Showing 18001 words to 21000 words out of 100319 words
Chapter 7 - Masarautar Jordan Book 1 Complete Document .txt
Zubur ya mike ranshi a ɓace.
"Wani munafukine ya gaya Abbie ina kaiwa Ashraf hari?"
Juyawa Uzaif yayi yabar falourn, dan shi bai damu da mulki kaman yadda Marhum da Mahaifinsu suka damu mulki ba.
***
*NIGERIA*
Abuja.....
Tashin hankali ya dadda samun mazauni a cikin gidanmu musaman da aka rasa inda Nake, dukda Ummi tana ɓoye damuwarta bai hana ranar da Labari yazo musu bana makarantar da naje yi a kasar waje sai da ta yanki jiki ta faɗi. Hajiya Nuratu ta sake dariya sannan tace.
"Eh k'uwwa bayan hari kuke, yarinyar da ta tafi karuwanci kuke damuwa da ita! Ku jira idan tazo muku d...."
"Amma Nuratu baki da hankali, da kike faɗan haka meye ribarki. Kodan Allah bai baki mace bane, amma ai ga yaran da kika ɗauko riko kalamanki zasu koma kanki."
Inji Hajiya Amnah.
Dukkansu Ummi najinsu amma bata jin zatayi magana, ita fatan ta ɗ'aya na dawo gida lafiya,
Shigowar Nannah shi ya tilasawa Hajiya Nuratu tayi shiru, cikin mutuntawa suka gaisa. Sannan ta zauna tana tambayar ya Ummi taji da jiki, duk suka ce da sauki. Shiru ne ya gitta a tsakaninsu, can sai ga Matar Abdullahi da yaranta, hannunta ɗauƙe da basket ɗin abinci itama tashigo zama tayi ta gaishesu.
Sun jima sosai kowannesu da abinda yake juyawa a ranshi...
Da dare Anim yazo ya gaida Ummi bayan yafitane ya samu Abba da maganar yasa a bincika sosai dan an samu ganin kiran da nayi daga U.S zuwa dubai daga nan ba a kuma ganin wani wani motsi nawa ba...
Sun jima suna tattauna batu akaina, kafin suƙayi sallama.
***
*JORDAN*
Haɗin girki na fara hankalina kwance,
Ina na fara kokarin dafa Felafel cikin kwarewa na fara haɗawa, ina gamawa na juye a cikin wasu manyan kuloli, sai lemonada. Shi kaman shaka yake.
Sai Zarb bbq wanda nayishi da naman karamar daba.
Fitarwa nayi, naje na jera akan dinner table, haka na ɗauki kwalɓar ruwa na kai, sannan nazo na fara cin abincina, ina ci ina jin wani iri a raina dan yau jina nayi a jikina ana nima na, gashi ina niman kusan wata bakwai, dan a yanzun wata huɗu a cikin masarautar, watana uku kafin shigowa cikin masarautar gashi bani da hanyar da zan samu labarin mutanen gidan tunda bani da y'ancin fita.
..... "Ke Yar African kizo Sultan zai ci abincinki."
B'ata rai nayi cikin gatsali nace.
"Idan banzo ba ya kwana da yunwa."
Zaro ido mutumin yayi kafin yace.
"Ni bazan iya kai sakonki ba, dan ina da yara da kanne mata, ke zaki iya kaiwa da kanki ko kuma na ɗauke ki dan naga rashin aukinki yafi..."
"Wato baka tsoron Allah sai wancar yaron?" fita yayi ni kuwa na cigaba da cin abincina, ina gamawa na mike tare da wnke hannuna, na fita.
Ina zuwa na same shi ya maida kujeran baya sannan ya ɗaura ɗaya aƙan ɗaya, idanunshi ɗauke da medical glass yana duba jarida.
Zuwa nayi na tsaya a tsaye akanshi, yaji zuwana amma yayi kaman bai san da mutum a gun ba, nima kuma ina jin shariya ne dan haka na cigaba da tsuyuwa, ni a tunanina yunqa zata sashi min magana, karshe mikewa yayi yabar min jaridar a gun yafita.
Kaii jama'a wallahi ban taɓa ganin ɗan renin hankali irin Sultan Ashraf ba, tsakani da Allsh cikinka ma sai ka nuna masa kai ɗan jan wuya ne.
...... Karshe haka na juyewa su Ghaniyu, dare ma haka da na gama na same shi ne a zaune ina gama jerawa ya mike, gyaran murya yayi su Ghaniyu suka shigo.
"Umarninka muke jira."
"Ku kaita gun Azrah."
