Showing 132001 words to 135000 words out of 149977 words
nuna akwai wani abun acikinsa.
Ganin yanda ta daga hankalinta yasa shiga damuwa ya ringa rarrashinta Yana tarairayarta har gari ya waye suka taso tana a firgice cikin tunanin qaqanikayi.
##MAMUH#
*_ZAFAFA BIYAR_*
*RUMBUN K'AYA*🔥
Hafsat Rano
*DAUDAR GORA*🔥
Billyn Abdul
*IDON NERA*🔥
Mamuhgee
*A RUBUCE TAKE*🔥
Safiya huguma
*KI KULANI*🔥
Miss xoxo
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200
ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN
0022419171
Maryam sani
Access bank
Shedarka ta 09033181070
MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN
09166221261
🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*
+22799643131
Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA
*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*🔥
69
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
69
Su Haj Maryamah tsawon lokacin Nan dayayi baya gari hankalinsu baa kwance yakeba sbd yanzu akwai Zainab da 'yarta a rayuwarsa,
Suna shakkar mugun halin Zainab na kwadayin abun duniya sun sani da yarta take amfani yanzu tana juya AQEEL din yanda taga dama,
A baya da babu Zainab a rayuwarsa idan watanni nawa zaiyi a tafiya Basu taba shida damuwa ko fargababa koma daga hankali Akan komai sbd tana shedan danta a koina Allah ya tsarkake Mata shi Amma gaskia a yanzu tana cikin lissafinda Babu makama Dan kuwa daga ranarda tayi wannan muguwar shedan ta AQEEL dinta ne ya maida 'yar Zainab din mace hankalinta yakasa kwanciya da kowace irin tafiyarsa.
Duk yanda zasuyi su tabbatarda idan da ita din yayi Tafiyar sunyi Amma Basu samu wani cikakken bayanin hakanba,
Har gidan IDON NERA din sunso zuwa Amma Tina girman gargadin AQEEL aka zuwansu gidan yasa Suka daure Basu tafiba Amma Kuma suna cikin wani irin mummunan hali na matsuwa da damuwa tareda hanawa Rai sukuni,
Al-Amin koyaushe ta takirasa ta tambayesa amsarsa daya ce AQEEL ASAD shikadai yayi tafiyarsa Kuma duk tambayar dasu umman suke Masa Bai taba fadawa AQEEL din suna tambayarsaba sbd kawarwa da kowa bacin Rai da wata damuwa.
Bilkees kuwa kota kanta basa bi Bayan debe Mata albarka da umman Cameroon keyi akan Dora Mata laifin komaima Dan data zabi maqalewa Mijinta akan shegiyar rayuwar show off din datakeyi a cikin Matan manya da duk hakan bai faruba da zaa samu Dan sauki Amma Ina tanacan ta rungumi qawaye da wayewa ta Bata musu tarbiyar mufeeda sbd duk inda take zuwa da ita take zuwa yarinyar gabaki daya ta Gama daukan halayen uwarta da dabiunta.
Haj Zainab ma fuskewa kawai tayi ta saka musu Ido kaman yanda uncle Lulu yafada Amma tabbas zuciyarta tana Shiga fargaba wasu lokutan da Dama sbd sanin Amal da taurin Kai zata iya saka AQEEL ya zabi tarewanta dan kawo karshen taurin kanta
Ita Kuma gaskia haryanxu batason tarewar Amal Acikin ahalin AQEEL din Dan haryanxu tasan Babu Wanda yakeda ranar saduda acikinsu,
Ga matarsa datafi Kama da mahaukata sbd zafin kishi nahauka zata iya aikata komai
Itakuma wlh suna taba Mata 'ya zata nuna musu asalin rashin mutunci da budewar ido a bariki data samu.
Dan Haka daga Haj Zainab harsu Haj Maryamah da umma Babu me nutsuwar zuciya a matuqar matse suke da ganin dawowar yayansu,
Gwara Haj Zainab tasan suna tare su kuwa tunanin rashin sanin tabbacin Yana tareda Amal din duk yabi ya halakasu da damuwa da tinani.
