Showing 36001 words to 39000 words out of 149977 words
yake Bata tsoro da girgizata,
Bata kaunar ko sunan fyade taji sbd Su Amal dinta,
Sbd sune taji zama acikin gidan da anguwar yane neman ficewa a ranta sbd tako Ina anguwar 'yan duniya da mutanen banza ne aciki uwa uba gidan nasu dasuke ciki duk da dokar Lulu na Nan Bata Bari ta lalaceba saima qarfi jajircewa datayi ta qarawa dokar karfi sbd 'yaya matane da ita.
Alhaji Bulama wani Dan kasuwa Kuma Dan siyasa shine ya nacewa buqatarta amma Sam taqi basa damar suyi lalata shiyasa yake sakar Mata kudi sosai Dan kawai ya samu sauya raayinta ta bashi Dama su huta..
A yanda ta Gama karance Shi tsaf ba sonta yakeyiba shaawarta yakeyi Mai tsanani itama Bata taba jin alamar zata so kowane namijin ba saidai shima tsabar nacinsa taqi yarda saiya bullo Mata da maganar aure...
Batayi mamaki ba hakama Bata Musawa aurenba Dan tana buqatan dauke 'yayanta daga gidan.
Auren akayi ta tare Dan babban gidansa dake kusada anguwar tasu take ta bude sabuwar rayuwa,
Bude hannuwanta tayi ta ringa qwaqwalar kudi a gurin alhaji Bulaman ba sassauci sbd tagama sani da gano auren shaawa yayi Mata Kuma Yana Gama cire shaawarsa sallamarta zaiyi Dan Haka itama ta rufe idonta ta ringa amsar kudade a hannunsa kafin tabari yai yanda yakeso da ita din.
Mugun zama sukayi na tsawon wata hudu kafin ya sakota,
Tasan zaayi hakan tunda ta gane manufar aurensa Dan Haka Bata damuba ta tattaro yayanta suka dawo gida bayan tasa anyiwa gidan babban gyara tareda fadada shi yakoma tamkar sabo Dan Haka kudin gidan ta qaru ga kowa.
Aurenta gidan Alhaji Bulama yasa idanuwanta suka sake budewa tas,
Tasake wankewa tas itama,
Daga ita har yayanta sun canja sunyi kyau da qarin lafiya abunsu,
Jikinta Mai kyau ne sbd batada qiba ko sakakken jiki Dan Haka saitayi fes fes abinta Kamar ba itace da yayan gabantab.
Ana cikin hakan babban tsautsayin Datafi tsoro a rayuwarta yaso afkawa siddinta Wato 'dan DS daya kusa lalata Mata ita,..
Maigadin gidan ne yaja siddin yakaiwa Suraj din sai gashi Allah yasa anga shigar siddin gidan akazo aka sanar Mata
Hankali tashe jiki na rawa ta Isa.
Mummunan gani tayi alokacinda ta taradda siddinta tsaye gaban Suraj harya zare Mata wando....
Sumewa take neman Yi agurin saidai karfin da tafarfasar zuciyarta ya riqeta
Jikinta na wani irin rawa ta qarasa da gudu ta fizgota daga gabansa Bata tsaya komaiba ta sauke Masa wasu irin mugayen marirrika guda biyar a jere kafin ta fidda wayarta ta dauki hotunansa..
Jikinta babu inda Baya rawa tace,
"Wannan shine karo na qarshe da wani daga zuriar DS ma zai Kuma kullon mace bare lalata,
Alqawarine wannan nayi muku da yardar Allah.
Juyawa tai da yarta zata fito ya biyota da sauri shima jikinsa na rawa yafara rokonta akan zai Bata ko nawane kada zancen ya fita
Ko mahaifinsa bayason yaji sbd zai iya komai idan yaji ya aikata abinda zai taba Masa mutuncinsa da muqaminsa...
