Showing 69001 words to 72000 words out of 100319 words

Chapter 24 - Masarautar Jordan Book 1 Complete Document .txt

Kakarta, ina ga baki san ina kika saka kanki ba."


Mikewa nayi tare da dirowa a gadon, jikina na rawa. Fita nayi da gudu, ni kaina bansan inda zani ba, dan su Abba sun biyo ni da sauri mukayi karo da Dudu, rike hannuna yayi na fashe da kuka, tare da faɗawa jikinshi nace.
"Dudu! Aanih! zasu kashe min Yarinya bansan me zancewa Abie ɗinsu ba."
Riko hannun yayi muka nufi ɗakin da aka kwantar dasu, tana kwance tare sa yar uwanta, ita tana barcin wahala. Wani mahaukacin soyayyarsu ce ta daki zuciyata na kura mata ido, sai yanzun na lura da bata kai Aamih haske ba, tana a haske amma me duh. Dan idan ka cika saka ido zaka ga fatarta har wani sheki yake, yayinda Aanih kuma tafita haske sosai dan itace Ashraf a fuska, amma a zahiri Aanih ta fita hakuri.
Sumbatar kumatunta nayi ruwan kwalla ya sauka a fuskarta motsi tayi, tare da sake yar kara irinta wahala. Kamar ance d'ago kai, harɗe hannunshi yayi a kirji. Kanshi yasha bandeji murmushi ya sake min. Na kauda kaina tare da mai dasu kan yaran, haka kawai nake jin wani abu na fisgana, wani irin yanayi nake ji akanshi.
A sannu nasake satar kallonshi, gira ya d'age min tare da kashe min ido, kunya ya bani na kauda kaina. Ina murmushi ƙasa ƙasa,


Har inda nake ya iso yana kallon yadda nake shafa kan Aanih, ina kuma jin idanunshi na yawo a jikina, lokaci guda ya saukar mun da mugun kunyarshi tare da ganin tulin girmanshi da ya cika min ido.
Hannunshi yakai zai ɗauki Aamih, hannunmu ya haɗu da juna. D'ago ƙai mukayi a tare muka kurawa juna ido, janye idanuna nayi daga gare, mai dashi nayi kan Aanih da take barci.
"Ina jin bakon yanayi a tsayuwarmu na yau idan kika bani dama."

Gyara kwanciyar yarinyar nayi na raɓe gefenshi zan bar d'akin, sai ji nayi ya riko hannuna. Tsigar jikina ne ya mike sabida ban taɓa shiga irin wannan yanayin ba sai yau. Duk abinda Anim yayi wasu abubuwa a tare dani ban tab'a jin kome a game dasu ba, kai ko Ashraf da shi na fara sani a duniyata ban ji kome ba, ina jin kewarshi na kata'i sabida halayarshi da suka min, ina son halayarshi fiye da kome.
Dawo dani yayi gabanshi, ya zuba min ido cikin sanyin murya yace.
"Zan iya hakuri har ki yayyesu, amma bazan jure shirunki ba. Am 45 now na rabu da Aieesha, pls ki taimaki gwauro irina ki bashi gurbin."

Dakyar na had'iye yawun bakina cikin inda inda nace.
"Abban Adil! Ina son fita."

"Zama da Sultan ya maida ki miskila irinsa ko? Ga sona a cikin idanunki but kina pretender kamar baki jin kome a kaina, ki bani dama na karshe rayuwata dake."
Ga baki ɗaya na gaza furta kome domin bansan wani irin yanaƴi nake ji ba, sake hannuna yayi sannan ya kwantar da jaririyar, addu'a yayi musu. Sannan yasani a gaba har bakin kofar da aka kwantar dani.


"Safinatu!!! Zan baki dama daga nan har ki yaye yaranki, don Allah karki cutar da zuciyata."
Jikina ne yayi mugun sanyi, sunkuyar da kaina nayi ina wasa da farcena wanda ban jima da musu lalle ba.
"Ina son mace me lalle! Haka yana kara mata martaba da kima."
Takowa yayi har gabana, dukda mutanen da suke kaiwa da komowa, bai hanashi sauke nauyin dake cikin zuciyarshi ba.


"Safinatu! Ki bani amanar kanki da rayuwarki, Insha Allah bazan baki kunya ba."


