Showing 87001 words to 90000 words out of 100319 words
Chapter 30 - Masarautar Jordan Book 1 Complete Document .txt
za a ɗauke su karfi da yaji a tafi dasu. Suna kuka amna na fahimci basa kai yaran gurin da Nannah take dan bata kaunar jin kukansu itama, cike da jik haushi na mike na zauna ina karewa Aamih kallo. Dan takaici take bani, inda aka sasu kuka daban ni da suka zo suna min daban. Jawota nayi ta fasa wani irin kara tana shiɗewa. Da sauri nayi kanta tare da cire mata. Zaro idanuna nayi ganin yadda kafadarta ya kumbura.
Kuka ne ya kwace min, cikin tausayawa nake kallonta. Duba Aanih nayi itama hannunta dai dai gwiwar hannunta a kumbure, tana kuka ɗaukarsu naƴi na fita dasu zuwa ɗakin Nannah wacce take zaune ana tirara mata gashinta, tana ganina ta mike da sauri ta amshi Aanih tace.
"Safinatu meye yasami Maryam da Asma'u."
Bakina ya gaza furta kome girgiza kaina nake cikin kuka. Bata iya cewa kome ba, ta kalle me tirara mata gashi, ɗaukar wayarta tayi ta mika mata, a hankali tashiga lalubar number can ta manna a kunne tace.
"Yanzun nake son ganinka."
Kashe kiran tayi sannan ta zuba min ido cikin ɓacin rai tace.
"Me ya faru dasu?"
Har na buɗe bakina zan gaya mata gaskiya sai kuma wani tunani yazo min da zaran na faɗa ba yarda zatayi ba, tunda iyakata kawo minsu suke bazance ga abinda ake musu ba. Sai nace mata,
"Faɗowa sukayi daga gado!"
Sunkuyar da kaina nayi, kallona tayi cikin rashin yarda tace.
"Toh daga yau idan kun kwana acan kuzo nan ku zauna sai lokacin kwanciya yayi kukoma."
Sam banji daɗin haka ba, amma babu yadda na iya tunda tafini Iko da yaran dan haka na gyaɗa mata kai alamun amincewa. Muna haka likitan yazo ya dubasu nan ya gano gocewa ce, ya musu gyaran amma sunsha kuka, ana gama musu na shigar dasu cikin d'akinta na basu nono sai da suka koshi har sun fara barci sai ga Natasha tashigo, da uban gadaranta tazo zata ɗauki yaran na dakatar da ita, ta hanyar cewa.
"Kinzo ki karasa min sune wanda kukayi bai isheku ba sai kin kara da wani, karki kure hakurina."
Cike da rashin kunya ta kalli tsakar idanuna tace.
"Kinsamu ma ana ɗaukar shegun yaranki marasa daraja a cikin msarautarmu, idan kika kuskura masarautar jordan tasan da ke yanke miki wancan siririn wuyartaki zasu yi, banza karƴa mara daraja."
Kura mata ido nayi bansan me zan faɗa mata ba. Amma ina kallon yadda ran Nannah ya ɓaci dan tashigo lokacin da Natasha take zagin gudan jininta, har da dalilin haka naki magana.
"Natah!!! A razane suka juya ita da Kawarta Amah, jikinsu na rawa matsa musu tayi suka wucce. Itama tabi bayansu, har cikin gidan sai da tayi musu tass sannan ta gargaɗesu akaina sannan tace.
"Yara bazan rabaku dasu ba. Amma Uwarsu basa'arku bace, nice na hana maganarki da Ashraf ba Binti ba, kar na kuma ganinki a gurinta......
😇😇😇😇
*Inayinki Mommy Sayeed keda sauran.....Mom Abul ƙema na gaisheki*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150 ne idan kuma Kati ne Transfer 200 ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode saura 19 pages Insha Allah*
Oum Muwaddah....
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAK'A WRITERS ASSO...._
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
BOOK ONE....
Page.٤٢-42
"Idan kuwa kika bari na kuma kamaki da laifi makamancin haka toh raina zai ɓaci kuma zan hasala, ita ɗin bakuwarmu ce kar na kuma ji kar na kuma gani."
Tana gama faɗar haka ta juya abinta dama faɗar ce ta kawota kuma ta gama, nima bata kyale ni ba da tashigo.
"Me yasa baki rama ba? Eyee bata kai Batul ba sa'ar Khalil ce dan haka daga yau duk wanda ya taɓa ki karki kyaleshi idan kuma na samu an taɓaki kinyi shiru zan baki mamaki."
Tana gama faɗar haka ta fito tabarni ina fama da yaran, karshe da taji kukansu yayi yawa ne tashigo ganin duk na rasa yadda zanyi dasu yasata taimaka min da ɗaukar Maryam, muna rarrashinsu har suka samu barci.
