Showing 3001 words to 6000 words out of 100319 words
Chapter 2 - Masarautar Jordan Book 1 Complete Document .txt
rai bani bace, sharri aka min wani katon badakare. Wanda kana ganinshi kaga (Kamal minna😹) tare da wani kato kamar (Jaheedu) suƙa ɗaure hannun matar sannan suka saka kanta akan wani katato, tana kuka tana kome, tace.
"Ya Allah ka kawowa Masarautar nan agaji da ceto, Ya Allah ka kawo wanda zai dakatar da abinda ke faruwa a cikin wannan masarautar."
Saka takobi sukayi aka gintse kan matar, ya faÉ—i kasa ihu Mujahida tasaka tare da yankan jiki ta faÉ—i, a gun. Lumshe idanu Feener tayi dan tabbas wannan masarautar ba kanwan lasa bace, babu sauki a cikinta balle wajenta. Yunkurin kashe sarki kawai an gintsi kan É—an adam ina kuma kayi wani abun da bai kai haka ba toh tabbas sai dai a cinye namarka É—anye.
"Kowa ya kwan dasanin cewa, duk wanda yayi yunkurin kashe Sarkinmu, shine zai fara shekawa Lahira dan haka ƙuma bakin Bayi kushiga hankalinku dan ƙuna kuskure zaka buɗe idanunka a lahira ne, na rantse da Allah sarki takobina a washe yake domin cusge kayikan mutane."
Korasu akayi kamar wasu dabobbi, inda aka nufi wani shashi daban daga masarautar aka kaisu, sunga bayi a cure guri guda suna ƙuka, wani yaro da aka barshi yana birgima yana kiran .
"Ammiih!!!"
Yabawa kowa tausayi dan ga duk alamu ya nuna cewa Uwarsa ce aka tsinke kanta, yadda yaron yake kuka saida yasasu duƙkansu kuka, a hankali Feener taje gunsa ta ɗagashi tare da rungume shi itama kwalla na zuba idanunta, tace.
"Ya isa ukty! Amminka tana cikin aljanna, kuma zata ji daÉ—i idan kayi mata addu'a."
D'ago kanshi yayi gana sauke ajiyar zuciya, ya kwantar da kanshi a kirjinta yana ce mata.
"Ammina zata dawo?"
Sake rungume yaron taÆ´o a wannan karon takasa tsayar da kukanta, domin tsakaninta da Allah take shasheka, wannan wacce irin masarautarta ce haka da dan adam da ruhinsa basu da kima, a yau da tashigo kawai tabbatar da wani alkarya tashigo, a yau tasan duniyar da tashigo, me cike da tsantsar zalinci da mugunta.
Shigowan wasu karfaffan mata yasata ɗago kanta, kallonta suka tare da taɓe baki cikin izgilanci.
"Ke bakar mutum! Daga wata duniya kike?"
D'ago jajjayen idanunta tayi sannan tace.
"Daga Senegal!"
"Yayi kyau, toh ku gabatar mana da kanku dan ace a cikiku akwai wacce take da kwarewa a girki hatta girkin dabobbi ta iya, dan sarkinmu bayi dame girki."
Mikewa tayi tana kallonsu tace.
"Nice!"
Dariya suka saka mata, sannan suka ce.
"A haka sarkinmu zaici a bincikin? Mutumin da baici na gogaggun turawa ba, amma muje a baki kayanki, mu kuma gabatar dake ga Gajin iko, kafin akai ki shashin da zaki zauna."
Wani shashi na gidan suka nufa dani, wanda yake da tsari na daban da masarautar. Ginin kawai abin kallone a haka nayita binsu har cikin, wani tangamemmiyar falo muka shiga me cike da kayan more rayuwa, ta sarakuna. Katon hoton wani farin dattiji cikin shigar alfarma. Fuskarshi cike da farin gashi.
Ko cikin falon bamu shiga ba, muka tsaya wata baiwa ce ta fito sakamakon jin sallamar Naja'atu.
Murmushi tayi tace.