*Wayyo Allah na ashe haka mace take ji idan tasame me sonta ji nake nafi kowacce mace sa'a.*
Ɗ'agowa naƴi da niyyar ce wani abu ina haɗ'a ido dashi sai naji bazan iya ba, haka nayita motsa bakina. Karshe na juya da sauri na shige ɗakin, na rufe kofar tare da sauke wata ajiyar zuciya.
"Wannan mutumin zai kashe ni da salonshi, mutum sai kace majnun"


"Didi ke kuma Lailah, eyye Our didi falling in love"
Ware idanu nayi dan ban tsamaci yan butan uwa suna cikin ɗakin ba, take na bone fuska.
"Toh Didi! Idan babansu Aamih yazo ya zaki yi?" inji Batul,
Wani tsuke fuska nayi, cikin ɓacin rai nace.
"Kinga nayi miki kalar matar yaro? Ai Ashraf saike Batul ni nafi karfin Yaro karami."


Bakinsu a sake suke kallona, cike da mamaki, fahimtar abinda yake yawo a zuciyarsu ya sani fara kame kame, Ummi tana kallonmu bata ce cikanku ba, sai dai da alamu bata ji daɗin furucina ba.
Dukda na jefa musu kokwanto haka suka share batun amma tabbas suna nazartan Alamarin fiye da tunanina, karshe ina zaune bayan tafiyarsu Ummi tare da jagorancin yan sanda. Karshe gidanmu sai da aka saka mana yan sanda.


"Didi!" d'ago ido nayi na kalleta, dake ina chatt da Dr.
"Dama da naji kince Abie ɗinsu Aanih Yarone sai ni! Am sorry da tambayar da zan miki, kuma wallahi ba cin fuska bane, kince yaro taya."
Tsuru tsuru tayi tana kallona jikinta na ɓari.
Saukowa nayi daga gadon na mikar da ita, sannan na bata labarin abinda ya faru.
Kuka sosai tayu tare da bani hakuri, tace.
"Bai kyauta ba"

"Eh amna kaddararmu"
Na gaya mata kamar ance ɗago kaina Dr na gani, fuskarshi a haɗe. Shigowa yayi sai da yazo kusadani ya hura min iskar bakinshi, tare da sake murmushi.
"Kinga fuakarki kuwa! Haka kike da jin tsoro? Gwara ki zama jaruma."


Murguɗa bakina naƴi cikin jin haushi naki ma cewa kome, ina hararanshi.
Hirarsu suka yi shi da Batul, sun jima kafin ya fita, ko minti biyu bai yi ba sai ga sakonshi ya shigo min har da fuskar mage.
*Am so sorry Angel😿*


*Toh meye kuma?😒*

*Ina son wannan kallon da alamu an tura that cute lips ɗinan*
Rike bakina nayi cike da mamaki ina ware idona akan screen ɗin na tura mishi tambaya nayi.
*Taya kasan na tura bakina?😙"


*Tun daga ranar da Kyari ya kawo ki a sume bayan kin same matsalan nan, bayan mu miki allura. Naga alamun Yar Ummi sakaliya ce*


Cizon lips ɗina nayi na kashe data.
Sai ga kiranshi ya shigo min, kin ɗauka nayi karshe da ya dameni nasaka mishi busy.


Ban kuma bin takan wayar ba, sai da yamma zanje bawa yaran nono ina shiga, na same shi yana riƙe da Aamih ta dawp normal sai zare idanu take, nuna min gurin zama. Cikin nutsuwa na zauna sannan ya mika min Babyn kallon agogon da yake ɗaure a tsintsinyar hannunshi yaƴi sannan ya fita.
Can da ta koma barci sai gashi ya shigo amsarta yayi ya kwantar da ita sannan ya ɗaura min Aanil. Itama fita yayi ina maida nonon cikin rigata yana shigowa, kwantar da ita yayi sannan yaja kujera ya sani a gaba, yana kallona kamar wanda yasami majigi. Ni kuwa kunya yake bani naga babba kamanshi yasani a gaba yana min rawan kai.
"Toh kice wani abu mana!"
Lashe lips ɗina nayi a hankali sannan nad'ago a hankali na saci kallonshi, aikuwa muka haɗa ido da sauri na kauda kai, cikin zolaya yace.
"Allah duk ranar da na kama mutum sai na cire ƙunyar nan na barshi sintir"
Mikewa naƴi na fita da sauri, ya biyo bayana yana dariya, manyan da kananun likitoti sai mamakin Dr Zaki suke, su abin dariya yake basu, wai lokack guda ya zama madness in love.
Kuma karku manta nifa har yanzun na kasa cewa ga Ajin da nasaka Dr ba, amma ina jinshi a cikin raina da zuciyata ƙo motsi yayi ina jinshi in my Body, balle kuma yayi magana sai naji kamar nafi ko wacce mace Sa'a. Da farko dai Dr ba baki bane dan shi yafini ma haske, yanayinshi sak da irin mutane Madaras, idan yana abu zaka rantse kace Shivarao ne, Babban jarumin andraprudashe, na kasan India, dukda ya, yana da tsari da zubin halittan manyan maza, mutum ne mai yawan gargasa, dan ko hannunsh zaka ga haka, balle kanshi dan a yanda na fahimce irinshi ba mamaki after 2weeks yake askin gashin kanshi.


