Showing 54001 words to 57000 words out of 100319 words

Chapter 19 - Masarautar Jordan Book 1 Complete Document .txt

kaɗa, shafa cikin nayi zuciyata cike da tausayin Yaron cikina haka kaddara ta kawo mu wata nahiya na daban..


***
*Jordan*
"Nazone abisa ka faɗun ahalin Banu Hashim, banzo dan muradina ba Ukshe nasanka sarai na kuma san waye kai, Ukshe kana da hannu a cikin alamarin Ashraf, mulki kuke so ya barmuku dukiyar da kuke bukata ya barmu, tsinke na masarautar bai ɗauka ba. Amma kuka zuba mishi makamai a jakarsa dan b'ata suna ga alummar musulman duniya, abinda kuka yi sam baku kyauta ba, daga ni har kai bazamu taɓa mulkin Jordan ba koda kuwa, babu wata a kasa amma ka kasa gane haka."

"Karka dame ni, idan baka da abinyi ni ina dashi." ya gayawa Abu Zarri.
"Ni keda abinyi kuwa dan yanzun haka nasa an tura videon yadda kuka zubawa Sultan Ashraf Mugayen makamai,karka matso kusadani, domin yanzun nasan inda ke min ciwo, sannan da kake gani na a nan ansan da zuwa na, kuma idan ban fita ba kaima rayuwar ɗanka tana cikin kazamar hatsari."
Cire hannunshi yayi daga cikin alkyaba, ya mika mishi Tap, yace.
"Taɓa cigaban mana! A duniya babu wanda yakai balarabe fasaha, dan haka karka manta jini ɗaya ke gudana a jikinmu, indai har zaka iya kasa fuska ni ɗin zaman me nake da bazan iya ba, shawara guda ɗaya na baka ka rabu da Ashraf kamar yadda ya zaɓi mace akan mulki, idan kuma kaki zaka iya fuskartan mutuwa dole."
Yana gama sambaɗa mishi magana ya amshe tap ɗin, ya kalle kan screen, Marhum ne an ɗaura mishi bindiga a goshi.
"Kana nufin d'ana da ka kama zan ji tausayinsane? A cikin zuciya ake gini buri da muradi! Dan tunda na fahimci ina da ikon juya sarki da mukararrabansa,naji a raina koda bala'i sai na cika masarafar ikona, wallahi ku mika shi ga Saudia ni kuwa kuncika min burina na zama Sarki, domin yaso min iyaka kuma nasanshi akan naci, godiya nake."


Cak Abu Zarri ya tsaya mamaki cike da zuciyarshi, a sannu ya juya ga Ukshe.
"Kai baka da kawazuci ne?"


"Kawazucina akan mulkin jordan ne kuma nasamu hakan dan haka zaka iya fita."


Murmushi Abu Zarri yayi sannan yace.
"Idan bana raye kenan?"

"Amma nagode maka da tuna min da kanka, idan baka raye fa? Zan zama sarki na har abada."


Abu zarri bai kula shi ba dan ya lura kaunar mulki da haukar son rike madafun iko ya zararra da Ukshe, sai dai su cigaba da masa fatan shiriya.
Yana fita ya bada izinin a tafi da Marhum kawai, dan ba zasu cigaba da kalle rashin adalci ba, sannan ya mikawa lawyer da yazo hannun suka gaisa, ya juya ga Ghaniyu yace.
"Nasan an zalimceka! Tunda a sanadin haka ka rasa kanenka da mahaifiyarka, ina ga ka ɗauki matarka kabi Ashraf duk inda zai je ka zame masa kariya amma karka manta a yanzun ba zai yarda da kai ba, sai kasan yadda zaka faɗa mishi gaskiya dan ya amince da kai. Akwai jaka karama me ɗauke da kuɗin amurka ka bawa Ashraf. Sannan duk inda kuka je ka tabbatar da ka gaya mana kodan halin rayuwa, sannan ka roka minshi yafe."
Daga haka yayi wuccewarsa, ba tare da yabi takansu ba,
(Ku cigaba da bin sarkakken labarin a hankali zan warware muku,)
Motar da aka ɗauki Marhum tare da jami'an tsaron kasar Jordan aka fita dasu daga masarautar, suka nufi airport
Basu same matsala ba, suka bar kasar dashi,
***
*Nigeria*
Suleja.....


