Showing 63001 words to 66000 words out of 100319 words

Chapter 22 - Masarautar Jordan Book 1 Complete Document .txt

"A'a ki shayar da yaranki!"
Girgiza kaina nayi cikin kuka nace.
"A'a Abbana! Ta tafi dasu kawai tunda suna da gatansu, kuma bugu da kari kabilar larabawa basu cika baiwa Yaro nonon mahaifiyarshi ba, dan sukan ɗaukesu zuwa gun reno."
Duk yadda suka so na amince da yaran fir naki, abin ya basu mamaki, haka suka watse zuciyarsu ba daɗi. Ni kuma dalilina nakin yaran ba kome bane yaja haka sai dan karsu fuskanci matsala. A rayuwarsu kuma bana son shakuwa ya shiga tsakaninmu yadda rabasu dani zai zama matsala.

***
Washi gari aka kuma tashi akan batu ɗaya, nima kuma na kafe akan ra'ayina, da aka kawo abin karyawa har da kunun tsamiya, aikuwa nasha sosai, bayan awa guda nonuwana suka cika sosai. Har ya kai dakyar nake d'aga hannuna, sabida cikarsu na kuma yi shiru. Dan kar ace na bawa yaran nono. Shigowar Dr yasa aka kawo min yaran, ina tura bakina ina kunkuni haka na basu suka sha har suka koshi, kallon Umma nayi cikin mamaki nace.
"Ummanmu! Yaran nan da shegen wayo suke dubi yadda suke shan nono kamar wasu mayunwat..."
Maganar tamakale min ne sakamakon shigowar Nannah da wasu tawagar mata da maza, har da Ghaniyu kamar na watsar da yaran nace.
"Akhee Ghaniyu!"
Murmushi yayi cikin girmamawa yace.
"Amirah Safinatu, sannu uwar gimbiyoyin Jordan, Ina mika gaisuwata ga Sarauniyar gobe a birnin Amman, Umarninki nake jira Sarauniyata."

Duk sai naji wani iri lokaci guda wani irin girma da dauk'ak'a sun hau kaina lokaci guda, haka tawaga Nannah suka shiga mika min gaisuwa, wasu mata suka zo gun yaran suka fara dubasu, abinda bamu taɓa lura dashi ba kodan ba a gun mu suke ba, tsakanin kirjinsu zuwa bayansu akwai wani abu kamar tasiwera(Map) wanda ya kara tabbatar musu yaran nasune, take suka shiga ambatar barakallah.
Cikin murmushi nan ta kalle wata dattijuwa tace.
"Amirah Humaidah na gaya miki binti bazata taɓa min karya ba, kinga shaidar toh haka ma Ashraf shima akwai tasweran masarautarsu a jikinsa."
Ni dai ido nake binsu dashi nan suka shiga godiya da kuma ban hakuri ga Umma, fita sukayi da yaran. Nace
"Allah yasa su tafi dasu nima na huta."
Make min bakina Umma tayi, dake sun fita. B'are musu baki nayi tare da sake kukan saƙalci kamar karamar yarinya nace.
"Allah bana son yaran! Gwara su tafi dasu."
Shafa sajenshi Dr yayi cikin murmushi, yace.
"Kina fama da yaranta! Babu wanda ya isa rabaki da yaranki."
Galla mishi harara nai tare da murguda mishi baki, nace.
"Ai kana da nono ka bas.."
Sake buge min bakina Umma tayi, cike da takaici tace.
"Amma baki da mutunci Yakolo, rashin kunyarki ya shahara, kuma ki fita idanuna."


Kuka nake har da majina,
***
A gidanmu kuwa, cikin girmamawa Ummi ta amshi bakin dan tasan da zuwarsu, hidima sosai aƙa musu, dan har Sophia da Nanah Asma'u suka haɗu akayi musu abubuwan tarɓa. Nannah tana gaya musu irin rikonda aka mata, godiya sosai sukayi. Sannan suka bawa Ummi da Abba hakuri da kuma irin abinda ya faru. Murmushi Ummi tayi dan haka kunya ya hana shi magana.
"Babu kome jarabtace kuma babu wanda ya isa kaucewa kaddaranshi, Allah yasanyawa rayuwarsu albarka."


