Showing 81001 words to 84000 words out of 149977 words
Maryamah din kamar yanda labari yazo musu daga wasu daga securities din gidan da aka raba wasu ke gadin wancan gidan nasa inda akai daurin aure.
Bilkees dake zaman boyon Kai itada yarta sbd su umma datasan suna jiran samun lokacintane Dan sosai taga bacin rai da fushin dasukai akan abinda tayi hakan yasa ta kame kanta a guri daya tayi qaryar rashin lafiya itama ta lafe itada yarta suna jiran qurar ta lafa suji inda aka tsaya idan anyi watsi an rabu har abada tsakanin su umman da Idon Nera da 'yarta.
Mufeeda a ranar da safe kamar almara taga bayanin auren AQEEL ASAD din na yawo Amma Bata wani damuba sbd tinaninsu wancan zancen ne aketa yawo dashi har lokacin sbd sunsan Babu ta yanda zaayi Yayi auren da ake fadan batareda sanin familynsa.,
Bilkees da mufeeda ta fada Mata itama Bata wani damuba Kai tsaye tace,
"Yanzu bana buqatan wahalarda Kaina da damuwar komai sbd su umma suna yaqin ne amma nice Mai qaruwa da hakan,
Ban buqatan sakawa kaina rashin sukuni akan Idon Nera da duka kwashe kwashenta sbd nasan su umma har abada bazasu yarda da alaqarta 'yarta,
Dan Haka Ni hakan ma yamun ba damuwarsu gabana yanzu ta Mijina zanyi Dan ko sunan wata MARYAMAH bazan Bari aringa fada agabasaba tunda an yanke alaqar tasu.
Mufeeda ma cikin son komai da umminta tafada ya tabbata tace,
"Amal Idon Nera itace damuwata Ni,
Ko inda daddyna yake ban kaunar ace tasake bi bare,
Wlh umme da munsan Haka abin zai zama da zamewa kikai ta auri Uncle SSG ma can suda suka Saba da duka wannan tashin hankalin su qarata nidai wlh ko alaqa da akace mamanta nada da umman daddyna naji ciwo da zafinsa tareda baqin ciki Mai tsanani akan hakan,
Nayi takaici da baqin cikin hada jini da ita ko yayane.
Bilkees ambatar sunan gidan Nafee yasata hade fuska tana Jinjina Kai mamakin Nafeen nasake Kamata Dan kuwa duk wannan rigimar da akeyi takasa kiranta ko zuwar Mata bayan ita a lokacin nata yaqin itace ta tsaya mata,
Zatayi lokacinta daga Baya idan tasamu kanta yanda ya Kamata.
Rashin ganin AQEEL tunda safiyar ranar yasata Kiran wayarsa cikeda narke murya ta fara magana ya dakatar da ita ta hanyar cemata Yana asibiti umma ba lafiya.
Da mamaki sosai tace,
Meya samu umman?
Shine bansaniba har umma na asibiti,
Wane asibitin ne zanzo yanzu tareda mufeeda.
Cikin rashin son Jan zancen yace,
"Karki zo ba wani sabon ciwon bane hawan jinin ne dakuma zuwan Abu
Kimata addua kawai
Doctors ma since kada a dameta hutawa kawai take buqata
Nima ganinan dawowa gidan zuwan anjima.
Tana kashe wayar numfashi ta sauke tana mamakin ciwo har sosai Haka Amma Bata saniba.
Bangaren su umman ta shirya ta nufa cikeda sanyin jikin dake nuna batada lafiyar itama.
Gaida umma dake kwance ba lafiyar itama tayi zatayi magana umman ta daga Mata hannu
da hannun ta nuna Mata batason magana Dan Allah ta tafi tabari saita dawo daidai tukuna.
Da mamaki Bilkees din tasake kallon umman tana cewa,
"To lafiya dai kuwa?
Ni hankalina yatashi Kuma da rashin lafiyar tamu duka nima fama nakeyi da kaina daqyar na iya tasowa nazo.
