Showing 60001 words to 63000 words out of 149977 words
din daya ganta a gabansa ta bayyana,
Bazai iya sake tafiyaba yabarsu koma menene zai iya dauka akan ya tafi yabarsu kamar yanda take fada...
Cikin wani mummunan yanayi na firgici da mutuwar jiki ya iya cewa,
"Mami bazan iya tafiya ba,
Bazan iyaba Mami,
Keda MARYAMAH kawai nake buqatan dawowarku rayuwana,
Mami Dan Allah kada ki koreni daga gareku....
Uncle Lulu ne yafito daga part dinsu yaga abinda yake faruwa da sauri ya qaraso gurin
Idanuwansa suka sauka kan DR SHAYKH AQEEL ASAD wanda yasani a jaridu kawai..
Mamaki da firgicine ya Kamasa alokacinda yaji AQEEL ASAD din ya Kira Haj Zainab da Mami,
Mami??
Itace Maminsa Kuma?
Ta Ina.....????
Haj Zainab din ya kalla yaga yanda idanuwanta ke neman cikowa da wata irin qwallar radadin zuciya..
Janye hannunta yayi daga na AQEEL din ya kallesa zaiyi magana Amma bashi AQEEL din yake kallaba idonsa na kan Mamin.
Janyeta uncle Lulu yayi zuwa ciki kafin yadawo ya kalli AQEEL din daya rintse idanuwansa zuciyarsa na radadi da Kuna.
Kafin uncle Lulu yayi magana juyawa yayi Kai tsaye ya nufi gate Yana fitowa da sauri malam Rabiu ya bude Masa mota yana isowa ya shiga suka bar gurin.
Haj Zainab ma tana shiga Kai tsaye sama ta wuce zuwa bedroom dinta ta rufe sbd tiriri takeji a zuciyarta Yana tasowa tareda rufeta koina..
Meyasa AQEEL ya bayyana a rayuwarsu bayan sun Dade da goge alaqar baya,
Mema zata iya cewa 'yayanta akansa idan sukasan waye shi agunta,
Sanin wayeshi agurinta zaisa Susan alqarta da rayuwarta ta baya wadda Bayan Mahaifinta da Mijinta Babu wani Abu na rayuwarta ta baya datakeson tunowa,
Me zata cewa 'yarta Siddi idan bayyanar AQEEL din tasa sukasan AMAL ce kawai 'yarta,
Tama Yaya zata iya fuskantar matsalolin da zasu biyo bayan bayyanarsa a rayuwarsu bayan ta rufe kofar duk wata damuwa da matsala a rayuwarsu sai wadda Allah zai qaddaro musu a gaba,
Tayaya zata iya barin AMAL tasan shine Wanda Mahaifinta ya barwa Amana da nauyinta akansa,
Bazata taba yarda yadawo rayuwarsuba sbd Babu wata alaqa kota zumunci kota jini datayi saura a tsakaninsu,
Kaunarsa a jininta take bazata taba Dena kaunarsa ba Dan kamar yanda takejinsu Amal aranta Bata taba Dena jinsaba kamar yanda har wannan lokacin Bai taba fita Acikin adduartaba saidai Kuma bazata Bari hakan ya dawo da quncin dasuka dade da gogewa a rayukansuba.
Cire komai tayi ta danne a ranta ta fito tareda yaranta sukai breakfast kowa ya fice harkokin gabansa.
AMAL makaranta ta tafi Siddi Kuma tana gida Bata fitaba,
Mommyn kuwa itada uncle Lulu sun fita inda acan take sanar dashi AQEEL ASAD shine Aqeel dinta na baya.
Mamaki da damuwa shima yashiga na bayyanar AQEEL din sbd asirinsu dasuka danne na shekaru Yana gap da bayyanuwa ga 'yayansu kenan,
Yaya Siddi zatayi idan taji itadin asalin batada alaqa ko daya da mommynta datake tsananin so,
AMAL ma tayaya zata iya daukan zancen AQEEL ASAD din shine Wanda ya daura auren iyayenta Kuma shine wanda Mahaifinta ya ratayawa nauyinta,
Kuma shine Wanda sanadinsa mahaifiyarta tashiga duk wani qunci da masifar rayuwa...
