Showing 78001 words to 81000 words out of 100319 words

Chapter 27 - Masarautar Jordan Book 1 Complete Document .txt

bari mana"
Dariya yaƴi sannan yace min.
"Ina da aiki, zan leko anjima."
"Ok Allah ya kaimu."
Nace mishi, da dare kuwa sai gashi munyi hira sosai. Har ya gama ya tafi.


***
Yau zamu bar Abuja zuwa Oman, amma ji nake kamar zan mutu tsabar bakin ciki. Da maraici jirginmu zai tashi kamar, zanyi hauka haka nake ji dan Dr yaki zuwa. Tun ina raba idanu har lokacin tashinmu yayi ba dr ba labarinshi, sai da aka fara kiranmu. A sanyayye na saɓi Aamih a kafaɗata hawaye na zuba daga idanuna.
Ji nayi an zare Aamih, ajiyar zuciya na sauke sakamakon kamshin turaren Adidas.
Cak na tsaya, a sannu yazo yaja hannuna muka shiga tafiya sai da ya kaini har cikin jirgin. Ya kaini gurin da zan zauna, ajiye min ƴarinyar yayi, a bazata naji lallausar lips ɗinshi ya sauka akan goshina yace.
"Zanyi kewarku Allah ya dawo daku lafiya. Idan kin sauka pls kk kirani."
Gyaɗa kaina nayi yasakai ya ficce daga cikin jirgin, naji ba daɗi wai ma dan ban zama matarshi ba kenan.


***
*SAUDIA*
Shigowa yayi ya zauna, idan ka ganshi za ɗauka yafi shekarunsa sabida ya wani tara kasumba da da gemu sai fuskarshi tafito ɗan das, zama yayi. Sannan ya kalle lawyer cikin son karin bayani.


"Yallaɓai! Gimbiya Safinah tare da Gimbiyoyin suna hanya gobe Idan Allah ya kaimu, nima yau zan koma"


Murmushin da yajima bakyi ba itace ta kwace a fuskarshi yace.
"Idan sun huta akawosu"


Gyaɗa kanshi yayi sannan yace.
"Yallaɓai dukkansu har da Mahaifiyarsu."


Cikin ko in kula yace.
"Idan zata zo ba, idan kuma taki koda karfin a kawo min yarana su naƙe buƙata."


Tsakani da Allah Ashraf ya nuna shi ya ranshi yake so, dan haka yake cewa lawyer idan yaga ba suda matsala a karɓa a hannuna dan yana gudun kar na lalata mishi yara da rashin kjnya.


Da haka suka gama tattauna, sannan lawyer ya tashi dan komawa masaukinshi.
***
Mun isa Oman da karfe biyu na dare, Nannah da wasu mutanen tare da Yan uwanta suka zo tarɓana, na gaji zaman guri ɗaya, ina sauka a jirgin na hangota cikin bakar abaya. Sakar beharen, tayi kyau da tanaɗe kanta da bakin mayafi.


Fuskana cike da kunya da nadamar ɓata mata rai danaƴi ta bar kasan, kallona tayi cikin farin ciki tasa hannu ta amshi, Aamih. Tana shafa kanta tace.
"Barka da zuwa Oman Y'ata takaina"


" Barka dai Nannah. Mun sameku lafiya ya bayan rabuwa."
"Alhamdulillah Safinah yasu takwara da fatan basu wahalsheki."
Murmushi nayi, muka isa gurin motar da aka jera, ɗaya daga ciki. Kiran Rover range. Aka buɗe mana muka shifa tare, sai hira take min ina binta da eh aa.
Har muka isa wata haɗaɗɗiyar masarauta, iya haɗuwa ya haɗu, shima tafiya muke a hankali har muka isa inda zamu sauka.
Kallon yadda kowa ke sha aninsa babu wani tunanin. Dare yayi, duk inda muka wucce sai an zube ana gaishemu.