Ko kallonta umma Bata sake yiba saima wani kallon Data Sakar Mata tanada tabbacin Bilkees din batada labarin auren mijin nata Dan Haka itama saitaqi fada tana ayyanawa da ba Yar Zainab ya auraba da wlh kyalesa zasuyi da auren suyi maganin Bilkees din,
Amma ko yanzu wlh sai tasan abinda tayi Bari dai su samu kansu sufara yakice Zainab da jininta ataredasu kafin suyi lokacin nata iskancin datayi musun.
Ganin ba fuska yasa Bilkees tashi ta tafiyarta,
Kai tsaye girki tasa akai na musamman da kanta ta jeresu a dining din babban palonsu daya raba samansa dasu.
Bayan sallar magrib ta fito fes cikin adon Riga da skirt na atampa dasukai Mata kyau ta fito babban palon suna fira da yarta hankali kwance.
Qarfe Tara da mintina hamsin da hudu ya dawo gidan daga asibitin da gobe insha Allah yakesa ran a sallamo umman.
Duk da akwai gajiya da ciwon kan yamutsin ranar ataredashi Amma nutsuwarsa da kamewarsa yasa kamar a lokacin aka Gama daurin auren
Yayi Mata kyau sosai Cikin shigar tasa ta daurin auren har lokacin.
Mufeeda sannu da zuwa Tai Masa kawai ta kyalesa ya wuce samansa ganin Yana buqatan hutawa.
Bilkees ce ta bisa cikin kulawa.
Koda ta hawo baya Palo Dan haka ta wuce bedroom dinsa Kai tsaye ta taddasa harya tube Yana daureda towel a qugunsa brown.
Fresh fatar jikinsa Mai hutu da lafiya ta kalla tareda Jin shaawarsa Mai qarfi sbd kakkarfar siffarsa dake sake daukan hankalinta da kwadaita dashi.
Qarasowa tayi ahankali tana murmushi ta tsaya gabansa tareda saka hannuwanta biyu akan towel dinsa tana Masa wani irin kallon tsananin so tace,
"Kwana biyun Nan baka zama meyasa ne?
Yau Ina kaje ne kayi irin wannan kyan?....
Sai alokacin ya kalli fuskarta ahankali Yana karantar fuskarta dake jiran amsarsa.
Cikin sauti Mara hayaniya da kwanciyar hankali Kai tsaye yace,
"Wani Auren aka daura min ayau.....
Cak ta tsaya da abinda takeyi da towel dinsa ta dago ta kallesa
Yayi maganar Babu shakka Babu fargaba bare wani damuwa Kai tsaye ko ajikinsa.
Wani murmushin kana Wasa ne ta sakar Masa tana jiran yadai fada Mata gaskia,
Shima wani lafiyayyan tsadaddiyar murmushinsa ya sakar Mata ahankali tareda juyawa ya nufi toilet dinsa yana gyara towel dinsa data kunce gabaki daya.
##MAMUH#
#LOVE
#AQEEL ASAD/AMAL SANDA IDON NERA
*_ZAFAFA BIYAR_*
*RUMBUN K'AYA*🔥
Hafsat Rano
*DAUDAR GORA*🔥
Billyn Abdul
*IDON NERA*🔥
Mamuhgee
*A RUBUCE TAKE*🔥
Safiya huguma
*KI KULANI*🔥
Miss xoxo
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200
ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN
0022419171
Maryam sani
Access bank
Shedarka ta 09033181070
MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN
09166221261
🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*
+22799643131
Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA
*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*🔥
42
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
42
Bayansa Bilkees tabi da kallo harya shige toilet ya rufe kofar hankalinsa kwance kamar baice komaiba
A qataicema ko waiwayota baiyiba bare yaga yanayinta da karbi zancen Dan murmurshinta na kana Wasa ne tayi Masa Amma shi nasa me yake nufi??
Wani makamancin murmushi tasake tana girgiza kai Dan kuwa Wasa yakeyi duk da baya wasan Amma yau kula soyayyarta ta motsa Masa ne yake Mata tsokanar soyayya.