A gaba suka sani har shashin bayi, inda suka kaini gun tsohuwar nan, tsayawa sukayi a bakin kofa. Na shiga na samu tana sallah. Zama nayi ta idar sannan muka gaisa, kallona tayi tana murmushi tace.
"Yau kece kika kawo min ziyara? Hmm anya ba Sultan bane ya aikoki."
Gyaɗa mata kai nayi, alamar eh. Matsowa tayi kusadani ta riƙe hannuna tana kallona, tare da cewa.
"Bansan me yasa nake jin bakin ciki idan naga yadda kome yake tafiya na rayuwar Sultan a hangunce bayan nasan kome amma bani da ikon yin kome akai, kodan nice nayi renonshi daga lokacin da aka kaini a matsayin me kula dashi ba, ina rokonki idan har biyanki akayi ki cutar dashi don Allah ki taf..."
Shiru tayi can kuma tace.
"Kiyi hakuri na tsaya ina miki shirme, akan abinda bai shafeki ba. Zaki kiyayye abubuwa guda goma sha ɗaya, na farko idan kika gama abinci kika jera zaki tsaya a gun har lokacin da ya fito, na biyu zaki buɗe kwanonin abinci yaga abinda yake so, na uku zaki maida hankali akan abinda idanunshi ya tsaya akai, na huɗu baya cin yaji da gishiri, yafi son ganye da y'ay'an itace, na biyar baya cin abinci a kala d'aya inso samu ne kiyi sama da kala biyar, sannak yafi son ruwan kankana da abarba, na shida idan kika saka masa zaki fara ci, dukka abincin. Sannan na bakwai zaki tsaya akanshi gudu kar ya kware, na takwas zaki na bashi kananun labari wanda zaija hankalinshi yaci abincin sosai. Na tara dole ki zama me hakuri dashi dan koda yaci abincin in bai masa ba zai dole ki sake dafa masa sabo, na goma idan ya gama godiya zaki masa sabida cin abincinki da yayi abu na sha ɗaya idan ya shiga ɗakin motsa jiki zaki bishi da ruwa tare da karamin towel sai y'ay'an itace d'akinshi kam akwai masu kula dasu iyakarki falourn ɗinsa.. Wannan shine dokokin ciyar da Sultan Ashraf."
Shiru nayi ina lissafo duk uban bayanin da tayi min, wanda nake jin babu ɗaya da zan iyayi tsallakewa, dan saura wata biyar na bar kasan koda ban same kanshi ba zanyi kokarin masa abinda dole wata rana ya nime ni. Toh meye kenan, mutum ba sakin fuska ba, ba hira....
Dafa kafaɗana tayi cikin tausassiyar murya tace.
"Ban sanki ba! Amma tunda naga ya turoki akwai wani abu na daban, kiyi hakuri da zama dashi sabida. Ya tashi babu kowa a tare dashi sai ni, nima ɗin iyakata kula dashi amma an hananin shakuwa dashi, balle na nuna mushi muhimmanci rayuwa, akwai binannun abubuwa sosai, tashi kije."
Mikewa nayi nasakai na fita dan jikina yayi mugun sanyi,
shi yasa yake abubuwa son ranshi bai tunina, toh me yasa Nannah taki gaya min kome, akwai abinda Azrah tasani na rayuwarshi amma tsoro da gudun faɗawa damuwa yasata yin shiru, meye yasa toh? Me take ɓoyewa akanshi, indai zata shiga damuwa akanshi tabbas akwai, ɓoyayyen alamarin da yafi karfinta. Dan haka kawai bazata tayi kokarin sanar min da wasu abubuwan da ke damunta ba,
*Shin Meke faruwa ne A Masarautar Jordan?*
Abinda na tambayi kaina kenan babu amsa, tunda ba wani na ajiye zai bani amsa ba.
***
Washi gari sai da na kusan makara, dan jiya da tunanin waye Sultan Ashraf na kwana, da gari ya waye na shiga haɗa mishi abin karyawa, banyi wani abubuwa ba dan babu lokaci..
Ina gama jerawa yana fitowa, ina tsaye a gun yazo saka mishi nayi, sannan nabi kan abin karyawa na ci, ɗaukar fork yayi yare da karamin wukar cin abinci ya fara cin y'ay'an Zaitun da na dafa, sannan ya shiga cin sauran abincin a yangance yadda yake taunar kaman wadda bakinsa ke ciwo tsayuwa nayi ina kallon abin mamaki dan ina kallon maza a rayuwata karo na farko da naga wanda yake cin abinci a yangance kamar ba cikinsa zai saka ba, ita kanta ruwan da zai sha kurɓa ɗaya ake mata a ajiye, wato babu abinda mulki bai sawa mutum yayi. Kaɗan yaci yasha ruwan coffee mara madara shima kurɓa yayi yabar sauran. Sannan ya mike tare da barin falourn da uwar harara na rakashi, wallahi bani bin kowani dokarka, dan baga dalili ba.
