Showing 48001 words to 51000 words out of 100319 words
Chapter 17 - Masarautar Jordan Book 1 Complete Document .txt
ɗan karamin part ne har da kitchen a ciki, koda zata so wani abu ta dafa da kanta, ajiyar zuciya na sauke. Sannan na zuɓe a jikinta tare da sake ajiyar zuciya. Murmushi ta sake tare da ɗan tureni cikin tsokana tace.
"Abinda Dudu bazaiyi ba shi kika fi aukinyi, baki san kin girma bane."
Tura baki nanayi gaba sannan na kara, kwanciya jikinta ina sauke ajiyar zuciya tare da maida kwalla, kamar yadda nasaka kaina akan cinyar haka Abdul ya ɗaura aƙan kafaɗarta muka shiga hiran. Cikin gajiya da mutuwar jiki nace.
"Ummina na gaji jikina ciwo yake min tare da mugun nauyi gashi bansan waye zai min tausa ba amma jikina na mugun damuna."
Gyara zama Abdul yayi sannan yace.
"Tun yaushe haka ya fara damunki?"
Juya idanuna nayi cikin jin daɗi yadda Ummi take matsa min kafafuna nace.
"Dudu kusan wata uku kenan, tunda abin nan ya fita."
Na karshe maganar a raunane.
"Tashi muje a dubaki."
Abdul yace min.
Taɓe baki nayi nace.
"Allah bani zuwa ko ina, bana son fita yanzun ma baka ji yadda nake jin amai bane, da zaka ce min mu sake fita."
"Kyaleta tukun ko zuwa gobe zansa Abideen ya kaita."
"Yawwa Ummina, Mother like no Other. Ilove you so much." na gaya mata ina lumshe idanuna,
Zaro ido Abdul yayi, sannan yace.
"Ina bolar mutanen da aka tsana Ummi kinganta ko akan idanunki kenan"
"Dudu har yanzun baka daina kishin nan ba." nace mishi tare da gwalo.
Gyara zama yayi sannan ya sunkuyar da kanshi, ya faɗawa Ummi abinda yayiwa Sophia.
Dariya tayi tare da cewa..
"Toh su me yar uwa shine har da koran yar mutane gidansu, baka ci riba wallahi ai bazata damu ba kaje kadawo da ita kuma ka Safina bazata koma ba, in dama dan itace ta zauna a nan, idan kayi hakuri zaka sha mamaki yanzun ka maida ita ɗakinta batun aure kuma ka jany.."
Cike da jin haushi na mike nace.
"Ummi kince ya maidata ya maidata, amma Aure kan wallahi sai yayi nice ma zan haɗa maka kaya ko sisinka karka kashe."
Make bakina tayi, cikin fushi tace.
"Me garinku! Ce miki akayi auren haka zai yi ba lissafi, dan ta miki laifi sai ku mata ramuqar gayya, kul kada naji ko na gani, aure bazan hanaka ba, amma ba yanzun ba kaje ku sasanta tukun."
Fuuuu na mike a falon na shige inda nake tsamani kitchen ne naje na saka furar sannan na fito zuwa ɗakinta ina shiga na zube a bakin gadon, tare da kwanciya.
Ban san tafiyar Abdul ba dan ban tashi ba sai uku saura, a gurguje naƴi alola, tare da gabatar da sallah. Ina cikin addu'a Ummi ta leko.
"Yakolo me kike so zaki ci."
Kasancewar sunan da take kirana dashi kenan sabida sunan Kakata ce dani. D'ago fararen idanuna nayi masu cike da barci nace.
"Taliyar murji da miyar jajjage amma Ummi na manja, sai ko alale duk wanda nasamu zanci."
Shiru tayi can tace.
"Ina ga alalen zaki samu taliyar zance a kawo min daga kano aƙwai Asiya kanwar Matar kawunku zatazo wani sati."
