Showing 48001 words to 51000 words out of 149977 words

Chapter 17 - IDON NERA BY MAMUHGEE CMPLT.txt

25 Nov 2024

6520

qunci da tsoro,
Allah yagani tanason Mijinta sosai,


Kuma zuwa wannan lokacin ta fahimci idan namiji yaso aure idonsa ya rufe a auren kaikuma kace baka yardaba karshe naka auren ne zaiyi rawa.,


Da daddare ta samesa Dan suyi magana Amma har lokacin Ransa a matuqar bace yake Bai saukaba..


Abinda takasa ganewa shine ba iya fashin auren yakejiba matakin dasu Idon Nera din zasu dauka na saka qarar ko wani Abu akanta akan abinda tayi din.


***Amal kuwa gabaki daya kashe wayarta tayi sbd ko sunan Hayat din Bata buqatan gani,
Idan Dama baifi qarfin matarsaba Baya iya controlling dinta Kuma ita yayi Mata alkawarin babu inda zasu hadu bare matsala ta biyo baya gashi sunje itada mahaukaciyar kawarta suna son saka Mata ciwon kai tun Bata auresaba.


Sidda ma takaicinta da mamakinta duka yaqare akan yanda matar Hayat din tasamu guts na aikata wanna rainin hankalin da rashin hankali.


Ita dai Amal ta tattara Hayat din da lamarinsa ta watsar tukuna sai idan taji zata iya saurararsa tukuna tasake bi takan maganar neman auren nasa.




***Kwana biyu Nafee ta dauka fushinsa da bacin Ransa Mai wucewa ne Amma sai abin ya shallake tinaninta sbd tafiya ma yayi kusan sati daya kafin ya dawo Kuma still babu wani sauyi a yanayinsa.


Tayi kukan,tayi adduar tayi fushin itama Amma duka babu sauki bare sauyi Dan Haka ta tattara makaman yaqinta tafara zubarwa sbd mafita dai Bata samuba sunyi sunyi Amma babu alamar samun mafitar Dan Haka tafara saduda akan lamarin Dan batason rabuwa da Mijinta,


Shikuwa daqyar yasamu ya kwantar da Kai gurin Haj Zainab da uncle Lulu aka janye zancen sukai hakuri saidai baisan ya makomar zancen aurensa yakeba da AMAL amma tunda Haj Zainab da uncle Lulu sun sauko yasan komai yawuce sauran gimbiyar yasamu ta sauko tayi hakuri.




Nafee kuwa nuna Masa tayi ta sauko gabaki daya ta hakura da auren nasa da AMAL Amma ta bayan fage itada Bilkees din Basu saki komai dukaba sunata fafutikan yanda zasu samu auren daya fara lalacewa ya qarasa lalacewa afasa gabaki daya.


Dukkanin mafita da hanyar neman lalata auren sun rasa face daya wadda kusan itace suka gwada farko saidai wannan karon babbar Kara zasu saka malaman addini su saka IDON NERA's a kotun musulinci Dan harga Allah barnar dasuke yadawa da koyarwa tayi yawa ga alumma,
Babban gidan karuwan da IDON NERA takedashi a garin yafi wasu makarantin girma nesa ba kusa ba.


Bilkees ce ta bada wannan shawarar Dan harga Allah cikin tsakiyar ranta takejin tsanar duka ahalin IDON NERA shiyasa har lokacin ko hotonsu babu Wanda ta kalla Dan ma kada ta zuciyarta tasake 'daci da kyansu da ake zuzutawa Wanda ya zama na banza tunda ya qare a rayuwar banza da wofi.






****Ajiye wayar hannunta tayi bayan tagama sauraron duka bayanin Barr Salahudeen,


Kallonta uncle Lulu keyi Yana jiran Jin abinda zata fada.


Numfashi ta sauke ahankali tana qarasa ajiye wayarta gefenta ranta na Dan neman baci tace,


"Qara ce aka Kuma sakani Kuma Wai malaman musulinci a kotun musulinci...


