Showing 24001 words to 27000 words out of 100319 words
Chapter 9 - Masarautar Jordan Book 1 Complete Document .txt
Maqbul ce sai kamshin citta da garlic yake, ji nayi raina yayi mugun ɓaci ina can ina fama ciwona ashe ɗan renin hammatan yana can yayi odar abinci.
Sauke abinda na ɗaura nayi na zauna akan kujera, ji nayi duk na kuntatta baki ɗaya,
...... Ina jin hirar su har suƙa watse, amma baƙon yafi surutu, dan ɗan akida baya faɗar kalmar da ta haura uku,
***
Washi gari da safiya, sai ga Amirah Raziyah tazo, bansan shigowarta ba sai ji nayi an rufe ni da duƙa, ta ko ina.
Duka sosai yana ɗakin motsa jiki yaji hayaniya, shine ya fito har zuwa kitchen ganin kanwar Mahaifinshi tana ɗaukar doka a hannu kamar yadda ɗanta ya ɗauki yayi rashin hankali.
"Ina jiranki idan kin gama."
Yau kam naji har ya kara da na kullum, juyawa tayi a fusace tace.
"Ashraf! Akan me zaka sa a wulakanta min D'ana."
Ba kulata ba yayi wuccewarsa ciki biyoshi bayanshi tayi, kamar zata tashi sama.
D'akinshi yashige bai fito ba, sai da ya share awa biyu cur, sannan ya fito ƴa zauna gun cin abinci, buɗe abinci nayi.
Kallon roasted nut yayi da kuma, soyayyar kwai, sai golden macarroni, wanda na dafa da namar gwangwani, na zuba masa, mai da dubansa yayi kan butar Coffee, garin zuba masa kwalla da suƙe zuba a idanuna ya zuba cikin tea ɗin, duk abincin haka kwallana ya sauka a cikin.
Mika min towel yayi nazo bayanshi ina goge masa gashin kansa, Amirah Raziyah ce tazo ta zauna, daƙe bai bani damar nasa mata ba, ita da kanta ta zuba kome. Tana shirin fara ci sai ga Amir Ukshe. Zama yayi shima, Amirah ta zuba mishi abinci.
"Hand..."
Bai kai karshe ba na bar, ina gab da shiga ɗakin yace.
"Don't touch anything."
Shigewa nayi, kallonshi sukayi sannan suka maida kallonsu ga junarsu.
Kowannensu yana fatan samun nasara akan abokin gwabzawansa.
Ina shiga naga wata arniyan suit ɗin da zai saka, silver ce tayi kƴau iya kyau, kallon laptop ɗinshi nayi wacce take kunne, haka kawai naji ina son duba. Email ɗina tunawa da nayi yace kar na taɓa kome, ya sani juyawa, aikuwa mukayi karo dashi. Inda kaina ya bugi kirjinshi bai damu ba ya raba gefena, ya kalle ni da wutsiyar ido, a ranshi yana cewa.
*Bata jin magana*
Fita nayi ya ɗauki files ɗinshi, ƴa fito ƴazo ya same ni a tsaye zama yayi naje bayanshi na fara aikina, ina gamawa na bar gun dan na lura da magana a bakunansu.
Ina barin gun kuwa Amirah Raziyana ta ajiye coƙalinta tace.
"Ashraf!!!"
"Sultan zaki ce" kanshi a duke yayi maganar kamar bashi ba, cikin kuluwa tace.
"Naji Sultan a wani hujja zaka rufe ɗan uwanka? Me yasa baka abu da tunani ne, ka rufe min yaro"
Miƙewa yayi ba tare da ya kallesu ba yace.
"Ina son zama daku?"
Mikewa Amir Ukshe yayi cikin ƙanƙar da kai yace.
"Sultan! Gobe zagayowar ranar haihuwarka, wanda yayi dai dai da ciƙa shekaru ashirin da shida a matsayin sarkin Jordan na huɗu."
Gyaɗa kai yayi sannan ya juya, yayi taku biyu cike da kasaita yace.
"Gobe!!! Ranar zagayowar Mutuwar Iyayena!!! Gobe zan buɗe fadar sarkin Jordan A Gobe Inshs Allah zanƴi abubuwan da na gaza yinshi na tsawon shekaru da dama"
Juƴawa yayi abinsa yabarsu tsaye,
" Tabbas ƙome zai lalace gobe"
Inji Raziyah,
Taku kaɗan Amir yayi cikin ƙaɗuwa yace.
"Zan dakatar da kudirinka gobe."
Fita suƙayi cike da tashin hankali fitowa nayi cikin murmushi nace.
"Insha Allah nan da wata biyu zan rabaku dashi."