Sheik Hayatudden Kamfut ne zaune shida y'an uwansa, Kan Ummi na bisa cinyar wata dattijowa, ta lumshe idanunta. Sai a jiyar zuciya take saukewa dan yau tun safe ta bar Suleja zuwa abuja, tun asuba tacewa Ummi ita tana zargin Mamie da Badar, akan ɓatar Binti. Kuma ta tafi kome zai faru(😎😏 Mamie mek sho yu run)

Sai da ya gama Addu'a sannan ya kalle Ummi cikin tausayawa yace.
"Mariamah kukan zuci kike? Karki zubda kwallarki dayawa a duk inda Safinah take Insha Allah yau zuwa gobe zata dawo gareku, da Allah muka dogara ba da wani ba, Allah da kanshi yace alkur'ani waraka ce."
Tunda Safinah ta ɓata har yau Ummi bata zubda kwallarta ba, sai dai kawai zata zauna tayi ta sauke a jiyar zuciya, kimanin sati uku zuwa huɗu kenan.
Alkur'ani aka raba irin bugun sokoton nan. Dan a cikin jakarsa yake, ya bawa kowa falle uku-uku, sannan ya fara da fatiha.....


***
Tunda Mamie ta isa garin Abuja tasa Abba ya kira kowa, cikin ruwan sanyi ta gabatar da abinda zatayi sannan ta fidda takarda tace.
"Aranar uku ga watan biyar, Nuratu kinyi waya da wannan number sau uku, ana saura sati Safina zata ɓata. Bayan kwana biyu acc ɗinki na bankin Access sun amshi naira dubu ɗari shida, daga wata acc ɗin, bayan sace Safina. Ranar goma ga watan shida kunyi waya da wannan number bar aka kuma turo miki da naira dubu ɗari bakwai, sannan an kiraki ne daga can tsakiyar ruwa atlanta ocean, ranar ashirin da ɗaya ga watan shida an kuma kiranki, tabbas kinyi kuskure. Waye shi?"


Zuba ke karyowa Mamie sosai duk yadda taso rike fitsarinta kasawa taƴi, dan ta jika inda take zaune jagwab
***
Yana shigowa ya ganni na kifa kaina da jikin gadon yana ɗago fuskana yaga na bishi sharaf na zube a jikinsa, ga bakina ya koma gefe. Yawu na fita me yauki haɗe da jini.
"Safeenah" ya shiga girgizani. Ganin bana motsi yasashi ɗaukata dukda nauyin da na kara. Haka bai dame shi ba ya fita dani da sauri. Kamar zai tashi sama, filin da aka tanada dan saukar privet jet ya nufa dani tare da kiran masu tuka jirgin. Suka taimaka mishi aka sani a ciki sannan ya kallesu yace.
"Ku tabbatar da kun kaita Abuja akan lokaci, idan wani abu ya sameta kuyi kuka da kanku."


