Showing 6001 words to 9000 words out of 100319 words
Chapter 3 - Masarautar Jordan Book 1 Complete Document .txt
***
"Yallaɓai Alexandra mun mun sami labarin an sami wata Yar african da."
"Benjem kaje kasan meye ya kawo Yar african masarautar jordan."
Daga haka yayi shigewarsa ciki dan yayi imani da abinda bokanshi ya gaya mishi.
***
Fitowa yayi zai tafi masalaci ya ganni a zaune na cusa kaina cikin cinyoyina, kauda kanshi yayi ya bar gun. Saukar bulala naji yasani mikewa zubur ina sosawa ciki mutumin ya nuna min na shiga, yana bina har kitchen ya nuna min, sannan ya nuna min bango inda aka kafa wata yar allo da aka saka jerin sunayen abincin da za'a girka......
#HZƘ
#MJ
#MD.....Follow me: Mai_Dambu
Oum Muwadda...
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAƘA WRITER'S ASSO_
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*
Page.٥
Wato ɗakin da aka kaini yafi kowanne axaba, dan yadda kasan gidan bread haka cikin ɗakin yake , ga hayakin tire gas, nasha mugun wuya kafin suka fiddani.
A kitchen suka watsar dani zan iya cewa ban taɓa cin azaba irinta yau ba nasan mutane zasu so jin taya akayi na bar iyayena nazo nan ake wulaƙantani kaɗan daga cikin tarihina.
Safinat Badr Kyari shine ciƙakken sunana. Mahaifina ya fito daga kabilar Kanuri ne daga kasar Nigeria.
Mahaifiyata kuwa Shuwa arba ce dan ko hausa bana ji sosai sai turanci da shuwa sai larabci.
Nice Babba a gidanmu ina da shekaru 32 sai, kanina Abdullahi wanda yake tsaƙanin 28/29 Yana da mata har da yara biyu sai Nanah Asma'u wacce take da shekaru 25 tana da aure da yaro ɗaya na batarta da tsohon ciki. Sai. Sai Fatima tana da shekaru 21. Kafin ɗan autanmu Khalil yana da shekaru 17 bana ya gama scndry.
Mahaifinmu nada mata biyu har da Umminmu uku kenan Hajiya Amnah babarbariya ce daga Bama, tana da Yara huɗu.
Maryam suna kiranta da k'iose Tana da shekaru 25 sa'a Nana Asma'u ce. Sai Kaltume tana da shekaru sha tara, sai Sa'ar Khalil dan rana ɗaya suka haihu da Ummi ana kiran yarinyar da Khalilah, Hajiya Amnah muna kiranta da Umma. Sai Hajiya Nuratu fitinanniyar gidanmu kenan,
Matar tasaka ni a gaba sosai musaman da taga Nannah ta janye ni ta kuma nuna musu tafi sona sama da kowani yaro a gidan, Hajiya Nuratu wacce muke kiranta da Ammin tana da yara maza babban ɗanta sa'an Fatima ne yana da kusan ashirin yana jami'a shi dasu fatima, sunanshi Abba lawan, sai Salamn shima sa'ansu Khalil ne, sai Ruwaidah tana da shekara goma sha uku, da ɗan karaminmu Anas.
Mu goma sha biyu ne cif a gidanmu, Abbanmu haifaffen garin Amman ne nakasar jordan, sabida Mahaifin Ibrahim yayi aiki a karkashin , Sultan Yasir tun kafin ya zama sarkin jordan kasancewarshi na likitar har zuwa lokacin aka kifar da mulkin sultan Yasir, ya tattaro ya dawo maiduguri. Daga baya masarautar ta nemi ya koma bakin aikinshi yaki. A lokacin Abbanmu yana aiki a babban asibitin maiduguri ya auri Umminmu. Da Kakanmu yaga ya dan manyanta sai ya tura Abbana Masarautar jordan.
Ya tawo da ummi ya cigaba da kula da sarki Abdullah har aka haifeni, a lokacin Sarki Abdullah ya auri Nana Asma'u daga Masarautar Oman. Tazo tasamu ina da shekara biyu, zuwanta yasa abubuwa suka fara faruwa, ganin haka muka dawo gida ni da Ummi. Sai dai duk bayan wata shida Abba yana zuwa mana. Ina da kusan shekaru bakwai Abbanmu ya dawo shi da Nannah inda tazo tayita jinyar zuciyarta sabida rabata da sukayi da d'anta. Wanda suke sa'anin da Abdullah dan shekarun Abdullah uku.
