Showing 72001 words to 75000 words out of 149977 words

Chapter 25 - IDON NERA BY MAMUHGEE CMPLT.txt

25 Nov 2024

6549

aka karbi Haj Maryamah cikin gaggawa Dan kamar heart attack ne tasamu.,


Umma ma Dole aka shiga da ita Dan dubata Dan ita jininta mugun Hawa yayi.


Bilkees ma miqa kanta tayi a dubata Dan kwakwalwarta ta tabbatarda tana rawar Dena aiki,


IDON NERA ta zama masifar rayuwarsu a taqaice,
IDON NERA ajalinsu zatayi daya Bayan daya kenan,
Wadda ta haifi Idon Nera ta haifo musu masifa da balain rayuwarsu
Hadda ita da batajina Bata ganiba batasan anyiba Amma masifar ta shafeta dumu dumu.


Securities aka Aiko Masa asibitin sbd Yan media da aketa fama dasu asibitin gashi Kansa ya dauki wani irin zafin dabai taba daukaba,


Maminsa yake Kira itama Dan yaji Yaya take kada itama ace wani abun ya sameta Amma Bata daukan wayarsa.


Uncle Lulu yakira Wanda ya basa tabbacin Babu abinda ya sameta Amma itama tana cikin wani mummunan halin na daci.


Rufe idanuwansa yayi Yana Dan dafe goshinsa ahankali zuciyarsa na sake daukan nauyi,


Bayason Jin komai baya buqatan komai face rufe Kansa yayi tunanin mafitar wannan tashin hankalin dayasan zaayi idan suka hadun,


Abin bacin Rai mai tsanani garesa shine yanda media suka Isa gurin harda hukuma.,,


Zaiji da wannan daga baya Amma dai yanzu ummansa da Maminsa su fara dawowa daidai tukuna.


Bilkees da aka dubata taga ta Dan dawo hayyacinta sulalewa tayi itada mufeeda suka koma gida zaman jiran tsammanin abinda zai biyo baya idan AQEEL yasan me sukai,


Amma ta batada Dana sani ko baqin cikin abinda ta aikata sbd tasan komai zai qarasa lalacewa babu maganar sulhu ko wata alaqar da zata mayarda AQEEL ASAD ga Idon Nera.




Har dare AQEEL ASAD na asibiti tareda mahaifiyarsa wadda Bata farfadoba sai asuba,


Umma kuwa andawo da ita gida masu aiki na kulawa da ita..


Bayan sallar asuba bayan gari yayi haske suka dawo gida da ummansa wadda taji jiki matuqa gabaki daya jikinta yagama sakewa saidai zuciyarta Bayan qara karfi datayi akan raayinta Babu abinda tayi,


Tsana da zafin datakeji akan Zainab din yafi kowane lokaci karfi da zafin gaske,
Baa taba cin mutuncinta da tozartataba kamar yanda Zainab da 'yarta sukayi Mata,


Umma Bilkees take tsinewa tun jiya da abin yafaru Amma ita Kuma zainab take tsinewa sbd itace sanadin komai da har Bilkees matar 'danta daya din ta zabi cin mutuncinsu da tozartasu a duniya.


Bazata iya tsayawa boye boye ko quncin zuciyaba Akan Wanda takeda cikakken iko Kansa Dan Haka suna dawowa gida ta tsaresa akan saiya zaba Zainab ko ita data haifesa.


Sa mamaki Mai hadeda boyayan firgici yake kallonta zuciyarsa na sauya bugawa..


Rintse idanuwansa dasukai jajir tayi tana danne hawayen dake cikowa acikinsu sbd zuciyarta dake zuba wani irin radadi.


Kasa magana yayi sbd sauyawa da nasa idanuwan sukai atake shima,


Umma ma jiran nasa zabin takeyi tana kallonsa zuciyarta na tsalle da idan ya zabi Zainab mutuwa yarta zatayi Wanda itama Kila ta samu bugawar zuciyar ta mace
Shikenan Zainab tayi galaba akansu tazama ajalinsu.


Ahankali ya miqe tsaye batareda ya iya cewa komaiba ya nufi kofa ya fice zuciyarsa na wani irin zafi da mamakin zuciyar dake kirjin mahaifiyarsa.


