da zaiyi din.
Bai gamaba ya wuce gida sai guraren 10:30 Dan Haka Yana Isa Kai tsaye ya shige sbd yasan su ummansa sun kwanta Suma.
Wanka yayi yayi Shirin kwanciya sbd yayi dinner tareda Al-Amin baya buqatan komai tunda duka familyn nasa boyon kansu sukeyi Wanda gabaki dayansu yabarsu su huta din.
Washe gari qarfe goma zai wuce da Haka 9 yafito a shirye yafara Kiran wayar Bilkees wadda tana gani taji sonsa da kishinsa na sake tafarfasa zuciyarta akan duk abinda yake faruwa duk da mufeeda jiya data dawo school tafada Mata Kamar fa Babu Wani abin arziki a maganar auren tunda gashinan komai shiru Babu maganar kawo Matar kokuma maganar tarewarsa wani gurin da ita.
Hakan ya Dan sanyaya zuciyarta tun jiyan Amma Dama tayi jiran ne ya nemeta da kansa Dan Haka ta daga wayar muryarta a narke Kamar wadda ke ciwo.
Ajiyar zuciya ya sauke ahankali Jin yanayin nata Dan Haka ya katse wayar kawai tareda nufar bedroom dinta abinda bayayi sbd itace Mai zuwa can sama gurinsa.
Kai tsaye bude dakin yashigo Yana kallonta tana zaune tana cin lafiyayyan breakfast da aka kawo Mata aka jera Mata Akan center table...
Bai kalli abincin ba ita yafara kalla kafin ya kalli abincin ya fahimci lafiyarta kalau kenan,
Juyawa yayi kawai ya wucewarsa sbd bazai iya Bata lokacinsaba gurin tambayarta lafiyar tata tunda alamun sun nuna
Kawai raayintane da ganin damarta na rashin zuwa garesa sbd kishinta.
Bangarensu umma ya nufa acan dinma Babu wata Fuskar ko kadan sbd gabaki daya sun dauke Masa wuta musamman ummansa dako ganinsa batason Yi.
Cikin nutsuwa ya sanar da ita tafiyar da zaiyi
batareda ta kallesaba tace Allah ya tsare ta miqe tabar Masa palon.
Umman Cameroon ce ta kallesa bayan barin Haj Maryamah palon itama Bayan ta danne zuciyarta ne ta iya cewa,
"AQEEL matuqar kana kaunar mahaifiyarka da farin cikinta tareda son gamawa lafiya da ita to dolenka wlh ka yanke aurenka da 'yar Zainab Dan Nima har abada bazan karbi wannan auren naka ba bare mahaifiyarka da kayiwa wannan cin mutuncin da tozarcinda har abada bazata Dena kukansa ba matuqar ba yanke alaqar ka dasu Zainab zakayi ba,
Meya baka shaawa a auren wainda Basu dauki auren a bakin komaiba?
Meye abin albarka atattare dasu?
Me zaka samu agurinsu Banda barnar suna da 'bacin suna Mara amfani kanada mutumcinka.....
Ahankali ya furta,
"Nagode umma Zan wuce time din tafiyana yakusa.
Miqewa yayi yanufi kofar palon ya fice yabarta da sauran maganganu a bakinta suna qona Ransa da cin Ranta Kamar zata bi hanya tana ihun Kiran Zainab da tsinewa zuriarta.
Haj Maryamah datake jinsu Yana ficewa taji zafi da ciwon zuciyarta na qaruwa sbd hakan na nufin baida niyar sakin auren kenan?
Wane babban balai Zainab ta aikata akan AQEEL dinne da duk duniya idan ba itaba bayaji baya ganin kowa??
To kodai shayar Mata da 'da tayi a wancan lokacin batareda sun saniba Dan kuwa wannan balain daga gani yasha Nononta ne.
Fitowa tayi gabanta na harbawa da karfi da tashin hankali da sabon radadi a ranta tace,
"Umma Zainab ta shayar mun da 'da Nononta......
Wani shock ne ya Shiga umma datake neman zamewa daga zaune ta fito da idanuwanta cikin mafi tsananin tashin hankali tace,
"Ta basa Nononta kikace?
Tabbas Nima wlh na yarda da hakan yanzu sbd nono ne kawai yakeda wannan qarfin daya kasa ganin kowa sai ita...