Haka na tattara abinci, nakai kitchen, sannan na dawo naga Ghaniyu a tsaye kamar bazance kome ba can nace masa.
"Lafiya?"
Girgiza kai yayi sannan yace.
"Meye ya haɗaki da Sultan?"
Zaro ido nayi ciki fargaba nace.
"Meye kuma nayi."
A raina nace.
*Muguntar sarki Zalimun ya motsa kenan yau*
Shiru yayi ganin yadda na ke kokarin ɓoye tsorona, yace.
"Wai idan kin shirya akaiki kasuwar zamani ki duba abinda kike amfani dashi na yau da kullum."
Boyayyen ajiyar zuciya na sauke sannan na koma kitchen ɗin na kintsa kome, na wanke hannuna, ina fitowa na kalle tulin takardun da suke kan table ɗinsa, page na ɗauka da biro na zauna akan kujeran shi na shiga, rubuta abinda nake bukata, kamshin turarenshi yasani ɗaga kai, yazo zai zauna kawai yaga na ɗare kujeran inata rubutu, shine ya koma gefe ya coge, tare da harɗe hannunshi a kirji,
(Ina ruwan shiga uku fitar takaba da molo😂)
#MJ#HZƘ#VOTE nd Share.......
Oum Muwadda.......
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: I just published "Page.١١" of my story "MASARAUTAR JORDAN!!!". https://my.w.tt/zCGf0qyIi3
*_HAZAƘA WRITER'S ASSO_*
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*
*_Labarin yasha da sauran_*
Sadauƙarwa ga masu ruɗewa😂😝
Page.١١
Washi gari aka tashi da shagalin musanman irin nasu na larabawa,shuwagabanin kabilu sun zo har cikin dakin taron masarautar. Tun safe da na gama abin karyawa yazo ya karya na goge mishi gashin kanshi, ya koma ciki ya sanya farar jallaɓiya, da alkƴaba ruwan zai ba. Wato golden coloure. Takalmi kamfanin Gucci yasaka. Ina cikin gyara falon ya fito.
Kallo d'aya nayi mishi a hankali na furta "Masha Allah."
Yau kam fuskarshi a sake kana gani kasan akwai Burbushin mutunci.
Zama yayi na zuba mishi aBinci. Yaci sosai sannan ya ɗago kanshi ya kalleni a sace sannan ya kauda kanshi yace.
"Gyara min ɗakin"
Ɓata rai nayi bansan lokacin da na tura bakina ba, ina magana kasa kasa.
"Yau ina cikin jin daɗi bani da loƙacinki amna Irfan zai min maganinki."
Shiru nayi dan natsani ya haɗini da Irfan ɗin nan. Ganin yadda na shiga hankalina yashi mikewa ya fita, da harara na rakashi cikin. Mita nace
"Yau anyi abin kai fitsari da kumfa."
Ni ɗaya sai mita nake da na gaji na zauna akan kujeran gun cin abincin na shiga tunanin gida, dan nasan ban kyautawa iyayena ba. Da Anim me zance musu idan na ka gida, ina naje? A gurin wa na zauna? Wannam sune tambayar da suke hanani sukuni, musanman idan na tuna da halin da Ummina zata shiga, ko a wani hali taƙe oho?
***
"Karka bari wani ya raɓe shi, dan yin haka zai haifar da damuwa. Ukshe ka kiyaƴƴe maganata, na gaya maƙa ka kiyayye maganata, na kuma gaya maka ka kiyayye maganata.. Na rantse da abin bautana idan ka kiyeyya abinda na gaya mulkin kasar jordan ya haramtawa Ashraf ka kiyayye maganata, kuma kayi ɗamara dan yanzun jordan zata dawo karkashinka, amma sai ka fuskanci kalubale daga kabilarƙa."
Gyaɗa kai Amir yaƴi cike da farin ciki yace.
"An gam..."
"Ba an gama zaka ce ba. Ukshe rayuwata na bada sabida kai, ko min kashin ƙusƙure mutuwa zanyi, ƙuma zan ɗauke hankali mutane akanshi yadda zaka manta da shi baki daya, Ukshe karka bari kowa ya raɓe shi."