Guri ta nema ta zauna tana jiran fitowarsa dan su qarasa wasan da tsokanar,
Ya Jima cikin toilet din Yana wanka a natse Babu gaggawa kafin ya fito daure da wani towel din daban ba wanda ya shiga dashiba fatarsa tasake zama fresh sai daukan Ido takeyi
Qafafunsa na sunyi fes Kamar Wanda baya fita dasu sbd tsabar hutu da tsaftansu.
Qamshin Aesop bath soap ne yake tashi jikinsa lokacinda ya kusanto ta kallon ya Dan Yi tareda wucewa gaban mirror Yana sake goge jikinsa da wani qaramin towel din batareda yace komaiba.
Tasowa tayi ta tsaya bayansa tana kallonsa ta cikin madubi tace,
"Daddyn M Meye kake nufi da wannan zancan dakayi?
Nidai banason wannan wasan Dan Allah kada ka sakemun wlh zuciyana bataso..
Ta cikin madubin ya dago Idanuwansa ya zuba Mata wani irin kallon daya sata sake mutuwa akansa Kamar bazaiyi magana ba sai Kuma ya bude bakinsa cikin muryarsa Mai nutsuwa kamar ko yaushe yace,
"Bayan auren danace Miki nayi ayau akwai wani zancen ne Dana fada Miki Wanda zuciyan naki bataso??
A hada mun salad shi kawai zanci bana buqatan komai.
Kallon cikin madubin taga kamar Bata ganinsa da kyau Dan Haka ta juyo gabansa inda zata gansa dakyau fes a gabanta.
Bai juyo ya kalletaba Saida yagama shafa tsadadden man fatarsa da turare Mara qarfi ya Dan juyo ahankali ya kalleta yaga yanda take kallonsa ahankali yace,
"Yaya?akwai wani abin ne?
Kasa magana tayi sai kallonsa takeyi kamar gunki sbd so take tagama Dora kowace kalmarsa gurin zamanta kafin ta hadasu ta fahimta,
Hannunsa ya daga ahankali yakai kan fuskarta ya Dan taba ahankali Yana kallonta yace,
"Are you ok???
Hannunsa ta riqe ta janye daga fuskarta annurin fuskarta na gushewa gabaki daya tace,
"Wane aure kake nufi Daddyn M?
Aure dai Aure irin nawa da naka?
Auren da zaka kawo wata matar ka Bata komai da komai kaman Ni??
Gurin closet dinsa ya nufa Yana Dan yamutsa fuska kadan sbd Bai dauka zancen ne Bata ganeba
Baikuma San wane ganewar ce batayiba Acikin simple amsarsa na cewa Aure yai ayau din.
Fararen silk long sleeve pyjamas na bacci ya saka ya juyo yaga yanda taketa binsa da kallo takasa magana.
Ahankali yakai hannunsa ya Kama nata yajata sukayo palonsa inda Bayan sanyin AC da qamshin Freshners masasu Dadi sai zallan Qamshinsa na victorious carbon daya Kama duka palonsa har bedroom dinsa.
Suna isowa tsakiyar palon ta zare hannunta daga nasa tana jifansa da kalli idanuwanta na sauyawa Kai tsaye tace,
"Bakace komaiba fa a tambayana.
Dakatawa yayi tareda juyowa ahankali ya Mata wani kallo Yana kame fuskarsa yace,
"Banason maimaita zance kinsani,
Aure nayi,kisaka zancen a kunenki da kyau sbd bazan sake maimaitawa ba.
Wucewa yayi Kai tsaye inda aka jera Masa abinci ya zauna da Kansa ya zuba orange drink yakai bakinsa yasha..
Hannu bilkeeyta Dora akai zata kurma wani mahaukacin ihu kaman yasani ya zare cup din daga bakinsa ya kalleta cikin katseta yace,
"Karkiyi wannan anan,
Meye kike tinanin zakiyi?
Ina iliminki na addini?
Aure fa nace ba wani abun ba....
Kasa riqe ihunta tayi ta nufi kofa da gudu batareda ta tsaya Jin sauran abinda yake fadaba stairs take saukowa batareda tana binsu daya bayan dayaba,
Hudu hudu take hadawa gurin saukowar
Tana isowa tsakiyar palon qasan ta kurma wani irin ihun dayasa mufeeda fitowa da gudu da rigar datake sakawa ba shiri..
