Showing 51001 words to 54000 words out of 149977 words

Chapter 18 - IDON NERA BY MAMUHGEE CMPLT.txt

25 Nov 2024

6516

ya kallesa a natse cikin sanyin kalami da kamewarsa yace,


"Muje time yayi.


Miqewa yayi tareda wucewa gaba Dan Dama conference meeting dinne kawai ya kawosa office din Hayat din da safen.


Inda zasuyi conference meeting acikin maaikatansu SSG din suka nufa Kai tsaye sbd suna gamawa AQEEL zai bar maaikatan yanada gurin zuwa Mai mahummanci da aka gayyacesa akan wani case na manyan Bata garin da aka Kama Ana tuhuma da yada barna Wanda akeson shigarsa cikin lamarin sbd qarfin dayake dashi a kotun musulinci dayake taimakwa sosai da dukiyarsa Mai yawa.


Sai qarfe goma Sha daya harda rabi suka kammala Dan Haka Kai tsaye yabar gurin,..


Yaso komawa gida Kansa ya 'dan sake yakuma sauya kayan jikinsa saidai lokacinda ya bada na zuwansa ganinsu yayi Dan Haka yace drivernsa ya wuce dashi can din Kai tsaye tunda yasan suna can sun taru manyan malaman Ana jiran isowarsa.


Yana Isa babban ofishin yaqi da barna a musulinci Wanda yake cikeda offices na manya malamai da manya alqalai na musulinci da manyan lauyoyin musulinci,


Babban guri Mai tsaro da dokoki tareda tsayawa addini da musulincin da musulmai harma da human rights duk sunada aciki.


Yana daya daga cikin manyan masu bada gudunmawa Mai girman tsoka agurin tafiyar da komai,


Bawani babba bane a shekaru sosai Dan kusan da yawan alkalan da malaman sun girmesa Amma Kuma Ana respecting dinsa sosai sbd tsayawa dakuma dukiyar dayake bawa agency din sosai ga kuma iliminsa a addinin da saninsa daya qara Masa girma da suna sosai agurin mutane bayan sunan dayake dashi a harkar business dinsa da aikinsa da uwa uba dukiya wadda ke qarawa mutane suna.


Isowarsa gurin yasa jamaa da Dama suka iso Ana Masa barka da zuwa..


Wani irin kwarjini da cika idone dashi Wanda yasa da yawa ake sauke Masa Kai koda an girmesa,


Yanada kamewa da haiba datake qara Masa girma a gurin mutane Dan haka ake yawan neman shaawara ko zaunawa dashi idan suna neman maganin matsalar data addabi bangaren aikin nasu,
Duk wani taro babba na addini dazai buqaci manyan mutane Yana daya daga cikin wainda baa iya Dena gayyata ta musamman wannan yasa da yawa suke kiranda da DR SHAYKH AQEEL ASAD sbd Basu ciresa cikin manyan malamai masu daraja da aka saniba gashi matashin daya fara zama dattijo abokin Manya,ga kudi ga ilimin Boko Dana addini ga kamewa da wayewar rayuwa Mai aji da tsafta.
##MAMUH
#AQEEL ASAD/IDON NERA
#PURELOVE/HOTLOVE




*_ZAFAFA BIYAR_*


*RUMBUN K'AYA*πŸ”₯
Hafsat Rano


*DAUDAR GORA*πŸ”₯
Billyn Abdul


*IDON NERA*πŸ”₯
Mamuhgee


*A RUBUCE TAKE*πŸ”₯
Safiya huguma


*KI KULANI*πŸ”₯
Miss xoxo


Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200


ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN


0022419171
Maryam sani
Access bank


Shedarka ta 09033181070


MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN


09166221261


πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*


+22799643131


Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA


*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*πŸ”₯
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
27
Kai tsaye cikin babban palon alfarma na tarbon manyan Baki aka nufa dashi Yana tafiyarsa cikeda nutsuwa da Dan kokarin sake fuskarsa dabai cika sakewaba.


Cikin girmamawa da mutuntawa sosai ya gaisa da Alkalai kusan uku da manyan malamai kusan bakwai sai Lawyoyinsu biyu.