Sunji mugun daɗi, tare da godiya. Sannan sukayita godiya, tare da alkhairori masu yawa, sannan Nannah ta gabatar da Nurse ɗin da zata kula da yaran har da ita kanta.
Kyauta masu daraja suka bawa yaran dani kaina, wasu manyan akwatina glass aka kawo suka ajiye a gaban Ummi sannan suka buɗe nan aka ciro wasu kambu, na yaran wanda akayi su da farin zinari wato (Whiter gold) sannan aka bisu da wasu beart na diamond(Lu'ulu'u)


Mikawa Abba Yarinyar farko Nannah tayi, tace.
"Ka zaɓa musu sunaye masu daraja, da kima."
Karɓa yayi ya musu huɗuma sannan ya mika mata, ta mikawa Dattijuwar, Aka sake bashi d'ayar yayi mata Huɗuma, sannan ya mika mata. Cikin girmamawa, Ghaniyu ya sunkuya gare shi yace.
"Kakan gimbiyoyin Jordan wani suna ka sanyawa uwanye ɗakina?"
Kallonsu yayi cikin nauyin baki yace.
"Tafarkon na mata Huɗuba da Asma'ulHusnah Tabiyun namata Huɗuba da MaryamSajida"
"Allahu Akbar!!!"
Kunya ya hanashi ɗago kai sai kwalla da yake sharewa, Ummi kan takasa magana, sai bin Abba take da ido. Kowa a falon jikinsa yayi sanyi, dan Abba bai taɓa cin karo da nadama irinta yau ba.
Mikewa Bakin sukayi sannan suƙa ce.
"A faɗawa Sarauniyar Jordan na gobe sun gode zasu koma idan yaran sunyi kwari akai musu suga dangin Kakarsu."


"Insha Allah zasu zo."
Inji Abba, rakasu duk yan gidan sukayi sai da suka ga tafiyarsu sannan suka dawo, Abba da Ummi suka dawo min da yaran, har da nurse sun zo sun samu anata rigima dani. Dudu yana tare dasu Nannah, har dasu Nana.


Cikin ɗaurewar fuska Abba ya ajiye min yaran, sannan yace.
"Shayarda su."
Ba musu na basu, sai da suka koshi sannan na cire su. Ban ɗaki na shige na sake ruwa sai da nayi kuka ya ishe ni na fito, lokacin Nannah har ta iso, gani nayi ana tattara kayanmu. Dr ya kalle ni sannan ya ajiye min kwalin waya, ta kowa yayi gaba dan har sun fita ni ɗaya ce, na rage zan saka hijab ɗina.
"Kiyi hakuri ki shayar dasu."
"Bazan iya ba, sanadin cikinsu na shiga garari."
"Karki butulcewa Allah rahamar da yayi miki" yace min a hankali.
Ina jin idanunshi a cikin jikina, dakyar na d'ago idanuna sai naga ya cika min ido nace.
"Ni ka kyal."
"Bashi zaki faɗa ba, me yasa kika kasa faɗa."
Cikin mutuwar jiki na ɗ'ago a karo na uku nace.
"Abinda nayi niyya kenan"
Zuba hannunshi yayi cikin aljuhunshi, tare da lashe lips ɗinshi. Lumshe idanuna nayi sabida ya tino min da Ashraf, bansan ya akayi ba sai ji nayi nace.
"Ina kewar Ash."
"Kina kewar Ashraf ko! Toh haka ma yayi ga waya nan hot8 ce bata da tsada ki rike sai ki welcome back, akwai numbeta zan na kiranki ina jin yarana ya suke. Sanna wancan shashashan bazai kuma damunki."


Motsin da naji a bakin kofa yasani lekawa,Abdul ne ya buɗe sai kuma ya koma, raɓa gefenshi nayi na ɗauki hijab ɗina, ban kula wayar ba.
"The phone!"
A hankali nasaka zararan tsintsiyar hannuna na ɗauƙa, na fita ahankali yana take min baya, duk wanda ya kallemu a lokacin sai ya kuma kallonmi, sabida munyi wani irin dacewa ne da juna, musaman da ya kasance fatarmu kusan ɗaya ne, dan shi ya fini hasken fata.
Wucce ni yayi yaje ya buɗe min motar, na shiga a hankali. Sannan ya rufe tare da cewa.
"Ki kula da yaran don Allah."
"Hm" nace mishi, haka Abdul yaja motar yana tsaye a gun.
Shafa kanshi yaƴi zuciyarshi fess, yana hango yuwar nasara a cikin alamarinsa, dunkule hannunshi yaƴi ya ɗan daki gefen kirjinsa, yana cewa.
"Miskilancinki ya girmama anan."
Yayi tap ɗin gefen kirjinshi, har da wani lumshe idanunshi.
***
Koda muka isa gida, side ɗin Umma aka wucce dani, ita kuma Nannah ta wucce side ɗinta, nan aka shiga hidima dani. Kamar ba gobe.


Hmm idan nace larabawa suna da mugun son yara banyi karya ba dan na gani akan idanuna, da dare aka kawo min yaran na basu nono fir naki nace barci nake ji. Fita nurse ɗin tai sai gata tare da Nannah, cikin rarrashi ta bani Takwararta. Amma kam naki bata karshe nasaka musu uku.
"Kiyi hakuri ki basu abincinsu mana Binti."