Yau datasan zai dawo tun safe take tunanin zuwa airport da kanta ta daukosa sbd ganin tareda wa yadawo.
Karfe goma Sha biyu jirginsu ya sauka
Bayan rawa da koina jikinta yakeyi Babu nutsuwar dake tareda ita,
Duk iya yanda yayi dubaran rarrashinta da tarairayarta ya kwantar Mata da hankali yayi Amma gabaki daya ta firgice Masa tashin hankali ne sosai Acikin ranta,
Mommynta saita kusa samun heart attack yau idan tayi Ido biyu da ita da wannan cikin ajikinta,
Su ummansa ma bazaa rasa me samun hayewar jininda zaa qare asibiti ba,
Ita matarsa Sam ko a cikin wannan halin Bata sakota a lissafi Dan tasan haukacewa kilan zatayi.
Al-Amin ne ya daukosu daga airport
Shima kallo daya yayiwa Amal yaga cikin jikinta sbd Doguwar Laura chiffon dress ce ajikinta data kwanta Mata duk da fadinta rigar Amma sbd yadin me rawane shiyasa ta kwanta jikinta ta fidda Mata dan qaramin cikinta dan wata uku.
Shiru yayi shima Yana Satan kallon Maigidansa dake riqe da hannun matarsa suna tahowa cikin kulawa
Sunyi wani irin fresh da kyau kaman wainda suka fita qasar,
AQEEL ASAD din har wata Yar jiki yayi yaqara zama Dan balarensa.
Al-Amin lissafin kwanakinsu acan yafara da har zaace ciki yasamu harya girma.
Barka da dawowa yayi musu Yana yiwa Amal sannu da dawowa itama kafin suka nufi mota ya bude musu Suka shige.
a motar ya sanarwa da AQEEL ASAD cewan Haj Maryamah tace fa itace zata daukosa daga airport Amma dai Bai sanar da ita wane time zasu sauka ba.
Wani sanyi jikin Amal yasake dauka Jin abinda Al-Amin yafada tasan bakomai yasa Haj Maryamah tace zatazo daukansa daga airport din da kantaba sai Dan taga idan shi kadaine yake.
Rintse Idanuwanta dasuka sauya tayi sbd tashin hankali tana tunanin meyasa tun farko Suka manta da zata iya samun ciki da wuri?
To Amma Kuma ita yanzu tana tsananin son cikinta sbd ubansa Dan Haka batasan ya iyayensu dake gaba da junaba zasu amsa cikin.
Riqo hannunta yayi cikin nasa yakai bakinsa yayi kissing ahankali ya kalleta cikin kulawa da sake kwantar Mata da hankali yace,
"Ki Dena Jin komai kada wani abin ya sameki,
Daga su umma har Mami Babu Wanda zaice komai gameda cikin Nan sbd nine nakeda abuna Kuma Ina tsananin son kayana duk Wanda ya yarda da ikon Allah ya amsa ya hutawar Kansa da damuwa da ciwon zuciyoyin dasuke fama dashi
Wanda ya karbi akasin Haka Kuma wahalace zamu taru muyita Yi Amma Babu abinda zai sama cikin Nan da yardar Allah sbd alokacinda Allah ya badashi Babu Wanda ya sani.
Kallonsa kawai tayi da idanuwanta dake laushi suna kokarin cikowa da hawaye Bata iya cewa komaiba.
Wayarta ce tayi ringing
kasa motsawa tayi Saida ya Dora idanuwansa akan wayar yaga sunan Maminsa ne akai ahankali ya sake ajiyar zuciya Yana daukan wayar ya miqawa Amal din takasa magana sai kame kame murya na rawa.
Kai tsaye tambayarta Mamin tayi idan sun sauka.
Shine ya amsa wayar sukai magana ya sanar Mata sun sauka suna hanyar zuwa gida.
Batareda tunanin komaiba tace sai sun iso sbd Bata taba tunanin wani gidan yake nufiba.
