Showing 66001 words to 69000 words out of 100319 words
Chapter 23 - Masarautar Jordan Book 1 Complete Document .txt
"Nima naga alama, dan su ɗin ma sun fiki wayo. "
Zaro ido nayi tare da sake bakina, mikewa tayi ya sakai har zai fita sai ga Anim, kamar an jehoshi.
"Wallahi baki isa ba! Indai ina numfashi sai na hanaki farin ciki, kuma zanga shegen da zai aureki."
Buɗe baki nayi zan magana, na sun fita tare da Dr.
Taɓe bakina nayi, zan mike sai ga Ummi ta fito, sabida jin hayaniya.
"Ke da waye?"
"Wancan wawan man sun fita da Dr!"
"Wa kenan?"
"Anim matawalle!"
Na bata amsa a takaice,
"Shine yake fadan maganganu haka!."
D'aga kafaɗa naƴi alamun oho shi yasani.
"Baki tunanin zai iya aikata kome? Ya kamata ki sami Abbanku da maganar a dakatar dashi fa."
Cikin rashin son tsawaita maganar nace.
"Ummi kyale ɗan wahalan ni dai nasamu Allah ya rabani dasi yaje can ya karata."
"Allah ya kyauta!" tace.
"Amin ya Allah"
Daga haka duk muƙa bar zance.
***
"Anim! Kana son na gayawa Feener gaskiyar abinda kake aikatawa ne?" Wani kallon banza wani kallon banza yayi Dr!
"Me kasani a kaina? Da har zaka min barazana"
"Eh toh idan na gaya mata
cewa, Anim kawali ne wanda yake da jirgin ruwa, inda ake baɗala ya kake tunani zata ɗaukeka."
Zufa ne yake keto masa kamar wanda ake juyewa ruwan zafi.
"Toh wannan kenan idan kuma na gaƴa mata cewa. Kana shan magani fa? Toh ni fa bani da damuwa kawai ina son ka janye kudirinka akanta."
"Dr kenan! Idan itama tana dashi fa?"
"Karka damu nasan bata dashi, domin shine last test ɗin da mata, karka ji kome gashi ka duba."
Takaici ne ya kara kamashi cikin harzuka yace.
"Dr kana wasa da wuta!"
Gyara zama dr yayi a cikin motarshi yace.
"Shi nafi son nayi wasa dashi. Tun tasowata,"
"Toh tabbas wutan zai zama ajalinka."
"Idan ya kashe ni shi gadin duniya zai, kana damun Safinah, baka taba tunanin idan wanda zak sota da gaskiya ya fusata ko tokarka baza a samu ba. Karka manta tana da Uba! Kani! Uwa Uba masoyi! Idan har ɓacin ran mutane uku nan ya ta azzara ya kake tunanin karka fusatani, dan Wallahi da bugu ɗaya zan saka a ɓatar min da labarinka, ba kai ba hatta Uban matanka wanda kuke kwaryan sama da na kasa, shima ba kyaleshi zanyi ba kafita harkanta."
Gyaɗa kai yake kamar kadangare,
"Idan kuma nami fa?"
"Kana wasa da rayuwarce."
Sunyi musayan kalamai masu zafi alwashin da Anim yaci bana wasa bane, fita Dr yayi daga motar.
***
Sbigowar Dr rayuwata ba sauki dan a cikin lokaci kalilan ya tafi da zuciyata, amma tsabar jan aji da miskilanci tare da ɗan taurin kai, naki amincewa dan Kullum Ummi sai tatuna min yarana da suke hannuna, gefe ɗaya ga Nannah da muke video call kullum itama, Ga wani irin soyayyar da yan gidanmu suke nunawa yarana.
***
Leke leke take murƴanta kasa kasa tace.
"Na maka alkawarin zan cika maka burinka nima yanzun hankalin Mahaifinsu ya koma kan shegun jikokinsa, har da Uwar yaran......"