Innalillahi wainna ilayhi rajiun
Mun shiga uku da wannan sabon tashin hankalin,.
Zainab ta cucemu taci amanarmu taci Amanar Alh Asad daya yarda da ita tun wancan lokacin,
Me nakejiΒΏ
Zainab nono Kika bawa AQEEL?
Wannan masifar wace iriceΒΏ
Rayuwar AQEEL ta lalace tun Yana qaraminsa sbd Zainab,
Ta shayar da Isa nonon karuwanci,
Ta Bata tsakaninsa da mahaifiyarsa,
Ta rabasa da mutuncinsa a Idon jamaa ta hanyar aura Masa karuwar 'yarta,
Yanzu me duniya zataji idan akaji nonon Idon Nera AQEEL ASAD yasha??
Uwa uba nono daya yasha da wadda aka yaudaresa aka daura masa.
Neman zarewa umma da Haj Maryamah din sukai da wannan mummunan tashin hankalin dasuka sakowa kansu,
Bilkees data shigo Bayan wucewar AQEEL ta taddasu Acikin wannan taradda din Jin tayi wani masifaffen Dadi Mai tsananin gaske ya rufeta musamman dataga suna shakka sai kawai ta daka tsalle ta tabbatar musu da ya taba fadar Kamar hakan Amma sirrinsa ne da Haj Zainab din.
Jinin umma Hawa yake kokarin Yi cikin tashin hankali saidai Bilkees din ta Kamata tana tausarta sbd ganin tasamu gabar datafi komai a cikin sauki.
Umma kuwa kuka tafara Yi tana sake debewa zuriar uwar Zainab dinma albarka da suka barta da ita bayan mutuwar malam da Basu zo sun dauketa sun rabata da rayuwarsu ba gashi duka ta zama jarabawansu itada 'yarta Haj Maryamah da jikanta AQEEL.
Haj Maryamah kasa danne zuciyarta tayi tacewa umma wlh tana buqatan sake ganin Zainab Dole saita fada Mata yanda tayi ta shayar Mata da danta,
Me Tasha tasamu nonon data basaΒΏ
Me takeso a rayuwarta
Ko duka abinda ta mallaka zata Bata ta fita daga rayuwarsu itada yarta subar qasar su koma inda bazai sake ganinsu tunda su kudine burinsu da kwadayinsu.
Ita kanta umma tana son fuskantar Zainab din tabbas sbd wannan gabar komai ya wuce tinaninsu
Basu dauka balain nata yakai can ba.
Umman Cameroon kallon Bilkees tayi duk da tana cikin tashin hankali da damuwa
Cikin baqin cikin ganinta itama tace,
"Wallahi tallahi naji zancen Nan ya fita a bakin Aurenki Dan kingama auren jikana kenan sbd kema kin nuna ba 'yar arzikin bace,
Albarkacin mufeeda kikace da tun wancan lokacin Zaki koma inda Kika fito Dan hada zuriar dake kema baida amfani tunda bakisan rufa asirin iyayen Mijinki ba.
Shiru Bilkees tayi tanajin umman Amma zuciyarta batajin komai sbd bullowar wannan maganar yasata Jin kamar an yaye Mata duk nauyin dake kan zuciyarta,
Qarshe dai ansamu abinda zai raba AQEEL ASAD dinta da Amal Idon Nera wadda takejin ma yanzu ko lokacin damun kanta akan auren batada tunda gashi kwadayinsu yasa anyi auren Amma AQEEL din ya barta Dan baya buqatarta.
Abu daya ya rage Mata shine yanda labarin zai fita batareda ansan itace ta fiddasaba sbd Dole sai zancen na ya fita duniya tasani a sheda aurensa da Amal Idon Nera ya haramta shikenan ta fita wannan masifar mai suna IDON NERA a rayuwarta.
*****AQEEL ASAD kuwa Kai tsaye airport aka wuce dashi baisamu ya biya gidan Mamin ba sbd yayi latti saidai sukai magana a waya,
Yauma driver yazo kaita school Amma taqi tafiya,
Washe gari ma haka driver Yakuma zuwa taqi,
Haka driver ya ringa yawo da zaman jira wuni a banza Amma taqi ma sake bi takansu,
Dawowar uncle Lulu ne daga tafiya ya tadda abinda yake faruwa ya Kira AQEEL ASAD din da Kansa ya rokesa akan ko shine yabari zai ringa kaita tunda batason driver din.