Hanyar gidan karatunsa Suka nufa Kai tsaye sbd bayajin Kuma matarsa zataci gaba da zama gidansu Yana buqatanta a taredashi Dan Haka ko baa kawo Masa itaba ya dauketa shikenan zata tare gidanta.
Yanda zuciyarta ke bugawa sosai da rashin sukuni da damuwa yasa numfashinta fara fita da sauri kaman me asthma,
Jin tayi harda mararta tafara murdawa tana Mata ciwo Dan Haka tasake rikicewa tana dafe cikinta hawayen dataketa riqewa suna gangarowa..
Cikin daure fuska sosai da damuwa akai ya riqota Yana kallonta yana tambayarta abinda yake damunta,
Kasa magana tayi sbd ciwon da mararta keyi sosai
Aikuwa take hankalinsa gabaki daya ya tashi ya riqota jikinsa Kansa na neman daukan zafi.
Al-Amin na ganin hakan tun kafin AQEEL yafada abinda zaifada Masa din ya juya motar da gudu ya Kama hanyar asibitin Dr tayo.
Ko kafin su Isa ciwon yaqara tsanani
Hankali tashe aka karbeta akai ciki da ita Dr tayo ma Kai tsaye ta wuce ciki Bata tsaya Masa bayanin zasuyi iya kokarinsuba.
Dafe goshinsa yayi tareda Dan rintse a hankali ya bude yanajin zuciyarsa na wani irin nauyi,
Tashin hankalin abinda zai faru idan iyayensu sukaga ganta da cikinsa ne yasa ta daga hankalinta har yake neman rasa abinda baima Riga yashiga hannunsaba.
Meyasa zata daga hankalinta bayan tasan Yana Nan Babu abinda zai faru idan duk me gani ya gani.
Numfashi Mai zafi ya Dan sauke ahankali a lokacinda Kiran uncle Lulu yashigo wayarsa.
Kasa dagawa yayi Dan sbd bazai iya magana a lokacinba da kowa.
Al-Amin Haj Maryamah itama takira Jin shiru Yana dauka ya sanar Mata ya daukosa suna asibiti.
Cikeda mamaki da fargaba tace,
"Asibiti Kuma?
Meya faru?
Waye ba lafiya da AQEEL din yake asibitin maimakon ya iso gidansa ya share wata harda qari baya nan.,
Bani AQEEL din.
Kai tsaye Al-Amin yace,
"Bazai iya magana ba yanzu Amma idan yadawo daidai Zan kiraki saikiyi magana dashi....
Jin hakan yasa haj Maryamah din sakin salati tana shiga tashin hankali da fargabar idan wani mummunan Abu ya samu AQEEL din.
Kashe wayar tayi takira wayar AQEEL wadda yakashe a lokacin.
Kiransa takeyi ba kakkautawa Amma wayar taqi shiga Dan Haka tasake shiga tashin hankali da damuwa.
Ganin takasa nutsuwa ga Al-Amin dinma tasake kiransa Amma yanata waya busy Dan haka sai kawai Suka fito da driver zuwa asibitin sbd sanin asibitinsu dayace basa wuceta.
Ita kanta Haj Zainab Jin shiru yasa takira AQEEL batareda ma tasan uncle Lulu yakirasaba Wanda shikuma shigarsu asibiti yagani shiyasa yakirasa yaji Wanda ba lafiya Dan Bai dauka harda Amal na cikin motarba.
Wayar Amal ta Kira itama Kuma baa dauka saita sharesu kawai tunda dai sun sauka lfy ai shikenan
Ajiye wayarta zatayi saiga Kiran uncle Lulu yana tambayarta ko su Amal din sun iso ne??
"Aa" ta basa amsa Kai tsaye tana qarawa da cewa takira wayoyinsu ta AQEEL a kashe ta Amal din baa dauka,
Amma tun dazu sukace suna hanyar isowa gida.
Dan tinani uncle Lulu yayi Yana cewa,
"Naga daya daga cikin motacinsa a asibiti ne Nima saina Kirasa naji sai Bai daukaba Kuma nasake kiransa akashe,
To Allah yasa lfy,
Amma dai inaga Bari na leqa asibitin tunda Ina kusa.