Maigadin na ganin hakan yasan wasa ya 'baci Dan Haka ya miqe da sauri zai nufota
A haukace tadauki sandarsa ta gora ta ringa dukansa ta koina tana musu ihu tana Kiran jamaa
Kafin kace me gidan yacika da mutane
Ta rufe Ido tanata ihu da neman daukin sun lalata Mata yarinya...
Dayake DS ya Jima da barin gidan 'dan nasa ne kawai aciki Yana aikata Barnarsa kala kala da Yan Mata da shaye shaye
Shikuma DS din da matarsa da sauran yaransa Mata da wancan Dan nasa daya da Lulu ya illata sun koma babban makeken gidansa dayafi wannan din so da Dama,
Kuma Daman sbd ya ringa lura dame basa barazana wato Lulu yasa ya zauna a anguwar
To yanzu daya Gama da matsalar lulun saiya tashi daga anguwar Dama ba mutuncinsa bane zama anan din.
Wani irin mummunan duka zainab tayiwa maigadin dashi Kansa Suraj Wanda yasa Dole akai Kiran hukuma tazo ta kwashesu
Itama tayi hakan ne Dan case din ya zama babba.
Ana zuwa gurin hukuma babu Bata lokaci yan anguwa suka bada shaidar abinda zainab ta fada
Aka Kai yarinyar asibiti aka duba bai Kai ga yimata fyaden ba Amma dai hukunci yahau kansu dagashi har maigadi gashi dukansu suna asibitin sbd Shi maigadi har haqorinsa hudu ya rasa dan harda Yan anguwar aka taru aka rufar musu da shegen duka Mai muni.
Zance yanata yaduwa a duniya da social media take hankalin DS ya tashi yayi duk yanda zaiyi Amma zancen yariga ya yadu mutane idanma baayi adalciba zainab a shirye take da Kai zancen sama inda komai zai sake lalace masa..
Matar DS ta samu zainab har gidanta ta fada Mata maganganu masu daci da tozarci,
Takirata da karuwa,
Mai 'yaya shegu Dan Haka kome akai musu ai ba fyade bane tunda sanaar uwarsu ce,
Ta kirata da Mara asali Kuma zuriar Yan daudu...
Tayi kukan data manta Yaya akeyin kukan ma sai aranar, saidai Kuma aikine ya tashi Dan kuwa qudurinta akansu ma sauyawa yayi,
Ds yayita nemanta a sirrance akan tajanye case din taqi sai shima ya bullo Mata da maganar aure Dan yayi amfani da damar su janye case din sbd yazama babba lamarin.
Kamar yanda ko yanzu tasan cewan auren manufa ne zaiyi da ita itama saita sakawa ranta hukuntasu da manufar tasa.
Amincewa aurensa tayi sai gashi cikin qanqanin lokaci akayi auren
Aka Kuma yada cewan sbd karamcinsa ya aure matarda 'dansa ya lalatawa 'ya shine abinda zaiyi ya kare mutuncin yarinyar da aka so lalatawar.
Hakan yasa mutuncinsa ya ringa qaruwa a idon mutane sai hakan ya ringa Masa Dadi musamman da zainab din ta fito ta nunawa duniya irin kulawa da kaunar dayake Mata itada 'yayanta...
Aikuwa hakan datake nunawa yasa DS sake mutuwa akanta da yayanta,
Matarsa Haj sadiya hankalinta mummunan tashi yayi ganin DS gabaki daya ya koma wani iri agun zainab,
Ga Suraj din har lokacin Yana gidan yari zainab taqi ma yarda DS ya tasa zancen,
Cikin salon daukar hankali ta nuna Masa abar Suraj din acan sai bayan zabe sai a fiddosa gudun yadawo ya lalata Masa komai tunda yanajin haushin an aureta din.
Aikuwa hakan akayi ds yabar maganar Suraj din akan sai angama zabe....