Bazai iya zuwa koina a yanzu face gaban Maminsa wadda ita yasan bazata taba basa zabi ba,
Zata fahimci kunci da 'dacin da zuciyarsa take ciki,
Bazata sakasa a tsaka Mai wuya ba..


Daqyar yake ganin gabansa Koda ya Isa gidan Maminsa wadda tun a gate aka bada umarnin Hana motar gidansa kowace irice shigowa gidan.


Wayarta yaci gaba da Kira gashi dare yayi sosai Amma Bata daukaba.


Cigaba yai da kiran Amma Bata daukaba....


Sake daukan zafi Kansa yayi,
Zuciyar ya dafe wadda ke Masa wani irin nauyi Mai ciwo..


Kiran karshe dayayi Mata tana dauka maganar data fada Masa ce ta saka zuciyarsa tsayawa cak.


Wani numfashi Mai wahala ya sake qasan makoshinsa yana jin Kansa na neman qarasa bugawa.


Gida yakoma batareda Yana cikin cikakkiyar nutsuwar zuciyaba,


Duniyarsa gabaki daya ta juye alokaci daya,
Iyayensa biyu dayake so da kauna fiyeda komai sun tsani juna tsana mafi girma
Tayaya zai iya zabar uwar data haifesa kokuma wadda haihuwarsa ce kawai batayiba Amma itace uwat tasa...


Wani irin mummunan yanayi yashiga Wanda yasashi kadaice Kansa baya buqatan kowa atareda dashi.


Yanda yaga dare haka yaga safiyar cikin matsanancin halin dayake neman illata qwaqwalwarsa,


Daga Haj Maryamah har Haj Zainab da umma da Amal Babu Wanda yayi bacci aranar sbd quncin zuciya da damuwa..


Haj Maryamah yafara tinkara Amma Babu wani sauki ko sassauci akan zancenta saima tsanani da lamarin ya qara,


Gurin Maminsa ya nufa wadda itama ta dauki zafin da Bata taba daukaba.


Da gaske takeyi ta yanke dukkanin alqarta dashi Wanda itama Haj Maryamah ta dauki nata zafin akan saiya zaba tsakanin ita da Zainab..


Neman rasa hankali da tunaninsa yakeyi,
Komai ya lalace tako wanne bangare.


Babu wadda takeda sassaucin sauraronsa acikinsu,..


Kansa yakasa dauka,.
Zuciyarsa ciwo da azabtuwa takeyi batareda yasan tayaya zai yanke wannan qiyayyar dasukaiwa sabon qulli Mai qarfi ba.


Karfe goma Sha daya da rabi ya Isa kofar gate din IDON NERA Rs cikin lafiyayyar motarsa malam Rabiu na jansa.


Kiranta yakeyi a waya har lokacin Bata dauka,


Rintse idanuwansa dasukai jajir yayi sbd zuciyarsa gap take da bugawa tareda Kansa,


Fitowa motar yayi ya nufi kofar gate din daidai fitowar motar uncle Lulu da Amal a gaban motar sai haj Zainab din a baya zasu asibiti zuciyarta ke ciwo sosai.


Ganinsa yasa uncle Lulu tsayawa suna kallonsa su dukan kamar yanda yake kallonsu fararen idanuwansa masu wani irin kwarjini da kyau akan AMAL wadda sai yau ne karon farko dayake kallonta...


Kallo daya tayi Masa ta dauke idanuwanta akansa tanajin idanuwansa akanta nauyin zuciyarta akan familynsa Yana karuwa.


Haj Zainab datai Masa kallo daya ta dauke Kai bude motar tayi ahankali ta fito suma duk fitowar sukai suka tsaya gabaki dayansu Banda Amal data qi fitowa motar.


Kallon Maminsa yayi yaga yanda gabaki daya ta fita hayyacinta da damuwa da tinanin komai dayake dawowa a lalace.


Meyasa suka zabi cutatar da kansu da kowa akan duk wannan fitinar dataqi qarewa,..


Shine namiji Kuma tamkar uba agaresu duk da shine 'dansu Amma a yanzu kamar shugaba yake agunsu su dukan,
Tayaya zai zuba Ido komai ya lalace maimakon gyara?
Tabbas zai kawo karshen wannan hayaniyar da yanke yanken alqar,
Idan sun yanke wancan alaqar shine zai daura musu wata alaqar wadda idan bashiba Babu Mai ikon yanketa saishi datake hannunsa.