Gyaɗa kaina nayi, ita kuma tafita, akan sallayar na gungura. Karfe huɗu da rabi na farka, tare da mika, sannan na nufi ban ɗaki nayi wanka. Anan na karewa kirjina kallo sunyi wani irin cika. Dan wani lokacin idan nasaka bra ciwo suke min, dake kuma bani da irin mugun halittar nan. Sai haka ya tafi da jikina, amma maganar gaskiya nayi mamaki cikar kirjina, domin sunyi girma ba laifi dan suna tsaye ne car..(😎 kar a fassara min maganata)
Marata na shafa naji yayi min ɗim, ɗan latsashi nayi naji yayi min tauri ga zafin da yake min dole na hakura na fito.
Dukda ina da matsala a duk lokacin da watana yaƴi amma nakan share wata biyu ana uku nayi hailata sai dai tunda nayi yunkurin zubda cikin. Ban kuma ganin hailata ba gashi har wata huɗu.
........ Ina idar da sallar la'asar na fito falon nasamu har Ummi ta gama min, zama nayi jikina har da rawa, ga yaji a gefena. Ci nake ina wani lumshe idanuna tsabar daɗi, ina cinyewa ta kuma kawo min karɓa nayi na cinye. Zaro ido tayi.
"Yakolo cikinki yayi yawa fa."
"Wallahi kuwa Ummina, bari na sha furar nan inaga zan koshi."
Ina shiga kitchen ɗin ta bini da ido, cike da tausayi. Bata san na fito ba sai da na shiga shan fura me sanyi, ina shanyewa na tuna da masara da ayaba. Ɗauka nayi na fara ci ta kwace.
"Haba ina zaki kai su?"
Tura baki nayi sannan nace.
"Ummi bana jin daɗin bakina babu tauna don Allah taimaki jaririyarki mana"
Yadda na mata sai da tayi dariya, sannan ta mika min ina karɓa na kwaɓa fuska nace.
"Ummina bari na ɗumama su."
Tashi nayi naje ɗumamawa, ni da naje abu daban sai gani na koma yin wainar fulawa, lekowa Ummi tayi taga abinda nake. Murmushi tayi tazo ta ja kujera ta zauna ina kwaɓa fulawar.
Har na fara soya tana murmushi, dan tun da nafara nake cin ɗaya ɗaya, kafin na gama na cinye kusan rabi.
"Anya Safinatu cikinki nan ba rowa yasaki ba."
Wanda zan kai bakina ne ya faɗu kasa, cokalin hannuna shim Ya faɗi.
"Kina mamaki bayan kinsha magani yafita ko? Ai tunda Allah ya tsara shi a kaddararki ba makawa sai kin haifeshi, shawara ɗaya ce ki nutsu har Allah ya rabaku lafiya, tunda na amince da kaddararki ina ga babu amfani ki sare, idan kikayi haka zan ɗauka dan mahaifinku kikayi idan kika haifa min cikin zanyi farin cikin ansar kaddararki hannu biyu. Kuma zanyi alfahari dake, shi yasa nace bazaki koma ba ki zauna a nan ki haihu."
Wani iri nasiha Ummina take min wanda yake bin jikina da duk wani gabba yana kashe min su.
Ga wani irin soyayyar da take gwada min akan cikina da kuma ni kaina, bansan wa tabawa aika ba sai ga kayan baby. Cikin katon jaka, kunya ya hanani ko kallon kayan, dan wallahi yadda na tsani Ashrf haka na tsani cikin jikina ya yaudareni da cewa zai zo kuma ya barni cikin hatsari.
........ Yau monday na fara zuwa asibiti, ina bin layi aka zo kaina. Sunana suka tambaya na gaya musu, sai da suka ce.
"Sunan Mijinki fa, kin bamu safina kawai."
Shiru nayi cikin tashin hankali na lalube wayata na turawa Abdul text lokacin yana tare da Anim, turo min yayi da "kisa Abdul"
Haka kawai sai naji zuciyata tayi min nauyi.