"Yes sir!" suka ce mishi, tare da fara tada jirgin, sumbrta Goshena yayi, sannan yace.
"Kece sila! Ina sonki da zuciya ɗaya kika maida min so cuta. Allah ya baki lafiya zanzo na aureki."
Rufe kofar yayi, tare da juya musu baya, har suka tadda jirgin har suka tashi sama.
D'aga kanshi yayi yana tare da bin jirgin da ido har suka ɓaccewa ganinsa. Tafiyar awa biyu ya fitar damu yankin tekun.
A cikin awa uku da rabi suka sadani ga wata karamar asibitia cikin abujar gudun kar a kamasu yasa suka rufe min fuskana, sai da suka gama kome sannan suka bar asibitin. Dr Muhsin shine yazo kaina domin dubani. Dake yaga sun rufe min fuska, kamar bazai buɗe ba, sai wani tunani yazo masa ya ɗaga mayafin.
"Safeena!!!"
Ya ambata da karfi, gumine ya shiga karyo masa, wayarsa ya lalluba ya shiga niman Abdul cikin tashin hankali ya same Abdul yace.
"Duk inda kake ka tawo asibitin Alheri."
Bai barshi yayi magana ba ya datse kiran, Abdul kuwa yana can, Nannah tana yanta Abba da Mamie.
..... Bayan minti ashirin ya iso, tsananin faɗuwar gaban da yake ciki, ya hanashi fitowa. A sannu ya tattaro yar jarumtarsa ya fito daga motar tare da rufewa ya nufi cikin asibitin, kiran layin Dr Muhsin yayi yana ɗauka yafito daga ɗakin da aka sakani, a sannu ya isa ɗakin. Tare da kura min ido, zuwa yayi bakin gadon ya ɗaga lulluɓen fuskana. Ji yayi kamar zai faɗi Dr Muhsin ya tallafeshi, kamar yaro karami yace.
"Da gaske Safinatu ce!"
"Be a Man! My frnd karka sa nace ka rako maza mana, ka tsaya mu taimaketa, yanzun nake son ɗiban jininta aje a gwada ko akwai sugar sai musan abinyi dan kaga yadda ta kumbura za a iya rasa Uwar ko Babyn."


Fita Dr yayi shi kuma yaja kujeran ya zauna, yana kallon kumburarren fuskana, har dr muhsin ya shifo tare da nurse da kuma, da bututun shakar iska, wato oxygen aka samin sannan ya bada dama aka ɗibe jinina, suka fita zuwa lab, can bayan wani lokaci suka dawo aka samin, mika mishi report ɗin yayi cikin lallashe yace.
"Bata da matsalar kome sai kumburin da tayi, zuwa an jima zamu kaita ɗakin gwajin zuciya. Sannan yana da kyau kakira mutane gida ka gaya musu."


Wayarsa ya ɗauka ya kira Ummi da suke tsaka da addu'a. Ya sanar mata,
Sannan ya kuma kiran Nannah ya gaya mata, tuni ta kyalesu Mamie wacce aka musu ɗaurin wulaƙanci aka watsa a bayan kanta.
........
Lokacin da Nannah ta gama zayyanowa Mamie abinda tasamu akanta, cikin rawan jiki ta amsa. Ba tare da jin kume ba Nannah tasa aka tafida ita har bayan gidan aƙa fara tsoma kanta cikin ruwan swimming pool. Da taga zata mutu shine ta buɗi baki zatayi magana Abdul ya kira Nannah.
Kota kanta bata bi ba, tafito inda tasa drvn gidan ya kawota asibitin.