Bansan wannan karon waye zai Kuma yin wannan yunqurin ba,


So nawa Wai akeson ganin bayana da ahalina?
Kusan komai na irin wannan rigingimun sun kwanta Amma Kuma yanzu ko wane me tsaurin Ido da zafin kan ne ya sake Kai sunana???


Uncle Lulu mayar da bayansa yayi ya Jingina da kujerar dayake Kai Yana Dan hade fuska yace,


"Ko waye wannan banajin yasan illar abinda ya aikata,
Me suke nema da wannan familyn ne dako yaushe ake Mana barazana da kotun musulinci.,
Yanzu me su Barr Salahudeen din sukace???


Wani numfashin son watsar da zancen kada ya dameta ta sake kafin tace,


"Zasuyi abinda zasuyi Amma bazani kotun ba idanma malaman sun tsananta ne zanje muyi magana Amma baa kotun ba,,shine abinda Barr yafada.


Amal ce tashigo palon sanyeda Riga da skirt na cotton lace Mara nauyi da ado sosai,
Ba dankwalin kayan a kanta sai qaramin gyalen data daura iya kanta da qaramar bvlgari handbag a hannunta sai key na motarta..


Siddi siddi ce a bayanta suka qaraso tsakiyar palon tareda zama Amal na cewa,


"Uncle barka da yamma.
Mommy Yaya dai Naga fuskanki a yamutse??


Siddi datake maqale kusada mommyn batama lura ba ta dago ta kalleta cikin kulawa tace,


"Mommy All ok right????


Numfashi haj Zainab din ta sauke tana kallon Amal kafin ta kalli Siddi tace,


"Yes baby,
Kan Amal datake kallonta har lokacin ta maida kallonta sbd Ko kadan Amal Bata Wasa da damuwar mummyn Koda mummyn tace babu komai Amal Bata yarda idan taga alamar damuwa ko tunani atareda ita tana ganewa Dan haka take nuna tata damuwar har sai mummyn ta cire komai duk da basuda wata damuwar sai irin wadda baa rasaba data danganci sanaoi da huldodinsu mummy dashi uncle Lulu din.


Cikin basar da yanayinta dake nuna ciwon kan da ake neman saka Mata da sabon lamarin daya bullo da batasonma su Amal su sani Dan dukkaninsu zafi zasu dauka.


Tana kyakkyawan murmushi Mai Fadi akan fuskarta tace,


"Sweetie babu komai kaman yanda nafada Miki ki Dena kallona Haka Mana.


Dariya siddi tayi tana kallon fararen idanuwan Amal din akan mummy tace,


"Mummy Nan gaba Amal ce zata ringa Miki juyamu duka.


Wani kallo Amal din tayiwa siddi zatayi magana uncle Lulu ya katseta dacewa,


"Karki biyeta sweetie idan na nutsu zuwa gobe idan kin dawo makaranta zanyi magana dake.


Ok Uncle" Amal din tace cikin muryarta me tattarreda rashin rawar Kai ko hayaniya.


Kallon Haj Zainab tayi yace,


Zanyi magana dasu Salahudeen anjima da kaina
Zan sanar dake duk yanda muka Kai qarshen zancen.


Miqewa yayi ya fice daga palon zuwa bagarensa dan yasamu magana dasu Barr cikin nutsuwa tunda acan basa son su Amal su San da zancen zasu kashesa batareda kowama daga familyn ya saniba tunda Daman an Saba ba yauba suke kashe case bataredama ko sunansu an Kuma maimaitawa a idan aka fadesaba.




Tashi Amal tayi ta nufe bedroom dinta Kai tsaye bayan ta cewa Bilkisu ta dafa Mata Noodle daya da carrot kawai sai dafaffen kwai.


Tana shiga bedroom din Jakarta da key na mota dake hannunta ta ajiye gaban mirror ta zare kayanta ta nufi toilet tana zare band dake daure da manyan kalban kanta masu tsayi.