Wani nauyin dayake maqoshinsa ya hadiye ahankali batareda yace komaiba ya juya mota suna tsaye ya dauko bunch na rafar 1k guda daya ya dawo gaban Mamin ya tsaya ya kalli cikin idanuwanta dasuke kokawar boye rauninta akansa.


Maida kallonsa yayi akan uncle Lulu ya miqa Masa kudin hannunsa.


Kallonsa uncle Lulun keyi da Dan mamaki kafin ya maida kallonsa kan kudin...


Magana uncle Lulu zaiyi ya katsesa da muryarsa Mai nutsuwa da kamew yace,


"Ka riqe a hannunka
Kaine namiji Kuma waliyi a ahalin sbd rashina Amma nine Mai ikonsu musamman MARYAMAH,
Wannan sadakinta ne gobe karfe goma na safe Zaa daura aurenta.


Sakar Masa kudin yayi a hannunsa Yana kallon Fuskar Maminsa da zuciyarta ta buga da karfi batasan lokacinda ta riqosaba alokacinda ya juya zai wuce.


Magana takeson Yi Amma takasa sbd harbawar da zuciyarta takeyi.
##MAMUH#
#MARRIAGE#
#HOTLOVE#BLACK AND WHITE LOVE.
#AQEEL ASAD#AMAL IDON NERA.








SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!


Makarantar Lafiya dake garin Kazaure (Kazaure school of health technology) tana farincikin sanardaku cewa ta Kawo wani sabon tsarin karatu a saukake na part-time Degree da Diploma a wasu kwasakwasai domin ma'aikata masuson karin karatu da 'yan Kasuwa wanda basu da isasshen lokaci.


Kwasakwasan kamar haka:


DIPLOMA


1.Dental surgery Technician


2.Medical X-ray Technician


3.Health Information Technician


4.National Diploma in Biomedical Engineering


5.Public Health Technician


6. Community Health Extension Worker (Re-trainee)


7.Junior community Health Extension Worker (JCHEW)


DEGREE


1. Health Information Management


2.Public Health


3.English Language


4.Public Administration


5.Business Administration


6. Economics


7. Accounting


8.Computer Science


9.Mass Communication


10.Agricultural Economics


Domin karin bayani a tuntubi wannan Lambobin:08035298851, 07066542055 ko Azo haraban makaranta dake No 3 Emir's Palace road off Kano-Daura road Kazaure a jihar Jigawan Nijeriya.
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
37
Riqe hannunsa Mamin tayi tana kallonsa cikin Shiga wani mummunan halin firgita da tsoro tafara girgiza Masa Kai tana kasa magana sbd jikinta dayake daukan rawa take,..


Cikin idanuwanta ya kalla wadda ita kadaice a rayuwarsa take samun irin wannan kallon daga garesa wato kallon tsaf da kyau a natse.,


Hannunsa ya Dora akan nata ya zare nasa tareda sake kallonta Kansa na sarawa cikin qaramin sauti Mai bayyanarda gajiyarsa Akan duka lamuran dake faruwa cikin wani natsatsen sauti ahankali yace,


"Kinsan 'danki magana daya yakeyi Mami.


Maida idanuwansa yai ahankali kan uncle Lulu dake tsaye riqeda sadakin a hannu cikin madaukakin mamaki da firgici shima gashi kusan equal rights suke dashi Akan Amal da zainab Dan Haka baida cikakken ikon hanawa Amma Kuma yanada ikon magana gwara dai a zauna a duba wannan babban yaqi ne ake neman daurawa ba aureba..


A hankali cikin nutsuwa yace,


"Al-Amin will text you the venue kafin safe inshallah.


Juyawa yayi ya nufi motarsa batareda ya sake kallon inda Amal takeba cikin motar tana Jin bazata iya fitowaba Dan Babu abinda zatayi dashi da familynsa daga yau din datasan su suwaye din tagama da matsalarsu tunda Daman Babu hadinta dasu.


Batasan meyake faruwa ba a wajen sbd motar a kunne take sbd AC dake aiki Kuma Daman Uncle din ficewa kawai yayi Bai tsaya kashewar ba,


Taga kudin daya bawa Uncle Lulu sai tasaki wani gajeran numfashi tana dauke Kai da tunanin bayada tinani idan har Yana tunanin bawasu mommynta wannan banzan kudin dako kudin man motocinsu gidan bazai isaba.