"Ina gaida uwar É—akin bayin Jordan meke tafe dake?"
Gyara tsayuwa Matar tayi, sannan ta nuna mata Feener tace..
"Gata nan mun kawota Gajin iko ya gantane wannan karon har da bakaken wake a cikin masarautar."
Zuɓa mata ido baiwar tayi kafin ta gyaɗa kanta tashige cikin wani falon, can sai gata tafito tace.
"Ku jira yanzun zai fito."
"Toh madalla."
Wasa-wasa sai da suka shafe awa ɗaya a gun kafin dattijon yafito rike da sandar dogarawarsa ta Azurfa kana ganinta sai wani irin shaiki take, zama yayk duk suka zuɓe tare da kai mishi gaisuwa. Jinjina kanshi yayi idanunshi kan Feener wacce kanta yake sunkuye bazato yace.
"Shekarunki nawa? Sunanki? Daga wani yankin duniya kike?"
D'ago kanta tayi taga yayi mata wani irin kwarjini da cika ido, sunkuyar da kanta tayi jikinta na karkarwa, bakinta na rawa har tana tauna harshenta tace.
"Safeenat Hadi! Daga senegal"
Bai kuma ce mata kome ba, ya maida hankalinshi kan agogon falon, sannan ya kalle Naja'atu yace.
"Ku kaita."
Mikewa sukayi tare da ita suka fita a falon.
Shiru yayi zuciyarshi nakin amincewa da baiwar Sarkinsu, amma bai da hujja hanata.
Can gun bayi aka maida ita, tare da nuna mata É—aki. Zuwa anjima za'a zo akaita, tare da jera mata dokokin zama a cikin gun girkin.
~_~
Bayan awa gudu sai gasu Naja'atu, kiransu Hindu akayi suka tafi wani bangare na gidan, aka sasu sukayi wanka, sannan aka basu wani riga iyakarshi ya rufe kirji,amma cibiyarsu a buÉ—e, yana sa guntun hannu, amma tawajen cikin kuwa wasu silala aka saka masu wani irin kara, sai wani wando me tsagu har cinyar gefe da gefe, ga wani jigidar karfen, sai wani awarwaro da aka basu suka saka. A kafarsu wanda yake bada wani kara cuuu.
Sai wani hula shima me karafun, wanda kana juya kai zai bada sautin.
Sakasu akayi a gaba, aka kaisu wani falo na daban gun cike yake da manyan mutane. Suna shiga gun aka sauke sauti dake akwai makaÉ—a, take aka umarce dasu fara rawa. Irinta larabawan zamanin Jahiliyya. Dake dukkaansu larabawane. Kuma sunsan kan rawan, ita rawan dai anayinta da k'ugune sannan anayi ana juya kowani kusurwa najikin......
VoteMj#Follow Mai_Dambu....
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: *_HAZAƘA WRITER'S ASSO_*
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*®2020*
*BOOK ONE*
Page-Ù£
Wannan dabi'ar da ake a cikin masarautar iya emirater council ne suƙe wannan ɗabi'ar. Banda sarkin dan sam bai ciƙa shiga sabgar ba, kodan kasancewarsa shi ɗin matashine ko da yake baza ace haka ba, dan idan akayi dubi da yanayinsa ba mazaune bane a masarautar, kaisu wani ɗaki akayi nan wata baiwa ta nuna musu yadda zasuyi rawan sannan suka fita zuwa wannan falon.
Inda suka same su da manyan cikin fadar, nan aka sake musu sauti suka shiga rawan yayinda makaÉ—a suka shiga sake musu sauti, gefe guda manyan fadar suna watsa musu salala, tare da ruwan taccecen inabi...
Duk wannan abinda ke faruwa Sultan Ashraf bai san da haka ba, shigowar Amir Ukshe ne ya tsayar da kiÉ—an da rawan. Zama yayi a cikin tattausar shinfiÉ—insa, yana karewa kowa kallo kafin yakishingiÉ—a aka cigaba da shagali.