Taso jan Abdul yana ɗibe mata kewar D'anta wanda bata kiran sunanshi. Sai Abdul yaki. Karshe nice taja, ni kuwa a lokacin da mugun son jiki tunda ta fara jana a jiki na sake zama sakaltacciya. Abba ya ya hajiya Amnah, wacce tana zuwa taga Nannah aikuwa hankalinta ya tashi, dukda Abba yana aiki amma albashin baya kai mishi yadda ya dace, ga fitinar Hajiya Amnah akan sai Abba ya kori Nannah yaki shine tayi fushi har da daka yajinta. Lokacin kuwa Allah ya saukarwa Abba wani iftila'i domin kuwa an koreshi a gun aiki ganin abinda zamu ci zai fi karfinshi Nannah ta kirashi mika mishi jakar da aka bata a masarautar jordan tayi, tace.
"Badar! Bazan iya biyan abinda kai min ba, dan ka ɗauko ni daga kasar jordan har nan kasarku, ka kuma ɗauki nauyin cina da sha, kana ɗawainiya dani, dukda kaki faɗa min an koreka a gun aiki ga ɗawainiyar Iyali gana yaranka ka ɗauki wannan dukiyar dan ni bansan me zanyi dashi ba, sun bani a matsayin sayan ɗ'ana sukayi, ina tsoron abinda ya faru a kan sarakunan baya ya komo kansh."
Muryanta ne ya shiga rawa alamun kuka zatayi fitowa nayi daga ɗakin naje kusada ita na ɗaura, kaina akan kafaɗarta cikin larabcin da take koya min nace..
"Nannah kiyi hakuri, idan na girma zan kawo miki d'anki nan kinji, kiyi addu'a na zama babba kinga sai kome yazo min da sauku."
Tunda tabawa Abbanmu kuɗin Allah yasanya mishi albarka, sai ma wani irin bunkasa dukiyar yake, dan kasuwanci yake daga dubai, lokaci yaja sosai dan har na gama primary schl zan shiga scndry a lokacin Nannah ta fara bani labarin, masarautar jordan. Dan bani mantawa na taɓa ce mata.
"Nannah taya zan shiga masarautar har na dauko miki shi?"
Dariya tayi sannan tace.
"Ke ba kamar sauran mutane bane kuma idan aka san zuwa kikayi zaki tafi dashi kashe ki zasuyi, ina son ganinki zama tankar sarauniya ki bar tunanin wancan duniyar."
Tura baki nayi cikin kunkuni nace.
"Nannah! Ni ki gaya min taya zan shig."
"Safinat! Masarautar babu tausayi ko imani, dai dai da kwalba idan kika fasa, hukuncine, sai kin wucce get huɗu da masu tsaronsu kimanin mutane ɗari uku, sannan ki isa cikin gidan bayan kin wucce dogon baranda kafin ki isa falon farko, wanda yake ɗauke da karti majiya karfu mutane goma suna tsaron falon farko, ki shige tacikin falon kije falo na biyu inda zaki samu. Wasu masu tsaro har mutane ashirin. Sannan ki yi tafiyar minti arba'in da zai kaiki cikin inda Sultan Ashraf yake. Taya zaki shiga? Wani hatsari zaki fuskanta na matsayinki na Y'a mace? Shin zai yarda ya biyo ki? Idan mugayen da suke tare da shi zasu barki ki fito musu da shugabansu? Idan suka san kudirinki na sace musu shugabansu me kike tunanin zasuyi don Allah ki rufa min asiri karki saka haka a ranki kinji yarinyar kirki."
"Amma Nannah ina ganin fit .."
Rufe min bakina tayi cikin damuwa tace.
"Ina gudun faɗa miki kome mutanen suna da nuna kabilanci musaman ke da kike da duhun fata. Suna kyamar bakaken fata."
Shiru nayi dan a lokacin banfi shekara goma sha biyu ba. Aukin tambayar tsiya.
Bunkasar da Abba yayi ne ya tattaramu muka koma abuja da kasuwancinsa dan yafi karfi tacan da lagos.
Bayan na gama scndry naki karatu a jami'ar kasan nan, rimi rimi akayi min kome a medicine inda aka kaini Ghana, ina zuwa can na koma Mass com, inda na shiga karatun babu wanda yasani a gida sai da nayi shekara ɗaya nazo hutu. Suka sani ranar nasha faɗa a gun Abba, ganin faɗan yaki karewa Nannah tafito tasa baki take Abba ya hakura, amma ya ji badaɗi.
Wannan dalilin yasa Hajiya Nuratu take kara jin tsanata. Musaman da yanzun kome Abba zai yi sai yaji tabakina.