Kafin ya Isa motar tini malam Rabiu ya fito ya bude Masa da sauri
Yana qarasowa ya shige,malam Rabiu ya rufe motar tareda zagayawa da sauri ya shiga yaja suka bar kofar gate din da speed kamar malam Rabiu yasan halinda ake ciki.


Wani ciwo da nauyi ne ya dunkule a kirjin Haj Zainab tayi saurin dafe saitin kirjinta tana rintse idanuwanta dake neman hawaye a idanuwanta Amma sun bushe take.


Ganin mawuyacin halinda take neman Shiga yasa Amal fitowa daga mota da sauri ta qaraso gurin tana riqota cikeda mamaki da damuwa take cewa,


"Mommy???
Lfy?
Uncle meya faru?
Meya fadawa mommy data Shiga wannan halin??


Kallon uncle Lulu takeyi tana kokarin riqo mommyn jikinta suna nufar motar.


Kasa cewa komai yayi sai sadakin daya zubawa Ido Yana Jin jikinsa na mutuwa tako Ina,


Me zasuyi da wannan lamarin idan ya tabbata?


Yaya zasuyi da tashe tashen hankalin dazai biyo?


Babu Dama ko halin tada rigima ko shigar da qarar rashin wannan auren sbd yasan Zainab ko wane matsananci Hali AQEEL ASAD zai sakata bazata iya qararsaba kokuma daga maganar duniya taji,


Balai da tashin hankaline yasan zaa bude shafinsa sabo akai wannan auren,


Idan ma Dan kawo sulhu da gyara ne to kafin asamu sulhu da gyaran sai anyi yaqin da baasan iyakarsaba.


Mota ya Shiga ya saka kudin a aljihunsa AMAL dake jiran yayi wurgi da kudin kokuma bawa securities su raba taga ya saka aljihunsa harda dafasu yaji zamansu ya zaunu a aljihun tsadaddiyar shaddar dake jikinsa.


Kasa magana tayi sbd ita idan Abu ya Bata haushi ko mamaki Bata magana,
Mommynta ta kalla wadda keta kokarin Hana kanta shiga babban tashin hankalin dayake cikin zuciyarta yanason bayyana afili.


Jini daya dayake yawo ajikinsu itada Haj Maryamah kowannensu ayanzu so yake ace yagama kwaranyewa gabaki daya sun wanke jinin dashine ya jadasu,
Akirasu da sunan jini daya ma soya zuciyoyinsu yakeyi,
Kona gangar jikinsu yakeyi tareda azalzal zafinsu Amma shine dare tsaka AQEEL zaiyi wannan babban tashin hankalin,


Tayaya?ta Ina?
Bazai taba yiyuwaba har abada su sake hada wani jinin,
Bazai yiyuba,
Bazata iyaba kamar yanda tasan Haj Maryamah tafison mutuwar AQEEL akan ya auri Jininta.,


AMAL dinta ma tasani bazata taba yarda da auren AQEEL ba Koda zaayi yaqin duniya,


Shi kansa AQEEL ba auren so bane
Auren kawo sulhu ne zaiyi da AMAL,


Rayukan kowa lalacewa zasuyi kenan aka wannan auren da Babu Mai so Babu Mai kauna...kowa a tsakanin duka bangaren biyu yafison talauci da wahala akan wannan auren...gwara musu tone tone akan wannan aure,
Su umma kuwa gwara kowa ya Fadi yamutu yaje ya girba abinda ya shuka akan su yarda da wannan auren.


Asibiti suka Isa da ita Bata hayyacinta gabaki daya ta firgice tashiga wani irin zazzafan yanayi,


Kirjinta dake ciwo suka fito Dan zuwa asibitin gabaki daya neman wancan ciwon tayi ta rasa ayanzu tashiga tashin hankalin daya zartasa gashi daga ita har uncle Lulu basama son Amal taji wannan girmamammiyar maganar.


BP dinta ne ya hau itama sai ciwon kai Mai tsanani daya sameta a qanqanin lokacin sbd tashin hankalin AQEEL,


Daga ita har uncle a matse suke dasu same kebewa suyi gaggawar neman AQEEL suyi magana dashi kota yayane su sakasa janye kudirinsa.