Sabuwar rayuwa zainab ta bude a gidan uban siddi batareda kowa yasan siddin DS ne ubantaba,
Kudi da Jin dadin rayuwa suke ja tako Ina hakama duk wani tattalin arzikinsa tanata janyewa tana tanadarwa 'yarta siddi Dan kuwa tayi alqawarin duk sai sunbiya abinda sukaiwa Lulu da marigayya siddi.
Koda aurenta da Ds yayi watanni Tara tagama tarwatsa gidansa Dan kuwa hatta matarsa Saida sukayi rabuwar kotu inda tun anan mutunsa yafara zubewa mutane,
Dan kuwa Haj sadiya cikin bacin Rai tonan asiri tai Masa Wanda zainab tayi amfani da hakan aka tada case din Lulu.
Tada case din Lulu yasa hankalin ds tashi haka zainab tasa ya ringa sakin kudi koina yanaso a sake rufe case din Amma baisaniba hakan yasake badashi da kuwa duka kudaden dayake badawa a banza suke tafiya....
Qanqanin lokaci rayuwarsa da iyalinsa tagama wargajewa
Akai zaben Kuma bai ci aikuwa qaramar hauka ta taso Masa gadan gadan.....
Bai qarasa Aron haukaba sai ranarda zainab tayi winning case din Lulu akansa sai gashi Lulu ya fito.....
Qarar qarshe data kusan buga zuciyar DS itace qarar yayiwa siddi fyade hartasamu cikin yarta ta rasu gurin haihuwa.....
Binciken asibiti da kotu ta bayar ya tabbatarda siddi yarsa ce Dan Haka aka yanke Masa hukuncin bin dansa gidan yari shima.
Dukiya Mai tarin yawa tasamu daga da aurensa Dan Haka fitowar Lulu ta sauya musu rayuwa gabaki daya...
Lulu yai kukan ganinta tare dana mutuwar siddi,
Daga Shi har ita zaman anguwar data garin fita kansu yayi gabaki daya sbd a rayuwa bayan Rashi da baqin ciki Basu San komaiba....
Amma a yanzu dasuke da 'yaya gabansu bazasu sake barin quncin kowa ya illata rayuwarsu data 'yayansuba.
Qaton gidan DS dayake kusa dasu tuni ya mallaka Mata Shi da Ana zaman Dadi kafin ta fara tarwatsashi Dan Haka gidan Mahaifinta ya dawo Mata.
Da gidan da gidan Lulu suka hade tareda maidasa wani irin babban gida da shaguna a waje suka zuba yan haya....
Mutuwar aurenta da Ds babu abinda yaja Mata sa suna da farin jinin manya Dan Haka cikin qanqanin lokacin takuma wani auren sadai shima baifi watanni huduba suka rabu Wanda Shi yamafi ds din arzki Wanda ta aura daga bayan..
Yawan aurace auracenta yasa Ake Mata kirari da IDON NERA,
sunan yafara binta ne tun anan kafin suka tattara sukabar garin sanadiyar wani Mai kudin data aura ya kaita Lagos...
Zuwansu Lagos da wata shida shima auren ya lalace daganan sai Bata dawoba Lulu ya sameta acan suka bude babin wata baudaddiyar rayuwar zaman Kai da budewar ido....
Kamar yanda akace zaman gidan yari qarin course,,,to hakan ne ga Lulu sbd yanzu daya fitone yake asalin hamshaqin tantirin Kansa bare sun dawo Lagos sun sake zama fitsararru..
Gidan kansu ne dasu na masaukin duk wata Yar barikin data rasa gurin zama to suna tallafa Mata sbd sabo da zama da karuwai da sukai tun acan dasuma gararin dasukai anan karuwan ne suka karbesu da mutunci sai basa iya ganinsu Acikin garari....
Da farko Suma Lagos din sunsha tsananin wuya da garari kafin suka gane kanta suka fara gwagwarmaya da Fadi tashi Dan duk arzikinsu da zainab ta Tara Saida ya qare musu a yawon Haya da wahalhalu a garin kafin da Lulu yaga ta kwabe masu suna neman wulaqanta kudin cin abinci ma na neman gagarsu ya tsunduma harkar dillanci Mata da alhazai shine fa suka fara daidaita...