Kafin awa ɗaya yan uwana da dangina sun cika asibitin, kowa yana min fatan samin lafiya, sun samu cikin ya fara kuzari nice ma dai ban farka ba. Sai da na share awa uku biyar cur sannan na farka, tunda na farka nake kare musu kallo dan gani nake kamar mafarki nake, ina son magana harshena yaƴi min nauyi, dan haka na sake lumshe idanuna barci yayi gaba dani.
Ban kuma farkawa ba, sai washi gari da misalin sha ɗaya. Buɗe idanuna nayi naga Ummi da Nannah, hannuna ɗaya na kai kan cikina naji yana kicking yadda ya dace. Murmushi na sake tare da cewa.
"Babynsu Nannah"
Kura min ido Ummi tayi taga nasake magana, tasowa tayi sannan tace.
"Kina son wani abu ne bama jin abinda kike cewa."
"Ummi baku fahimtar me nake cewa kenan."
Nan ma Nannah tazo tace basu fahimci nake cewa ba. Saka hannuna nayi na shafa fuskana naji bakina ya koma gefe. Kuka nake son yi amma na kasa, da karfi na rufe idanu na, na shiga sauke ajiyar zuciya. Ina jin Ummi tana kiran Abdul tare da gaya mishi halin da nake ciki.
Barcin dole ne yayi gaba dani, dan ban farka ba. Sai karfe biyu ina buɗe idanu na, sai akan Anim. Mugu ɗan masara ana goyaka, kana karya uwarka. Kukan da ban samu damar yi bane ya kwace min na shiga fisge-fisge saura kiris na faɗo daga gadon Abdul da Nannah suka tare ni, fita ABDUL yayi sai gashi tare da Dr Muhsin. Alluran barci suka min Idanuna na kan Anim.
Ajiyar zuciya Nannah ta sauke, tare da cewa.
"Abdul ko za a cire abin cikine wannan wahalar tayi yawa, kullum babu sassauci daga wannan sai wannan, gabaki ɗaƴa Safinah ta fita hayacinta."


"Ai matsalar shine cikin bai cika bakwai ba, amma da zaran ya cika bakwai insha Allah zamu cire babyn, dan girman cikin ma yana rinjayarta." Inji Abdul,


"Ni a ganina ku bar cikin ya shiga watansa in yaso sai a cire mata, dan nima na karaya da alamarin Safinah, na yau daban na gobe daban."


"Kuma ana cire mata yaron zan bawa Alhaji Zubair yayan Nuratu it....


👏👏👏
_A cikin duniyar nan kowa ya tara abin fada, amma kalilan suke iya ajiye nasu, ba sauki rungumar Alamari me wahala ga karamar irina, Hidimar miji da Hidimar yara.... Ba abu me sauki bane ɗaukar nauyin da bai zame maka tilas ba, idan kiɗa ya sauya dole rawa ya sauya....._




Uom Muwaddah...
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAƘA WRITERS ASSO_


*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*
_Na sadaukarda wannan shafin ga Iyaye mata masu fafutukar kare Yaransu....A cikinsu Har da Mahaifiyata Allah ya jikanki da Rahama👏_
Page.٢٨- 28


" Ban tab'a karo da mutum mara mutunci irinka ba, banza mugu fasiki, mujirimi kawai. Kafit."
Maganar da ban karasa ba kenan na haɗiyen dole, sakamakon jin bakin d'an iska da nayi cikin nawa, duka nayita masa. Tare da ture shi da karfin tsiya, na kuma tofa mishi yawunsa a fuska, kazamin banza shafo yawun yaƴi, tare da lashewa har yana lumshe idanunshi, girgiza kai yayi da takaici ya kamani. Bansan lokacin da na ɗauki kwallo goriba na kwalle goshinsa, kam uban bala'a alkur'an sai akan idanun Abba. Tsabar na tsorata garin na yunkura zan mike sai da naji bayana ya amsa, tare da zuban abu a jikina.
"Safinah! Rashin mutuncinku har ya kai ya taɓa mutumin da yake jeka ka dawo akanki, yau zaki gaya musu."
Dakyar na mike dan naga yana gun Anim wanda goshinsa ya fashe, zasu fita ni kuma na shige gurin Ummi, ga baki ɗaya na birkice domin dakyar nake ɗaga kafana, ga cikin da yawo kasa baki daya.
"Ummi!"
Na kwala mata kira da karfi sannan na durkushe a gun, sabida jikina wani irin rawa yake, har cikin kashin jikina rawa suke. Ga zufan da yake karyo min haɗe da wani mugun sanyi me shiga jikin mutum.