Numfashi Haj Zainab ta ajiye tace ok yaje ya duba din Allah yasa lafiya ba wani abun yafaruba daga dirowarsu.
Uncle Lulu na Isa asibiti baiga AQEEL ba Al-Amin yasamu gani Kuma shine ya sanar Masa Amal dince ba lafiya Ana ciki da ita.
Meya sameta Kai tsaye ya tambayi Al-Amin din cikin damuwa da tinani.
Shi kansa Al-Amin basan mezaice Yana damuntaba tunda ba sani yayiba Dan Haka ya sanar Masa baida tabbacin ko Meye matsalar gaskia.
Haj Zainab ce takira uncle Dan takasa samun nutsuwa da sukuni daga ita har anty Fareedah da siddi dake tareda ita.
Yana dauka ya sanar mata Amal ce aka kawo asibitin ba lafiya sosai.
Wata irin ajiyar zuciya Haj Zainab din ta sauke sbd Hana kanta Shiga mummunan tashin hankalin Mai rikitarwa.
Saida tayita jero ajiyar zuciya tasamu daidaiton kanta tasake tambayarsa accident sukayi ko me?
Shima baida tabbacin wannan din da Haka sai kawai Suka kashe wayar Suka kamo hanyar asibitin hankalinsu a tashe Suma.
A bangaren Dr tayo tasamu ta shawo kan matsalar Amal din wadda firgici da tashin hankalin data sakawa kanta ne yasa BP dinta Hawa sosai sbd yanayi na ciki da Abu kadan yakesa BP dinsu Hawa ya iya haifar da matsala babba,
Hawan bp dinne yasa mararta qullewa Amma komai yadawo daidai sun samu ta nutsu baccin ma da akaso tayi takasa Dan Haka aka dawo office din Dr tayo da ita ta kwanta a qaramin gadonta Yana zaune gefenta Dr tayo din ta bude cikinta dayayi Dan tsininsa tafara Mata scanning sbd AQEEL din yasamu nutsuwa.
Haj Maryamah ce Suka fara isowa asibitin saidai ko Gama fitowa motar basuyiba su Haj Zainab Suka iso Babu Wanda ya kalli Dan uwansa sbd tsanar ganin junama da baqin cikin ganin juna.
Haj Maryamah tafara wucewa da ummarta sukai gaba umma na debewa Haduwar tasu albarka.
Itama Bata tsaya ko kallon inda sukeba itada nata iyalin sukai gaba Kai tsaye zuwa office din Dr tayo da uncle Lulu yace su samesa a kofar office din.
Suma su haj Maryamah office din Dr tayo din Suka nufa da Al'amin yace musu Yana can
Da mamaki suka qarasa sbd Dr tayo dai likitar Mata ce me zata iya yiwa AQEEL din.
Suna Isa Kai tsaye Haj Maryamah tayi knocking daya tareda bude dakin Suka shiga umma na bayanta ko rufe kofar basuyiba Haj Zainab da siddi suka sako Kai.
Dukkaninsu tsayawa cak sukai bakin kofar dakin idanuwansu akan cikin Amal dake bude ana scanning.
##MAMUH#
*_ZAFAFA BIYAR_*
*RUMBUN K'AYA*🔥
Hafsat Rano
*DAUDAR GORA*🔥
Billyn Abdul
*IDON NERA*🔥
Mamuhgee
*A RUBUCE TAKE*🔥
Safiya huguma
*KI KULANI*🔥
Miss xoxo
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200
ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN
0022419171
Maryam sani
Access bank
Shedarka ta 09033181070
MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN
09166221261
🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*
+22799643131
Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA
*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*🔥
70
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
70
Haj Zainab ce ta Dan qarasa shigowa da kyau idonta akan cikin tana kalla kaman dai Bata Gama gane me take gani dinba.
Siddi da Anty Fareedah kuwa kusan mutuwar tsaye sukai da mamakin duniya tareda kasa gasgata abinda suke gani.