Me kuma ake kullawa...😹
*Toh yanzun Muhawara zai ɓarke dan nasan ayan tambaya za a wurgawa Dambuje😎😏😒😂*
Oum Muwaddah....
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAƘA WRITER'S ASSO_
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*
*_Labarin daban yake da sauran Ina son ku sani duk cikin labaruna babu ƙamar wannan ba dan kome ba sai dan tsayinshi da faɗinsa Ina ga yaka mata ku nutsu ku bi labarin Idan nai kuskure ku an karar dani domin na gyara dan babu wanda yake cikakke Yanzun muna Book 1 ban gama ba shi yasa na zaɓi na baku Book one Kyauta sauran labarin zaku iya saya a saukakkakiyar Furashi! Masu ganin Feener ta wahaltu a barta haka toh ashe kuwa da sauran kallo, Waye zata aura? Shin meye makomarta? Masu ganin a sake Ashraf! Idan naga comments ɗinku dariya nake, idan kuka bi kome a sannu zan warware wasu kulin na book one kafin na shiga book 2 ku duba wasu abubuwan me kyau na labarin ku zubda marasa kyau na cikin labarin dukda dai duk abinda Marubuci zai saka sai ka samu akwai me kyau akwai mara kyau fatanmu muyi tarayya akan aikin Alkhairi👏_*
Page.٣٢-32
"Toh munafuka annamimiya! Allah ya toni asirinki, wato dake
Za a haɗa baki a cutar da gidana Nuratu me na tsare miki yau zaki bar min gidana Makirar banza makiran wofi" kwace wayar yayi yaga. Alhaji Anim.
"Em...em.. Alhaji ba wan..."
"Gafara can zaki kula min wani makircin toh anyi walkiya, kuma Wallahi kiƙa sake wani abu yasami Y'ata da jikokina, ni hukuncina me saukine, hukuncin da Nana Asma'u zata miki wallahi Allah kaɗai yasani."
Yana gama faɗar haka ya juya tare da barin falonta, cizon yatsarta tayi tare da cima wani kudiri.
***
Rayuwarmu sai muce Alhamdulillah wani irin kulawa muke samu ta bangagori daban daban, Uwa uba Dr da ya zame min wani jigo na rayuwata, dan karfi da yaji ya zamewa su yan biyu Uba, musaman ya kawo min danshi Adil. Ya kwana biyu dake yaron yayi wayo. Kusan shekara huɗu. Da zai koma ni dasu Ummi muka mishi siyayya aka cika babban jaka,dake me ɗa wawa ne ganin Abinda mukayi kamar yayi hauka. Dan murna gani yake kamar na amshi tayin da yake, ni kuwa kallonshi nake kawai bawai me min bane, haka kurum nake ji ban masa adalci ba. Kuma dole duk wanda ya fito nima na yayi hakuri har sai na yaƴe yarana,
Daga ni har yaran jego ya amshemu, munyi bulbul. Dan ruwan none yana isansu sosai, sabida Ummi tasan abinda zanci ko nasha ruwan nono ya kawo. Gefe guda tana gyarani ta ciki da waje. Dukda na koma ɗakinta amma bana yawo kafana ba takalmi a cikin ɗakin, balle kuma na zauna babban mayafi ko hijab.
Ina samun kulawa gaskiƴa yadda ya dace, dan dudu ma ba abarshi abaya ba, Rigakafi da ake zuwa ni a gida ake zuwa min, abu guda da gaza fahimta shine anki barina ko sau ɗaya na fita koda kuwa bakin get ne.
***
Gyara zama Alhaji Kamil Matawalle yayi fuskanshi cike da zallar ɓacin rai. Kallon Abba da Dr sai kuma Dudu. Cikin cunku shashiyar murya yace.
"Ina me baku hakuri da abinda Anim yake muku, kuma Insha Allah zan tsawatar mishi."
"Ba kome Alhaji! Mungode da ka sauraremu. Allah yasa mudace "
"Nine da godiya."