Idan zance a cikin zaratan maza waye gwanina zan iya rufe idanu nace Dr, dan takowani lungu ya iya saita soyayya meyin lugulugu da zuciyar D'aya mace. Balle ni kuma da nake uwarsu wance, A iyakan rayuwata wannan karone na fara son ɗa namiji bawai shirmen da nayi tayi aka Anim, Idan da Dr na samu a farko zaiyi wuya na, tsallaka na bar aurenshi, sabida irin mafarkin danake yau gashi na same shi, mijin da zai girmama Alamarina. Na sameshi, ya fahimce ni,kuma ya fahimci kaddarara, kuma tsaf yake ya zauna dani, gaskiya ina cikin farin ciki.
Haka mukayita shirrita dan kana ganinmu kasan sabin shigane a love, dan mun kasa ɓoyewa a gaban kowa.
***
Washi gari ina zaune akan abin sallah, inata jiran kiranshi dan ya sabar min da haka,
Tura mishi sako zanyi sai ga nashi sakon ya turo min.
*Ina da Meeting kuma zanje ganin shugaban kasa sabida nike duba lafiyanshi By Angel*


Sai naji ba daɗi, tura mishi sakon fatan alkhairi nayi nace.
*Ok Baby! Allah ya bada sa'a! Ubangiji ya kare min Honey."
Sai da sakon ya tafi naji kunya ta kamani.
*Alhamdulillah ni kika kira da Baby ina son sunan kibar honeynan Baby ma ya isa*




*_Bawai ku turo min kuɗin ku nake nufi ba, na gaya muku ne kafin na gama Book One Free ne, bana son sai na gama nace muku Two na kuɗine tsaf wasu zasu zageni akan haka, kuma Am Sure that akan na maida na kuɗi dayawanku zasu daina Comments da Voting sai dai nasan haka bazai sani kasa a gwiwa ba._*




Oum Muwaddah...
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAK'A WRITERS ASSO...._


*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*


_Jordan Historical_


*©2020*
BOOK ONE....


UMMU ALMUSTAPHA kina girmama Chakwakiyya,
MAMAN SADEEQ ta zauren Sainah ina jin daɗin comments ɗunki.


Fatan Alkhairi gareki Aunty Umma🍀

Uwar miji uwar kankanba, BabarTankwali me katon kai😂😹 Daga ke sai Aunty Umma kuka nuna min Sonso nagode......


Masu tambaya Number da Acc kuyi hakuri na shiga page.40 zan saka muku, ku fara booking👏 Ina muku sonsoriya😹


Page.٣٤-34


Murmushi nayi cikin jin wani farin ciki ya lulluɓe ni, na tura mishi.
*Don Allah ka nutsu idan kaje gaban shugaban kasa karka kwafsa*


Ina tura mishi na kashe wayar dan nasan yanzun zai addabi rayuwata da sako.
Komawa bakin gado nayi na zauna, na gaji da asibit gaskiya.


Cire hijab nayi na ninke, sannan, ina idarwa Ummi tana shigowa, kallonta nayi cikin zolaya nace.
"Ummina! Gaskiya munyi fushi ni su. Princess"
Taɓe bakinta tayi cikin ko in kula tace.
"Ai zamanku nake dasu, sai ku sani a koma inda na fito."
Kunshe dariyana nayi sannan nace.
"Haba! Hajiya Ummina ai bai kai haka ba, tunda gashi har da sammako kikayi, dan ganinsu. Shi yasa nake jin kishinsu."