"Ashraf!!"
Nacewa matar kaina a sunkuye, "Amma baki jima da aure ba ko? Irin wannan kunyar har ina."
*Da kinsan matsayin cikin da kallon banza zaki min* nace haka a raina.
Nasha yawo a cikin asibitin dama privet ne, ina gamawa Abideen yazo ya ɗauke ni, sai wash wash nake. Shi kuwa yayita dariya wai nafi kowa ragonta.
***
*SAUDI*
Shiru lawyershi yayi yana kallon yadda ya koma, can lawyer ɗin yace.
"Yallaɓai!"
D'ago kanshi yayi cikin kokarin ɓoye damuwarshi yace.
"Ina jinka"
"Kayi magana man, wallahi mahaifiyarka tana cikin damuwa, sai."
Naɗe hannunshi yayi sannan ya koma jikin kujerar yace.
"Kace mata karta damu haka Allah ya nufa, ta roka min ita wacce tazo dominta da ta yafe min, sai me?."
"Baiwarka Safinah!"
Kuraqa lawyer idanu yayi kamar zai cinye shi da su. Sannan ya sauke su akanshi tare da kauda kanshi, haɗiye yawu lawyer yayi sannan yace.
"Tana ɗauke da cikinka?"
Dunkule hannunshi yayi kamar zai kai naushi, ya ɗago tare da bin lawyer da ido, sannan ya mike zai bar gun lawyer yace.
"Tana cikin halin rayuwa dan sanadin cikin zuri'arta sun tarwatse."
Bai saurari Lawyer ba. Ya koma ciki kwalla na zubo mishi. Tabbas har da hakkin Safinah ke ɗawainiya dashi, ya lalata mata gobenta ya kuma ɓata mata rayuwarta, gashi har da rabo a tsakaninsu.
Gwara ya amince da laifin dan bai san yadda zai fuskanci safinah ba, shi da yace nan da wata biyu...... Lumshe idanunshi yayi.
***
*Abuja*
Shan gabanshi tayi cikin bala'i da masifa tace.
"Nice zaka munafutarta bayan kaji abinda karuwarka tayi na ƙunya aka fasa maganar aurenku shine yanzun ka koma binta. Na rantse sai naga bayanku ada can ma sabida Innarka na amince a yanzun kuwa zaka gani dani kake zance."
Bai kulata ba yayi ficcewarsa. Ya rasa inda zai kai fitinar Rabi wallabi ta buwayi rayuwarshi, bai san inda tajiyo ya koma niman Safinah ba, shi abinda yasani yana tare da Abdul, kuma yana samun labarinta kuma Insha Allah sai ya aureta.
***
Shiri nake amma jikina a sake, dan bana son zuwa asibitin dukda yanzun cikina watanshi na biyar kenan, ina jin yadda yake juyawa. Gashi yayi wani mugun girma, har ma yana son fin wataninsa, a yanzun babu takalmin da yake min sai silifas, duk zuwan Abdul sai yayi min tsiya wai na tara tsokoki kumatai, tabbas haka ne dan a wata biyar na zama ruguzun ruguzun. Gashi na kara buɗuwa sosai, ina gama shiryawa na fito. Yau babu Abideen da zai kaini, sallama nayiwa Ummi nayi addu'ar fita a gida, sannan na nufi bakin titi. Ina jirar taxi sai ga wata Audi, me tintec. Sauke glass ɗin akayi na kauda kaina. Me motar yace.
"Malama Safinah! Shigo na kaiki mana." da mamaki na kalle shi sai na kauda kaina.
"Kishigo cikin ruwan sanyi dan duk nan da kike gani akwai mutanenmu, kuma zasu iya sakaki a cikin motarda karfin tsiya, kawai ki shigo."
Shafa cikina nayi a hankali naji yadda yake juyawa sakamakon bugun zuciyata, kwalla ce ta zubo min me zafi, nasaka hannu na buɗe motar, bakina ɗauke da addu'ar niman kariyar Allah. Ina jan kofar ana sako hannu tabaya aka shaka min ɗan farin kyale, bingirewa nayi da barci ....