Cikin nutsuwa aka fara karanto halaye da babbar shaharar da IDON NERA sukai a barna,


Shiru yayi kyakkyawar fuskarsa na Dan sauyawa da irin munanan abubuwan da aka fada wainnan IDON NERA din na aikatawa,


"Ita asalin IDON NERA din aurarrakinta iya wainda aka kiyasta aka sani aure goma Sha daya,
Sauran aurarrakin nata da baasan dasuba awainda tayi ne kafin daukakarta sai Wanda taje har qasashe biyu tayi ta dawo Wanda hade lissafinsu abin ba dadin fada,


Duka wannan auren babu Wanda tayi da zuciya daya,.
Da manufofi takeyinsu Kuma ta kashe auren ta fito Kai tsaye babu shakka ko tsoron Allah,


'yayanta biyu duka babu mai tarbiya gashi Suma ta dorasa akan wannan muguwar tarbiyar ta auren masu kudin suna fitowa domin yada barna,


Yayanta dasuke uwa daya uba daya 'dan daudu ne na musamman dayake tareda manya Yana yada tasa barnar shima,


Babban gidan barna na karuwai dake garin Nan nasu ne ikonta ne,itace uwar karuwai da Yan daudu,


Tako Ina yada barna sukeyi,


Akwai babbar qungiyar manyan karuwai dasuka zama manyan Mata sun mallaki gidaje da dukiyoyin kansu suna sake lalata tarbiyar alumma da wasu dabiu da halayensu,


Ita IDON NERA ta tsaya musu tako wane bangare na hukuma,
Tanada manya connections,
Tanada manyan mutane,manyan Yan siyasa masu mukamai maana manya qasa,
Tanada manya tako Ina dasuke tsayawa aduk lamuranta..


Tana amfani da 'yayanta Mata guda biyu gurin mallaka da juya manya yanda takeso, maana yayanta sune mukullin barnar datake aikatawa manya da yawa suna tsaya Mata sbd kwadayi da shaawar auren yayan nata,
Dayar tahau hanyar uwar na aure aure,
Dayar Kuma a yanzu itace take yanda takeso da manyan mutane,


Sun tarwatsa aurarrakin mutane da Dana da nasu son ran da ganin iko
Qarshe dai kullum sake samun qaruwar karuwai da yan daudu akeyi na yayan musulmai da dama da yawa duk a qarqashin iko da sunanta...


Anyita rigingimun daukan mataki akan wannan barnar tata datake yawa Amma babu wani nasara sakamakon koyaushe juyar da dalilan akeyi a kashe to wannan karon lamarin ya dauki zafi sbd motar karuwai biyu da aka Kama masu qananun shekaru dasuka tabbatarda a qarqashinta suke,


A bangare daya Kuma yarta AMAL IDON NERA tana yunqurin lalata aurarrakki da dama gurin amfani da kyanta gurin raba maza da matayensu na sunna da 'yaya da ubaninsu..


Karshe dai anyi magana da lauyoyinta da manya da suka Shiga zancen mafita ake nema akan lamarin nata Dan Haka aka yanke shawarar janye shariar zaa zauna da ita ayi sulhu tareda magance yawan barnar datake yadawa.


Wannan shine taqaitaccen bayani Dan kadan akan Haj Zainab IDON NERA..qarasa zancen lauyan musulincin yayi Yana dagowa ya kalli AQEEL ASAD Wanda ya Dan Yi qasa da Kansa Yana rintse fararen idanuwansa sbd sunan da aka ambaci wannan matar dashi Wanda agurinsa sune ne mafi girma da tsarki da kauna a rayuwarsa gabaki dayanta...


Yayi baqin ciki da 'dacin Jin wannan sunan Ita wanna matar takedashi..


Bude idanuwan nasa yayi ahankali tareda Dan jinjin Kai Kawai ahankali sbd harga Allah basan ma me akeson yaceba akan lamarin Dan lamarin wannan IDON NERA din yayi Muni da girmama sosai,
Da alama babu ilimin addini kwata kwata a tsakanin familyn IDON NERAn sbd komai lalacewarta Bai Kamata ta lalata rayuwar 'yayanta sbd su din Amanace Allah yabata Dan 'yaya Amana ne ga iyaye..