Mikewa sukayi sannan suka fita, a waje suka haɗu dashi, kowa ya ɗauke mishi wuta, shima ko a jikinshi ya shige.
......
Mikawa Ummi Sajida nayi na mike zan shiga ban ɗaki naji wayata na tsiwa. Ban ɗakin na shiga sannan na fito banbi takan wayar ba na ɗauki Husnah wacce take lashe bakinta, murmushi nayi cikin jin daɗi nace.
"Ummi! Aami ta cika niman rigima kalli yadda take lashe bakinta, kamar bata ci kome ba."
Dariya tayi sannan tace.
"Aikinga ita Aani bata da rigimarta, ga hakuri."
"Hmm! Allah yasa karsu ɗauki miskilanci wancan shashashan uba..."
D'im naji an kaiwa bakina duka, da sauri na ɗago kaina ina dafe bakina cikin rawan murya nace.
"Ummi bafa da Dr nake ba, wancan yaro."
Sake buge min bakina tayi, na rike kaman zanyi kuka nace.
"Ummi sabida Ashraf."
Wani dukan takawo min na kauce, cikin jin haushi tace.
"Uban yaranki kike kira da shashasha? Har da cewa yaron can ga shaidan yarontaka a hannunki, ima yarone sai ki girmama shi kodan yaranshi, balle."
Shiru tayi kodan girman maganar da zai fito bakinta,
Ko yayya kika ga ɗ'a namiji ki girmama alamarinsa, da kike kiranshi yaro ai sa'an Abdul ne kuma kinga Abdul yana da mata me yasa baki taɓa kiran Abdul da Yaro ba sai Uban y'ay'anki! Bana son reni, ba mamaki Allah ya nuna miki iyakarki ne dan renashi da kike yi, ko ba haka ba?"
Abunka da sokuwa(😹) sai na shiga bata labarin artabun da mukayi, har lokacin da abin ya faru da kuma dawowa na gida.
Cikin tausayawa ta kalle ni sannan ta kalle yaran, tayi murmushi sannan tace.
"Lokacin da kika ki maganar auren, kowa yayi mamaki, amna da kika ce karatu zaki, sai naji sam ban amince da tafiyarki ba. Dukda haka na kasa dakatar dake, har Abbanku na gayawa bana son tafiyar dan jikina na bani babu alkhairi."
Siraran kwalla suka sauko mata, gogesi tayi tare da sumbatar goshin takwaranta. Sannan tace.
"Da nayi yunkurin hanaki, ba mamaki rabonsu ya zama ajalina, tunda Allah ya nufa sai sun zo ɗin toh babu wanda ya isa dakatar da ikon Allah, naji daɗi da taimako kikayi. Allah yasa hakan ya zame miki izina da duk masu taurinkai irin naki. Sannan kafin Nannah ta tafi taga ya min Baban yaran yana can a saudiya a rufe."
A razane na dago kaina inakallonta, jikina sai rawa yake. Nace,.
"Ummi! Me ya faru da Sultan ɗin? Kinsan sabida ni yayi murabus. Innalillahi"
Kuka ne ya kwace min, ba kome yasani kuka ba sai makomar yarana, ubansu a rufe.
Ta gaya min dalili rufe shi, bayan naci kuka na koshi nace.
"Zai rina! Dan mutum ne me tsananin ko in kula, ga wani miskilancin da yake ji dashi Ummi Wallahi maganar da kika ga Ashraf yayita sosai ki duba girman Alamarin, maganarshi bata wucce harrufa huɗu, itama ɗin dan ta zama dole ce. Ban taɓa ganin miskili irinshi ba, zan iya cewa idan da zaki matse shi bai sai meke faru a cikin masarautar ba, shi yasa suka kayi amfani da yardaddenshi ya zuba mishi makaman."
"Allah ya kyauta! Wallahi na tausya mishi, yaro karami a cikin miyagu."