Ajiyar zuciya ya sauke Mai nauyi tareda yanke shawarar AQEEL ASAD bazasu taba barin yadawo rayuwarsuba kodan asirinsu dasuke rufewa na 'yayan IDON NERA shegu ne ya tabbata,
Gwara rayuwarsu ahakan
Koda Ana Kiran yayanta basada uba baa fito Kai tsaye akasan da gaske cikinsu a kwai wadda aka Haifa ba aureba,
Bazataso rayuwar Siddi ta shiga wani mugun haliba akan wannan gaskiyar.
*****hakan yasa duk wata hanyar da AQEEL ASAD zai ganta ta tashe ta Bata Bari kafa ko daya,
Dawowarsa ya tayar Mata da daya daga cikin mikin data rufe daqyar a rayuwarta,
Tana kaunarsa fiyeda yanda take tunanin zata iya ganin damuwa da kuncinsa Dan Haka ta zabi nesanta kanta da duk indama zai samun damar ganinta...
****Ta nasa bangaren gabaki daya familynsa da maaikatansa sun rasa gane Kansa,
Komai nasa yatsaya sbd Mamin data toshe duk hanyar dazai ganta suyi magana.
Kullum da safe a IDON NERA Rs yake wuni,
Ba dare ba Rana koyaushe Yana hanyar gidan Wanda yasa hankalin malam Rabiu tashi matuka sbd lamarin ya girmama matuka,
Babban abinda yafi daga Masa hankali shine yanda bayanshi Babu Wanda yasan halinda Maigidan nasu yake ciki,
Tsoronsa na gaba Kuma idan ba shima kaddarar fadawa tarkon IDON NERA bace ta Kamasa ya zaunce hakan.
Su kansu securities din gidan sun tabbatarda shi din Mai kafiya ne akan abinda yakeso Dan Haka duk yazo cikin girmamawa suke tarbonsa Amma basa bude Masa gate sbd gargadin hajiya madam dinsu mai karfi shikuma dayake family issue ne yaqi amfani da karfinsa da ikonsa gurin ganinta Dan idan yaso a mintina kalilan zaa gabatar Masa da ita din a gabansa Amma kuma Maminsa ce ake magana akai bazai taba tirsasataba saidai Kuma Yana gab da sakata a inda batada zabi saita gansa.
MARYAMAH yake buqatan sanin inda take,
Ita yakeson sanin wacece Acikin yayan asalin MARYAMAH Amma a iya bincike Babu MARYAMAH kwata kwata a tarihin sunanta da 'yayanta...
Hankalinsa tashi yayi wani irin tsoro da firgici Mai tsanani ya lullube zuciyarsa Idan har hakan na nufin MARYAMAH ta rasu kome???
Tsananta zuwansa gidan yayi Wanda ya hada da zuwa office dinta Dan kuwa ayanzu hankalinsa bazai taba kwantawaba saita sauraresa.
Gabaki daya ya shiga qunci da damuwar data saka hankalin iyalansa tashi,
Baya baro IDON NERA Rs sai dare sosai,
Da safe can ne gurin zuwansa farko,
Tun zancen na a boye saigashi yafara fita Wanda hakan yayi mummunan bawa mutane da duniya mamaki,
Meye hadinsa da zuwa gidan IDON NERA?
Shima duk kamewarsa da ilimin addininsa da mutuncinsa da girmansa yafada tarkon kenan..
Wannan zancen da aka fara yadawa mutuncinsa yafara rawa a Idon manya masu tsananin ganin mutunsa musamman malaman addininsa yasa Haj Zainab basa damar ganinta sbd sukai koma karshe ta fahimtar dashi batada wani alaqa da duk Wanda yake rayuwarta ta baya.
Da daddare ne bayan sallar ishai ya iso gidan wannan karon gate aka bude musu driver yashigo da morarsa data fi duka motocin dake harabar gidan kudi.
AMAL datake tsoron su hadu Bata gida, siddi Kuma ta koma Abuja ayau din, uncle Lulu yasan da zuwan nasa Dan Haka Yana part dinsa tareda matarsa da 'dansa yabasu Daman maganin matsalar tasu.
Palo ta tsaya dashi tareda zaunawa a natse cikin tsadaddiyar kujerar palon ta nutsu ta kallesa da kyau tana sake nutsar da kanta..
Kafin tayi magana shine ya rigata da zaunawa kujerar datake kallonta,
"Mami Ina Little MARYAMAH??