Kowa idanunshi ya rufe, musaman Amir da Ra'ees ya gargaɗeshi akan kar su bari Sultan ya shiga fada, yau gashi ya ambaci mutuwar iyayenshi da maganar mulkinsa kenan dole ƴau ya nemi ra'ees.
Itama Raziyah tana komawa gida takira bokanta na Turkiya.....
Ɓangaren Sultan kuwa tunda ya shiga binciƙe a laptop ɗinss.....
_Alƙawari ya ciƙa ƙo.....Burinsu d'aya muradinsu ɗaya.... Nashine ya banbamta da nasu....Itama nata burin nan....Nawaye zai ciƙa_
'''Allah nagaji......Kuƴi manege idan nasamu hali toh amma banyi alƙawari ba.....dan bana ɗaukar alƙawari.....✌'''
*#MJ#HAZAƘA#VOTE*
Oum Muwaddah
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: *_HAZAƘA WRITER'S ASSO_*
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*
*_Labarin daban yake da sauran..._*
Page.١٢
"Iƴakaci suka kamani nace kaine kasani yin kome kuma kaga dole a yanke mana hukunci tare mu mutu tare." na gaya mishi haka,
"Kee mahaukaciyar ina ce da zaki ce nine na saki wallahi karki jefa ni cikin matsala." yace min kamar zai fashe da kuka,
Kauda kaina nayi tare da fashewa da dariya nace.
"Ka shiga hannuna, kuma dole ka amshi hukuncina."
Ɓata rai nayi sannan nace.
"A kunnen Amir."
"Shikenan na amince." murmushi nayi sannan nace.
"Yawwa yaron kirki."
Da sauri na bar gidan, ina addu'ar Allah yasa karsu nime ni, Allah cikin ikonsa, kuwa na shiga kitchen ina cikin taya wata, aikin sai ga Sahela. Tashigo duba girkin da muke tayi sannan ta kalleni cikin harshen turanci tace.
"Daga wata ƙasar kike?"
Kauda kaina nayi sannan nace mata.
"Senegal!"
Shiru tayi tana kallona, sannan tace.
"Ina son a girka min abinci me kƴau dan ina da bako daga masarautar marocco inda hali ayi mashi irin girkinsu, sannan a tsaftacce kome gudun faruwan matsala. Idan yaci lafiya ya koma gidanshi lafiya kuntsira idan aka samu matsala kuyi kuka da kanku."
Tana gama zabga kashedinta ta cikawa bujenta iska. Ranar a kitchen muka wuni. Dan sai Biyar muka gama abincin. Shashinmu na nufa naje nayi wanka tare da gyara jikina, ina gamawa Ghaniyu na aikowa yana nima na.
... Da sauri na fita. Ina zuwa na same shi bakin kofar fita daga masarautar, a gaggauce yace min.
"Anjima zan zon da Sheik Habibullahi, dan ya duba Sultan."
Gyaɗa mishi kai nayi san.nace
"Ince ba dai malamin tsubu bane?"
"Eh gaskiya wannan baya cikin malam da kike tunani. Dan yasan abinda ya dace." yace min,
Shiru mukayi dukkanmu muna sakawa da kuncewa a ranmu, katse shiru nayi da cewa.
"Dai ka tafi, anjima zan xo."
Nace mishi tare da komawa cikin gidan.
***
*BANU NAZIR*
"Ya shugaba! Sun kashe yarinyar ta hanyar bata guba ne da karfin tsiya, bayan Sultan Ashraf ya saketa, sannan ba iya kisarce matsala ba su shida suka mata fyaɗe, sam basu kyauta ba, sanadin haka kakanta ya kashe kansa."
"Ba kashe kai bane! Kisan kaine kuma sun lakato tsuliyar dodo dan sai na girgiza masarautar baki ɗayanta, idan banyi haka ba, bancika ɗan halak ba."
Inji Alexandra,
Shiru manyan fadar Alexandra sauƙayi, kafin wani dattijo wanda ya fisu shekaru yace.
"Idan zaku yanke hukunci, ku dinga dubawa meke faru? A yanzun haka nasami labarin Sultan Ashraf ba lafiya."
Yuuuu sukayi da idanunsu akanshi, suna jiran kanun labaran daga bakinshi. Gyara zama yayi ya faɗa musu abinda yake faru.
Nan suma suƙa kulla tasu ta yadda zasu rusa jagorancin Amir Ukshe.
***
Da dare na fita tare da nufar gidanshi. Ina zuwa nasamu babu kowa, basu iso ba. Tsayawa nayi daga waje gudun farun irin wancan dukar dan har yanzun jikina ciwo yake.
......