Har na koma. A sannu gidanmu ya fara cika, kafin na gama jami'a gidan an cika ba laifu. Shekaru biyar na dawo daga Ghana, naje bautar kasa a Imo. Ina gamawa nasamu aiki da gidan radio na kasa dake Kaduna,
Amma Nannah taki dole aka dawo dani Abuja, dukda shakuwar da mukayi da Nannah baisa idan nayi laifi ta ɗaga min kafa ba, faɗa take min sosai.
Lokaci ya tafi dan bayan na fara aiki na koma makaranta nayi degree na biyu, abin mamak shine na koma kamar me cutar junnu dan bana kaunar maganar aure, kuma lafiyata lau, ganin haka ya ɗaga hankalin Iyayena. Murmushi nannah take kawai idan taga sun sani a gaba suna min faɗa, bata hanasu dan nima da nawa shegantakan, cikin ruwan sanyi manema suke zuwa min karshe basa kwana biyu na koresu, fata fata kuwa. Ni a tunanina idan nace zanyi aure waye zai cikawa Nannah burinta shiyasa naki auren kowa, tunda nasa a raina zan dawo mata da ɗanta na kuma ji na gani.
Na taso da wannan burin a raina ko iyayena basu san da shi ba hatta itama Nannah bata sani ba dan tabar min maganar, ni kuwa tausayinta yasani kudirawa a raina sai na dawo mata da ɗanta.
Bayan shekara biyu da rabi na gama degree na, na biyu. Wanda yayi dai dai da haɗuwana da Anim. Sabon shugaba gidan radionmu, da wasa muka fara sama sama, sai gashi mun kulla soyayya, wanda yaje har gaban iyayenmu. Aka tsayar da magana maganar aure a tsakaninmu, tunda naga haka hankalina ya tashi. Karshe na nemi Aliee dan kasan jordan ne na zaunen syria ne, mun haɗu dashi a ghana ne yaje wani course. Nan nima n kirkiro tafiya course ɗin shekara guda. Dakyar aƙa d'aga bikinmu, dan ma Anim yana da mata har da yara biyar.
Kuma dan bokone sosai irin mutanen nan masu akidar boko, dan haka ban sha wuyar shawo kanshi ba ya amince aka. Kwana uku tsakani na wucce jordan. Sau uku ina niman aiki a cikin masarautar suna hanani, karshe sai Aliee ne ya faɗa min basu bani aiki ba dole sai nazo a matsayin baiwa, banso haka ba. Amma babu yadda na iya idan na tuna yadda a gidanmu, dukda an aurar da ƙanena haka bai taɓa damuna ba Ammi tayi min gori har dasu habaici baisa na damu ba, a yanzun nayi na damar tsallake auren Anim da nayi gashi ba biyan bukata, tunda nazo a baiwa dole naga tasku. Da gatana nazo ana wulakantani dan ko Aliee ban faɗa mishi abinda ya kawo ni ba.
***
Ajiyar zuciyar na sauke, tare da goge kwallana. Dakyar na mike na shiga jan jikina zuwa ban ɗakin na watsa ruwan zafi me mugun zafi, sannan na fito na maida kayana. Abinci Samin ya ajiye min na ɗauka naci. Cikin jimami yace min.
"Me yasa kike da taurin kaine? Ki bar katsalandan a cikin masarautar nan."
"Samin kenan aiko mutuwa zanyi sai na faɗawa Sultan gaskiya, mulkin zalunci akeyi a wannan masarautar da cin zalin."
"Zaki sha wahala!"
"Kasan wahala ita shirya masa ake ba"
"Kinsan yarone bai da hankali a matsayinki na babba ya kamata kija girmanki, ki kiyayye doka."
"Ni zan faɗa maka Ashraf yarone tunda. "
Ganinshi mukayi akanmu, kamar bai ji me muke cewa ba, ya shiga kitchen ɗin ya ɗauki abinda zai ɗauka yafita, yau babu mulkin babu bada oda toh ina ma yake magana, kullum fuskar nan a ninnike, sai kace wanda aka aiko masa da sakon mutuwa.
Ina jin Samin ya gma abinda zai yi, bayan ya min sai da safe. Ni kuma na baza hakarkarina a gurin......
😩 Insha Allah ina kaiwa page 10 zan ajiye typing....
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAƘA WRITER'S ASSO_
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_
_Jordan Historical_
*®2020*
*BOOK ONE*
Page.٤
Time table ɗin na duba naga jerin abincin kamar haka.
Break Fast:+ Roasted nut & Bedouin tea
Lunch:+ Kunafa & Zarb tea & fatter.