"Shegune zan basu nono n?"
Wani ba hangon mari Aka tsinka min, tare da kara min. Jikinta har rawa yake, a razane na ɗago kaina,mukayi ido biyu da Ummina, cikin fusata tace.
"D'aukesu nace! Ki kuma kiran da wani suna ni dake ce."
Kuka na fasa tare da yin baya nace.
"Wallahi bazan basu ba, dan ai."
Ban taɓa ganin ɓacin ummi sama da yau, dan hannunta har ɓari yake, tana niman abinda zata min rutsi da shi sai akan kwalbar Humra. Kafin mu farga. Sai rutse min kai tayi, ta kuma ɗauke yaran ta mikawa Nurse dan Nannah tun da nakira yaran da shegu. Da kuma marin da Ummi tayi min, tasa kai tafita. Tana kuka sosai dan ta hango kiyayyar yaran a idanuna, sam bana kaunar yaran kamar yadda bana kaunar Ubansu.
Allah ga jego ga caskaleni da Ummi tayi, sai da taga bana iya jan numfashi sannan tafita, ta kuma kawo min yaran ta buga min tsawa tace.
"Tashi ki basu? Wallahi kika bari Nannah ta bar kasan nan da yaran nan Safinatu Wallahi! Tallahi!! Baki bina bashin rantsuwa sai na miki Allah ya isa......"




Dagske Nannah zata tafi da yaran bayan ta hango kiyayyarsu a Idanun Safinah?
Shin dagaske Anim ba zai sake dawowa Rayuwar Feener ba?
Shin wacce nasara Dr Yake ganin yuwar samunsa?
Shin Safinah zata amince ta shayar da yaran?


Wani hali Masarautar jordan take ciki?

Tsakanin Ukshe da Abu Zarri waye zai hakura ɗan uwanshi ya mulke shi?


Adnan daga Banu Hussein yaje gurin Alexandra, na Banu Nazir dan niman Haɗinkai, shin da gaske Alexandra zai amince dashi.


Ya Makomar Sultan Ashraf A magarkama...


Yanzun muka zo rabin labari book one...


Intermission..




Oum Muwaddah..


[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAƘA WRITER'S ASSO_


*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*



*_Labarin daban yake da sauran._*



Page.٣١-31
Fita Ummi tayi ta barni da ciwon jiki, Umma ce tazo ta taimaka min na gyara jikina, sannan tayo min faɗa taje ƙuma ta ɗauko yaran a gurinsu Ummi. Ta bani so na shiga bawa Asma'ulHusna, kwalla na sauka a idanuna yana ɗiga a fiskar yarinyar, buɗe idanunta tayi yan kananu dasu. Wallahi sai naji wani irin tausayinsu ya cika min zuciya, ina ganin ta koshi dan ta zare bakinta, na ɗauke na kwantar da ita, sannan na dauki MaryamSajida. Itama na shiga bata nonon, kwanciyar rigingine nayi na kifa Sajida a kirjina dan tafi kankanta, Husna akan cikina dan tafi Sajida girma.


Shigowa Ummi taƴi taga duk muna barci, ɗaukar su tayi tabarni ni ɗaya. Ina barci,
***
Washi gari dan tun cikin dare da. A farka naga basu nan nasan Ummi tazo ta dauke su, dan haka ban bi tankasu ba. Na shiga bayi nayi wanka, ina fitowa na sai ga Ƙhalil. Turata nayi taje ta ɗauko min, kayana yar dogowar riga iya gwiwa, sai wandon legings dark blue, kasancewar atamfar holland ce, fari ne me ratsin dark blue, sai nake hadawa da Legings ɗin. Simple makeup nayi sannan na yane kaina da gyale kashka, dark blue me stone fari, haka ma takalmina farine me ratsin dark blue, kallon kaina nayi naga nayi wani fayau. Agogon ɗakin na kalla, sannan na lumshe idanuna na dauki agogon na makala, bayan na saka yan kunne na. Ban saka lips stick ba, na shiga kallon kaina naga nayi mugun kyau.
Komawa nayi gurin kulolin abinci na zauna kunun gyaɗa na garin tamba, shi na fara sha a hankali. Har na koshi buɗe ɗaya kular farfensun kan rago na sha kaɗan. Tunawa da kalaman Ummi na jiya ya dawo min ban san lokacin da na mike ba, na nufi cikin falournta. Ina shiga naji ana gaisawa, Dr ne zaune Yarinya ɗaya na kan cinyarshi Dudu yana dauke da ɗayar, wani boyayyen ajiyar zuciya na sauke, ganin yaran. Fitowa Nannah tayi Ita da me renonsu, Ghaniyu ya shigo zai ɗauki kayansu, cikin girmamawa ya gaishe ni. Hankali na baya gareshi sama sama na amsa mashi, sannan na kalle Ummi wacce fuskart ta nuna Alamar farin ciki a takaice zance kowa murna yake zasu tafi da yaran, sai Nannah ce ta kalle ni taga na sadar da kaina kasa, ina wasa da bazaar gyalena.
Takowa tayi har gabana. Sannan ta riko hannuna cikin murya me sanyi tace.
"Na tafi da yaran?"
D'ago idanuna nayi, kuka ya kwace min, girgiza mata kai nayi.
"Umminki ta miki dole ko? Idan baki sonsu zan tafi dasu na rene su cike da soyayyarki."
Tuna girman Allah ya isa da Ummi tayi min, yasani cewa.
"Zan shayar dasu."
"Anya Binti! Ba dole aka miki ba?" banda sokanci irin tawa sai na kalle Ummi, na sunkuyar da kaina nace.
"Ko ɗaya kawai zan shayar dasune"
"Idan kinsan zaki cutu na tafi da su, ke kuma Allah ya baki lafiya."
Gyada kaina nayi tare da cewa "Amin"