Wani daci ta hadiye na abinda zata fada Masa kafin ta dauke kallonta daga Kansa tace,
"Batanan,
Tana nesa tayi aure.
Wacece daga cikinsu Maryamah??
Kallonsa tayi da mamaki tace,
"Babuta anan,kamar yanda nafada maka tayi aure tana nesa Bata Nan..
Kunkuyar da Kansa yayi ahankali zuciyarsa na sosuwa sbd ya tabbatarda duka wannan rashin buqatarsa ne arayuwarsu take nuna Masa.
Ahankali ya dago cikin sauti mai sanyi yace,
Bakya buqatan dawowata a rayuwarku Mami??
Nayi laifi Mai girman da bazaki yafemunba saidai Mami wallahi zuciyata ce kawai da Bata magana tasan irin girma da mahummancinku acikinta,
Laifina babbane Dana tafi tun farko na barko,
Bansan meyasasa Kika bar gida ba,
Bansan meyasa kike gudunaba
Ina rokon gafara da yafiyarki Mami Amma Dan Allah kada ki rabani da kanki kokuma hanani sanin inda wacece MARYAMAH Acikin mutum biyun da ake Kira da 'yayanki.
Ajiyar zuciya ta sauke ahankali tareda kallonsa cikin sabuwar nutsuwa da kulawa tace,
"AQEEL ASAD,
bazan taba fushi dakaiba
Idanma nayi na yafe maka
Saidai inason kasani ni ayanzu wata daudace da kowane Mai mutunci yake qin raba,
Wannan ba Zainab maminka bace da kakeso da alfahari da ita
Wanna Zainab IDON NERA ce,
Nice uwar dakin karuwai,
Nice nakeda gidajen karuwai da qungiyarsu,
Sunana qaurarrene a duniya yanzu,
Banda baqin ciki Banda kunya banda takaici ko Dana sani na hakan,
Kamar yanda kaji Ana fada 'yayana basuda uba,
Babu Wanda yasan ta yanda na haifesu Dan Haka bamuda wani abin bugun gaba ko alfahari daya wuce dukiya da muke rayuwarda mukeso da ita,
Kai din babban mutum ne a yanzu,
Babban masani addini ne da ake alfahari dashi koina,
Kanada mutunci da suna,
Kanada girmanda Bazanso alaqarka daniba ya zubar maka da duka wainnan abubuwan,
Kayi nesa Dani,.
Ka nesanta kanka da duka ahanalina,
Sunanka zai lalace zaka rasa mutuncinka a addininsa idan ka bayyanawa duniya alaqarka da hamshaqiyar karuwa IDON NERA........
Wasu irin hawayene suka gangaro Masa daya kasa riqewa,
Kowace kalmar data furta deep yanka sukewa zuciyarsa,
Wane mutunci da radadi yafi sunanda take ambata din,
Wane mutunci da girma yakai ya tsaya akan tsamota daga wannan mummunan suna da duniya ta santa dashi..
Hawayensa suka saka jikinta sanyi Amma Dole ne ya nesanta Kansa dasu.
Zubewa yayi gabata tareda sunkuyar da Kansa Yana tsiyayar hawayen dayake riqewa a Ransa tsawon shekaru na rashinta.
Wallahi ayanzu daya gansu kome suka zama bazai iya rabuwa dasuba.
Maimakon tayi fushin da yanke sauran alaqarta dashi kasawa tayi zuciyarta ta karshe sbd ganin hawayen babban mutum kamarsa
Duk da agurinta shi din yarontane datake goyawa tana basa abinci abaki.
Kasa riqe kanta tayi daga kaunarsa Mai tsanani dake qasan ranta ta bayyanar Masa da kaunar tata a fili ta tsiyayo da hawayen kewarsa da tuno muguwar rayuwarta ta baya.