A can cikin garin kuwa bayan lokacin da Ghaniyu yaje, yasamu an kawowa Malam Habibullah wata mara lafiya, yana fama da ita. Dan haka ya tsaya jiranshi.
***
"Ukshe! Yayi nasaran raba Ashraf da mulki tabbas dole na dakatar dashi dan bazan cigaba da ganin yana aikat..."
Bai karshe ba ya rike wuyarshi sakamaƙon shake mishi wuya da Irfan yayi, suna cikin wannan kokuwar sai ga Ammar babban ɗan Amir Abu Zarri yashigo ganin, yadda ake shirin kashe masa mahaifi, bai san lokacin da ya ɗauki wani kwalba ya jefi keyar Irfan, sake Amir Abu yayi ya faɗi kasa sumamme,
Shi kuma Ammar yaje kan Babanshi ya ɗauke shi suƙa fito daga cikin ɗakin, ya kuma bawa masu tsaron kofar izin karsu bar Irfan ya fita, shi kuma ya wucce da mahaifinsa Asibitin.
***
Daga falour bakin Amir Ukshe Raziyah tafito fusƙarta cike da farin ciki, shima bayanta ya biyo ƴace.
"Ki kula sosai, dama Abu Zarri ne ya tsare mana gaba, indai Ashraf ne bani da matsala dashi. Dan wannan halin da yake ciki ma ya ishe shi, haka zai zauna har karshen rayuwarsa kowa ya manta."
"Ni haka ma bawai yayi min bane amma bazanki shawaranka ba ai da kasheshi mukayi haka zai fi alkhairi."
"Me kike ci na baka sauka, ki jira nan da wani loƙaci mulki zai dawo hannunmu,"
"Dukda haka naso da kashe shi baki ɗaya dan ina gudun kar wani abu yazo ya lalata mana shirinmu"
"Idan muka kashe shi zaiyi wuya muma mukai labari, haka ma wadatar dashi."
Haka suka tashirya yadda zasu kawar da duk wanda zai kawo musu shunku.
***
*NIGERIA*
Abuja.... 4pm
A firgice Ummi tafarka daga barcin la'asar ɗin da tayi akan abin sallarta, salatinta yasa Khalil da Fatima wacce muke kira da Batul. Da sauri suƙa nufin kanta, mika mata ruwa Khalil yayi wanda tasha kafin tayi sallar la'asar.
"Sannu Ummi! Lafiya..?"
Inji Khalil, janshi baya Batul tayi tare da dakatar da shi.
Sallama yayi tare da shigowa falon ganinsu cirko cirko akanta yashi tambayar "Lafiya?"
Inji Abdullahi, " Ya Abdul Ummi ce mukaji tayi salati, shine muka bata ruwa ko Adda Batul" Inji Khalil,
Zama yayi kusada Ummi ya ɗaurs kanshi akan kafaɗar, yace.
"Ummi! Don Allah ki rage sanya damuwa a ranki, Insha Allah duk inda Safinah take zata dawo lafiy..."
"A'a Abdullahi! Safina tana cikin hatsari, naji haka a jikina tana gab da faɗawa cikin hatsari na ganta cikin mugun yanayi tabbas tana cikin mawuyacin hali." a raunane ta kai, kafin waninsu yayi magana tasake wani irin kuka mara sauti tasake a hankali me mugun taɓa zuciyar me sauraro tace.
"Ƴa Allah nayi tawassali da sunayenka tsarkakku masu daraja ya Allah ka jarabce ni da abinda zuciyata zata iya ɗauka Ubangiji baiwarka tana cikin wani hali ya RahamanRahim Ya Allah badan na iya ba Ya Allah dan karfin mulkinka ka kare Safinatu a duk inda take."
Addu'ar da tayi kenan, duk falourn sai da suƙa zubda kwalla, shigowar Nannah baisa su fasa kuka ba, Abdul ne yayi ta maza ya faɗawa Nannah abinda ke faru, itama dai ƴau tun safe take yawan jin faɗuwar gaba tare da tunanin Safinah da ya addabi zuciyarta, gefe guda kuwa na zuciyarta yana son tabbatar mata da zarginta amma bata amince da hakan ba.
"Maman Bint ki daina kukan nan haka, Insha Allah Bint tana nan dawowa, Insha Allah ki daina takura zuciyarki da tunanin wani abu zai same ta da izini Ubangiji alkhairi ne zai faru da ita."
Da kyawawan kalamai Nannah tashawo kan Ummi tayi shiru, ita ba ƙome ke ɗaga mata hankali ba ƙome bane sai idan ta tuna cewa Safinah mace ce, me rauni ce bazata iya kare kanta ba idan wani abun kare kai yazo mata babu shakikinta a tare da ita, waye zai kare mata wani abun waye zai ceceta idan wani ya farmaketa cikin kuka tace.
