Showing 99001 words to 100319 words out of 100319 words
Chapter 34 - Masarautar Jordan Book 1 Complete Document .txt
musu wanka, amma yan butan uwa ina zuwa kusadasu zasu shige jikinki kamar sunga Dodanniyya."
Tashi nayi ina dariya, nace.
"Wallahi a cikin kwana biyu da dawowanshi. Suka ɓaci haka da mugun kiuya ai dalilin barowa ta can wai dan"
Bansan lokacin da nayiwa bakina linzami ba, tabbas a cikin wawaƴe ni babbar wawuya ce, dan tsakani da Allah nake shirin facala mata iskancin da Ashraf yayi min.
(Nace ko baki kira kanki wawuya ba Fans ɗin Ashu zasu kiraki dan kar suƙe kallonki.😏😎😏)
"Au dama sabida yaranshi kika gudo?" Ummi ta watsa min tambayar.
Take na fara firitendi(😹 ina son turancina) da cewa.
"A'a kawai kinsan larabawa da son yara, kuma ɗaukesu yake bani sake ganinsu, kuma bayan haka ina kewar gida. Shi yasa nace azo a ɗauke ni."
Murmushi taƴi dan taji nine kawai amma bawai ta yarda bane.
"Ai sai kije ki musu wanka, kar ruwan ya hucce."
Na mike cikin sauri na shiga da Aamih na cire mata kaƴanta da pampes, na shiga, ita kuma taja Aanih ta cire mata, ina fitowa da Aamih ta amsheta sai ihu take tsalla mata,, ina gamawa yar uwan na kawota nima naje nayi nawa, sannan na fito ina goge jikina.
D'aya daga cikin jakar da nazo dashi, Ummi ta buɗe. Kayan yarane masu mugun tsada, da kyau. D'ago kayan tayi kuma iri ɗaya sai banbanci kala.
Su kansu kayan irin shigar masarautar Jordan ce, kome na ciki golden da ratsin ja.
Ciro musu wani Overall taƴi light blue da ɗigon pink, a ciki sannan takamasu tasanya musu pampas, da kayan ta kuma kame gashin kansu a tsakiya. Sai kukan banza suke mata, ni kuwa ina ta dariya dan fadarsu da yaran ya burge ni, sai ta gama kare musu zagi, sai ta dangware goshinsu. Aikuwa su fasa kuka(😂) sai tace musu.
"Na dakeku dan kofar masarautar garinku masu idanu a tsakarka, dube su."
Ta kuma dangwaresu, aikuwa takwarata Aamih taja kuka, tana kallonta tare da jan kukan ta tsalla.
"Kaii! Ummi da alamu zaki gigita Sultan wallahi ya kirani yafi sau ashirin, a bashi yaranshi." inji Dudu.
Yana rufe baki kiran na sake shigowa, ɗauka yayi yace.
"Gani a gidan! Amma taƴa zasu."
Kara wayar yayi a ƙunnen Aanih, wacce take wangale bakinta kamar kofar garinsu, shiru tayi tare da sake bakinta.
Amsar wayar nayi na kara a kunnena. Shirme fa yake gaya musu, tare da shiririta sannan shi kanshi yadda yake maganar zaka rantse da ALLAH matseshi akaƴi, Kashe kiran nayi ban kai ga mikawa Dudu wayar ba ya kuma kira.
"Don Allah ka buɗe wata jaka zaka ga kwalin Ipad, a saka a caji tare da wifi ɗinsa yake, zan na kiransu ta nan."
"Ok."
Dudu yace da sauri yana buɗe jakunkunar, can ya samo sannan yakai jikin Abin canji.
Ni dai ina kallon duniya, yaushe akayi wannan sayayyar, koshine fitar da yayi lokacin muna hotel ɗin nan da na shiga wanka, *oho* nace a raina.