##MAMUH#
#LOVE/HOT
#SISTERSLIFE
*_ZAFAFA BIYAR_*
*RUMBUN K'AYA*🔥
Hafsat Rano
*DAUDAR GORA*🔥
Billyn Abdul
*IDON NERA*🔥
Mamuhgee
*A RUBUCE TAKE*🔥
Safiya huguma
*KI KULANI*🔥
Miss xoxo
Littafi daya---400
Biyu---600
Uku----800
Hudu-----1k
Biyar din duka----1200
ZOKI BIYA KUDINKI TA WANNAN ACCOUNT DIN
0022419171
Maryam sani
Access bank
Shedarka ta 09033181070
MTN CARD KO VTU ZASU SAKA TA NAN
09166221261
🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪🇳🇪
*Ina yan uwa 'yan nijer?*
*Zaku saka katin AIRTEL ta wannan number sannan ku tuntubeta*
+22799643131
Littafi daya---450CFA
biyu---650CFA
uku----850CFA
hudu----1050 CFA
Biyar----1250CFA
*A DADE ANAYI SAI GASKIYA!*
*Thanks for choosing us*🔥
*_Arewabooks@Mamuhgee_*
31
Lokacinda suka dauka batareda sun saniba yasa Koda suka Ankara da time din lokacin tafiya ya wuce sbd karfe biyu harda mintina,
Malam Rabiu Kam tuni ya shige cikin securities yayi kwanciyarsa tuni bacci ya daukesa.
A yanda ya takura Mata da Kuma kwarjini da girmansa yasata ta sanar Masa kadan daga cikin rayuwarta Amma Bata sanar dashi waye MARYAMAH ba har lokacin hakama Bata sanar dashi dalilinta na barin gidaba da yankewar alaqarta da mahaifiyarsa ba har abada.
Amincewa dashi da Tai kawai yasashi Jin wani babban nauyi ya saukar Masa daga zuciyarsa Dan Haka bazai takurataba zaibita ahankali ya samu damar gani da Kuma Jin inda MARYAMAH take sbd itace zai fara janyewa daga rayuwar tadawo hannunsa ta hakan yasan Mamin zata dawo hannunsa itama sbd matuqar ba dawowa sukai hannunsaba bazai taba samun kwanciyar hankali da wannan rayuwar dasuke cikiba,
Fatansa ma ya kansace da gaske MARYAMAH din aure takeyi baa mata wannan mummunan shedan da akewa Maminsa wadda kome zaa ce akanta bazai taba kaucewa ko gudintaba duk da asalinsa ya kasance Mai tsanani kaucewa da gujewa qazantacciyar rayuwa ko qazantaccin mutane,
Amma gashi ayau Allah Yana jarabtarsa ta wanna hanyar.
Sai bayan sallar asuba Haj Zainab ta tashi ta nufi sama Dan gabatar da sallan,
Shima kasancewar Babu masallaci a kusa yasashi yin alwala yayi sallah taredasu malam Rabiu da dayan security dinsu dayake musulmi a harabar gidan harma da Uncle Lulu Wanda Dama tare suke sallah da Taju kullum asuba.
Suna idarwa gari yafara haske AQEEL yayi magana sosai da Uncle Lulu Wanda shima Bai fada Masa wacece MARYAMAH ba kawai dai ya bude Masa zance sosai na sanadin barin Zainab din gida da shariarta da ummansa harma da zamanta gidan yari kusan so biyu ko ukuma.
Sosai hankalinsa ya tashi ya girgiza da duka zantukan da kusan yakejinsu Kamar a mafarki.
Palon yakoma jikinsa a mace Dan kuwa sai yanzu yakejin kunya da takaicin Kansa daya takurawa Mamin harsaida ya tado Mata da quncin data Jima da dannewa da rufewa cikin ranta...
Shigowarsa palon yayi daidai da saukowar AMAL Idon Nera daga sama,
Sanye take da fararen kayan baccin Riga da wando masu tsantsi..
Bata lura dashi ba kamar yanda Bai lura da ita dinba wayarsa zai dauka ya bar gidan sbd Kansa dake sarawa da maganganun dayaji.
Itace tafara ganinsa
Cikin mamaki Mai tsananin gaske da tsoro tace,
"Ya Salam,
Meyake faruwa Anan??
Juyowa yayi Jin muryarta data sauka kunnensa kamar ta Maminsa a dah,
Fararen idanuwansa dasuka na sauya sbd rashin bacci da damuwa da ciwon
Ya zuba Mata gabaki daya Ya kalli fuskarta datake fresh sbd tashinta kenan daga bacci..
Dauke idanuwansa yayi daga kanta sbd aqidarsa ta rashin kallo
Musamman ita da kayanta kusan koyaushe hakan suke.
Juyawa yayi zai wuce saiya dakata cak tareda juyowa da muryarsa Mai taushi da nutsuwa yace,
"You are??????
Wani kallo Tai Masa tana mamakin shi din waye dazai shigo har ciki bayan ba kowa mommyn ke shigowa dashiba..