"Mamin Bint!! Mace fa bata da karfi, idan wani ya farmaketa fa? A wannan duniyar da imani yayi karanci idan wasu suƙa cutar da ita fa, kasancewarta Ƴa mace me rauni taya zata tsira, wallahi nasan babu makawa Safin..."
Kwarewa tayi wanda ya haifar mata da tari me karfi, sai da aka bata ruwa tasha, ajiyar zuciya ta sauke tace.
"Allah kai kafini sanin halin da taƙe ciki"
Daga haka bata kuma magana ba, sai dai kwalla yaki barin idanunta......
Nannah bata bar gidan ba sai karfe biyar da rabi, lokacin Alhaji Badar ya dawo.
***
*JORDAN*
9:pm
Ganin dare na kara duhu, ga wani tsoro tare da faɗuwar gaba, yasani juyawa zan bar gidan, ban taɓa tsamanin zan ganshi ba sai ganinshi nayi a gabana, wani irin yanayi naji tare da tsoron da ya cika min zuciya baya nayi a razane na juya da mugun gudu cikin gidan, aikuwa ya rufa min.
Sakamaƙon duhun falon, bansan meye a gabana ba nayi tuntuɓe dashi take na zuɓe a gurin, zan mike naji kafar tayi min nauyi. Dole na mike da sauri kafin nace zan gudu ya bangajeni da kirjinshi na faɗi can gefe akan hannuna, sai da naji karan kashin hannuna. Kuka ne ya kwace min dukda falon akwai duhu sosai nasha mamakin yadda yake gane inda nake, matsawa nayi da sauri na shige ɗakinsa, nasamu na tura ƙofar zan rufe ya kaiwa kofar doka, kuka ne ya ƙwace min miƙewa nayi na shiga bin bango da bayana,, hmm ashe makunin wutar ɗakin na ta inda nake ja a jikin bango aikuwa wutar dakin ta kunnu, ashe jiya a duhu na ganshi, ƴau kam a haske nayi ido biyun dashi.
Bansan lokacin da ihu ya kwace min ba na rufe idanuna da mugun karfi, fincikoni yayi ya cillani saman gadonshi kaina ya bugu da allon gadon, bibiyu na fara ganinshi, yunkura nayi zan mike yayi maza ya diro kaina, kuka ne ya kwace min nace.
"Karka min haka Ashraf, don Allah karka rabani da kome na, gwara ka kashe ni kawai."
Kifeni da mari yayi wanda ya ɗauke min jina da ganina, kafin na dawo daga hutun rabin lokaci Ashraf ya keta min rigana har cikina, duka na kai mishi tare da yakushe fuskarshi, amma ina yaci karfina, kuka nake kalaman Nan yana dawo min.
_Taya zaki kare kanki? Karki tsomma kanko cikin wancan masarautar kyaleshi inda rai da rabo zamu gana, a matsayinki na ya mace taya zaki fuskancesu har ki samu damar ɗauko shi? Don Allah karki aiƙata abinda zanji na tsani kaina, dan matuƙar suƙa ganoki kasheki zasuyi idan ƙuma basu kashe ki ba zasu cut..."
Wani irin azaba ce tA dawo dani daga gajeriyar tunanin dana faɗa, tureshi nayi da mugun karfi na kwaci kaina, amma, kasancewa karfinmi ba daya ba, sake kamoni yayi ya shake min wuya. Ina ji ina gani na rasa kimata, darajata, budurcina, tun daga shekaran da na balaga nake tattalinsa, Ummi da Nannah suka tayani tattalinsa ta hanyar faɗa min sharuɗar da zan kiyayye, wanda bazan rasa shi ba, nima nabi. Yau gashi garin taimakon da tausayi nazo inda aƙa bautar dani, aka wulakantani, uwa uba aka rabani da Alfarmata. Ni Safinatu na rasa Darajata na yaudari iyayena, har da mijin da zan aura na tsallakesu na tawo ciƙawa Nannah Muradinta, gashi hakkin Iyayena da Anim ya kamani.
Ganin yadda yake kara tsaga jikina nayi wani yunƙuri nacire hannunshi ɗaya a wuyana, garin ya maida hannun zoɓen azurfan hannunsh......
*_A koda yaushe labari takan sabunta kanta, musaman wanda kake muradin isar da sako....Zan baku dama faɗi ra'ayoyinku....
Meye ya jefa safinah cikin wannan matsalar... Idan na gama page 13 naga Writerup ɗinku da sakon da wannan shafin ya kunsan zan sake muku musaman Whatspp grps ɗina ƙune zaƙu fara karanta Page 13 hmmm Wattpad kan na baƙu 12 ku more gobe