Har muka isa cikin gidan, anan naga tarba na musaman. Dan kamar Ashraf ɗinsu suƙe ganina.
Har dakin Nannah takaini anan naga wani irin duniya da aka narkan, a cikin ɗakin jikina ne yaƴi sanyi ganin yadda matar ta zauna a gidanmu kamar mara galihu, sai jikina yayi mugun sanyi.
A bakin gado ta zaunar dani sannan tashiga hidima da ni, masu aiki sunayi da jikonkinta, abinda ta fara bani madara da tumaric, nasha sai jikokinta kuwa wanda ama tasaka aka haɗa musu, ruwan wanka har da wasu irin turaruka, wanda yake cikin wani fure.


Gaskiya mun same tarɓa me kyau, ina fitowa doguwar riga nasama na gabatar da sallar dake kaina kafin na juya na kwanta, lokaci guda barci yaƴi gaba dani, ban san lokacin da aka dawo min da yaran ba dan barci yaci karfina.


Koda ta leko tasamu ina barci ga yaran da suƙe gefena suma suna tabarci, ɗakinta ta wucce. Inda tasame yan uwanta ana hira..
Abisa aladar Larabawa basu cika barci da dare ba, sunfi gane suyita yawo ko a zauna ana hira ana kurɓan shayi, Da safe kuma idan manyane su rama barcinsu idan yarana ne. Idan sun dawo makaranta zasu yi ina nasan ban wucce Oman ba tsabar barci yayi daɗi, banji kukar Aanih sai da ita Nannah taji tazo dauketa, taba ta ruwa tasha sannan ta.
Tashe ni na bata nono. Ina bata ina gyangyaɗ, dakyar na bata tasha ina ganin ta koshi na tintsira sai barci nima muka nayiwa kaina masauki, haka Nannah tafita tare da min addu'a.


Ta rage mana karfin Ac ɗin, sannan ta lulleɓe mu da babban bargo sannan tafita a dakin, jin d'umi yasani gyara kwanciya ashe bani ɗaya bace har da yaran


***
*Baya bata kad'an*


Jirginmu na tashi yan uwana da Dr suka fito, kawai aka fara.....
*Aka fara Me......"




Kuyi hakuri da pagen ba tsayi...😎
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150 ne idan kuma Kati ne Transfer 200 ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode saura 25 pages Insha Allah*


Oum Muwaddah......
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAK'A WRITERS ASSO...._


*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*


_Jordan Historical_


*©2020*
BOOK ONE....


MOM SAYEED, RAHAMA AHMAD, MAMAN KHALIL da MY ZAHRA sauran Yan Team ɗin Hajja Ƙaka, toh tana miko GWS......


Wannan Naki ne sis FAUZIYAH kiji daɗinki...
Page.٣٧-37


" Nadai gaya miki ki rabo da wancan me zubin Inyamuran, ina dalili! Me zakiyi da mutum dinkinkina."
Ta shigo min ɗakina tana mita, zuba mata ido nayi cike da takaici kamar zanyi magana sai kuma na kyaleta, sabida karan wayata ɗauka nayi na manna a kunne Cike da jan aji tare da miskilanci.
"Hmm!"
Murmushi ya sauke wanda ya doki dodon kunnena, lokaci guda ya saukar min da wata kasala, har sai da na lumshe idanuna.
"Beauty! Ina jiranki pls"
Ajiyar zuciya na sauke tare da sake wani munafikin murmushi nace.
"Ok!"
"Thank You!"
"Are Welcome My Beauty" ya faɗa, bai kashe kiran ba. Nima kuma haka muna manne da wayar a kunnenmu, sai murmushi muke sakewa junanmu.

Sake baki Hajja tayi tana kallon Ikon Allah, musaman da taga sai murmushi naƙe sakewa kuma ban kashe kiran ba, zama tayi a bakin gadon. Tace,
"Da alamu sai Badaru ya ɗauko masu maganin Aljanu dan bana tunanin lafiyarki lau, kin manna abu a kunne ke ɗaya sai dariya kike ai wani taga haka yace ba lafiya dalla aji."