***
Wani kitchen aka kaini mai girman gaske, kome na cikin kitchen É—in royal colour ne, wato komi na na cikin kitchen É—in ruwan golden ne hatta cokala da kofuna duk iri É—aya ne. Bangaje ni da akayi ne ya dawo dani daga duniyar kauyanci, tsaki matar tayi cikin izgilanci tace.
"Matsalar akawo maka bayi daga africa kenan, gashi tazo ta buÉ—e baki tana kallo kamar wata doluwa, zaki wucce ko sai nasa guard sun zanemana ke"
Gaba nayi ina raba idanuna, bansan me zanyi musu ba dan haka na tsaya a gun ina kallon yadda suke haɗa girki kai kace taro ake. Kafin na ankara sai ji nayi an zabga min bulala a jikina, a razane na ɗago wani murɗeɗɗen mutum ne sanye da farin riga da bakin wando anyi masa tambarin masarautar a gefen kirjinshi ta dama, dariya duk masu girkin suka saka, nuna min aikin wata dattijuwa yayi, an ajiye min, kasancewa an faɗa musu na iya girkin larabawa su gwadani sannan akaini ɓangaren da zan zauna.
A sanyayye na karasa gun na tsaya buÉ—e panpo nayi na wanke hannuna, sannan na kalle abinda zanyi. Man zaitun da y'ay'anshi, zuma, da tafarnuwa sai kayan kamshi dangin curry masala, da kuma kaza katuwa, sai dankalin turawa da kayan miya tattasai ja da kore tumatir manya guda huÉ—u, sai wani maggi wanda yake da faÉ—i sai albasa, dafa kafaÉ—ata tsuhuwar tayi sannan tace min.
"B'akuwa wannan shine irin abincin da Sultan Ashraf yafi so, da fata.."
"Kee! Tsuhuwa koma bakin aikinki ko kuma jikinki ya nusardake inda kike." inji mutumin da ya zane ni, da sauri matar koma bakin aikinta.
Shiru kitchen É—in ya É—auka baka jin kome sai karan ajiye filet ko wani abu ko kuma cokali. Cikin sauri na fara aikina, ana wanke kazar ajiyeta a matsami ruwan ya gama É—igewa, sai a koma kan irish É—in shima a yanyankashi ba yankan chips ba. Yankar albasa akwance, za'ayishi sai a ajiye a cikin wani bowl akoma kan kayan miyar shima yanyankasu ke, a zuba akan dankalin, sai a zuba man zaitun da zuma a cikin kayan miyar tare da maggin da y'a'yan zaitun nan a cakuÉ—asu guri guda, sai a É—auko kazar a zuba a cikinta, idan dama an raba kazar ta kirjine sai a saka zare da allura a É—inketa, idan kuma ta kasa aka buÉ—eta sai a juye takasar, amma larabawa sunfi buÉ—eta ta kasa.
Sai a É—inketa sannan a sake niman bowl azuba man zaitun, da maggi a haÉ—a ashafa a jikin kazar sai a saka an pan É—in oven a saka a cikin.
Duk bayan mintuna goma zai ayita buÉ—ewa ana zuka wuka a ciki, yadda za aji dahuwarsu.
........ Bayan mintuna talatin da biyar aka ciro, matar da take da alhaki kula damu, itace zata fara dubawa. Tana gama dubawa ta kalleni tura min tayi gabana, cikin tsukewar fuska tace.
"Kici."
Cikin sanyin jiki na yanki namar na kai bakina naci, suna ganin naci suma suƙa rufawa namar, tass suka cinye.
...... Daga nan suka sani dafa normal tea. Irin nasu na larabawa wasu ganyenma bansan su ba sai yau, ina gama suka sake bani aiki. Kai nasha azaba dan kafata har rawa yake. Dakƴar suƙa sallame ni daga kitchen ɗin.
***
Ina shigowa ɗakinmu nasami Yan matan nan, suna kuka cikin sauri na karasa gunsu na zauna a tsakiyarsu. Daura kansu suƙayi a jikina tare da fashewa da kuka, suna cewa.