Rintse idanuwansa yayi ahankali tareda ajiye cup din hannunsa sbd saukar ihun nata har cikin kunnensa.
Ajiyar zuciya ya sauke ahankali batareda yaji zafinta ba ko laifinta sbd tabbas yasan zata shiga damuwa saidai Kuma aure anyi Babu Wani sauran abinda ya rage Wanda zai iya yiwa kowa,
Dukkaninsu Babu Wanda zai sakarwa fuska ko bawa damar komai aka maganar auren Nan tun daga kan iyayen nasa har su Matan nasa sbd gabaki dayansu tako wane bangare Babu Mai naam da auren Dan haka Babu wadda zai bawa Dama ko daya akan tinkararsa da wani zancen.,
Itama Bilkees ayanda take yanzu idan ya lallabata qarasa rikicewa zatayi tayita haukar dazai jawo musu attention na duniya da sabuwar fitina Dan Haka zai barsu su dukan kowa yagama borinsa ya dawo hayyacinsa Dan Kansa.
Couscous da aka dafa da veggies ya zuba kadan yaci yasha ruwa ya miqe yaje yayi brush yadawo ya zauna ya saka Kiran Maminsa wadda tariga tayi bacci lokacin.
Mufeeda data fito a matuqar gigice da gudu tayi kan umminta tana Kiran sunata hankali tashe tana cewa,
"Umme waye ya rasu?
Ina daddyna?
Meya samesa?
Hajiyar Cameroon ce ta rasu??
Masu aikinta ma da gudu duk suka fito suka tsaya daga nesa bakin kofar fitowa daga kitchen suna kallonta cikin tsoro da tashin hankali da mamakin abinda ya faru.
Wani kukan ihun takuma sakewa tana neman shaqewa jikinta dukkaninsa na rawa tace,
"Aure aka daurawa daddynki yau mufeeda mun shiga uku mun lalace da wannan qaddarar Mai wuyar cinyewa..
Innalillahi wainna ilayhi rajiun...
Masu aikin najin hakan sukai saurin sulalewa sukabar gurin tin kafin a San da tsayuwarsu a sauke fushin kansu.
Sakinta mufeeda tayi da sauri tana fiddo idanuwanta gabaki daya waje hankali tashe tace,
"Umme aure kuma?
Daddyn?
Da gaske ne abinda muka gani ake nufi?
Umme badai Amal Idon Nera ya auraba????
Sai alokacin Bilkees ta dakata da kukan datakeyi Mai tsananin gaske ta kalli mufeeda zuciyarta na sake rufewa da wani irin zafi da ciwo ta girgiza kai tana cewa,
"Bazai aura Amal Idon Nera ba sbd su umma sunfison yabar duniya daya auri 'yar Idon Nera.,
Shima bazai taba yarda da hankalinsa da iliminsa da wayewa da girma da dukiyarsa ya auri karuwa kuma 'yar karuwa ba.
Zai yiyuba,su umma bazasu taba yarda ya aura Yar IDON NERA ba...
Wani irin sanyi da mutuwa jikin mufeeda yayi ta zame tayi zaman Yan bori gefen ummin tata idanuwanta na cikowa da hawaye masu tsananin zafi tace,
"Wllhi umme ita ya aura tunda Kikaga umma na asibiti na asibiti ta Suma na tabbatarda Akan auren ne...
Yanzu kenan daddyna ya auri karuwa??
Umme da kinsani kinbarsu can sun qarata a gidan uncle SSG gashinan yanzu tadawo kan Daddyna
Ni wlh bazan iya fita mutaneba idan ta tabbata daddyna Amal Idon Nera ya aura.
Kuka ta fashe dashi tana nufar dakinta da gudu sbd Jin takeyi kamar zuciyarta zata fashe.
Bilkees kuwa bacewa kukanta yayi bat sbd maganar mufeeda din data hasko mata gaskiyar data kasa hangowa,
idan har ba 'yar Zainab din AQEEL ASAD ya auraba Meye zai saka su umma hawan jinin gaggawa da qarewa a asibiti.