Koma menene Lamarin yayi munin da bazai iya shigaba Amma dai yabada goyan bayan a dauki matakin gyara da kawar da barnar sbd alummar gaba da Basu taso ba kada barnar tayi yawa.


Tattaunawa sauran alkalan da malamai sukayi aka bawa lauyoyi damar su sanar da lauyoyinta Kiransu gareta a gobe...


AQEEL ASAD yabada uzurin bazai samu zuwaba gaskia so duk yanda sukai yayi Allah yasa hakan shine sanadin shiriyarta da zuriarta.


Fitowa yayi ya shiga motar drivernsa yaja suka bar gurin.


Wani sanyayyan numfashi Mai sanyi ya sake Yana Dan kokarin yakice tinanika akan masu irin wannan rayuwar barnar da sabon ubangiji,


Shi ya rasa wani bangarene Mai mahummanci a rayuwarsa Amma gabaki daya rayuwarsa tayi duhu baya cikin walwala da farin cikin daya Kamata sbd kullum da Abin yake kwana yake tashi tsawon shekaru Amma yakasa sabawa da rayuwa babusu Babu masaniyar halinda sike ciki,
Ganin yakeyi Allah bazai barsaba idan har wadda tayi dawainiyarsa fiyeda tasa uwar,.


ta sadaukar da rayuwartaba ta basa kaunarta da dukkanin rayuwarta,


Taci kashinsa,
Tasha fitsarinsa da guminta,


Amma karshe tana can tana garari a duniya batareda yasan wane Hali ko rayuwar take cikiba alhalin shi Yanada arziki da wadatar da zuriarsa zasuyi rayuwar hutu da wadata har jikokinsa Kila,


Meye amfanin Arzkin idan har wadda ya dage ya zamo wani abin dominta Bata tareda shi hakama Alqawarin daya dauka mata ya tashi a iska,


Menene makomar alqawarinsa akan MARYAMAH wadda ayanzu yasan ta girma batareda tasan Shiba...


ahakan Yaya yake jinsa bare masu aikata laifi irin wannan da qazamar rayuwa Mai tattareda daudar qazantaccen lefi Amma suke rayuwa hankalinsu kwance sbd kawai sunada iko a hannunsa Wanda shima ta hanyar suka samesa.


Ahankali ya Dan rufe idanuwansa dasuka sauya ya bude Yana waiwayowa kadan ya kalli wayarsa datake vibrating a gefensa na shigowar Kira.


Hayat ne,
Numfashi ya dan sauke ahankali ahankali tareda daukan wayar ya Dora akan kunnensa a natse yace,


"Aslm,Yes HayatΒΏ


Ajiyar zuciya Mai zafi Hayat ya sauke daga can bangaren Yana kokarin danne bacin Ransa yace,


"A ASAD we need to talk,
Yaushe Zan sameka?


Kallon time yayi kafin cikin Dan mamaki yace,


"Akwai matsala ne?


"Ina buqatan ganinka inaga zanzo anjima kokuma na sameka gidan baqinka da karatunka anjiman.


"Alright" yace Yana ajiye wayar gefensa.


Suna Isa gida ya fito mota ya nufi sashen mahaifiyarsa Kai tsaye Yana kashe duka wayoyinsa.


Zaune take kan 2 seater dake babban palon nata na alfarma da aka tsarashi kamar na sabuwar matashiyar masu arziki..


Hutu da daular duniya yasa jikinta Yana Nan a daidai Babu wani tsufa daya bayyana sosai sosai atareda ita saidai manyanci da Kuma ilimin Boko Dana addini datake Yi ayanzu sbd kusan sbd AQEEL ASAD din suma sun koma Yan addini gidan.


Tun Bai qarasa shigowaba tasan da shine zai shigo sbd kusan kaf duka jamaar gidan da masu aikin gidan da securities dasukasan waye maigidan to tabbas sun sheda qamshinsa daya na musamman daya Gama Kama jiki da dukkanin abinda yake tabawa.


Asmau dake aikin sake gyare palon Haj Maryamah din tana Jin qamshinsa ta tattara kayan aikinta tabar palon.