Wanka tayo ta fito da bathrobe ash ta nufi gaban mirror ta shirya sharp sharp sbd sallar dake Kanta ta laasar da bataiba sbd fitowarsu lectures kenan ta dawo gida.


Skirt da hijab na sallah ta saka tayi sallah tana idarwa Bata tashiba akai magrib ta miqe tayi tana idarwa tayi adduointa ta miqe tareda zare kayan ta maida closet ta janyo wata doguwar Riga Mata hannu ta saka ta nufi comfortable resting kujeran dake dakin nata ta zauna ta janyo wayarta daketa haske alamar Kira.


Hayat ne me kiran,
Qaramin numfashi ta furzar tareda maida wayar ta ajiye tana miqewa ta fice dakin.


Kitchen ta nufa Dan duba idan an dafa mata abinda tace din sbd batason abinci Mai zafi Sam shiyasa tace a dafa din kafin ta fito ya rage zafi.


Tana shiga ta tadda an dafa Mata din Dan Haka anan kitchen ta zauna kan dan qaramin dining din ciki tanaci tana Dan fira sama sama dasu Bilkisun Dan Dama kusan gidan itace tafi sakewa dasu bayan mummy wadda ta dauki duka masu aikinta kamar 'yayanta ko qannenta tunda a qarqashinta suke.


Siddi ce Sam Bata wani sake musu Amma Kuma bata wulaqantasu,
Uncle Lulu kuwa babi abindama yake hadasa da masu aiki idan ba masu gadi da securities dinsuba na gidan Suma Kuma baya wani zama bare yasan yanda zaiyi treating nasu unfairly barema suna aikinsu yanda ya Kamata Dan Haka Yana musu ma yakeyi duk lokacinda yasamu damar tsayawa dasu din.


Fareedah ce take Dan wulaqanta masu aikin gidan sbd ta taso gidansu basusan darajar masu aikinba Amma Kuma ahankali ta tattara ta Dena itama ta Dena kyararsu sbd anan basa hakan
Tana denawa din itama saitaji ta raba kanta da wahala sbd wani lokacin wahalarda Kai ne da sakawa Kai ciwon Rai faman ihu da wahalarwa ga masu aikin.




Karfe bakwai da rabi sukai dinner dinsu gabaki dayansu Kamar yanda suka Saba
Suna gamawa kowa ya nufi inda yake so
Wasu sukai dakunansu wasu Kuma palon sama suka nufa Dan acan suke fira iyasu familyn kawai baqi basa zuwar dasu palonsu na sama.


Amal dakinta tanufa sbd tanada abinda zatayi.




Uncle Lulu kuwa yayi magana dasu Barr Salahudeen sun basa tabbacin lamarin yazo da Dan tsauri Amma dai zuwa gobe zasu kashe zancen kwata kwata inshallah.


Sanarda IDON NERA yayi tace Gaskia Dole su kashe zancen zuwa gobe Dan har tafiya takeson Yi Amma wanna qarar zata tsaida ita ta Bata Mata lokaci.
#MAMUH#
#PURELOVE#MARRIAGE#
DS AQEEL ASAD#AMAL IDON NERA#
#SISTERS






*_ZAFAFA BIYAR_*


*RUMBUN K'AYA*πŸ”₯
Hafsat Rano


*DAUDAR GORA*πŸ”₯
Billyn Abdul


*IDON NERA*πŸ”₯
Mamuhgee


*A RUBUCE TAKE*πŸ”₯
Safiya huguma


*KI KULANI*πŸ”₯
Miss xoxo


Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200


ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN


0022419171
Maryam sani
Access bank


Shedarka ta 09033181070


MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN


09166221261


πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*


+22799643131


Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA


*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*πŸ”₯
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
26
Washe gari tunda safe uncle ya fita zuwa Office dinsu inda zai tattauna dasu Barr Salahudeen akan maganar data fara qular dasu tun jiya Ana abu daya ankasa magana daya.


Isowar Barr Salahudeen da Salis babban Yaronsu makusancinsu shida Haj Zainab din yasashi kallonsu Yana kallon lokacin kusan karfe daya Amma sai lokacin suka samu barowa daga offishin Alkalin kotun..