Katse kiran nayi a kufule nace.
"Meye matsalarki Hajja."


Na mike ban ɗaki nashige dan bazan iya da hajja ba, sam bata da kunya kome zata faɗa a tsirarar shi take faɗa kuma bata damuwa da abinda zai fito bakinta kome tafamjama famjam.
Nasan na ɓata lokaci gurin wanka, ina fitowa daure da towel tana zaune abinta, zama nayi na fara gyara fuskana da jikina sai da na kyalkyale ko ina, sannan na ɗauko bra ɗina zan saka amma dake matar nan yar duniya ce, karkata kanta tayi.


"Hmm. Me zaki sanyawa rigar nono, ba dai wannan abun ba? Abu sai kace me kirgan dangi, wai ma na tambayeki taya kike shayarda yaran nan ne dan naga sun musu miri-miri."


Juyawa nayi na kalli bakin kofa na tabbar ba kowa juyar sa kaina nayi, cike da bakin ciki nace.
"Zoƙi ficce min a ɗaki! Dan ke ɗin nan sai kija ayiwa mutane girgizan kasa ana zaman lafiya da maganarki nan da kike yi mara daɗin ji balle gani."

Haushi na bata aikuwa tatura min baki, tana taune asuwakin bakinta, gown ɗin Atamfa nasaƙa, wanda aka fidda min shap ɗina sosai ganin yar sa'idon bata fita ba na ɗauki pant ɗina da under na shige ban ɗaki sororo tayi tana kallona, cike da alajabi har na fito. Taɓe baki tayi irin ko ajikina, na zata har zucine sai da nazo ina fesa turare tace.
"Yanzun Yakolo saka kayan ma, sai a ban ɗaki wata uwar zan gani, kika iya saka kwanseti a gabana sai wandone zaki gudu ban ɗaki, ko ce miki akayi zan kalleki ne."


Naɗe gyale na nayi cikin sauri nace.
"Ke kika damu"
Na fita da sauri, rakani tayi da harara tana dafe gwiwarta zata mike daga bakin gadon, na sake shigowa da sauri na kalli fuskana sannan nafita da mugun sauri.
"Ba dole kita sauri ba, sam yarinyar bata da auki, sai kace bulaliya."


Ita kaɗai tayita mita tsabar masifa nacinta.
.....
Tunda na fito ya kura min ido. Ko kiftawa bayayi, zuciyarshi cike da farin ciki, yayinda fuskarshi taki ɓoyewa sam. Har na iso jikin motar na tsaya hannuwana harɗe a kirjina , nace.
"Assalamun Alaikumun"

"Amin Waalaikumun Salam, Beauty! Barka da zuwa."
Buɗe kofar yayi tare da zaro kafafunshi waje, a hankali ya yunkuro yafito, sai yanzun na lura da girman da Hajja take cewa yayi min, tsayi yake dashi sai faɗi. Kuma yana da murɗaɗɗiyar jiki, kana ganin tarin tsokoki, lumshe idanuna nayi sakamakon kamanceceniyar da suke da Ashu, sabida shima yana da k'iran irinta zaratan mazaje.
Hura min iskan bakinshi yayi. Fuskarshi ɗauke da murmushi yace.
"Kina tunanin Babansu Twins ko?"
Ya ɗaga min gira, tsuke fuskana nayi tare da tura bakina gaba nace.
"Baby!!"
Ware idanunshi yayi, cikin jin haushi nace.
"Ba halin nayi tunani sai kace na wncan yaron nake yi"

Dariya sosai na bashi, dan yakasa rikewa yasai yi yake kamar yaga taɓaɓɓiya, haushi ya bani na juya zan koma cikin gida yayi wuf tare da riko hannuna, a tsiwace na buɗe baki zanyi magana, muka haɗa ido dole na haɗiye sannan na kalle hannuna da ya riƙe.