"Sabida sun kwace miki fadarki ko?"
Naji muryan shi, kallonshi nayi tare da masa magana da ido, baka shiga meeting ɗin ba.
Kallon Ummi yayi ita kan hankalinta nagun ajiye min abin karyawa,
Gefen kirjinshi ya zana da yatsar hannunshi, sai ya kama tare da ɓata fuska, sannan ya watsa yatsunsa, ban san lokacin da nace.
"Ta fashe!!"
A razane Ummi ta juyo tace.
"Wacece?"
"Dr mana!"
Ina juyawa babu shi babu alamarshi, itama kallon kofar tayi, taga bakowa.
Dafe goshina naƴi nace.
"Baki ganshi ba anan har yace min su Aanih sun kwace min Fada"
Kallon Mahaukaciya tayi min, share zance nayi na cigaba da kallon kofar.
Kunna wayata nayi na ajiyeta a kasar pillow. Abin karyawa da Ummi ta kawo min na ɗauka zan ci sai na tuna banyi brush ba. Kawai na shiga ban ɗaki zan wanke bakina, da fari ina buɗe panpo ruwa ya zuba na fara wanke bakina, kamar ance kalli madubi. Sai naga yayi dishi dishi kamar an buɗe ruwan zafi gogewa, me zangani Anim ne bakinshi na ɗigar da jini. Ya ka turo hannunshi da mugun zafin nama zai shake wuyata.
Addu'ar niman kariya daga miƴagu da shaiɗanu nayi da mugun karfi har sai da madubin ya tarwarse. Shi kuma na nemishi na rasa, burushin da banyi ba knn, na fito bakina duk kumfa.
"Ummi!!!"
Na kirata babu ita babu dalilinta babu kuma abincin da takawo min, kara wayata tayi naje nasaka hannu zan ɗauka, sai naji kamar a cikin ruwa na tsoma hannuna, ina zarowa jini ne.
A tsorace na cigaba da addu'a take jinin ya ɓace, Ummina nagani cikin rawan jiki nace.
"Ummina!!!"
"Ina kika shiga ne! Gamu nan zuwa da abin karyawa."


Wasu siraran hawaye ne ya zubo min nace.
"Ummina akwai matsala!!"

"Name?"
"Sai kunzo "
***
A hanyarsu ta zuwa suka haɗu da wasu mabarata har zasu wucce.
"Zakari ɗan tsaya na bada sadaka."


Tsayawa yaƴi sannan ya dawo da motar baya, duba jakar tayi taga babu karamar chanji. Sai dubu ɗaya cirowa tayi ta mika musu sadakar, Dukkansu makafine, sai da ta buɗe kofar ta saka musu a kwanon.


"Allah ya bada lada, ya kare miki gabanki da bayanki, ya kuma maidawa masharratan sharrinsu."


"Amin!" tace Zakari yaja motar, dan shi yaji sauki baya tare da wata damuwa. Nima sabida Aanih muke asibitin.


Suna barin gurin makafin nan babban cikinsu ya kallesu yace.
"Zuciyar Maryama da yaranta me kyau ne, yanzun zamu biya bashin da mukaci."


"Kawu ina Tanimu Dari!"
"Yana saudiya "
Shiru sukayi can suka ɓace.
***
Ina zaune duk tsoro ya gama cinye ni, murɗa kofar ɗakin akayi. Ummi ce da Zakari suka shigo kallon tsoro nake masu.


"Lafiya Safinah?"
A hankali na isa gabanta, kura mata ido nayi cikin kuka nace.
"Ummina!!"
Kallona tayi zatayi magana, damshi naji akan hancina, na share a hankali, jini ne yake ɗigowa daga hancina, zan buɗi baki nayi magana naji abu ya cika min wuyana zuwa bakina, kasa nayi da kaina sai ga gudar jini ya faɗo. Mikewa nayi.


Lokaci guda duƙ wani kafar jikina zubda jini yake, mikewa nayi jiri ya kwashe, na zube a jikinta.
...... Suna meeting wata Nurse ta shiga, dama hankalinshi yana kaina.
'Dr Zk! akwai matsala fa, matar nan fa tana zubda jini."
Mikewa sukayi shida Dudu, suka fito har suna bangaje junarsu.
A tare suka shigo ɗakin, kafin Dudu ya ɗauke ni, har ya ɗauke ni yayi waje dani, har lokacin zubda jini nake. Dakin gobe da nisa suka shiga dani, aka fara kokarin tsayar da jinin amna abu yaci tura.


Sunfi awa biyu akaina babu wani labari, dafe goshi Dr yayi. Sannan suka fito,
Kafin wani lokaci yan uwana duk sun shiga damuwa,
Zuba min ido yayi zuciyarshi ba daɗi, zama yayi ya sarkafe hannunmu, ya kai gefe fuskanshi. D'aya hannunshi yana shafa kaina,
"Safinatu! Na miki alkawarin zama dake a kowani hali. Kuma zan tabbatar miki."
A hankali ya mai da min hannuna, sannan ya fita.
........
Cikin fararen kaya suka bayyana a cikin ɗakin.
"Kawu wannan wani irin sihirine?"

"Eh toh Iqibal! Wannan mugun sihirine da mugaye a cikin bil Adam suke aikatawa,"

Shiru wanda aka kira

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login