Kai tsaye ya sanarwa uncle Lulun Idan bazata bi drivern ba ta zauna Babu Wanda zai ringa kaita.
ganin tanason zuwa school din dakuma wasu guraren shiyasa uncle Lulu dasu mommyn suka rarrasheta daqyar ta yarda tafara bin driver din Wanda sai ranar yafara ganinta.
Daga ranar kullum tunda safe yake zuwa ya zauna jiranta har lokacinda zata fito yakaita makaranta yakuma jira ko yaushe zata kai tagama ya dawo da ita gida.
Sauran gurarenma datakeson zuwa duk shine yake kaita daga school batareda tadawoba sbd idan tadawo mommy Bata barinta fita sbd iya school ake nufin yabarta aringa kaita.
Su umma kuwa yau suka nufo gidan Haj Zainab badan sunsoba Saida sukai kwanaki suna tausar zuciyarsu akan zuwan sbd Dole suzo su funkaceta akan maganar idan ta shayar dashi ta fada musu kokuma su makata kotu su nuna Mata iyakarta.
#MAMUH#
#LOVE/ROMANCE
*_ZAFAFA BIYAR_*
*RUMBUN K'AYA*π₯
Hafsat Rano
*DAUDAR GORA*π₯
Billyn Abdul
*IDON NERA*π₯
Mamuhgee
*A RUBUCE TAKE*π₯
Safiya huguma
*KI KULANI*π₯
Miss xoxo
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200
ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN
0022419171
Maryam sani
Access bank
Shedarka ta 09033181070
MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN
09166221261
π³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺπ³πͺ
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*
+22799643131
Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA
*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*π₯
46
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
46
Yau sai kusan yamma ta Gama abinda takeyi a cikin makaranta Dan Haka tana fitowa daga lectures Kai tsaye mota ta nufa a Dan gajiye.
Doguwar A shape ce ajikinta na atampa navy blue wadda tayi Mata kyau sosai sai qaramin Chantilly veil da bvlgari handbag,
Fuskarta ba kwalliyar komai akai
Ta nufo motar tana kalla batareda tayi mamakin sauya motar da Ahmed yayi ba numbern motocin gidansa yasa take ganewa duk lokacinda Ahmed ya sauyo motar daukarta.
Kai tsaye ta qaraso motar
Ahmed ya fito da sauri ya bude Mata kamar yanda ya Saba
A natse ta shiga ba zato tagansa a Bayan zaune cikin milk Yadi Mai taushi da tsadan gaske,
Gabaki daya sanyayyan qamshinsa ya Gama rikita motar
Ba zato ta kallesa da idanuwanta dasuka Dan matse
Bai juyo ya kalleta ba waya yake amsawa ahankali cikin nutsuwa.
Jan motar Ahmed yayi suka bar cikin makarantar
dauke idanuwanta tayi gabaki daya tareda maidawa kan hanya fuskarta ba sakewa ko kadan.
Gama wayarsa yayi ya ajiye ahankali tareda waiwayowa kadan ya kalli gefenta idanuwansa akan qaramin gyalenta dayake gefe daya kawai.
Jin idanuwansa na yawo ajikinta yasata kasa motsi tana Jin zafi na saukar Mata.,
Maida idanuwansa yayi kan farar fatar wuyanta dake bayyane.
Ahankali ya dauke idonsa akai ya bude Baki a natse yace,
Meye wannan din da Kika yafo??
Shiru tayi Masa batareda ta juyoba ko amsawa.
Sake maimaita tambayarsa yayi Nan ma takuma yimasa shiru.
Maida kallonsa kadan yai kan Ahmed Kai tsaye yace,
"Mu wuce gidan Karatu.
Juyowa tayi ahankali Jin abinda yafada taqi kallon fuskarsa dake sake sakar Mata zafi ahankali itama tace,
"Ku ajiye Ni Zan hau drp na qarasa.
Bakinta da yayi maganar ya kalla itama Jin baice komaiba yasata juyowa ta kalli fuskarsa idanuwansu suka hadu a fuske ta Dan janye nata Idon tana kokarin sake magan ya katseta da cewa,
"Meye wannan ajikinki nace??
Jikin nata ta kalla a sace taga gyalenta yake kalla dan Haka saita qi cewa komai.