A wani babba gidan karuwai suke zaune wanda ya hada mutane sama da 40,
A gidan kowa karuwanci sukeyi shine sanaarsu,
Ita Kuma zainab auren masu kudi shine nata,
Suna nan suna karuwancin Basu Tara komaiba ita Kuma a aure biyu ta Tara wani irin arziki suka tattara suka koma sabon gidansu itada Lulu dasu Amal sai sabuwar Mai aikin datayi....
Sunan IDON NERA yayi sunane a aure auren manyan data ringa Yi a garin Wanda yaja Mata attention din mutane sbd zuwa lokacin manyan gaske take aura,
Asalinta da kowa ya sani shine karuwanci Wanda har lokacin Bata taba jin shaawa ko tunanin tsayawa ko so daya tace ita ba karuwar bace,
Duk Wanda yaji ya fahimta ita karuwa ce to aje hakan Dan kuwa tai Nisan da saidai a fada a iya inda kake badai a fili ba.
Business sukeyi sosai Wanda shima ya karbu Kuma sunanta yasake habbaka sunan kasuwancin nasu,
Ta goge,
Ta sauya,
Takoma kamar ba uwar Yan Matan dasuka fara girma ba a gabanta,
Ta rufe idonta batajin komai Bata gane kowane yare saina NERA,
Shi kansa lulu baka ganesa Dan kuwa yakoma hamshaqin Dan daudunsa mai hulda da manya
Dan kuwa shine asalin wanda yake kutsawa ya shiga ya fita ya samo Masu rumbun nerar da zainab ke aurewa.
Babbar kaunar dake tsakaninsu da karuwai baya sauyaba tana Nan dan haka gida garesu na musamman dasuke bawa karuwanda basuda mafita gurin zama wasu Kuma sune suke zama gatansu
Ire iren wainda karuwancin bai Gama shigarsuba kenan...
##MAMUH#
#HOTLOVE/AMAL IDON NERA
#AQEEL ASAD
*_ZAFAFA BIYAR_*
*RUMBUN K'AYA*🔥
Hafsat Rano
*DAUDAR GORA*🔥
Billyn Abdul
*IDON NERA*🔥
Mamuhgee
*A RUBUCE TAKE*🔥
Safiya huguma
*KI KULANI*🔥
Miss xoxo
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200
ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN
0022419171
Maryam sani
Access bank
Shedarka ta 09033181070
MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN
09166221261
🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*
+22799643131
Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA
*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*🔥
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
20
Rayuwarsu a Lagos da gwagwarmaya da wahala suka Kai matsayinda suke a yanzu,
Mutane babu ruwansu da wahalarka,.da zufanka, da gwagwarmayarka, da dararrakun baqin cikinka Amma daga ranar da aka gano kuskure daya atareda Kai zaa fassaraka,zaa bika da zantukan gaskia da sabaninsu,hakam zaa bika da tsinuwa da kalamai maka mantansu,....
Daga ranar da aka haifi siddi ta gano hakan Kuma taji hakan daga gurin 'yar uwarta, jininta Dan Haka duk abinda duniya zata kirata dashi kokuma ake kiranta dashi Bata damuba sbd ko tace aa babu me shedarta......
Kowa Yana aikata kalar nasa laifi ko sabo tsakaninsa da ubangijinsa ne
Dan Haka itama wannan shine nata laifin,
Ta zabi aurarrakin datakeyi ne akan karuwanci Wanda mutane suka kasa rabasa da karuwancin sbd abinda takeyi din karuwan ma sunason samun damar Yi Amma Basu samu ba Dan basuda kamar hajiya Lulu Wanda shine sanin manyan gwamnati na gida Dana waje....