Wani busashen yawu ta hadiye daqyar tana Jin jikinta n sanyi Kuma,
Me ake nufi da ita?
Su umma boye Mata ne akai kokuwa tunda dazu ta shiga gurin umman Cameroon din Amma Bata fada Mata komaiba,
Cutatarta akeda niyar Yi kome?
Boye Mata zaayi kamar yanda suka boye Mata alaqarsu da zuwansu gidan IDON NERA tun farko?
Hummmmm" ta sauke wani numfashi Mai nauyi da zafi..
Indai kuwa boye Mata akeda niyar Yi tabbas akwai wuta a qasa kwance Dan kuwa zataga yanda zaayi rayuwa a wannan zuriar da wannan auren da kowa yake maqiyin kowa.
Tashi tayi a haukace zata nufi kofar fita wata zuciyar ta hanata
Ta dawo qafafunta na wata irin rawa takai kanta dakinta tana Shiga ta rufe ta zube qasa tareda sake fasa kuka Mai qarfi tana dafe kirjinta dake tafarfasa.
Dannar zuciyarta tayita yi tana kuka sbd tasamu bin komai ta fahimci abinda ake nufi da ita Dan tasan Idan tayi haukar Komai lalace Mata zaiyi batareda tasan Ina makamar zancen takeba.
Wani zafi da radadin zuciya ta kwana dashi tana kuka,
Yanda taga Rana Ido biyu Haka taga Daren Idon tsaye,
Jin takeyi zuciyarta na tafasa da tsanar duk Wanda yake gidan na zuriar AQEEL da Idon Nera gabaki dayansu.,
Mufeeda ma Ido biyu taga safiya cikeda damuwa da kukan datasha qarshe ma da wani irin zazzabi ta tashi umminta Kuma da ciwon kai Mai tsananin gaske dayasa ko fitowa taqi yi,.
Taga Kiran AQEEL ASAD a wayarta da safen Amma yaqi daukan wayar karshe kashe wayar tayi gabaki daya.
Daga ita har mufeeda Babu Wanda ya fito yaje gaidasa kaman yanda suka saba suna sake kowace ta rufe dakinta Tama wi fitowa.
Yasan abinda yake damunsu Dan Haka Bai takura neman nasu ba yabari su sauko tukuna.
Baiyi breakfast ba qarfe goma yafito a shirye cikin milk luxury yadi Mai taushi.
Kai tsaye sashen ummansa yaje yafara duba umman Cameroon wadda itama Sam taqi yarda tagansa taqi fitowa daga dakinta tace ace Masa yaje kawai batason ganinsa sai uwarsa tadawo zatayi lokacinsa.
Yana fitowa malam Rabiu ya taso ya bude Masa mota ya shiga suka nufi gate securities na matsowa gurin motar suka Masa barka da fitowa cikin girmamawa.
Suna fitowa daga gate din gidan malam Rabiu yahau titi Kai tsaye hanyar gidan IDON NERA ya nufa sbd yasaba zuwa yanzu kusan kullum saisun biya da safe kafin AQEEL din ya wuce office dinsa.
Tun Basu qarasoba Securities suka hango lafiyayyar motarsa a tafe
Dan Haka suka tashi sa sauri suka bude Masa gate suna Masa barka da zuwa cikin girmamawa.
zaune suke a Palo suna Shirin yin breakfast daqyar siddi ta shawo kan Amal ta fito da ita yin breakfast din fuskarta babu walwala ko kadan saidai ta Dan sake daga kumburin kukan datayi jiyan sbd Bata sake wani kukanba tayiwa kanta alqawarin hakan.
Kayan bacci ne fafare qal ajikinta Riga da wando gajeru masu tsantsi
ba bra ajikinta hakama ko Babu komai akanta daga ita sai slippers farare masu laushi.
Siddi ce a gaba sai ita a baya fuskarta takoma Yar Qarama sbd rashin isasehn bacci.
Anty Fareedah ce da Haj Zainab a zaune suna jiran saukowarta uncle Lulu yayi tafiya yau din tunda safe sbd akwai da abinda zai kaisu kaduna Amma sbd halinda ake ciki Dole shi kadai sai salahudden yabi jirji ya wuce.