Zama sukayi Barr Salahudeen na sauke numfashi me Dan zafi Yana zare farin glass din fuskarsa ya ajiye gefe Yana dawo da kallonsa kan uncle Lulu yace,


"Sir Lulu wallahi wanna karon matsala suke son bamu sbd Kamar ta inda qarar ta fito Suma sunada power sosai Kuma sunada qarfi a Bangaren amfani da musulincin...


Ajiye wayarsa uncle Lulu yayi Yana zare nasa glass din shima Yana kallon Salis da shima duk nasa ran yake a matuqar bace da koma wane Dan iskan ne keson kawo musu rainin hankali da wulaqanci a rayuwarsu dake tafiya daidai.


Maida kallonsa yayi kan Barr Salahudeen Yana kokarin danne bacin Ran dake cin Ransa yace,


"Barr Salahudeen kaman yanda kasaba kasan yanda zakayi wannan maganar ta 'bata,
Ta mutu,a rufeta gabaki daya kafin gobe ko sunan Zainab da IDON NERA kada akuma ambata kwata kwata a wannan kotun,
Ko nawa ne kaman yanda kasani Salis zai bada a tabbatarda zancen Nan Bai sake tashiba bare fita.


Sir Lulu insha Allah kafin goben zamu tsaya muga yanda zaayi.


Gyada musu Kai Kawai yai Yana Jingina da lafiyayyar kujerar dake office din nasa Dan ko magana bazai iyayiba sbd Ransa da yayi zafi,


Wannan hukumar musulinci ake magana wadda duk connections dasuke dasu bazasuyi aikiba agurin sbd kowa na shiga zaayi tir dashi sbd Cewa zaayi sun cin mutuncin addini da malamansa,


Su kansu sunada iko da damar da zasu kashe case komai girmansa cikin mintina kalilan Amma wannan ba damar wani nuna wani budadden iko ko girman dasuke dashi sbd tir da Mugayen diban albarkar da zaa bi zuriarsu dashi akan sunyiwa addini tsaurin Ido Dole a boye zasu bullowa lamarin suyi watsi da qarar kafin daga baya suyi lokacin Wanda yayi qarar Dan bazasu yafewa ko waneneba yakeson tarwatsasu a boye ba.




Koda ya dawo gida Bai fadawa Haj Zainab babu abinda aka samu akaiba akan zamcenba sbd kada ranta ya baci ta daga zancen duniya taji maqiyansu sufara musu dariya anfara fin qarfinsu.




Barr Salahudeen da Salis harma da wasu manyan lauyoyin guda biyu a ranar sun nuna duk wata basirarsu Dan kashe qarar akan wanna qarar rashin hujja ce Amma babu abinda ya girgiza malaman da alqalan sun tsaya akan sai Haj Zainab Idon Nera tazo kotu itada Lulu Idon Nera.




Zafi kan lauyoyin ya dauka Wanda yasa Dole suka sanar dasu Haj Zainab abinda ake ciki qarshe manyan hayoyin datake dasu tayi amfani Wanda ya sake tsanananta case din
Sadai sun samu yanda suke so zancen yafara sanyi.


Daya daga cikin alqalan dasu bilkees suke sakarwa wasu irin matsiyatan kudi suna qarya da sunan Mijinta DR SHAYKH AQEEL ASAD akan yasan duk abinda yake faruwa ne ya sanar dasu IDON NERA sunfara nasarar kashe zancen.


Cikin bacin Rai da baqin cikin wannan mummunan labarin yasa suka saka aka fidda zancen a Media take aka San da rikicin Idon Nera da kotun musulinci Ana Kuma jiran aga Suma malamai da alqalan musulinci idan tafi qarfinsu.




Fitar zancen a koina ya lalatawa su uncle Lulu komai Dan kuwa tini aka yada zancen a kafafen yada labaran media..


Su Amal sai alokacin sukasan me yake faruwa.