Wata jarida Haj Maryamah din ke karantawa tana Jin shigowarsa ta dago kanta fuskarta a sake da kulawa da kaunarsa Mai tsananin wahalarda ita sbd takasa samun cikakken 'danta yanda kowace uwa ke samun 'yayanta.


Kyakkyawar fuskarsa Mai cikeda zallan kwarjini da nutsuwa tareda kamewa take kallo shima ita din ya kalla bayan yashiho da sallamarsa Mai nutsuwa.


Zama yayi a kujerar dake gefenta idanuwansa suka sauka akan jaridar datake karantawa ta ajiyewa wadda take daukeda sunan IDON NERA da manyan Baki a gefe daya..Wanda ita umman Bata damu da karanta labarai ire irensuba tunda ta fahimci IDON NERAs din wasu manyan hamshaqan karuwai ne sai Bata ko duba duk inda zaa ambaci sunan sbd suna ko abinda ya hada alaqa da sunan karuwai wani babban lamarin ne datayiwa tsana ta cikin jini da ruhi,
Kuma kusan kowa yasanta yasanda ko sunan dayayi kama da masu irin wannan rayuwar baa ambata agabanta shiyasa duk rikicin gidan SSG Bilkees Bata sanar Mata ba Dan tasan baa ambatar irin wainnan qazamar rayuwar a gabanta.


Bai tsaya karanta sauran bayanin ba ya dauke Kansa daga Kai Yana cewa,


"Umma barka da yamma?
Ya bp din? Dr Aisha tazo ta duba yau kuwa??


Numfashi ta sauke tana Jin dadin kulawar dayake Bata wadda zatace bayan ita kulawar sosai dayake bata Babu sauran Wasa da sakewa tsakaninta dashi daga biyayya sai kulawa sai bin umarninta,


So take danta yayi dariya,
Yayi walwala,
Ya sake yayi raha ko doguwar dariya da farin ciki a gabanta Amma duka Bata samu ganin wannan ba Dan Haka sai rayuwar ta zama kamar ba shi kadaiba itama rayuwar quncin takeyi da rashin walwala da farin ciki,


Mufeeda ce sanyin idaniyarta datake debe Mata kewar AQEEL din take Mata Wasa da hayaniya da dariya da duk wani rawar Kai da walwala,
Sai Bilkees datake zuba nata rayuwar yanda takeso a gidan itama.


Adduarta da rokonta datake yawaita sadaka da ciyarda mabuqata shine Allah yakawo sauyi Mai tsarki da tsafta a rayuwar AQEEL ASAD dinta,


Allah yakawo lokacin dazataga danta cikin farin ciki da walwala tareda dariya akan fuskarsa....


Kuma kullum adduarta da sadakar datakeyi akan addua biyune,


Bayan kawo farin ciki rayuwar 'danta dayar itace Allah ya cire Zainab da 'yarta kwata kwata daga zuciyarsa sbd sune Quncin dayake cin rayuwar danta,


Bata fata ko a mafarki ko wata Mai suna zainab tasake shigowa rayuwar AQEEL ASAD dinta Dan ita tini ta goge sunan daga kowane fanni na rayuwarta,


Kamar yanda Zainab tayi Mata alqawarin ko Mai sunanta bazata Kuma ambata da bakintaba Haka itama tayiwa kanta da rayuwarta alqawarin ko Mai suna zainab bazata Kuma alaqa dashiba a rayuwarta har abada.


Agurin umman yaci abinci tareda ita a dining suna Dan magana harya Gama ya miqe bayan ya goge bakinsa da tissue yabar sashen gabaki daya.


Yana Isa babban part dinsa dayafi koina girma a gidan ya nufi master bedroom dinsa Kai tsaye Yana balle maballan farar qal din tsadaddiyar long sleeve din dake ciki ta suits din dake jikinsa.


Yana Gama zare rigar yako daga Shi sai dogon wandon suits din
Lafiyayyar fatarsa Mai daukan hankali ta bayyana tareda faffadan kirjinsa dayasa Bilkees data shigo dakin Kai tsaye Jin wata sabuwar tsimammiyar kaunarsa na rufeta koina..