"Hm! Ummi kenan wallahi na tausayawa matar da zata aureshi dan wallahi makiyanshi sunyi nisa kiyayyarsu akanshi babu sauki zasu iya zubda jinin kowa dan suga bayanshi, kuma abinda zan iya cewa nayi shine ankarar dashi kurakuranshi, da ace har yanzun yana sarkine da na tunatar dashi matan da suke a wulakance a cikin masarautarshi, Ummi kinsan abinda na fahimta ga mulki ga dukiya amma sun gaza samin nutsuwa dashi, gani suke kamar ya hanasu watayawa. Shi yasa sukayita kokarin sai sunga bayanshi, Allah yana kareshi. Akan shi naji na tsani mulki da sha aninta bana kaunar milki, Alhamdulillah ina cikin farin ciki da yaranshi matane kuma basu da gurbi a cikin masarautar da mulkin."
"Toh Allah ya tsare! Amma abun da ɗaure kai."
"Indai akan mulki da dukiya ce babu ɗaure kai dan kowa yasamu rana zai baza shanyarsa son ranshi."
Munyi masa fatan ya cinye wa'adinsa, lafiya.
***
*SAUDI*
Mika mika mishi iPad ɗin Lawyer yayi cikin girmamawa, amsa yayi, ya kalli yaran cikin wani masifafan soyayyarsu.
"Har ta haihu??"
"Kamar yadda na gaya maka yarinyar ta fuskanci matsala a rayuwarta, sannan Fahad ya tabbatar min akwai mutane biyu da suke bibiyar rayuwarta, d'aya likitane. Babu sharri a tare dashi ɗaya kuma Fahad yayi bincike akanshi shi yasaceta, lokacin da cikin yaran. A halin yanzun bata fita sabida gudun kar ya kuma saceta."
Dunkule hannunshi yayi idanunshi sunyi wani mugun ja ya kuma buɗesu, sannan yace.
"A tura masu tsaro"
"Yallaɓai! Ghaniy.."
Yadda ya ɗago kanshi sai da yabawa lawyer tsoro dan har jini jini yake ganin ya kwanta akasan idanunshi,
"Baiwata da Yarana! Kome ya faru kaine. Saura wata takwas na fito."
Yana gama faɗar haka ya mike,
Har ya isa bakin kofa,
Cikin yaren Urdu yayi magana(Jama'a me Ashraf yake nufi da canza yare😎😒😏 Gulmar ma baza a barni nayo cikin salama ba)
Shi kuma Lawyer yace
"Toh! Yallaɓai"
Lawyer na komawa masaukinshi ya ciro laptop ɗin Ashraf ya fara aiki
***
Yau yarana watansu Uku, wanda yayi daidai ɓarin da matar dudu. Tayi, dukda Ummi ta hanani zuwa ji nayi hankalina ya tashi, dole na shirya yaran na saka jakar goyon baby na Sajida Wacce nake kira da Aanih, sai Husnah wacce nake kira da Aamih. Aanih a gaba Aamih a baya, sannan na fito tare da bawa Zakari daman ya kaimu asibitin kamar zaiyi kokari sai ya fasa muka fita,
Muna barin cikin gidanmu, wata jibgegiyar mota tana rufa mana, kamar zasu bi takanmu Zakari ya matsa musu yana mita, munzo traffic, sai ga wata mota tazo da mugun gudu, zata shege damu. Abin mamaki sai gani mukayi wata babbar tanka tabi ta kanta.
Ai ganin haka yasani fasa ihu, tare da kamkame jikina, karan jiniyar yan sanda da fire service,
Da sauri nasakai zan fita naga an shigo tare da ture Zakari gefe, akayi baya da motar, zanyi magana dani har zakari aka watsa mana hoda.
"Eh kome ya kammala karkashin jagorancin D28 Code 29 grps"
Iya abinda na iyaji kenan, sannan wani kafirin barci yayi awon gaba dani.