'yayanta tuni akai musu tambari da sunan shegu basuda uba Dan babu wadda akasan ubanta acikinsu,
Taji ta gani takuma dauka saidai Kuma nerarta na sake zaunuwa Ana mantawa da yayanta shegu ne kamar yanda ake fada...
Ta badawa yaranta gata da Jin dadin da duk wani Mai uwa da uba zai nema,.
Rayuwar yayan hutu da gata sukeyi tareda abinda ransu yakeso sbd mahaifiyarsu da yayar mahaifiyar tasu Haj Lulu sun tsaya musu yanda ransu yakeso...
Karuwai mutanensu ne haryanxu akwai Amana tsakaninsu dasu Dan kuwa sune mutanen dasuka karbeta alokacinda batada kowa batada komai batada gurin zuwa,
Allah shine gatanta Kuma shine ya qaddara yankewar wahalarta acikinsu dan haka duk inda suke Bata qyamarsu tana musu kallon nata me shiyasa ta zama tamkar uwar karuwai a garin lagos,.itada Lulu sun sun tsaya musu sun zama gatansu,...
Babbar qungiyar karuwai Mai zaman kanta akeda a garin Mai sunanta,
Lafiyayyun tsayayyun manyan Mata da Yan mata ne dasuka Sanku suka amsa sunayen Mata Kuma sukeda manyan connections a qungiyar,
A garin duk wata babbar Mai zaman kanta Yar arewa harma daba Yan arewan ba a kungiya suke duk da kowacce tanada gidan kanta da ikon kanta Amma suna tsayawa junansu,
IDON NERA ta tsaya musu,
Tasan manya,
Tayi auren manya,
Tana hulda sosai dasu
Dan Haka duk Wanda yake qarqashinta baya wulaqantuwa a hannun hukuma sbd wannan wani ciwo ne dake ranta da bazaso kowace mace ta wulaqanta a hannun hukuma ba sbd tashiga taji daci da ciwon hakan Kuma har abada bazai fita ranta ba.
Duk arzikin dasukai Basu taba raba gida ba da Dan uwanta,Rabin jikinta Lulu saidai kowa da babban sashensa Amma tare suke zama dining gabaki dayansu cin abinci as a lovely and happy family...
Babban quality din dasuke dashi a rayuwarsu shine suna tsananin so da kaunar juna tareda tattala juna,,,,,wannan din itace ta tsaya ta saka musu wannan aqidar sbd har abada bazata so 'yayanta su dandani kowane bangare na rayuwar data dandaba.
A yanzu datake Haj Zainab IDON NERA baya ita da Lulu babu wanda ya taba sanin ba itace ta haifi ba,
Haka daga AMAL har siddin basusan ba uwa daya uba daya sukeba kamar yanda babu Wanda yasan da IDON NERA din da Lulu ba uwa daya uba daya sukeba,...
IDON NERA shine Kamar family name dinsu kokuma ace Surname dinsu sbd kaf dinsu da Idon NERA suke amfani a komai nasu idan aka cire AMAL da ita kadaice takeda qarin sunan sanda Acikin nata sunan....
Passports, credentials da komai nasu Surname dinsu shine IDON NERA,
Da wannan sunan duniya tasansu,
Ta San arzikinsu,
Ta San su din asalin hamshaqan uwayen karuwai ne masu zaman kansu ne....
Yawanci tafiye tafiyenta qasashe da yayanta takeyi duk da karatu sukeyi Amma yayanta sune sanyin idaniyarta Bata cika tafiya ba taredasuba..
*_MAMAN SAYYEED COLLECTION_*
Assalama alaikum
Hajiya ta matsalarki. Breast ne(nono) to y'ar uwa matsalarki ta kare in sha Allah kikai amfani d ingantaccen maganinmu na gyaran breast maganina herbal ne bashi d side effects ko daya mun hadashi d ingatattun kayayyaki d larabawa suke amfani dashi gurin gyaran nono
Y'r uwa maganinmu yana ciko d breast nono ko yakai silifas lalacewa in sha Allah kikai amfani dashi nononki zai gyaru su ciko suyi bul bul maganinmu kowace mace zata iya amfani dashi Mai shayarwa, Maison yaye, budurwa, duk zasu iya amfani dashi muna garin kano muna tura sako kowane state d yardar Allah 08063114606 sannan munada in gantacciyar zumar kiba, hips, breast acikin farashi kalilan zaki samu naki ki gyara jikin ki y'ar uwa 08063114606 kano.