***
Wani irin d'akine me cike da tarkace kaman na bokanci, Juya musu baya yayi cikin ɓacin rai yace.
"Kowani wayewan gari ina kara jin nisar dake tsakanina da ita, itace burin zuciyata amma mutuwa tayiwa gangan jikina iya ka da ita, me yasa kuka dawo dani bayan can yafe dacewa dani? Bazan iya hakura da ita ba dole mutafi tare dole tabini mu cigaba da rayuwarmu a can."
"Ranka ya daɗe ai"
"Karka min kome Nuratu! Kece kika dawo dani idan narasa Safinah."
Daga haka ya koma jikin Wani abu ya kwanta.
Fitowa sukayi Hajiya Nuratu ta kalle Kawarta Salmah a dame tace.
"Salmah! Nayi danasanin tadda wannan alamarin gashi yana niman zame min alkakai"
"Karki damu Nuratu zamu san abinyi babu abinda zai faru sannan kiyi ƙoƙarin ganin Yarinyar ta dawo."
Gyaɗa kanta tayi dan ta gamsu da shawarar da Kawarta ta bata, har gida suka ta sauke Salmah, sannan ta wucce gida. Jikinta a mace sabida bata san ta yadda zatawa Abba Magana ba, dan tana gudun kar ya d'agota. Dan haka ta ajiye a ranta zuwa ranar girkinta ta masa magana.
***
Duk yadda naso kauda kaina akan wancan fitsarariyar yarinyar na kasa, domin iskanci take min a bayan idanun mutane, ranarda ta kaini bango munxo cin Abinci Nannah tafi nima mana visa, zamu tafi Umra daga nan ita zata duba yaronta.
Ni da yarana muka fito gurin shan iska, ashe ita da kawayenta suna can gefen lambun da muka zo, ina rike da wayar da Nannah ta bar min, yau ma gwada sa'ata nake ko zan sami Numbersa. Amma shiru takaici ya ishe ni.
Aamih ce naga tana kokarin mikewa tsaye bakina a sake, dan naga basuyi wani rarrafe ba, dan yanzun ne ma Aanih take ja, ita kuma Aamih take rarrafen zaki. Abin alajabi sai gashi ta mike tsaye, aikuwa ta fashe da dariya, shiru nayi ina lissafin wataninta, sai naga basu wucce wata bakwai ba, dan yanzun kusan watanmu biyi kenan À Oman. Ai ganin haka itama Aanih ta shiga kokarin mikewa dariya na musu tare da rungumesu, ina cewa.
"Aanih kiyi hakuri kawai Aamih ta fara, tunda itace Babba."
Ihun Aamih tayi tare da rungume ni, ɗago kaina nayi ina mamakin. Ashe Natasha ce ta kawayenta. K'amkame ni yaran sukayi suna kuka, murmushi nai tare da rungumesu.
"Ayya! Yaran karuwa kuna tsoronmu ko? Karku damu uwarku ce zata iya ja muku dan tana koƙarin shiga hurumin Sultan Ashraf, dan shi ɗin mallakina ne, idan kuma kikayi gigin shiga gonata toh tabbas zanyi abu, kiyi tunanin irin wuyar da kika sha. Mana na haihuwarsu saura wata d'aya a sakoshi idan na kuskura naganki dashi."
K'ak'aɓe hannunta tayi sannan ta harɗesu a kirjinta, a gadarance tace min.
"Zan ɓatar dasu."
Shiru nayi jikina na kara sanyi, har tabar gurin ban iyace Uffan ba sai da masu tayani renon yaran suka zo sannan na mike bayan sun ɗauki yaran nabi bayansu. Tun daga wannan lokaci nake gujewa kaina abinda zaisa Nannah haɗi da Ashraf.
Bayan kwana biyar muka tattara sai macca, inda muka sauka a wani gida mallakin sarki Abdul Muttalib, daga nan zuwa harami ba nisa tafiyar minti goma ce. Tunda muka shiga garin muka isa idan muka tafi Ibada bama dawowa sai inzamu ci abinci. Idan muka dawo kuma bamu sake fita sai lokaci la'asar.
Daga maka muka wucce Madina ziyara, daga can kuma Nannah tasani a gaba muka koma riyad acan ake rufe dashi.
Kamar nace bazanje ba haka nake ji amna babu yadda na iya, bamu isa da wuri ba. Sai biyar dan haka bazamu same zuwa kurkukun ba, dole sai washi gari..
A masaukinmu nida yarana Masu renonsu har su biyu, Natasha da Nannah a ɗaki ɗaya,
....... Ina kwance naji karan shigowar sako.