#MJ#HZƘ#Vote......
Oum Muwadda......
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAƘA WRITERS ASSO_
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*
Allah yasaka da alkhairi nagode sa addu'arku jiki yayi sauki sosai
Page.٢٤
Zare jikina nayi cikin na Anim, a hankali naja bargon da ya lulluɓemu na sauka rigata da na hango a kasa, nayi maza na suturta jikina. Sannan na shiga ban ɗaki, fitsari nayi. Jin cikina ya takure guri guda yasani shiga cikin kwanon wankan na cika da ruwan ɗumi na fara wanka. Ina idarwa na lumshe idanuna, tausayin makomar rayuwata nake.
Buɗe idanuna nayi cikin sauri bansan shigowarsa ba, sai hannunshi nayi a kirjin, buge hannun nayi.
"Wai meye ne haka? Ni bana son iskan...."
Buge min bakina yayi bansan lokacin da nace.
"Allah ya isa min"
Sake buge bakin yayi. Sannan ya cigaba da murza dukiyar fulani na,
Wani munafukin nishi na sauke, tare da tura kirjina gaba. Ina lumshe idanuna, loƙaci guda kwalla na zuba daga idanuna.
Shiga cikin ruwan yayi, tare da kwaɓe kaƴansa. Hannunshi naji yana shirin wuccewa kasata, nayi maza narike, idanuna akanshi muryana na rawa nace.
"Don Allah karka min haka! Karka manta kaima Ubane zaka ji zafi idan akawa Yaranka ha..."
"Ki bar gaya min Maganar banza domin ai baki min adalci ba da kika watsar da aurena, sannan kika dawo min wani abu daban, ina raye kika watsar min da virgin ɗinki abinda na tanadawa kaina, kika bawa wancan ƙaton bayan kinsan akwai mamallakinsa, sannan banyi magana ba nazo inayin abinda yadace zaki min Allah ya isa."
Bakinshi ya kai wuyata yana lasa tare da kai hannunshi kan cinyata yana shafawa a hankali, bani da abinda zanyi kuma bana jin zan iya yin kome, sai kuka zan iya cewa na tsani kaina da rayuwata badan kashe kai haramun bane da na rataƴe kaina na huta da masifar rayuwa.
Ganin yadda nake kuka wiwi yasa shi ɗaga hannunshi a jikina cikin takaici yace.
"Amma shi balaraben da ya same a ɓagas ince bashi kanki kikayi ba tare da gardama ba sai ni da muka ajiye maganar aure a tsakaninmu. Wai ni kam meye laifina son da nake miki shine laifi ko kuma soyayyata a gareki."
Mikewa nayi tare da ɗauraye jikina na fara kokarin fita yayi maza zai fincikoni na dafe cikin tare da kura mishi ido. Murmushi na sakar mishi tare da cewa.
"Ina ga baka san abinda ake kira da sarauta da mulki ba, sabida baka taso cikin gidan da suke da nasaba da mulki ba, kana k'etare iyakarka. Idan har jarumar Uwa zata iya sadaukar da rayuwarta dan soyayyar d'anta me kake tunani zatayi akan soyayyar jikanta, ba barazana nake maka ba kayi a hankali da shiga hurumin daular da babu irinsu a cikin yankin Jaziratul Arab."
"Tsoratani kike!?"
Ban kalle shi ba, nace.
"Shawari nake ba."
Fita yayi daga cikin ruwan cin matsanancin ɓacin rai yace.
"Ke kin isa?"