Motsinta yasashi juyowa ya kalleta tareda maida hankalinsa gurin nufar hanyar toilet dinsa Mai tsananin girma ya shige Yana zare wandon ya shige Jacuzzi Yana sakarwa Kansa ruwan dumi bakuma masu zafiba.


Tasan abinda yasa yayi Mata kallo daya kuma baice Mata mo kalma dayaba wato shigowa Kai tsaye ba sallama kamar yanda musulinci ya bada umarni.


Ajiyar zuciya ta sauke tana juyawa Dan kuwa koma menene ita sam Bata jin haushi Kuma Bata taba jin haushiba aduk abinda yake faruwa da rayuwar auren nasu tunda dai shi din mallakinta ne Kuma baya nuna Mata qi hakama Yana tattalinta tareda Bata kulawa da kauna to me kuma zata damu kanta dashi bayan ta tsaya tsayin dogarai ta Hana kowa shigowa rayuwarsu Dan kuwa a shirye take tsaf da Hana kowace mace rabar Mijinta uwa uba mahaifiyarsa Bata son ya wani qara auren sbd batason kwashe kwashe.


Wanka yai yafiti daureda brown towel Mai dan girma jikinsa na tsiyayar ruwan wanka dake tsiyayar tsantsi a fatarsa sbd tsantsi da lafiyarta.


Cikin navy blue plain tsaddan yadin manya yafito qamshinsa na tashi ahankali ya nufi dayan gidansa dayake ganin baqi acan tareda karatunsa na addini da wasu ayyukansa na office da sauransu.


Babban gidane daya tsaru matuka tareda tsari Mai kyau da nutsuwa.


Koda ya Isa Hayat na gidan na jiransa Dan Haka sallar magriba suka fara Yi a babban masallacin daya gina hade da gidan nasa ta gefe daya.


Suna gamawa suka dawo ciki
Suka zauna lafiyayyan palonsa ya kalli Hayat din da idanuwansa a natse Yana sauraron bayanin dayake Masa akan su Nafee da Bilkees ne suka shigarda qarar IDON NERA sbd auren 'yarta daya da zaiyi.


Kallonsa AQEEL ASAD din yakeyi idanuwansa na Dan bayyanarda mamakin duka bayanan abubuwan dasuke faruwa din.


Shiru yayi and dukkaninsu sun aikata abubuwane dabai taba tunanin zasu aikata din ba,


Meya hada Hayat din da aure a irin wannan gidan,


Su Kuma Matan menene yakaisu Shiga irin wannan maganar ta wainda rayuwarsu kwata kwata Babu abin dadin fada aciki.


Babban abin mamakin shine ta yanda Hayat da girmansa da mutuncinsa zai iya daga hankali Haka akan mace irin wannan harda rabuwa da iyalinsa akan hakan.






Har kusan dare sosai suna tare suna tattaunawa Wanda kusan duka mamaki ne da damuwa ma sosai AQEEL ASAD din yashiga akan 'dan uwan nasa gameda wannan masifar data shigo rayuwarsa.


Yana dawowa gida Bai nunawa Bilkees yasan komai akan lamarin bak kamar yanda Bata fada Masa shigarta shaani irin wannan ba da mutuncinta harsu iya Shiga lamarin Wainda mutuncinsu koina baa fada da kyau Saida fata shiriya yake musu kawai.


Washe gari a gidan SSG da rikicin sosai aka tashi Wanda ya ja Hayat din yayiwa nafee saki daya


Hakan ya kawo damuwa sosai da tashin hankula a tsakanin ahalin umma ma sai alokacin tasan abinda yake faruwa take tashiga mamaki da tashin hankalin meyakai Hayat hulda da irin wainna mutanen gashinan sun zamo mummunan masifa a rayuwar familynsa sun rabasa da matarsa.


qarfe goma AQEEL ASAD yabar office dinsa drivernsa ya jasa zuwa Inda zaayi meeting din Alkalai da manyan malaman tareda lauyoyin IDON NERA da lauyoyin musulinci..