Ahmed tuni ya kama hanyar gidan Karatu ganin baida niyar sake magana shima saita sake juyowa ta kallesa tana son magana Amma izzarta na hanata Dan Haka tai shiru tareda dauke kanta itama.
Babban gate din gidan Ahmed shige da motar bayan an wangale musu kofar gate din.
Danne zuciyarta tayi yaqi juyowa ta kallesa
Dan jiran takeyi ya fita motar Ahmed ya wuce da ita gida.
Ahmed na parking ya bude motar ya fice Dan Basu guri.
Fitar Ahmed yasata juyowa ta kalli gaban motar zatayi magana ya zuba Mata fararen idanuwansa takasa cewa komai cikin mamakin abinda ya tsaya jira a motar ta Dan kalli gefensa zatayi magana ya katseta ta hanyar bude motar ya fice ba tsammani taji ya bude ta gefenda take cikin kulawa.
Qin juyowa tayi ta kalli kofarma gabaki daya saita fiddo wayarta ta saka Kiran Ahmed Wanda daga shi har securities duka suka bace bat daga harabar gidan suka koma daga waje.
Wayar Ahmed na ringing ya daga ko magana baiyiba AQEEL ASAD ya saka hannuwansa masu tsayi ya karbe wayar daga hannunta cikin nutsuwa tareda sunkuyawa ya dauketa gabaki daya ya nufi ciki ita Yana kallon fuskarta dake bayyanarda fushi da bacin Rai me tsanani.
Bai ajiyeta koinaba sai tsakiyar master bedroom dinsa dake gidan
Yana ajiyeta ta fizge jikinta a zafafe ta nufi kofa ko Isa batayiba Yakuma dawo da ita ta baya
Duk yanda yake kaucewa haduwar jikinsa da nata saida suka hadu sosai ta bayanta ya matseta cikin jikinsa ahankali yana sauraron yanda take kokawar kwacewa.
Fuskarsa yakai wuyanta ya shaqi qamshi data tashi jikinta Mai sanyi na
Boadicea kafin yakai bakinsa kunnenta ahankali ya furta,
Menene wannan din Kika yafa??
Cak ta tsaya daga mutsu mutsun datakeyi sbd numfashin daya sakar Mata Mai zafi a kunne da wuyanta
Yasa zafi sauko Mata tako Ina..
Bai janye bakin nasa daga kunnentaba yasake cewa,
"Uhumm Ina jiranki??
Rintse Ido tayi ta bude qamshinsa da numfashinsa da jikinsa dayake zagaye da nata yasata Jin numfashinta Kamar Yana toshewa ahankali ta zare jikinta tareda matsawa gaba batareda ta bari ta juyoba.
Qarasowa yayi ya Kama hannunta ya dawo da ita kan lafiyayyar sofan sake dakin nasa ya zauna tareda kokarin zaunar da ita Amma ta kafe taqi zaunawar...
Tashi yayi tsaye gabanta kirjinsa na gap da gugar nata ta daga qafa zatayi baya yakai hannunsa ya yangota ahankali ta fado jikinsa ya riqeta da kyau ba tareda ya matsetaba Kamar Wanda bayason takura qashinta.
Haduwarsu hakan yasa numfashinta sake toshewa taqi yarda ta dago Dan batason kallon fuskarsa.
Idanuwansa ya zuba mata Yana Jin gyalen nata data fita dashi Yana yankar zuciyarsa Amma taurin kanta da kafiyarta ya hanata bude Baki tayi magana.
Wuyanta yake kalla zuwa fuskarta dataki kallonsa.
Hannunsa yakai ahankali zai taba gyalen nata tayi saurin dagowa suka hada ido.
Bazata iya jure kallonsa ba Dan Haka ta motsa zata qwace jikinta kirjinsu Yakuma Mannuwa Dana juna..
Ahankali ya janyeta daga jikin nasa da Kansa yana dauke kallonsa daga kanta.
Yana sakinta ta bude kofar bedroom din ta fice fuskarta na bayyanarda bacin Rai da fushi Amma zuciyarta bugawa takeyi da qarfi sbd tsoro da mamakin abinda ya faru din.
Mota ta nufa Kai tsaye ta Shiga ta zauna sai alokacin tasamu numfashinta yafara warwarewa.
Saida tayi mintina hudu a motar kafin ya fito