Wani banzan kallo na mishi sannan na fito, ba kaya yafito tare da niman nayi magana ya ɗirka min tijara, ni kuwa bani da lokacin haka. Falo na fito tare da kwanciya a dogon kujera, tun da nasan inda nake ban kuma fita ba, na mikawa Allah alamarina sannan ta ko ina sallah nake, dan bansan inda alkibilar take ba. Bana jin daɗin kaddarata amma yana iya tunda a juye tazo min, nayi imani da Allah rayuwata bata da amfani, dan daga wancar matsalar ta toshe still wani zai buɗe, a iyakar rayuwata ban taɓa jin bakin cikin d'a namiji ba sai yanzun.
Tunda naga na kwanta shima sai yazo ya kwanta a kujera me cin mutum biyu, ya zuba min ido ganin yadda nake barci. Haka ya matuƙar burge shi, dan haka ya ɗauko tap ɗinshi ya fara min hotuna.
.... A yanzun na daina mishi magana, kallonshi ma banaƴi abinci kuwa sai naga zai taɓa min lafiyar cikina, zanci amma ina cikin damuwa sosai, a cikin kwanaki uku zuwa huɗu har kafafuna sun kumbura. Gashi ko nan da ban ɗaki na shiga haki nake, duk sai naji na masifar gajiya. Sai mugun ciwon kan da ya sani a gaba musaman idan na kwana tunanin Ummina da yan uwana, toh nan ne fa, zan tashi fuskana a kumbure.
***
*Suleja*
Duk inda ake tsammanin ina nan babu ni babu labarina. Mamie tana sane da haka amma tayi banza da kowa ta cigaba da tsabgar gabanta.
Tunda Abba yaga Nannah batabi kansu ba shima ya shiga hidimar gabanshi, dukda tazo da kwararru a sarafa na'ura amma abin takaici, babu abinda suka samu sai tarin bakin ciki, domin mutanen da suka sace ni, gwanayen ne a harkan kwamusa.
....... Zaune take riƙe da casbi, tayi nisa a tunani. Nannah ta dafata cikin damuwa tace.
"Don Allah ki rage damuwarki akanta Insha Allah zata dawo cikin Amincin Allah."
Murnmusawa tayi irin me ciwon nan sannan tace.
"Nannah! Ba tunanin Safeenah nake ba, sabida nasan ita ɗin kamila ce. Dukda bata faɗa min yadda tasami cikin ba nasan haka kawai Safeenah bazata mika mutuncinta wa kowa ba, sai mijin aurenta, Nannah tausayin cikin jikinta nake, dan nasan Safeenah damuwar da take ciki bazai bata damar nutsuwa taci wani abu ba. Shine tunanina,"
Dafe goshi Nannah tayi, tace.
"Har yanzun bincike ake, Insha Allah zata dawo lafiya."
"Hmm" Ummi ta iya cewa, dake babu wanda ya taɓa tunanin Mamie tana da masaniya inda nake, karewa ma kamar bata san ɓatana ba gudun kar a zargeta sai da abin ya faru tafi kowa damuwa, gefe guda tana zuga Abba wai karuwanci nake, gwara yasan nayi kafin nahaifi shegen, idan ba haka ba kuwa sai an cika mishi gida da shegun jikoki, jin haka ya kira Ummi yayi mata cin mutunci na fitan hankali tare da cewa idan na dawo daga yawon duniya tasani na fidda miji ko kuma ya badani sadaka.
***
*Saudia*
Yana kwance a ɗakinsu idanunshi a lumshe, yana jinjina karfin cin amanar da Ghaniyu yaƴi masa, Ghaniyu yaƴi masa domin shi ya shirya masa kayanshi, hatta wanda zai saka shi yashirya masa, shi yasa lokacin da suka zo rabuwa yake share kwalla, tunawa da yayi matuƙar ya amsa bashi da masaniya akan kayan idan aka tambayeshi waye yake zargi zai ambaci Ghaniyu yasa yayi shiru, kuma a bisa dokar matuƙar ka bawa kotu wahala sai an ɗaureka bayan an wnke ka, sai an baka wani watanin a cikin gidan yarin kabawa shara'a wuya. Lumshe idanunshi yayi