Rashin amsarta yasa ya juya zai wuce kamar daga sama yaji itama Kai tsaye cikin muryarta Mai rashin hayaniya tace,
"AMAL IDON NERA......
Cak ya dakata daga fitar dayake dap dayi...
Bai juyoba baikuma tafiba Saida yagama juya muryarta cikin Ransa dake Masa sautin muryar Maminsa..
Kenan dai itama Yar Maminsa ce...
Wucewa yayi batareda ya juyoba.
Yana fitowa harabar gidan malam Rabiu da zuwa lokacin yagama saddakarwa tunda gasu da kwana gidan IDON NERA ya taso ya bude Masa kofar mota sukai ribas suka fice daga gidan.
Suna fita abin mamaki abin mamaki saiga wasu Yan jarida biyu suna bin motarsu da hotuna.
Gudu malam Rabiu ya qarawa motar suna barin ikeji din.
Gida suka nufa Kai tsaye,
Yana fitowa motar ko qarasawa sashen ummansa baiyiba ya nufi bangarensa.
Bilkees dake zaune a babban palon tana jiran isowarsa
Yana shigowa ta miqe tsaye tana kallonsa cikin tsananin mamaki da tashin hankali..
Kallo daya yayi Mata ya nufi hanyar palonsa zuwa bedroom dinsa..
Binsa tayi Abaya tana cewa,
"Tafiya kayine baka sanar Mana ba??
Ina kaje harda kwana Haka?
Tunda safe naje wancan gidan baka can Kuma Babu alamar acan ka kwana?
Please kace wani Abu man.....
Dakatawa yayi daga zare kaya dayakeyi ya juyo ahankali ya kalleta cikin rashin son daga hankali yace,
"Calm down please Bilkees
Meye ne? Ba gani nadawo ba,
Banajin Dadi Ina buqatan nutsuwa kaina na ciwo,
Idan na nutsu Zan sanar dake koma okay???
Rungumesa tayi ahankali tana gyada Kai da cewa,
"To please kada ka sake irin hakan
Banyi bacci ba yau,
Inata tunanin inda kake,
Kuma dai zaka fadamun kace???
Gyada Mata kai yayi ahankali tareda Dan shafa fuskarta yakai soft lips dinsa yayi kissing kumatunta.
Zarewa yayi ya nufi toilet.
Yau baiyi workout ba sbd ba gidan ya kwana ba Dan Haka brush da wankan ruwan zafi yai ya fito ya shirya cikin White fendis ya kwanta sbd Yana buqatan baccin dazai warware Kansa.
Bayan yakwanta ficewa Bilkees tayi ta nufi kitchen ta bawa masu aiki umarnin kalar abincin dazasu dafa ta wuce gurin ummansa takai Mata labarin bayajin Dadi ne ya kwanta shiyasa Bai shigoba gaidata.
***AMAL kasa hakura tayi ta tsare mommynsu da tambayar waye wannan din,
Yanke zancen Tai da cewar wani 'danta ne datake kauna tun lokacinda tana Reno Ana biyanta da abinci kafin tasamu aikin Yi.
Abin mamaki Amal kuwa sai gashi da daddare yasake zuwa gidan nasu,
Dinner ta musamman akai a gidan dominsa Wanda yasa Mamakin AMAL qaruwa akansa.
Sanyeda white hoodie Balenciaga yazo Wanda suka maidasa kamar sabon matashin saurayi,
Fari ne shi sosai shiyasa duk kayansa kusan kaloli masu duhu ne Haka yake saka abinsa,
Tunda yashigo palon qamshinsa ya doke duka qamshin turarukansu,
Kwarjininsa yasa Shi kansa uncle Lulu basa girma yakeyi sbd daman manyane abokansa kamar yanda akace yaro da kudi abokin manya,
Uncle Lulu yafisu sanin waye AQEEL ASAD din shida yake Shiga manyan sosai yasan yanda suke da AQEEL ASAD tunda kudi sungama shiya Masa girma da matsayi.
Saida kowa ya zauna cin abincin AMAL ta sauko sanyeda doguwar Riga Mara hannu kamar yanda ta Saba saka abinta.
Qamshinsa ne yasata kasa basarwa ta dago ta kalli gurinda yake zaune ya gama gauraya musu koina da qamshinsa.