*_Maman Sayyeed collection kayanta farko ne idan Ana maganar gyara karku tsallake ayi Babu ku_*
*********
******Haj Zainab IDON NERA a yanzu hamshaqiyar kanta ce datake da abin kanta taci ta tada wuya a Jin Dadi da arzki bakuma wai an Dena abinda aka Saba din bane saidai aji da komai ke qarawa da girma....
Kyakkyawa ce duk da zamanta babbar mace Amma har lokacin fes take qyam Kamar babar yayarsu AMAL ba mahaifiyarsuba Dan Haka take zuba lokacinda Acikin manyan mutane,
Baya bayan Nan wani hamshaqin balaraben Sudan ta aura shi nasa auren ya Dade tunda tayi shekara biyu dashi a Kuwait zaune kafin suka rabu inda arzikin data samu agunsa ya kere na Koda yaushe take gabaki daya tagama miqawa ta wuce sanin wasuma daga cikin manyan mutanen dasuka santa,
Babban abinda yake qara kusancinta da manyan hamshaqan masu dollar shine duka manyan Matan dasuke taredasu a qarqashinta suke,.
Itace take toshe duk wata hanyar da zaasan suna neman Mata sbd kada mutuncinsu ya zube,
Itace sirrinsu na boyewa ko toshe musu duk wata matsalar da zata taso data danganci bacin suna Haka Kuma itama Bata barin Ana cin zarafi ko tozarta duk wata macen Dan ana Mata kallon karuwa Dan Haka sai takeda connections tako Ina da matsala zata bullo.
Yayanta sun girma sun zama Yan Mata masu tsananin farin jini ga manyan mutane sbd kyau da ajinsu tareda gatan dasuke dashi koina
Sbd itama ta zama babbar mace Mai arziki kusan da Dama wasu na yiwa yayansu shaawarsu wasu Kuma kansu Kuma bawai qananun mutane ha manyan masu NERA a hannu..
Tanada kyakkyawan buri akan yayanta da Haka Bata taba shaawar aurar dasu Dan kudi ba tunda kudin ba matsalarta bane akwaisu ba adadi,
So take yayan nata su tsayu a karatunsu su tsayawa kansu kafin Auren ya biyo baya duk da hakan batajin zata aurar da yayanta inda baa gane yaren NERA,
Yayanta insha Allah tana musu fatar rayuwar arziki da yayansu ma,
Zuriarta gabaki daya ayanzu Bata fatar tayi talauci Dan Haka takeda buri da fata akan yayanta tareda gatan Allah bless a cika Mata wannan burin.
Daga AMAL har siddi sun San basuda uba,
Idanma sunadashi to Basu taba tambaya ba sbd umman Bata bada fuska ba hakama sun bar kowane irin sirri momynsu ta boye Akan asalinsu da Bata taba fadaba,,,,
Uwarsu da yayan uwar tasu sun tsaya musu a komai Dan Haka basuda wata damuwar Dan ance basuda uba to bai damesuba sbd suna taka duk rayuwar dasuke so Wanda masu uban ma basa takawa..
Lulu IDON NERA ahakan Zainab IDON NERA ta takura Masa yayi aurenda baiyi niyaba sbd wata Yar tsohon daya daga cikin Mazanta ta maqale tana son lulun....
Mahaifinta Mai kudin gaske ne Kuma itace kadai yarsa dayakeda Amma ta nace lulun takeso duk da ya kusan haihuwarta.....
Su Kuma duk inda yaren NERA yake suna ganewa