Kusan kashedin da Ra'ees yayitawa, Ukshe kar asami matsala dan rayuwar ra'ees ne a cikin hatsari, sakamakon wani shirin da yayi na kawar da Ashraf daga mulkin ƙasar Jordan.
......... "Abu Zarri! Yaron nan yau zai shiga fadar can fa."
Murmushi Amir Abu Zarri yayi sannan yace.
"Bani da matsala dashi, kuma ai dama ance yana cika ashirin da tara zai amshi mulƙinsa, kuma ya ciƙa gara ya amshi mulkinsa. Ko wasu zasu rage son zuciya."
..... Karamar dariya Amir Uƙshe yayi sannan, yace.
"Kana ƙoƙarin adana ɓacin ranka, nan gaba ma sai magana yafi karfinka, ka gya..."
Shigowar Ashraf cikin ɗakin meeting, yasa shi yin shiru tare da mikewa tsaƴe. Masu kula da lafiyarsa suka ja masa kujeran.
"Bismillah."
Ya furta a hankali, idan baks lura da leɓɓansa da suka motsa, bazaka fahimci basmalla yayi ba.
Ajiye masa yar briefcase ɗinshi akayi, ya kare musu kallo sannan ya buɗe jakar a hankali ya zaro takardun ya ajiye a gefe, sannan ya ɗago kai yace.
"Gashi ku nemi sauran ku basu."
Mika musu takardun irfan yayi, suka gama dubawa sannan Abu Zarri yace.
"Doka ta goma da ta sha ɗaya batayi tsauri ba, sannan yaushe zamu yarda mu bawa Yahudawa dam.."
"Dokata ce haka"
Murmushi Amir Ukshe yayi sannan yace.
"Banga wani abin d'aga hankali a nan ba, dan ni dokar tayi min."
"Kace doksr tayi?" ya wurgawa Amir Ukshe tambaya,
Gyaɗa kai yayi, cikin gamsuwa Sultan ya ciro wani takarda ya turawa Amir Ukshe, yace.
"Case ɗin Angela"
Dauka yayi yana dubawa, sake tura mishi wani yayi cikin sanyin murya yace.
"Wannan kashedin Marhum ce"
Dauka Amir yayi yana dubawa, cikin sakin fuska yace.
"Insha Allah haka bazai sake faruwa ba, yarinya taci albarkacin sarki ya shiga Fada, mun gode."
"Sultan!! Ka janye bawa Banu Nazir muƙami, gwara Banu Hussein dukkansu musulmai ne." inji Amir Abu Zarri
"Duk yadda kuka gani."
Shiru sukayi Abu Zarri ya Amshi takardun ya suƙe, wannan sai na gomane ya bari dan shi an saka babu bambancin Kabila duk wanda aka kama da laifin ya kashe wani da gangan hukuncin kisane,
doka ta farko ce idan aka kama wani yayi yunkurin kashe sarki hukuncisa shima kisace, doka tabiyu kuma, duk wani shugaban da aka kamashi yana bin bayan me laifi zai sauka a mukaminshi ne kowaye shi kuma ba iya sauƙa ba har sai ya ajiye taran kuɗi, sannan ana jan kunne da cire ƙuɗi a baitul malin masarautar.
Daga ɗakin taron ɗakin shagali Amir Ukshe yajashi suƙa tafi. Inda yasamu mutane musanman attajirai da wasu daga kabilu guda biyun nan.
***
Bayan tafiyarshi akazo aka korani zuwa, shashin bayi, nayi mamakin faruwar haka. Amma ban d'aga hankalina ba, nasan kodan cikinsa zai nime ni.
....... Bazance me ya faru ba, sai dai naji kishin kishin ance yabar garin, ya koma gun aikinsa.
Yau kwana biyar kenan, kullum sai anzo an ɗauki yan matan ɗakinmu ba, ba'a dawo dasu sai dare. Ashe da ina cikin kariya ce zamana a shashin Sultan ƴanzun kuwa, ina cikin hatsari domin kuwa sau biyu ana farmaka na,
Karshe komawa d'akin Azrah nayi, naje na zauna. Ita kam ana ɗan shakkarta.
Maidani kitchen akayi na cigaba da aikina, sam hankalina yaki ƙwanciya da tafiyar da akace Sultan yayi.
Azrah nasamu da cewa.
"Mama! Hmm nifa ina jin akwai matsala zanje na duba gidan Sultan."
Shiru tayi tana kallona can tace.
"Ki bari mana idan ya dawo sai muje dake ko?"
Gyaɗa mata kai nayi badan nason ba, dole na hakura dan kwanakin da