"Safinah! Haihuwar ce."
Gyaɗa mata kai nayi cike da azabar da yake addabar gangan jikina tare da yin dagadaga da ruhina, duk sai ta ruɗe kamar bata taɓa haihuwa ba, komawa ban ɗaki tayi ta ɗauko kujera ɗan tsuguno, ta nuna min yadda zan ɗaura hannuna a kai tafita da sauri, sai side ɗin Umma.
"Amnah zoki taimake ni Safinah ina ga haihuwa c.."
Ai Ummi bata gama maganarta ba Umma ta fita da sauri, suka nufo side ɗin Ummi, umma tace.
"Har cikin yakai haihu ne?"
"Eh toh ina dai tunanin bakwai kenan."
Suna shigowa kukan ɗan karamin jariri na musu maraba da zuwa, da sauri Ummi ta ɗauko hijab ɗinta ta mikawa Umma ta saka jariri a kai, ta shiga niman inda kwalin rezanta yake. Tana samu ina sake wani nishi tare da cewa.
"Ummina ki yafe min"
"Iƙon Allah har biyu? Sannu da aiki Safina."
Inji Umma yanke cibiyar ɗayan akayi dan basu samu hankalinsu da su fahimci gender yaran, yanke ɗaya cibin sukayi, kara na saka sannan na zuɓe a gun ina tauna harshena, ranar Ummi tashiga mugun tashin hankali, Umma ce tayi maza ɗauki wani. Karamin roba ta cusa min a bakina, tare da nima min doguwar riga suka saka min, hawaye ke zuba a idanun Ummi, kota kan yaran basu bi ba.
"Maryam! Babu lokaci kira mana Dudu."
Jikinta na rawa ta fara niman wayarta, wadda yake kan dress mirror, amma sam hankalinta bai je gun ba. Asalima birkicewa tayi sabida ganin jinin dake zuba. Umma ce ta gani bata cewa Ummi kome ba, ta ja hannunta ta zaunarda ita a kusada jariran, sannan ta kira Abdul.
"Maza kazo Safinah ta haihu, kuma tayi sarkewar hakori muna cikin tashin hankali."
"Gani nan a cikin gidan."


Kashe wayar tayi, sannan ta kalle Ummi tace.
"Karki manta Allah yana tare dake karki bari Safina taga karayarki akan idanunki, yin haka shi zai ta shiga sabo.."
"Ummi zaman me kuke yi baku san rayuwarta na cikin hatsari ba, Ummi ki jida yaran ki yanke musu cibiyar tunda sun tawo tare, sannan ki naɗesu kufito Zakari ya kawo ku dan ɗakin yan bakwaini za a kai su."
. Sa hannunshi yayi ya cinciɓeni tare da fitowa waje dani, Umma na bin bayanshi, ganin ya ɗaukoni yasa Zakari ya buɗe masa motar yasakani, shiga Bayan Umma tayi, shi kuma ya zagaya zai shiga mazaunin drve. Abba ya shake mishi wuya, tare da kifa mishi mari.
"Abba don Allah ka bari na kaita asibiti, rayuwarta na cikin hatsari."
"Idan ta mutu uwarka ce? Ni zaku renawa hankali ku haifa min shege a gidana, dan."


"Abba!!!"
Ya kirashi da karfe, cikin ɓacin rai ya kwace rigar yace..
"Wallahi idan ban takeka da mota ba Allah ya tsine min Albarka."
Ganin da gaske yake Ummi ta daka mishi tsawa.
"Kul!! Bawan Allah, muje ka rabu dashi Allah ya kyauta."
Gabar motar ta shiga, dole Abba ya matsa, Abdul ya fita sai huci yake, tare da dukar kan motar, Har suka isa asibitin. Dauka na yayi, tare da shiga ciki dani, su Ummi suka rufa mishi baya.
Yana shiga nurse da likitoti suka, tare shi aka shige dani ciki. Sannan ya faɗawa wata nurse ta amshi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login