"Kiyi hakuri mana" yace cikin wani irin murya, d'ago idona nayi na kalle shi. Bansan lokacin da kwalla ya shiga saukowa daga idanuna ba, sake min hannuna yayi sannan yace.
"Kiyi hakuri, wallahi bansan dariyar zai sakaki kuka ba, kiyi hakuri bazan kuma ba."
Buɗe motarsa yayi ya ɗako tissue ya mika min, goge kwallar nayi, kaina a sunkuye. Dan kunyar kaina nake ji na kukan da nayi akan abinda bai taka kara yakarya ba.


"Kinsan me yasa na miki dariya! Sabida kin kawo abinda hankali bazai ɗauka ba, tabbas Babansu Twins yarone kamar yadda kika ce, amma ya kamata ki ɗaga shi daga cikin jinsin yara ki kaishi cikin na manyan sabida, Yan biyu, da kuma nan gaba zan kara fahimtar dake abinda nake son ki gane."


"Meye haɗinka da kawar Batul?" na tamvaye shi tare da tsare shi da idona,
D'age min gira yayi cikin tsokana, ya shafa kanshi sannan yace.
"Idan kin amince, rana d'aya za a kawo min ku."


Kallonshi nayi bakina har rawa yake nace.
"Kana nufinm"
"Eh ku biyu zaku zauna,"
Kauda kaina nayi cike da zafin rai nace.
"Ok, kaje ka zauna da ita dan ni ba zan zauna da sa'ar Batul muna gogayya da ita ba."


Mamaki na bashi yadda na ɓata rai, akan yace mu biyu zamu zauna, murmusa min yayi sannan yace.
"Kin cika kishi! Bana fatan rike mata biyu, amma ki sani kishi ke haifar da kishiya, ki sassauta kishinki ni mijin mace ɗaya ce
tal."


"Wacece a ciki ni ko Ita."
Na tambayeshi, gyara tsayuwarshi yayi tare da kura min ido, yace.
"Banda sai anyi aure zaki halatta min wallahi da idan ɗauke ki yanzun na kaiki cikin gidana, babu wanda zai kuma kallon tafin hannunki."

Kallonshi nayi cikin wani bakon yanayi, haka kawai naji ina tausayawa ƙaina, lokaci guda idanuna ya fara da ruwa. Sunkuyar da kaina nayi sabida saukarsu. Suna d'isa a kasa.


"bansan me yasa ba, bansan me nake ji ba, kawai ina tausayawa rayuwata ce idan na rasaka, Dr ka tafi kawai dan ina jin tsoron kar na fara sonka kuma nazo na rasaka."


Takowa yayi gabana tare da soka hannunshi a cikin aljuhunsa d'aya yace.
"Ki d'ago kanki ki kallr cikin idanuna, ce min kina sona."
Girgiza kai nayi wani irin kuka ya kwace min, dafa jikin motar nayi, nace.
"Ko baka ce ba, ina sonka mahaukacin son. Wanda zai iya tarwatsa zuciyata idan na cigaba da ɓoyewa, Hameed kaje kawai idan kacigaba da zama dani bazaka karu da kome ba, sai tsantsar damuwa"


"D'ago kice min na tafi ni kuma zan iya juyawa." ya faɗa min yana kusantar inda nake.
"Bana son Adil da Ammah su."


"Ke! Lafiyarki kuwa kinzo kinsa garjeje a gaba , kina kuka shi kuma da yafiki shirme yabi ya rikice kai jama'a duniya tayu lalacewar zabi."


Da gudu na shige cikin gida ina kuka, koda na isa falon ban tsaya ba na shigesu Ummi da suke zaune.