Ran Amal yayi mummunan baci matuqa musamman da kusan kowa neman abin yadawa akeyi akansu koyaushe tunda sun zamarwa mutane qayar maqoshi,wasu Kuma sonsu sukeyi suna matuqar burgesu.


Kamar yanda kowa ya Santa batada hakurin reni bare wulaqanci Dama babu Wanda ya Isa yayi Mata,


Mahaifiyarta itace rayuwarta babu Mai taba mahaifiyarta Tai shiru akan hakan,
Duk zagi da Mugayen sunayen da ake kiransu dashi musamman mummynsu bai taba damunta ba sbd tasan ba halayensu bane Kuma sunan Bai taba damun mommynba shiyasa suka taso da rashin damuwar duk abinda zaa fada akansu Amma Banda cin zarafi ko yunqurin tozartasu
Shi wannan wani abune da basa dauka, Dan kuwa suna amfani da iko da dukiya su koyarda duk Wanda yashiga huruminsu da niyar tozarci.


Kaf ahalin Haj Zainab itace wadda idan aka taba a ahalin kowa yake gaggawar kasa jurewa sai inda karfinsu ya qare.


Wannan cin mutuncin da aka bullo dashi Rana tsaka zaa musu ta tabbatarda daga matar SSG ya fito dan Haka zata nuna musu tafisu zama karuwar dasuke tinani.


Senator jarma mahaifin Anty Fareedah shima Kai tsaye yashiga cikin zancen da kamar familynsa ne su sbd 'yarsa dake cikinsu tana aure cikin kauna Mai tsanani da kwanciyar hankali da aminci.


Kusan shima Mijin Siddi yanata nasa kokarin gurin ganin an kashe zancen Amma tako Ina kamar anyiwa case din hayaqi.


Su Bilkees kuwa sai alokacin duniya tayi musu Dadi hankalinsu yakwanta suka tattara zancen dasukasan zuwa yanzu maganar auren yagama lalatuwa suka watsar zuciyoyinsu fes suda 'yayansu.




Karfe Tara na safe Amal ya fito daga gidansu cikin motarta Ford fiesta fara Ranta har lokacin quna yakeyi sosai akan haukar matar Hayat ta isheta gwara ta nuna Mata su waye IDON NERA.


Kai tsaye Office dinsa ta nufa sbd yanata Kira Bata dauka batajin zata kirasa da Haka ta nufa office dinsa Kai tsaye.


Tana Isa babban building din tayi parking ta fito motarta Kai tsaye ta nufi reception Bata tsayaba ta nufi office dinsa Kai tsaye dayake receptionist din ta San itace Sabuwar Amaryar Sir din nasu sai Bata tsayar da itaba saima sannu da zuwa datake Mata Amma ko ta kanta Amal din batayiba ta wuce.


Tana Isa kofar office dinsa secretary dinsa ya taso da sauri Yana Mata sannu da zuwa bakinsa a washe Amma ganin yanayin fuskarta yasashi Dan takaitawa da cewa "Welcome Ms AMAL" kawai.


Zaune yake Yana waya cikin black suits dasukai Masa kyau sosai
Wani mahummin conference meeting zasuyi da turawa shida Amininsa akan wani kasuwancin hadin gwiwar dasuke dasu shiyasa yayi shigar suites din.


Shigowarta yasashi katse Kiran cikeda mamakin ganinta da Kuma sanyin jikin ganinta bayan tsawon kwanaki data qi barinsa ganinta.


Dayake yau batada school futan safe ne zuwa gurinsa kawai Dan Haka blue pencil jeans me ajikinta da farar free Balenciaga sweater data bayyanarda wayewarta da rashin ruwanta a lamarin kowa sai nata.


Kanta silk Versace scarf ne wayarta daga wayarta sai key din motarta a hannunta sai qamshinta Mai sanyi da kashe jiki tareda Kama guri ahankali.


Tasowa yayi cikeda kaunarta data Gama Masa illa Yana kallonta Yana cewa,


"AMAL da kinkirani kinsan cewa zanzo.....