"Binti zan koma gida, dukda Umminki tace min na tafi da Nanny da nakawo idan akwai matsala ki gaya min zanyi kokarin magancewa da Izinin Ubangiji, don Allah ƙarki ji haushin yaran dan basu da laifi."


Gyaɗa kaina nayi, ina kallon Dr da Dudu suƙa rakata, ni kuwa kamar an dasani a gurin.


Sai da Ummin tace min.
"Hmm! Sakarya sokuwa kawai, kalleki kamar me hankali nan kuwa babu wanda yafiki shashanci."
Tana gama faɗar haka tayi wuccewarta. Shiru nayi dan ina gani ta ɗauke yaran ta barni a tsaye, jan kafana nayi na bita ɗakin, na zauna a bakin gadon. Tana haɗa musu madara, cikin sanyi naja Sajida, na ɗaurata akan cinyata. Sannan na ja zip ɗin rigana wanda yake gefe na shiga bata nonon, tana kamawa sai da nayi tsigar jikina ya mike, dan tun da aka fara takaddama ban taɓa jin kome ba, sai yanzun da naso susha dan kaina, aikuwa ɗan mitsitsin bakin nan ya rike nipple ɗin, sai hakan ya matuƙar bani sha awa, ban san lokacin da na janyo wayar Batul dake kasan pillow na ɗauki hotonmu tana sha, duƙda da karama ce amma fa da kuzarinta, ina ganin ta koshi na cire nonon na bawa ƴar uwan, sam na manta da Ummi da take ɗaƙin, sai ɗauƙarsu hoto nake. Sai da tace
"Indai nono zaki basu toh ko ajiye wayar in kuma hoto xaki yi fita min a ɗaki."
Ajiye wayar nayi na cigaba da basu abincinsu.
Suna koshi ta mika min wani kofi me ɗauke da tea, an zuba wani gari kamar kuka, na kafa kaina na shanyetass.
Har ina lashe bakina, cikin ɗaurewan fuska tace.
"Maganin bayamma ce, kuma ki kula da ciye ciye dan basuyi kwarin da hantarsu zata ɗauki kowani kwamacalarki."
Tana gama faɗar haka tayi wuccewarta ban ɗaki.
Bayan dawowarsu Dudu ya gaya min dr na falour kamar bazan fita ba, na dai daure na fito.
Zama naƴi a kujeran da ke kallon nashi, nace.
"Ina kwana?"
A dakile ya amsa min
"Lafiya!"
Kamar wanda na masa dole, ganin zai min iyaye bai san ni miskilan. Nima a jinina yake, ga kuma wanda na koyo a gurin wancan gayen, banza nayi dashi sannan na mike zan koma ciki, sai da yagana kusan shigewa yace.
"Baki ji ba"
Waiwaye nayi na fara niman wacce yake nima, ban samu ba.
"Kana niman wata ce?"


Kauda kanshi yayi kamar baya falon yace.
"Kamar haka!"
Dawowa naƴi na tsaya abayan kujera nace.
"Hmm!ina da abinyi"
Kallona yaƴi sosai, a ranshi kuwa cewa yake.
*Na haɗu da miskila*
Kauda kaina naƴi na cigaba da kallon kofar falon, can yace.
"Ban ji daɗin abinda kikayiwa Mahaifiyar Baban twins ba."
D'ame bakina nayi snnan na tura gaba, kura min ido yaƴi yana jin wani yanaƴi na daban,
"Shi yasa nake miki uzuri dan har yau kina fama da kuruciya."
Wurga mishi harara nayi tare da murguda bakina nace.
"Ai ni sa'arsu Twins ne."

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login