Bin bayana yayi da ido, bai masan me hajja ke cewa ba, shi damuwarsa nice, haka ta gama surutunsa.
Haka ya shiga motarsa ya bar gidan zuciyarshi ba daɗi, na rasa gane meke faru dani matukar zan haɗu da Dr tausayinshi nakeji haka mukayi kusan kwana goma, dakyar ya dakatar da shirmen da nake mishi. Tsakanina da Hajja kuwa toh ko Tom nd Jerry sun sallama mana, domin kuwa taƙanzo tamin maganar banza ni kuma na shareta idan ta buwaye ni ce mata nake Hajja ko zamu nimo tsohon irinkine a ɗaura muku aure, bata kuma bin takaina.


........ Tsakanina da Dr soyayya ɗoɗarr domin kuwa na gabatar dashi har anyi magana, karewa ma Sadakinsa na hannun Iyayena, an bari sai na yaye yarana wanda suke da wata huɗu zuwa biyar.


***
Watansu Aanih bakwai aka shirya mana tafiya zuwa Oman, tsakani da Allah nasaka Ummi agaba ina kuka bazani ba, dan nasan idan naje sai su nemi rike min yarana wanda nake ji yanzun kamar rayuwata ce su ɗin ko ciwon hakori suƙe tare muke dasu, dan har tsokanata Dr keyi wai amka uwar son yara, bana jin kome, gefe guda har da tunanin dr yake hanani tafiya, dake Ummi ta harbo jirgina sai tashiga rarrashina da cewa.
"Ayya Uwata kwana nawa ne kamar yau ne fa, har kun dawo."


Da ire iren magana masu daɗi da laushi, tasamu na amince amma sati biyu zanyi, murmushi tayi a ranta tace.
*Ta yaro kyau take bata karko*
Kin gayawa Dr nayi, ranar da yaji. Ya kirani amadadin nai mishi magana sai na saka mishi kuka, na rasame zance mishi.
"Ya isa Beauty! Dalilin da yasa kika ɓoye min kenn bazaki iyafaɗa min ba sabida kuka zaki min? Karki damu duk inda kike kisa ranki muna tare, insha Allah zan biyoki soon, an jima zanzo."


Daga haka ya kashe kiran, ranar nayi kuka me cin rai sosai dan gani nake kamar basu min adalci ba,.


Da dare da yazo kasa sake jiki nayi inata ɗari ɗari, dake yanzun a falon Abba muke hiran haka ya gama shirunsa sannan ya ajiye min rafan kuɗin Oman har guda uku, sannan yasa kai zai fita. Cikin sauri nabi bayanshi na rungume shi tare da sake kuka ina cewa.
"Kayi hakuri bazan kuma ba"
Wani irin yanayi yaji ya sauko mishi tare da kasala me mugun kashe jiki, janye hannuna yayi wanda nasa na kamkame shi, ya janyo ni gaba cikin damuwa yake kallona.
Lumshe idanunshi yayi cikin damuwa yace.
"Toh ya zan miki! Nazo amadadin ki tarɓe ni da kalamai masu daɗi sai kuma kika sani a gaba da kuka, kinsan yadda nake ji. Banda kar na shiga hakkin yaran nan ba, wallahi bazan bar gari yawaye ba tare da kin zama mallakina ba."


Lumshe idanuna nayi tare da saka hannuna a wuyarshi na kara tsayina tare da d'aga kafana, haɗa fuskarmu nayi kafin yayi yunkurin dakatar dani, na haɗe bakinmu guri guda. Kallon fuskana yake musaman yadda kwalla ke sauka wannan na koran wannan a guje, a sannu ya buɗe min bakinshi na rasa yazanyi, kawai sai na nemi janye bakina daga gare shi, rike bayana yayi da hannunshi duk biyu ya zura harshenshi cikin tare da lalluɓo nawa, buɗe idanuna nayi da sauri. Lumshe nashi yayi sannan ya buɗe. Yana kallon cikin kwayar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login