Tsakani da Allah Dudu ya biyewa Shirmen Ashraf, yafita can sai gashi da layin Mtn, tura mishi number yayi. Duk wannan bidirin da ake ko sau ɗaya baice ina nake ba, sai Ummi ce ma da suke buɗe kayana, suka ga dukiyar da masarautar Oman suka bani, take suka shiga Sharhi akai, Sophia da Nana Asma'u da suka zo. Min sannu da zuwa suka fara kiyasa kuɗin manyan abin wuya da yan kunne, take suka shiga niman jin kuɗaɗensu, ina jinsu, dan sai lokacin nake karyawa, Umma da tashigo itama sai da tayi girmama alamarin, Madam kan da tashigo kasa hakuri tayi cikin son mu shirya tace.
"Yar nan ga inda arziki yake, ki saki wancan dukundukun, ki kama Ashurafa, tunda yarone ai zaki mori kuriciyarsa. Kinga wancan Malohon tsufar dake zai yi jininshi tayi kauri, wannan kuwa jininshi harbawa take, sosai kuma zaki ce na gaya miki."
Salin Alin na bar ɗakin, sabida maganar wannan tsohuwar ba kan gado, kunya sai ya kasheka ita kuwa bai sumar da ita ba.
"Kilaki an dawo daga barbaran D'an taurene?" ko ban faɗa ba kusan wacece. Murmusa mata nayi.
"Eh magajiyar karuwai Uwar ɗakin Yan daudu, na dawo ban kawo miki kasonki ba, ba saikin zo amsa ba, dan duk inda kilaki take dole asamu uwar dakinta, zan kawo miki kasonki dan shin basarake ne yafi karfin taure."
"Toh mara mutunci yar isa wacce ta ajiye y'ay'an gaba da fatiha."
"Eh mana, nida natashi karuwancin riba biyu nasamu, ga Yara ga Dukiya, kuma ni yau zanyi karuwanci wallahi nafi karfin matsiyacin me kuɗi sai irinsu Sultan Ashraf wanda suna cinka zasu ajiye maka arzikin yanke talauci, nan da Kanwarki Ade tazo kafin ta koma sai da ta sace min dubu goma taje aka cire mata ciki, dake ita nata Asirin ya rufu shine bari ki bankaɗe na wasu, sannan Hunaidah da kuke cewa tayi aure mijin yarasu shine dangin mijin suka kwace dukiyarshi hhhhh! Mamie. Ko dai taje an juye mata fetir a cikin injin ɗinta kuma batasan wani gidan mai ne aka mata wannan juye, bane ni me sa'a ce ko yau nashiga wani gida bani da kaico sabida Ubansu ya mallaki abinda zai rukesu har karshen rayuwarsu, ki iya da harshenki, idan yarana shegune toh tabbas ina Alfahari da cewa Ubansu ya mutu akan kaunarsu, dan koda wasa wani yayi gigin lakatarsu hmm wata miyarsai a makota ni kaina bansan meye balaraben Kasar Jordan zai aikata ba, amma nasan ya kware a bada umarnin a yanƙe kan mutum daga gangar jikinsa, Allah ya baki sa'a haukarki ta taɓa mishi idanunshi."
Duk yan cikin ɗakin Umminmu cirƙo cirko sukayi, dan ba karya Mamie ta kaini bango kuma na fyaceta na huta da iskancinta, kuma wallahi ta taɓawa Ashraf Y'a toh wallahi idan ya haukace zanga me iya dakatar dashi.
"Wallahi Nuratu kinyi asara! Yaushe zaki daina kishi da Safinah wad'ancan murɗa murɗan yan matan da kika kwaso ba a miki magana ba sai kece zaki sanya yar masu gida a gaba, muguwa me kashin awaxa kashin tsiya".....
(Kaii Hajja Kaka matsalana dake Ove Acting, kome sai ta faɗi abinda babu shi a cikin kundin balaga😹🏃)
_Yan Paid grp kuyi hakuri mu gama book One, Insha Allah 8 more kullum amma sau ɗaya idan kuma zaku amince 4 more da safe insha Allah da dare 3 more toh Insha Allah zan baku a Book 2-3 da yardan Allah in yaso wannan book one tunda free ne du kare a 3 more ko yan lelena ina ji daku kamar yadda nake ji da Yar magen makotarmu😹😎_
*Masoyana na Nijar ga number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a dalla 100 +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150 ne idan kuma Kati ne Transfer 200 ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode saura 13 pages Insha Allah*
Oum Muwaddah......