Dinner:+ Mansaf & Shawarma &Fresh Juice.
Na yau kenan, abinda na fara kayan haɗin na nima musaman na karyawan safiya. Wanda nagani a cikin store abinda na fara shine niman wasu bread masu zubin gurasa, na haɗa kayan haɗi kasancewa ana haɗa roasted nut da y'ay'an cashew ko gyaɗa, kuma naga haka na haɗa dukda bani da tabbacin zai ci, bushashen ganyen shayi na bedouin na haɗa da minannas da citta da kanunfari na dafa. Kamar yadda naga Nannah tana dafawa idan ina gida.
Kafin karfe shida na gama sannan na gabatar da sallah a kitchin ɗin nayi har da alola dan kitchen ɗin har da bayi a ciki.
Ina idarwa na shiga juye abincin a manyan warmer, ina fita dasu falo inda aka tanadar da dinner table. Ina gamawa na koma kitchen ɗin na wanke kayan da na ɓata sannan na goge ko ina nafito dan kome na kitchen ɗin black & whiter ne.
D'an jimawa da nayi a kitchen ɗin na fito, ganin masu tsaron lafiyarshi a gaban table ɗin abincin sun zagaye abunci. Juyawa nayi zan koma rigana ya kama wani flower kafin na tare ya faɗu kasa, fassss ya bada sauti sai da gidan ya ɗauka. A fusace sukayo kaina jikina ne ya ɗauki rawa, kafin nasan abinyi sun rufe ni da bulala, sai da suka min tiliss sannan suka sani tattara kwalaɓen, na zuba a kwandon shara.
Sake sani a gaba sukayi har gaban abincin cikinsu ya sunkuyo da kanshi dai dai fuskana yace.
"Ki ɗiba kici."
Kwallar ke zuba a idanuna ga zazzaɓin da yake cin jikina na dukar jiya, ga kuma na yau a hankali na kai hannuna na buɗe warmer na shiga ɗiban abincin na ci sai ruwan bedouin tea nasha, da kuma normal ruwan kwalba nasha, ina gamawa suka tattara abinci aka fita dashi. Can sai gasu sun dawo suka zuba kwanika, babban ya kuma sunkuyar da kanshi yace.
"Girkin yayi kyau, amma Sultan bazai ci abincinki ba kasancewarki bakar fata dan haka zaki zauna a nan kina dafawa karanunkan da kuliyoyinsa abinci sai gyaran gidan kece zakiyi tayu za'a kawo wanda zai na girka mishi nasa abinci naki girkin dabobine."
"Taɓɗijam wa mage da kare zan zauna ina girka musu abinci"
Abinda nake faɗa knn a raina, bansan sun bar gun ba, sai da na ɗago naga duk sun bar falon.
Wato haka kogin kaddara ta kwasoni zuwa bakin gaɓɓar da bani da hanyar gottawa.
Koda na maida kwanikan kitchen zama nayi na fashe da kuka dan duk jikina ciwo suke min ga wani zafin azabar da shatin bulalar yake min.
Duba agogon kitchen ɗin nayi naga takwas har da rabi, da sauri na fito na duba Machine ɗin shara na shiga share ko ina, na falon. Ban gama sharewa ba sai karfe goma tsabar girman falon.
Sannan na shiga goge gidan tsaf na gama, wani show glass na hango cike da turaruka, tsautsayi ya ja ni zuwa gun. Wai nasaka a falon, ina zuwa zan buɗe naga hangoshi sanye da kayan sport wando da rigar ta kamfanin R&B. Hannunshi rike da goran ruwa, sai zufa yake gogewa. Bansan ya akayi ba jikina ya kama rawa ba kafin dai san abinyi nasha wani kwalba ya faɗo, tasss ya bada sauti.
(😂 Feener kin cika shishigi ina ruwanki ki tsaya inda aka ajiyeki mana)
Wallahi kaman a kunnen kartin nan fasa kwalbar sai gasu sun shigo kallona sukayi, nima kuwa na tsura musu ido dan har na fara kwalla. Basu duke ni ba sai dai sun sani kwashe kwalbar turaren sannan suka fita dani, aka kaini d'akin sanyi. Suka wurgani. Sai da nayi minti talatin sannan suka fito dani bana numfashi. Ruwan zafi suka watsa min har sau biyu.
Kaii Jama'a bawa baida yanci kuskure kaɗan zakayi kaji ajikinka.
Dakyar na farka suka sani a gaba har shashinmu na sake sauya kayana, babu yan matan nan kuka nake ina dana sanin zuwa na masarautar jordan, dole