Sai dare sosai suka dawo gidan Bayan anbawa Haj Zainab magani acan ta tsaya Tasha yayi Yan awanni aka sake dubata akaga BP din ya Dan dawo normal tukuna suna dawo.


Babu Mai magana a motan sbd kowa da nauyin da damuwar dake zuciyarsa,


Har suka Isa Babu Mai magana Dan Haka suna Isa Amal takama hannun mommynta sukai ciki shima Uncle Lulu fitowa motar yayi yana sake shafa sadakin AQEEL ASAD a aljihunsa ya nufi bangarensa da matarsa ke jiransa.




Har bedroom Amal ta raka mommy Saida taga tayi Shirin komai ta kwanta take bacci ya dauketa sbd magunan da aka Bata akwai Mai saka bacci sosai batareda taso hakan ba Dan waya taso Yi da AQEEL ASAD adaren sbd goben nayi komai zai iya sauyawa batareda sun samu lokacin dakatar dashiba,


Fitowa Amal tayi ya nufi dakinta bayan taga baccin mommyn yayi nisa.


Tana shiga bedroom dinta tubewa tafara yi ta nufi toilet tayi wanka ta fito sanyeda bathrobe pink tana qamshin shower gel dinta na asalin original makari.


Sama sama ta Dan shafa Mai da body spray ta saka White silk Riga da wandon bacci ta kwanta bayan ta kashe wayarta gabaki daya.


Mintina kalilan bacci ya dauketa sbd itama kanta dake Dan ciwo.


AQEEL ASAD daga IDON NERA's Bai koma gidansa ba Kai tsaye gidansa daya na karatunsa ya wuce Wanda shima Babu abinda ya rasa na luxury life din dako wane attajiri yake buqata.


Koda ya Isa a Daren Al-Amin na gidan ya rigasa isowa Yana jiransa sbd Kiran da yayi Masa akan ya samesa yanzu.


Kallon Al-Amin yayi Bayan ya zauna ya kafin ya maida kallonsa kan shigogon hannunsa na patek Philippe ya kalli time kafin ya kalli date din ranar.


Maida kallonsa kan Al-Amin yayi cikin nutsuwa da yafada Masa daurin auren da zaayi goben da dauran bayanan abubuwan da zaiyi.


Dagowa Al-Amin yayi yana kallonsa da idanuwansa ba Dan fili sbd tsananin mamaki.


Cikin girmamawa yace,


"Ok sir zaa gudanar da komai kafin time din daurin auren inshallah.


Harya juya yadawo yace,


"Names na invitations din Sir???


Rufe idanuwansa yayi ahankali zuciyarsa sai alokacin take kokarin ambatar sunan MARYAMAH da wani sunan..


Ahankali yace,


"AQEEL ASAD and AMAL SANDA....


Subucewa iPad din hannun Al-Amin tayi sbd rikicewar dayayi lokaci daya.,


Saurin tarota yayi Yana riqewa dakyau murya na Dan rawa yace,


"IDON NERA???


Batareda AQEEL din yasoba ya dago idanuwansa dasukai laushi ya zuba Masa su.


Da sauri Al-Amin din Yakuma juyawa Ya nufi kofa Yana cewa,


"Sorry Sir,
Angama.


Ficewa yayi Yana daga wayarsa Dan Kiran inda zaa hada lafiyayyan invitation da zai watsawa manyan mutane da jamaar Dr AQEEL ASAD din kowa zai sama nasa kafin safe lokacin daurin auren.


Acikin Daren kwana Al-Amin yayi aikin hidimar daurin auren kafin safe komai ya kammala cikin qanqanin lokaci Dan haka Koda safiyar ranar ta waye da labarin auren AQEEL ASAD aka tashi wanda ya sama harda SSG Hayat da baya qasar.


Gidansa ya dawo da safiyar ranar anan yayi shirinsa tsaf cikin wani lafiyayyan tsadaddiyar luxury milk Cashmere.