*Hey Beauty ya kike*
Zubur na mike zaune ina zare idanuna gwada kiran wayar nayi yaki d'agawa, bansan lokacin da kuka ya kwace min b, da nasake kiran nabiyu ya dauka, yana jin shashkar kukana. Kashe kiran yayi ya kuma turo min da sako.
*Toh ya isa mana! Ina tare da shugaban kasa kinga ba halin nayi magana da kowa.*
Cikin kuka na tura mishi da cewa.
*Amma me yasa ka kashe kiranka kasan ydda nake ji kuwa! Ji nayi bani da farin ciki don Allah karka hukuntani da laifin da bansan nayi ba.*
*Beauty ba haka bane ina cike da kewarki, musaman cutie lips ɗinki nayi kewarsu, ji nake kamar nafito ta waya na cigaba da cinye bakin da me bakin.*
Zaro idanu nayi tare da kallonsu Aanih da suke barci kunya ta kamani na tura mishi.
*Baby! Ka fara bani tsoro da kunya don Allah bar maganar haka*
Dariya ya turo min tare da cewa.
*😹😂 Beauty ai dole kiji tsoro nidai wallahi duk ranarda kika shigo hannuna, zaki faɗi gaskiyarki domin kuwa sai na cinye ba iya, kuma bazan koshi dake ba, hmm karki sani faɗar maganar da zanji kunya nan gaba."
*🙈🙉🙊 Wayyo Allah na don Allah bar maganar haka, dan zaka iya sani daina kulaka dan ni kuma kunya nake ji.*
*Kunyar me? Ai ni bana fatan kiji kunyata, idan likita irina yaji kunya toh kawai ya ajiye aikinsa, dan kunya batashi bace! Safinah kece macen da zuciyata ta buɗewa kofarta kika shiga, don Allah ki rike min ki dan kece nake jin zan iya raba farin ciki dake Ina miki so da duk zuciyata."
*Baby!!!"
Shiru yayi sai na rasa abinda zance mishi nace .
*Don Allah muyi magana ta Whatsp.*
*Ba yanzun ba Baby dan nasan video call zaki ce muyi, daga hiranmu na yanzun na fara jin bakon yanayi a jikina musaman na tuna da sumbatar nan me zafi jinina na ta fasa komena yana harbawa fiye da kima plss karki kirani dan zan iya shiga wani hali.*
Wallahi bansan lokacin da tsoro ya kamani ba na tura mishi da *Hmm mukwana lafiya ni wallahi tsoro kake bani.*
Dariya ta turo min tare da cewa.
*Sai ma kin shiga hannun namijin duniya kiga yadda ake jiyar da mace soyayya da jin daɗi toh nan ne zaki fahimci tsoronki na gaskiya*
Sakon na shigowa ina kashe wayata, ina zan iya da manyan magana sam dr bai da kunya yanzun, dan ma baya tare da hajja wallahi sai ya lalace dan ita magana bai mata nauyi ko laushi.
..........
Washi gari tun asuba da na kunna wayata nake ganin sakonshi. Murmushi nayi cikin jin daɗi nake walwala, har sai da Nannah ta fahimci ina cikin farin cikin sai ta zata ko dan zamu je ganin Ashraf ne. Itama sai ta kama murna, bayan mun karya ne aka kwashemu sai can tare da lawyershi.
Koda muka isa ajiyemu akayi na wani lokaci kafin aka fito dashi.
Wato tsarin gidan yarin da ban mamaki yake, akwai gefen masu mugayen laifi wanda za a zarta musu da hukuncin Shika(😜) akwai gefen masu karamin laifi na iya waadi, akwai kuma gefen irinsu Ashraf, zan iya cewa shi a gidan Yaran an ajiyeshi ne dan baya tsinana kome sai dai a girka a bashi ya kwashi gara, shifa tsabar gata kome yi masa ake gashi ana turo mishi kuɗi da wasu abubuwan bukata, sabida yana da galihu. Tunda muka isa inda zamu ganshi kaina ke sunkuye kirjina na bugawa, ga wani irin tsoro da ya mamayeni.
Sallamarshi ya dawo dani daga duniyar da na nutsa, cikin farin ciki Nannah taje ta rungume shi tare da sumbatar goshinsa, murmushi yayi wanda yasa dimple ɗinshi luɓawa yace..
"Ammihna ai da kun hakura nan da sati biyu zan dawo."
Girgiza kai tayi, cikin farin ciki tace.
"Idan na mutu kafin lokacin fa?"
Karan Aamih yasashi kallon inda muke.