Rufe fararen idanuwanta Tai tareda budewa Kai tsaye tana kallonsa ta bude baki tace,


"Kasan me abinda matarka takeyi kuwa?
Kasan meyasa tun farko naqi yarda da auren masu mata??
Sbd irin wannan rashin hankalin da hayaniyar ne,
Meyasa matarka zata ringa shiga alamuran family na??


Hayat kafi kowa sanin bazan aurekaba matarka namun wanna haukan tun ban shigaba wlh na shiga tamun makamancin haka saina saka anrufeta asibitin mahaukata har tsufa ko kai bazaka fiddotaba,..


Meye hakan?
Meye matsalarta damu?
Sbd zaa aura Mijinta??
To tun wuri ka janye maganar auren tunda bazaka iya controlling dinta da haukantaba.....


Zafi Kansa ya dauka sbd idan ran Amal din ya baci Dama Bata saurarawa
Gashi ya kasa fahimtar kokuma yarda da Nafee nada saka hannu a lamarin tunda ta saduda ta hakura da rungumi qaddara Amma Kuma bazai nuna qin yardarsaba kada Amal din ta sake Hawa tun Bata furta kalmar fasa auren ba tazo ta furta..


Shirunsa yasa Amal kallonsa cikin tsananin bacin Rai da mamaki tace,


"Like seriously HayatΒΏΒΏ


Dama mezata tsammata agurin me Mata sbd matansu sungama maidasu wawaye and useless.


Juyawa tayi ranta a matuqar bace da har tayi gangancin yarda zata auri Hayat din tun farko bayan Daman batada raayin auren masu Matan.


Cikin sauri da damuwa yayi saurin zagayowa ya tareta Kansa na sake daukan zafi gashi meeting dinsa ya kusa Baqonsa ma yakusa isowa ga rigimar Amal din Kuma wadda bazaitaba son bacin ranta ba.


"Amal koma menene na Miki alqawarin Zan duba komai da kyau Ni kaina bazan taba barin duk Wanda ya tabaki ko familynki ba....


"Hayat please kaje kaji da kanka Kuma,.Ni na Gama da Nan Kuma..


Kofa ta nufa ranta a bace kafin takai hannu kan kofa aka turo kofar ahankali cikin nutsuwa tareda shigowa Kai tsaye sbd baiyi tunanin akwai mutane a kofarba.


Kirjinsa da nata ne ya kusan haduwa batareda kowannensu yasan da zuwa kowannensu din ba.....


A lokacin daya kowannensu ya ja baya musamman shi din da har qamshin jikinta ya shiga hancinsa Sosai sbd kusan dasukai Sosai.


Qamshin tsadadden Turaren VICTORIOUS CARBON na Boadicea da Bata taba jinsa agun kowaba yasata dagowa zata kalli Wanda yake daukeda wannan coolest qamshin Mai nutsuwa.....


AQEEL ASAD da baya buqatan ganin ko waye tunda ya shaqi qamshinta ya fahimci mace ce,


Tana dagowa ya tabata ya wuce ciki office din sanye cikin Royal blue Slim fit D&G suit qamshinsa na gauraya office din Kai tsaye sofa ya Isa ya zauna sai alokacin ya dago manyan idanuwansa masu kyau da kwarjini Mai nutsuwa ya kalli Hayat Wanda shigowar AQEEL ASAD ta sanyasa kasa bin Amal wadda itama Bata waiwayoba ta fice ranta a bace.


Wani numfashi Mai zafi SSG din ya sauke tareda dawowa ya zauna Yana kasa kallon AQEEL ASAD wanda yasan bazai ce Masa komaiba akan ganin mace a office dinsa duk da babu ta inda Amal tayi Kama da maaikatansu bare yayi tunanin maaikaciyarsu ce duk da yasan ko Kallonta AQEEL ASAD baiyiba barema ya damu da sanin wacece.


Zaiyi maganar gyara zancen ganin mace da AQEEL ASAD din yayi Dan kare Kansa,
AQEEL ASAD din ya katsesa da dagowa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login