Haj Maryamah Dan sake bude nata idanuwan tayi dakyau akan cikin kafin ta maida idonta kan AQEEL daya ke gefen Amal din kaman Wanda zaa budewa cikin yaga lafiyarsa.
Umma da bakinta koyaushe shiyake fara magana a dan rude tace,
"Zainab ciki ne ajikin 'yarki kome?
Maryamah kina ganin cikine ajikin yarinyar nan kokuwa wani ciwon ne ajikinta.
Amal data shiga tsananin firgici da kunyar da Bata taba sanin girmataba
Hannuwanta na rawa ta rufe cikin tana kokarin tashi zaune Dr tayo ta dafeta tana cewa tabi ahankali.
AQEEL kuwa miqewa tsaye yayi Yana kallon Dr tayo ya tambayeta idan ta Gama duba Amal din.
Gyada Masa Kai tayi alaman tagama din.
Tayar da Amal yake kokarin Yi batareda yaji komaiba gameda zuwan na iyayensu.
Amal dake kallon mommynta jikinta na rawa ta janye daga jikinsa tareda miqewa tsaye da kanta tana kasa kallon mommy dake Mata wani irin kallon mutuwa a mamaki.
Daqyar Haj Zainab ta iya bude Baki tana kallon Amal din jiki a matuqar sanyaye ba qarfi murya ma a sanyaye tace,
"Amal ciki ne ajikinki??
Kowa tsit yayi Yana jiran amsar Amal din Banda AQEEL dayace Dr tayo ta Dan Basu guri tana fita ya dawo da kallonsa kan Mamin Kai tsaye cikin nutsuwa yace,
"Mami ki.....daga Masa hannu tayi ta dakatar dashi fuskarta ha walwala ko kadan.
Amal din takuma kalla Kai tsaye tace,
"Ciki ne ajikinki???
Sauke Kai Amal tayi hawaye masu tsananin zafi suna gangaro mata jikinta na wani irin sanyi da mutuwa sbd Bata taba zatan alokaci daya kowa zai gane halinda take cikiba.
AQEEL ne yasake kallon Mamin Kai tsaye ya amsa Mata tambayarta da cewa eh cikine Kuma bayason a daga hankali akai tunda ba laifi bane Kuma sosai yakeson abinsa adduarsu kawai yake buqata ba wani tone tone da tiqewaba....
Amsarsa tasa zuciyar haj Maryamah data umma harma data Zainab din bugawa da qarfi
Haj Maryamah take ta dafe kirjinta dake gazawa tana kallonsa tace,
"AQEEL jinina a jikin Yar Zainab???
Kallon cikin na Amal tayi take idanuwanta suka fara dishi dishi tsaban tashin hankali da baqin ciki da wani irin zafi Mai ciwo da nauyi.
Umma kuwa kuka ta fasa tana kallon Zainab tana binta da kalmar ta cucesu taci amanarsu sai Allah ya saka musu.
Haj Zainab datayi mutuwar tsaye itama sbd takaicin Amal da mamakin tareda kasa yarda da wannan abin dake faruwa sbd wannan cikin Bai nuna na wannan tafiyar bane
Wannan cikin ya Jima da samuwa,
Itama wasu zafafan hawayen takaicine suka gangaro Mata ta share tareda juyawa batareda tace komaiba tabar dakin.
Anty Fareedah da Siddi kuwa gurin Amal data fashe dakuka Mai qarfi sukayi suna rarrashinta.
Haj Maryamah ma kuwa Dole AQEEL ya tarota sbd neman zubewa datakeyi da sauri aka Kira Dr tayo aka Kasheta zuwa wani dakin aka kwantar Ana bude Mata fanka da AC lokaci daya sbd wani irin zufa datake fesowa tako Ina ga numfashinta na neman toshewa sbd hayewar jini.