*Sarki ya tabbata ga Ubangijin makagin halittar farko da na karshe*
Abinda ya faɗa kenan a ranshi sakamakon tozalin da yayi da Aamih takwaran Nannah, wacce suke fitinannen kama dashi, karasowa yayi har inda muke yasaka hannunshi ya ɗauketa dan tana kan cinyata..
Ko kallona baiyi ba, ya rungume yarshi, lafewa tayi a jikinshi har tana lumshe idanunta.
"Maryam itama baka ganta ba."
Dan ita tana hannun Natasha ce, juyawa yayi ya amsheta tare da rungumesu a kirjinshi, kwalla na zuba mishi na tausayin yaran, yace.
"Ammihna! Ina sonsu fiyye da kome a duniya, sai dai kaddararsu tazo a hangunce, amma haka bazai hanani nuna musu kauna ba."
Sai ya sumbaci wannan ya sumbaci wannan cikin zakalewa Natasha tace.
"Sultan nima zan tayaka kaunarsu ."
Da wutsiyar ido ya kalleni yaga kaina a sunkuye ina fama da waya, mamakine ya kamashi wai kowa yana murnan ganinshi amma ni hankalina yana kan waya, zama yayi suka fara hira. Can Nannah tace.
"Binti! Baki baku gaisa da Ubangidanki ba"
D'ago kai nayi cikin nutsuwa nace.
"Nah! Ban lura bane muna magana da Dr ne." sannan na ɗan kalle shi nace..
"Sannu!!"
Banza yayi dani kamar badashi nake ba, sai da Nannah tace mishi.
"Habibi! Binti tana gaidaka."
"Ammihna! Yaran nan sun kai na yayewa ne?"
"Baka gaji bane Umminsu tana gaisheka"
B'ata fuska yaƴi sannan ya kalleta ya kuma kalle ni yace..
"Bafa gurina tazo ba! Tunda tazo ta rungume phone ɗinta"
Da mamaki na d'ago kaina yadda take iya dogon magana, ba tare da gajiyawa ba, shi da yazo ya ɗauki y'arshi ko kallona baiyi ba sai nice da nace masa sannu zaki amsawa, tsuke fuskana nayi tare da haɗe girana. Sakamakon
Jin tana lallashinsa wai ya amsa gaisuwata kodan yaran,
"Yawwa"
Yace min, satar kallonsk.hi nayi ya kara girma zance kenan dan yanzun yafi da, sannan ga Uban kasumbar da ya bari, sai fuskarshi tayi kallar ta mage.
D'an karamin pink lips ɗinshi ya ɗaura a goshin Aanih ya sumbata, kauda kaina nayi naga sakon Dr har goma. Na shiga bashi amsa muna hira, jin dariyan Aamih sosai take kyalkyalewa, wato idan ba abin dariya ba yaran nan basa min dariya, amma yau d'aya da suka ganshi sun manta dani, d'ago kai nayi muka yi ido biyu mukayi dashi, sake haɗe rai nayi tare da hararanshi da wutsiyar idona dan sai yanzun,
Kauda ƙanshi yayi cike da mamaki *Yaushe yarinyar nan idonta ya buɗe?* yake tambayar kanshi.
(Ni kuwa nace tun ranar da akayi zunguran farko😯😂)
*Masoyana na Nijar ga number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a dalla 100 +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150 ne idan kuma Kati ne Transfer 200 ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode saura 18 pages Insha Allah*
Oum Muwaddah......
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAK'A WRITERS ASSO...._
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
BOOK ONE....
Page.٤٤-44
Wucce su naƴi naje na ɗauki Aamih da take kwance na wucce da ita ɗ'akina, muka kwanta barcine ya soma fisgana naji kiran sallah dole na mike na shiga ban ɗaki nayi alola.
Kukan Aamih naji na fito da sauri wanda yayi dai dai da shigowarsa shida jelarsa, ganin yarinyar a dungure yayi maza ya ɗauketa, tare da saɓata a kafaɗarshi yana jijjigata,.
Juyawa yayi ya kalle Natasha, take tafita ya juyo ƙaina. Yarinyar tana kafaɗarshi ya cigaba da shafa mata baya har tayi shiru, d'ago yayi yaga bakinta na zubda jini alamar taci da bakine, d'ago kanshi yayi. Ya zuba min idanunshi wadda suka kankance da zallar madarar masifa, kauda kaina nayi naje na ɗauki Hijab ɗina da sallayar.
Na shinfiɗa zan tadda sallah, ganin naki na kula shi balle har ya kai ga munyi fada, ya sashi juyawa ya fita a d'akin tare da yarinyar ni kuwa nayi sallahta a nutse. Ina idarwa wayata na kara, number Dr.
A gurguje nayi addu'a sannan na ɗauki kiran da na uku kenan.