Isowarta Bata saka ya juyo ya kalli gefenta ba sbd Haka Allah yayisa,
Itama Bata damu da sake sanin meyasa yasake zuwa gidanba ta zauna suka fara cin abincin.
Uncle Lulu ne kawai ke magana sai mommyn wadda take kallon yanda yakecin abincin cikin nutsuwa da kwanciyar hankali..
Sama sama Amal taci abincin ta miqe tabar gurin sbd bazata iya Bata lokacinta gurin ganin yanda uncle Lulu da mommyn keyiwa baqon ba.
Tana tashi Anty Fareedah ma tagama ta tashi shima goge bakinsa yayi da tissue ya tashi.
Yau magana yayi sosai da Mamin akan duka abinda yasani gameda barinta gida...
Ya nuna Mata yanason ta dawo garesa Kamar baya..
Kai tsaye ta dakatar dashi da wannan zancen kafin ta Dora Masa sharadin duk ranarda yayi Mata maganar mahaifiyarsa ko komawarta rayuwarsu daga ranar zata sake yanke alaqarta dashi har abada..
Ganin irin bacin Rai dayake cikin maganarta yasashi barin zancen a lokacin Amma Kuma alqawarin daya dauka Yana Nan saiya dawo da ita rayuwarsa itada MARYAMAH.
Tun daga lokacin ya maida gidan IDON NERA gurin zuwansa batareda laakari da sunansa dazai baci ba da mutuncinsa da girmansa,
Aduk zuwansa gidan saiya roki Maminsa MARYAMAH Amma har lokacin taqi sanar Masa inda take,
Bai taba kawo tunanin AMAL ba
Ya yarda da MARYAMAH itace yarta daya da batanan,..
Amal gabaki daya Babu ruwanta da duka zuwan dayake gidan sbd lura da miskilin mutum ne na karshe,
Takasa gane alaqarsa da zuwa gidan koyaushe Amma dai koma menene kamar yanda ta lura da halayyarsa ko kallo biyu baya Mata duk kyau da daukan hankalinta da ake fada,
Shine mutum na farko dayake hulda da gidan IDON NERA Amma Bai taba yimata kallon burgewaba ko bayyana shaawar aurenta.
Tattara zancenza tayi ta watsar taci gaba da sabgoginta.
Tun ummansa da Bilkees na tununin ayyukansa da meetings dinsa ke hanasa zaman gida sosai har hankalinsu yafara tashi musamman umman da batason wannan shirun nasa tsoro yake Bata,
Bayyanar Zainab shine mafi mummunan kaddarar da zata dawo mata, Dan Haka koma menene itadai kada ya zama ya dawo da bincikensa na neman Zainab da 'yarta.
Bilkees kuwa tashin hankalinta da firgicinta kada Allah yasa koma Ina yake zuwa yanada alaqa da Mata Koda Matan aurene,kodama tsofine.
Yawan zuwansa ya ankarar da duniya halinda yake ciki,
Ta bangare daya SSG yadawo daga tafiyar da yayi Kai tsaye ya tada maganar aurensa...
Kai tsaye Amal ta bada tabbacin wallahi bazata auresaba,
Tashin hankali da firgici Hayat din yashiga Dan Haka a Daren ranar ya shirya ya Isa IDON NERA Rs.
Isarsa tayi daidai da fitowar lafiyayyar motar AQEEL ASAD daga babban gate din gidan ya hau titi da ya wuce batareda ya lurada isowar Hayat dn ba.
Mamaki ne ya kusan kashe SSG ganin fitowar AQEEL ASAD a gidan.
Juya kan morarsa yayi sbd bazai iya shigaba Yana baqatan tabbaci tukuna.
Washe gari PA dinsa yasa yaje Dan tabbatar Masa da AQEEL ASAD na zuwa gidan.
PA dinsa kuwa har qarfe goman dare Yana anguwar Saida yaga fitowar AQEEL ASAD din ya tabbatarda shine kafin ya bar anguwar.
Washe gari karfe goma ya Isa office dinsa hankali kwance saiga Al-Amin yashigo office dinsa zuciyarsa na wata irin rawa da tashin hankali da mamakin.
Tsadaddiyar luxury Cashmere dark blue ne ajikinsa
koina office din kamshin victorious carbon yakeyi da sanyin ac daya qarawa kamshin sanyin kamshi.
Dagowa yayi ya