***
Fitowar Dr kenan daga Asibiti, zai shiga motarshi,, sai ji yayi an Duke keyarshi da abu, durkushewa yayi tare da rike keyar, sai ganin mutumin da ya duke shi, ya faɗi a kasa, ko shurawa. Sakamakon harbin da aka mishi ta keya har sai da yafito goshinsa, lumshe idanunshi yayi sannnan ya yanki jiki ya faɗi a gurin.
***
Buɗe idanuna nayi a hankali na sauke akan Ummi wacce nake hango ɓacin rai a idanunta, mikewa nayi da hanzari kaina yayi mugun sarawa dole na koma, ina lumshesu nace.
"Ummina! Yarana fa?"
Wani banzan kallo tayi min cikin matsanancin ɓacinrai tace.
"Dk cikin yarana, kece kika fita zakka. Ko yayya na saka doka sai kin rusa min ita, yanzun badan Allah ya kare ba, me kike tunanin zai faru. Wallahi Safinah ki fita a idanuna na rufe."
"Don Allah Mariama ki rabu da ita haka, da muka samu duk suna raye barka zamu sannan mu godewa Allah, sai Dr shima ya farfaɗo Insha Allah, Ubangiji zai shiga tsakaninmu da duk me nufarmu da sharri, yanzun haka munyi magana da Hukumar yan sanda, kuma Allah zai bamu nasara."
"Alhaji hankalina bai kwnta ba Ina ganin Safinah ta tattara tabi tafi Oman zatafi samun kariya a can."
Shigowar Mataimakin IG, yasata yin shiru, gaisawa sannan yace.
"Alhaji Badar! Mun sami labarin kaida iyalinka tare da Dr Katagum ake hari, amma abin mamaki ba maharan bane suka turo mana sakon D28 Code 29Grp"
🏃🏃🏃🏃🏃Yacn kaina har ciwo yake,
_Domin cancare chakwalkwalin Chakwakiyar zaku iya sheke naira 150 a cikin asusun bankina kaitsaye domin dakon Book 2, idan kuma Katine zaku iya Kumdume katin Mtn na naira 200, Mu kafta saura pages 28 na karkare Book One ga wata Chakwakiyyar ta fashe kune min taku...Karku manta idan transifer ɗin kati Vtu 200 ne idan kuma kaitsaye ne zuwa asusuna na banki 150 ne sayan nagari mai da kuɗi gida Arashin araha ake barin tayi, koda kuɗinka sai da rabonka abin dace ne ɗan fari ya mutu idan kun shirya naji motsinku daga marubuciyarku wacce bata san raggonci ko lalace ba ƙullum suburbuɗeku take da labarai sinki sinki_
Oum Muwaddah......
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAƘA WRITER'S ASSO_
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*
*_Labarin daban yake da sauran._*
_Kun gane Nufina kuwa? Book One free ne daga page 1 to 60, Book 2 zuwa inda zan tsaya na kuɗine wai ina gaya muku ne ku shirya tsaf_😹
Page.٣٣-33
Zaro idanu nayi waje, tare da kifkifitawa, nace.
"Ummi ina yarana?"
Buɗe min bakina tayi cike da jin haushi matar da tun da tahaifeni ban taɓa jin tayi zagi koda Qaniyarki bata taɓa faɗa a gabana, sai yau wai itace ke ce min.
"Suna gidan Qaniyarki"
Zaro idanu mukayi hatta Abba sai da ya kalleta anya ita kuwa.
"Ummi zagi kikayi fa!" inji Khalil, juyawa tayi a fusace tace.
"Qaniyarka zan fasa muku kai, haba jama'a ke ɗaya kin addabi rayuwar kowa, Haba don Allah Safinah anya kina son ganin dai-dai a rayuwarki kuwa, ke ko damuwa da rayuwar yaranki bakyayi, toh idan Sajidah ta mutu sai ki san yaren da zaki gaya Ubanta da