"Feener! An wulakantamu anci zarafinmu, bayan munyi musu rawa sai da suka nemi yin lalata damu. Feener har da Sarkin ma."
Zaro idanu nayi waje, Zakiya tace.
"Feener Mujahida an mata fyaÉ—e tana bay.."
Turesu nayi na shiga ban É—akin na sameta tsugune rungume da jikinta tana wani irin kuka, durkusawa nayi na rungumeta. Cikin kuka tace.
"Feener! Narasa darajata, dama haka bayi suke fuskanta? Na rasa iyaƴena a yakin syria ban taɓa kuka irin nayau ba gashi akan idona sarkin wannan masarautar yake tamin haddi bayan sun wulakantamu. Feener zan gudu."
Girgiza mata kai nayi cikin kuka nace.
"Kiyi hakuri"
Narasa me zan gaya mata, dakyar nasata tayi wanka, sannan tafito a hankali abincinmu aka kawo mana, a wulakance aka ajiye mana, nice na cigaba da lallashinsu har suka taɓa abincin zan fara ci kenan aka buga kofar mikewa nayi na buɗe.
"Kizo mu kaiki shashin Sultan Ashraf yau zaki fara aikinki."
Fitowa nayi na bi bayan mutumin. Fita mukayi daga shashin bayi sannan muka nufi cikin wani shashi wanda yafi kowani shashi kyau da haÉ—uwa,
Tazarar tafiyar da yake tsakanin get É—in gidan da cikin tafiyace ta minti arba'in da biyar, amma cikin sauri muka isa gidan, bansan yadda zan kwatanta muku yanayin gidan, domin baka jin motsin kome a gidan sai takuna, kasancewa takalmina flat ne toh kuma yana bada sautin, tun da muka haura barandan. Masu tsaron gidan suke bina da kallo sabida sautin takalmina, falon farko da muka shiga, aka dakatar damu, wani bulalar me kama da itace aka zabga min a kafana, sai da nasake kara.
"Shiiiii!" shine abinda me tsaron kofar falon, ganin haka mutumin da ya kawo ni yasake murmushi can kasa makoshinsa Æ´ace.
"Ghaniyu muna godiya da tarɓan da tasamu,"
D'aga mishi hannu mutumin yayi, muka wucce, kwalla ne ya shiga saukowa a idanuna, tare da tarin dana sanin mara amfanin da nakeyi tun bamu isa cikin ba. Falon farko babba ne na fitar hankali, ga kaÆ´an alfarma a cikinsu. Sannan muka ratsa falon dan mun samu da mutane suna zaune babu wani hayaniya ko magana asalima zaman hutawa suke.
Haka muka wucce su babu wanda ya dago ya kallemu, balle kasa ran zasu mana magana, wani dogon korido mai tsayi shima tafiyar minti goma zakayi ya kaika kofar falo na biyu.
Muna zuwa aka buÉ—e mana kofa, muka shiga ciki mun sami mutane biyu a zaune kowannensu da abinda yake yi, sannan muka wucce, inda mukayi tafiyar minti ashirin da É—aya, sannan muka nufi wani tafkeken falon me cike da abubuwan burgewa, irinta gidan sarauta. Babu kowa a falon sai tv da yake aiki. Tsayawa yayi a gun sannan ya kalle ni tare da mika min, takarda yace.
"Idan Allah ya nufa zamu sake saduwa toh sunana Sheik, zaki iya tsayuwan jira har lokacin da ya fito sai kisan yadda zaki bashi takardan domin yasan da cewa kece bakuwar da zaki fara girka mishi abinci sannan kiyi takan tsantsar da aikinki domin nan ba'a san kuskure ba kina yin abu kaÉ—an zaki ji a jikinki."
Yana gama faÉ—ar haka ya juya ya tafi, abinshi.
Jingina nayi da bango ina kallon Inda Allah ya kawo ni. Bayan wasu mintoti, na gaji da tsayuwa na zame na zauna, na cigaba da tsammanin fitowar sultan, shiru kake ji.