Sabuwar damuwa AQEEL yashiga ganin halinda mahaifiyarsa tashiga din Dan Haka Dole yabar Amal su Anty Fareedah Suka tafi da ita gida sai shi yaji da Haj Maryamah din da umman Cameroon dataketa kuka tana debewa Zainab da zuriarta sbd duk suka hadu da zainab ko zuriarta sai sun dangana da gadon asibiti ko ita ko yarta,
Wannan masifar tayi musu yawa,
Wace masifa tafi ace yau jininsu je ajikin Yar Zainab,
Zainab dai ta tabbata itace muguwar qaddararsu.
Kukan datakeyi da tsufanta yasa AQEEL yace Al-Amin ya maidata gida sbd sosai ta Shiga nata tashin hankalin Amma dayake ita duk tsananin tashin hankalin yanada wuya ta samu attack ko somewa Dan zuciyarta nada tauri.
Haj Zainab ma Bata tsaya jiran kowaba ta bar asibitin da motar dasuka zo da ita Dan batasan me zata tsayaba Kuma tayi,
Zafi goma da goma ne,
Maganganu marasa Dadi da tsinuwa umma ke jifanta da 'yarta dasu akan wannan lamarin da itama 'yar tata ta rufeta sai alokacin take sani tsabar sun taru itada AQEEL din sun Raina Mata wayo sun maidata Yar Iska.
Tana barin asibitin uncle Lulu ya dauko su Amal din a tasa motar Suka nufo gida har lokacin kuka takeyi ahankali jikinta na sanyi da yanayin yanda mommy ta dauki fushi Mai tsanani.
Daga Anty Fareedah har siddi Babu Wanda yayi Mata wata maganar cikin sbd kada su qara Mata damuwa rarrashinta kawai sukeyi musamman Siddi da wani bangaren na zuciyarta ke tsananin farin ciki da samuwar cikin duk da tana cikin mamaki Mai girma itama na yaushe aka samu cikin bayan dukkaninsu sunsan Babu ko kallon jituwa a tsakanin Amal din da AQEEL ASAD.
Uncle Lulu dai Bai iya cewa komaiba Dan kuwa mamakinsa qalilan ne sbd Daman yayi zargin zargin hakan aduk lokacinda yake haduwa da motar AQEEL ASAD a anguwarsu tunda safe idan yafita jogging,
Da farko Bai kawo AQEEL din bane Saida ya ringa haduwa da motar akai akai a layinsu saiya tabbatarda shi dinne Amma Bai tabbatarda gidansu yake zuwaba da sassafiyar.
To idan Hakan ne yanzu da cikin ya bulla badai a cikin gidan aka samu cikinba.
Suna Isa gida uncle Lulu ne ya saka Amal din gaba da kansa sbd Hana duk wata rigima da fadan da zainab zatayi dan shi kansa kunyar ayita maimaita zancen cikin yakeyi Dan abune dayazo a bazata gaskia.
Tunda aikin Gama ya Gama Dole suyi hakuri su zubawa sarautar Allah Ido.
Suna Shiga palon Amal taja gefe daya ta rakube ta tsaya sbd mommy dake zaune a palon na kasa tana Hana kanta fushi sbd tsananin zafi da ciwon abin datake ji,
Tayaya Amal zatayi ciki tana zaune gida batareda ankai karshen matsaloli anyi tarewaba,
Yaushe ma aka samu cikin?
A Ina aka samesa?
Tsawon wane lokaci cikin yake?
Me take tinani lokacinda ta bari ta dauki ciki,tana tinanin su umma zasu yarda su karbi cikin ne??
Wani sabuwar rigimar ce kawai ta debowa kanta ta debo Mata gashinan tun yanzu umma na debe deben albarkar data saba yimata.
Guri dukkaninsu Suka nema Suka zauna Banda Amal data kasa zama ta tsaya a gefe da ciki tsuru.
Cikin Haj Zainab ta qurawa Ido zuciyarta na nauyi tareda wani irin kunci da baqin cikin hada zuriar da zatayi dasu umma Rana tsaka Babu zato Babu tsammani.
Ita kanta har ga Allah batason hada iri dasu kaman yanda tasan sunfi son balai Akan su hada iri da ita,
Meyasa AQEEL zai Mata Haka Bayan yasan kwata