Yana buqatan Shiga wannan lamarin dole kobai so ba sbd kawo sulhu da qarshen matsalar gida da rayuwar Dan uwansa Amininsa Hayat sbd a yanda kauna Mai qarfi da kusancinsu yake dashi bazai Bari gidansa ya lalace ya tarwatseba akan wannan masifaffiyar qaddarar data shigo rayuwarsa.


Jin isowarsa yasa aka dataka da komai aka jirasa Yana isowa aka tarbosa cikin wani farin soft tsadadden yadi
Komai nasa nutsuwace zalla aciki da sanin Kai tareda kwarjini.


Yana Isa ko qarasawa ciki baiyiba lafiyayyar motar Haj Zainab ta iso gurin tareda motar uncle Lulu da lauyoyinta biyu.


Sanye take cikin purple and pink lace dayake kwance ba nauyi sbd tsadarsa,
Mayafin jikinta zuwa handbag da takarmin qafarta Babu Wanda ba manyan kudine suka siyesaba.


Kyanta kuwa kamar yanda aka Santa Yana Nan shiyasa Suma malaman suke dauke kallonsu daga gareta Dan kaucewa iskar shedan.


Shi Kansa uncle Lulu kana ganinsa kasan Nera ta zaune ta kwanta a rayuwarsu Dan Haka Kai tsaye suka qarasa office din da ake jiransu hankali kwance ba alamar damuwa.
##MAMUH#






*_ZAFAFA BIYAR_*


*RUMBUN K'AYA*πŸ”₯
Hafsat Rano


*DAUDAR GORA*πŸ”₯
Billyn Abdul


*IDON NERA*πŸ”₯
Mamuhgee


*A RUBUCE TAKE*πŸ”₯
Safiya huguma


*KI KULANI*πŸ”₯
Miss xoxo


Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200


ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN


0022419171
Maryam sani
Access bank


Shedarka ta 09033181070


MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN


09166221261


πŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺπŸ‡³πŸ‡ͺ
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*


+22799643131


Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA


*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*πŸ”₯


*_Arewabooks@Mamuhgee_*
28
Lauyanta ne a gaba kafin ita da uncle Lulu a baya suka shiga..


Gurinda za zasu zauna aka nuna musu suka zauna gefe daya tareda lauyyinsu,


Ajiye Hermes handbag dinta tayi a gefenta tareda fuskantar jamaar dake babban offishin taron.,


Kai tsaye ta gaidasu gajerar gaisuwa batareda ta tsaya qare musu kalloba ta maida hankalinta gurin sauraron bayanan da aka fara korowa na munanan Lefuka da barnar da akeda tabbacin tana aikatawa kuma ake aikatawa a qarqashinta..


Batason Jan zance da batawa juna da zaman sulhun lokaci Dan Haka Kai tsaye Babu boyo ko shakka ta zayyano abubuwan da ake aikatawa da sunanta wainda tasan batada alaqa ko hulda dasu ko bayanansu Bata kawoba sbd Bama yarda zaayiba dan Haka atafi ahakan..


Lauyanta ne ya karba zancen da fara bada hakuri dakuma godiyar yarda da sulhun da akai,


Kallon Haj Zainab din yayi wadda itama ta dago lokacin zatayi magana idanuwanta suka sauka akan Fuskar data sakata sarqewa da yawun bakin da zatayi magana dashi...


Tari Mai qarfi ne ya rufeta hannuwanta na daukan rawa a hankali..


Cikin kulawa da mamakin abinda ya sametan uncle Lulu ya kalleta Yana Dan tasowa da bayansa dake jingine jikin kujerar dayake kai ahankali yace,


"Yar uwa Yaya dai?
Are you ok??


Kasa magana tayi sbd tsananin da tarin ya qara sosai
Take idanuwanta suka fara ja ta dafe kirjinta tanayi..


Da sauri Barr Salahudeen ya leqa waje yace Salis yakawo Mata ruwa da sauri...


Ko awane masifaffen Hali take na dimuwa ko ciwo ko hauka
Bazata taba kasa gane AQEEL ASADULLAH ba,
Kamai girma da manyanta da zaiyi da sauyawar da zaiyi kuwa bzata taba kasa ganesaba..


To Amma meya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login