Awa É—aya ya wucce wasu awowin suka wucce bai fito ba. Can da naga har lokacin sallah yayi bai fito ba, sai na juya na fita niman inda zanyi alola da sallah. Karshe dai sai da na dawo shashin bayi nayi sallah sannan na koma.
Ashe ina fita shima yana fitowa, ganin takarda asaman kujeran falon yasashi sanin an shigo falon yana ciki bai bi takai ba yayi ficcewarsa, zuwa masalaci. Koda ya dawo a falon farko ya tsaya sabida mutanen da suka zo masa dubayya, da kuma mishi Jajjen ya jiki. Suma dai matasane sa'aninshi kuma yan Kabilarsa na Banu Hashim, daga cikinsu kuwa har da Jikan Amir Ukshe.
A hankali nake takowa sabida ba'a son karar takalmina ko sautin da zai dame mazauna gidan.
Da sallama na tura kofar na shiga duk sunji sallamar amma babu wanda yayi yunkurin amsa min, asalima kamar basa gun kare musu kallo nayi anan na fahimci dukkansu yan bana bakwai ne.
Abinda yasani cewa haka kuwa ba kome bane sai dan luran da nayi dan akala bazasu wucce 28-29 ba, domin babu wanda ya haura talatin. Taɓe bakina nayi na wucce,
Har inda aka kaini, tsayuwa na cigaba dayi, wasa wasa banga idanun sarki ba sai bayan sallar la'asar, na gaji da zama na mike zan koma can shashin bayi, ina rike handle kofar zan fita shima ya rike zai shigo. Bazata muka buÉ—e kofar tare, har sai da kaina yayi karo da kirjinshi.
Da sauri nayi baya ina zare idanu, bai tsaya bin takaina ba yayi wuccewarshi, bin bayanshi nayi da ido tare da dafe goshina nace.
"Wayo ni Safinatu! Toh waye sarkin ne? Toh ko wannan ne? Amma ai lokacin zuwanmu baya falon mutane huÉ—u muka wuce a falon farko, na biyu kuma mutane biyu ne, ai ko shine Sultan Ashraf É—in?"
Ni kaÉ—ai nayita lissafin can nace.
"Toh kenan sarkinsu yarone, taɓ dole yayi abinda ya gadama,"
Tsaki nayi cike da takaici.
"Mugu azzalumi sai da ya ɓatawa Mujahida rayuwa dan sun ɗauki mulki sun bashi, Allah ya is...."
Ganin fitarshi nayi da sauri nabi bayanshi ina cewa.
"Ji mana! Don Allah zoka min iso da Sultan Ashraf."
Nayi haka ne dan na cire tantamar dake raina, ko kallo ban ishe isheshi ba, sai ma masu tsaron lafiyarshi da suka tare ni suka kaini wani dakin duhu. Me kula da bakin kofar É—akin ya shiga yayita zane ni. Har sai da nayi laushi, wanda yaja har na suma, sannan suka watsa min ruwan kankara, a firgice na farka sabida azaba ko kuka ban samu damar yi ba,, cikin kakkausar mutumin yace.
"Daga yau ko tsuntsu kika ga zaiyi kuka wanda zaisaka Sultan cikin damuwa ke zaki kora mishi,, sannan ki tashi kije kiyi aikin da aka kawo ki yi, Sannan sultan baya son hayaniya koda kuwa ta fashewar abune toh zaki ji a jikinki"
Jawo yayi ya watsa a waje tankar kayan wanki. Dakyar na mike zuciyata na min zafi, lura da nayi dare yayi sosai yasani niman hanyar can shashinmu.
Koda naje buÉ—e kofar falon na biyu najishi a rufe dole na dawo falon Sultan, abin bakin ciki koda na shima nasa a rufe karshe sulalewa nayi na zauna, na fashe da kuka.
"Wani tsautsayine ya raboni da gatana nazo nan ana wasan kura dani." abinda nace knn ina kuka.