Qamshinsa daya fara shiga hancin Haj Zainab Bayan Bilkisu ta bude Masa kofa yasata waiwayawa ta kalli kofar alokacin ya shigo take ya sauya musu iskar palon da kamshinsa Mai dadi.
Anty Fareedah ma kallo daya tayi Masa ta miqe tsaye tana kasa sake kallonsa sbd cika idanun dayakewa mutane.
A natse tana Dan sake fuska ta gaidasaa shima ya amsa batareda ya kalleta sosaiba.
Maminsa ya qarasa gurinta itama ta miqe tsaye tana kallonsa kafin ta amsa nutsatsiyar gaisuwarsa tace,
Muje breakfast kayi breakfast tukuna.
Cikin yanayi na kulawa ya kalleta sbd ko a yanayin fushi yasan Mami Bata qin basa kulawa.
Magana zaiyi su Amal da basu lura dashiba Saida ta iso tsakiyar palon taji qamshin data tabbatarda nasa ne ta kame fuskarta nauyin zuciyarta na neman dawowa.
Siddi ce itama cikin sakin fuska da girmamawa tace Masa Good morning.
Waiwayowa yayi ya amsa batareda itama ya kalleta sosai dinba..
Maida kallonsa yayi kan Amal ya zuba Mata fararen idanuwansa yayi mata kallon sakanni kafin ya dauke Kansa ya dawo da kallonsa kan Mami datake kallon Amal tana jiran taji ta gaidasa kosa a maqoshi ne.
Ta gabansa tabi ta wucewarta Kai tsaye zuwa hanyar dining batareda ta damu da kallon da kowa yabita dashiba musamman Anty Fareedah dake kollon kayan jikinta da suka lafe ajikinta.
##MAMUH#
#LOVE/HOTLOVE
#AQEEL ASAD#AMAL SANDA
*_ZAFAFA BIYAR_*
*RUMBUN K'AYA*🔥
Hafsat Rano
*DAUDAR GORA*🔥
Billyn Abdul
*IDON NERA*🔥
Mamuhgee
*A RUBUCE TAKE*🔥
Safiya huguma
*KI KULANI*🔥
Miss xoxo
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200
ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN
0022419171
Maryam sani
Access bank
Shedarka ta 09033181070
MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN
09166221261
🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*
+22799643131
Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA
*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*🔥
43
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
43
"Amal"
Haj Zainab ta Kira sunanta alokacinda take gap da qarasa barin gurin.
Dakatawa tayi batareda ta juyoba Saida Haj Zainab din tace,
"Dawo Nan.
Juyowa tayi ahankali ta dawo har lokacin Bata sake kallon inda yake shima tun kallon farkon da yai Mata Bai sake kallontaba saima time daya kalla daga Cartier watch dake daure a hannunsa.
Siddi da Anty Fareedah wucewa sukai sukabar gurin sbd ganin yanda mommyn ta Dan kame fuska.
Amal na zuwa Kai tsaye tace Mata,
"Meye hakan?
Kasa magana Amal tayi sai dagowa datayi ta kalli mommyn cikin Dan mamaki da muryarta Mara nauyi tace,
"Me nayi mommy??
Maganarta yasashi sake Dan kallonta kafin ya maida kallonsa kan Maminsa sbd time dinsa na tafiya yanada abubuwan Yi ayau din.
A natse Kai tsaye yace,
Mami ba buqatan komai
Karki damu tako Ina,
Zanji da komai,
Zan tafi inada baqi dasuke jirana yau.
Juyawa yayi har zai wuce ya dakata tareda juyowa yakalli kayan jikinta dakyau kafin ya maida kallonsa kan Haj Zainab data rasa abin cewa
Cikin nutsuwarsa da kamewa yace,
"Mami next time kada takuma fitowa ahakan.
Juyawa yayi ya wuce yabar Amal tana binsa da kallon mamaki da takaicin maganarsa.
Harya fice Bata Dena bin hanyar dayabi dinba da kallo tana tausan juciyarta akan damar daya samu.
Haj Zainab ma tashiga mamakin sbd qarfin ikonsa akan