Daga Bilkees harsu umma da Haj Maryamah dakowa yake fushi da kowa a gidan basusan dawowarsa ba da safen har shiryawarsa da ficewarsa kamar yanda basusan abinda yake faruwa basusa labarin komai sbd mufeeda ma dake harkan Social media sosai bata cikin kwanciyar hankalin kunna wayarta sbd zancen rikicin tun kwanaki daketa yawo Ana maganar shiyasa ta goge duk wani app dinta dazaisa tagani ta zauna ahakan sai baya kwana biyu komai yawuce.
#MAMUH#
SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!


Makarantar Lafiya dake garin Kazaure (Kazaure school of health technology) tana farincikin sanardaku cewa ta Kawo wani sabon tsarin karatu a saukake na part-time Degree da Diploma a wasu kwasakwasai domin ma'aikata masuson karin karatu da 'yan Kasuwa wanda basu da isasshen lokaci.


Kwasakwasan kamar haka:


DIPLOMA


1.Dental surgery Technician


2.Medical X-ray Technician


3.Health Information Technician


4.National Diploma in Biomedical Engineering


5.Public Health Technician


6. Community Health Extension Worker (Re-trainee)


7.Junior community Health Extension Worker (JCHEW)


DEGREE


1. Health Information Management


2.Public Health


3.English Language


4.Public Administration


5.Business Administration


6. Economics


7. Accounting


8.Computer Science


9.Mass Communication


10.Agricultural Economics


Domin karin bayani a tuntubi wannan Lambobin:08035298851, 07066542055 ko Azo haraban makaranta dake No 3 Emir's Palace road off Kano-Daura road Kazaure a jihar Jigawan Nijeriya










*_ZAFAFA BIYAR_*


*RUMBUN K'AYA*🔥
Hafsat Rano


*DAUDAR GORA*🔥
Billyn Abdul


*IDON NERA*🔥
Mamuhgee


*A RUBUCE TAKE*🔥
Safiya huguma


*KI KULANI*🔥
Miss xoxo


Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200


ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN


0022419171
Maryam sani
Access bank


Shedarka ta 09033181070


MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN


09166221261


🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*


+22799643131


Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA


*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*🔥


38


*_Arewabooks@Mamuhgee_*


38


Tun sallar asuba uncle Lulu yake yawon son magana da zainab sbd tun tsakar dare shine mutum na farko da aka turowa iv din ta waya,


Kwana yayi Yana juya sadakin a hannunsa,


Ita kanta Anty Fareedah ba qaramin firgata tayiba da Jin maganar auren,


Amal da auren Dole?


Mai Mata Kuma?


Harma da budurwar 'ya,


Bayan duk wannan AQEEL ASAD 'dan Haj Maryamah...


Numfashi Mai zafi ta sauke Dan kuwa lamarin akwai rudani Mai girma Amma Kuma ta wani bangaren auren yayi Mata 100% sbd AQEEL ASAD shine Mijin nunawa duniya da Amal dinsu zata samu Kuma abin nunawa duniya Suma AQEEL ASAD ya zama sirikin ahalinsu na IDON NERA,


Zasu sake samun power da suna kamar yanda itadai takeso.


Har qarfe Tara saura uncle Lulu na yawon son magana da zainab Amma har lokacin maganin baccin Bai saketaba,


Bayason Amal tasan meyake faruwa shiyasa yaqi nacewa sai ya yada zainab din Kamar yanda ita ta rokesa aka Dan Allah abar mommyn tayi bacci tunda duk kwanakin Bata samun bacci sbd damuwa.


Ganin yanda Amal ta Dage aka abar mommyn tayi bacci isashe yasa Dole yabarwa Allah yaje ya shirya zuciyarsa na wani irin bugu da tsallen rashin sanin abinyi.


Lokacin daurin auren da aka saka yayi saura kadan,


Manyan mutane zasu taru shi zaa tsaya jira bayan yasan sadakin na hannunsa Kuma shine zai bada auren,


Koya je ko kar yaje yasan auren kamar an daura ne Dan Haka gwara yaje yabada auren Babynsa AMAL Kamar yanda ya basa na siddi


Dan wannan shine burinsa na ganin ya aurar dasu su dukan to Amma na Amal din yazo da babba rudani da firgici.


Dan Haka zuwan nasa kamar Dole ne baida zabi bayan na qarasa shiryawa yaja motarsa Kai tsaye ya nufi babban masallacin AQEEL ASAD din dake hade da gidan karatunsa cikin shigarsa ta alfarma.


Amal kuwa wanka tayi takoma bedroom dinta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login