Showing 96001 words to 99000 words out of 100319 words

Chapter 33 - Masarautar Jordan Book 1 Complete Document .txt

Fita tayi daga ɗakin, sai ga maids sunzo zasu fitar min da kayana, ɗauka sukayi har da na yaran nidai bance kome ba, har gurin mota Nannah ta rakani, inda ta rike hannuna cikin sassanyar murya tace.
"Binti! Idan na rabaki da farin cikinki ban miki adalci ba, sabida cika min tawa muradin kika rasa taki, idan nace bazaki tafi da yaranki ba, toh na zama muguwa mara halacci, dan haka ki ɗauki kome da ya faru a matsayin kaddara ga yaran can mun bar miki har kiyayyesu, sai dai nasan dole zai zo amsarsu mungode kiyi hakuri da sanyaki kuka da mukayi kinzo cikin farin ciki yau gashi zaki koma ranki ba daɗi, ki gafarcemu. Sannan kyautarki da kika samu a masarautar anyi gaba dasu da fatan zaki yafe mana kura kuranmu."
Hawaye ne ya zubo min daga idanuna, nace.
"Nah karki damu ni ban taɓa rike kome a raina ba."
Buɗe min mota tayi na shiga.
"Nagode! Ki gaida mutanen gidan, suyi hakuri ban musu sallama ba."

Lumshe idanunta tayi tare da murmushi, ban sami nutsuwar zuciya ba sai da motar tashi. Ina ɗaga mata hannu tana ɗ'aga min.


Sai da muka bar cikin masarautar, na sauke katuwar ajiyar zuciya, sam banyi tsammanin ganin yaran ba, sai nagansu sunci kwallayi, har da abin wuyar wanda akayi ɗan kwaɗon da shap ɗin heart, na diamond. Kiran saudiya,
Wayata na ciro daga jaka, na haska fuskarsu, suna barci hankalinsu kwance, murmushi nayi.
"Kinji daɗi hakan?"
A zabure na leka, Wallahi Ashraf ke jan motar.


"Koma ki zauna"
Zama nayi zuciyata cike da tsoron kar ya min tsiya, koda muka isa shi da kanshi ya fidda min kayana, ya kaini har ciki sannan ya juya ya sumbaci yaranshi, ko Allah ya kiyayye bai ce min ba. Nima kuma ban damu ba, na zauna inata raba ido ta inda zanga Dr.
Biyu da rabi sai gashi nan yatawo fuskarshi ɗauke da murmushi, yazo ya zauna kusadani. D'aura kaina nayi a kafaɗarshi nace.
"Alhamdulillah! Ina cikin farin ciki."


"Shagwaɓaɓɓiya kawai! Kinsa hankalin kowa ya tashi sai kirana Dr kyari yake."


Murmushi nayi a raina nace.
"Kaine bakasan abinda wancan yaron yake kokarin min bane."


Muna zaune har karfe uku muna hira, lokacin da aka fara sanarwa muzo, ya ɗauki Aanih da jakarmu, ni kuma na ɗauki Aamih, da ɗaya jakar.
Sai da ya kai gurin aunawa sannan ya dawo ya kwashi sauran, babban burina na ganni A cikin jirgi, kawai ana gama duba kayana, kodan jakukkunar suna da tambarin masarautar ne yasa ba a tsananta bincike na ba.
Sai da muka zo mika passport nan ne nawa yace.
D'auke ni a hankali
Ji nayi zufa na karyo min, a raunane na kalli Dr nace.
"An sace min passport ɗina"
Kawai na fashe da wani irin kuka.
"Ki kira Nannah mana!"
Da sauri na ɗauki jakar na ciro, jikina na rawa sai da ya amshi wayar ya kirata, ya gaya mata halin da muke ciki sannan ya kashe kiran ya faɗawa matar da take amsar passport
.....
Da sauri na tashiga ɗakina, ta sameshi zaune, yasaka passport ɗin A gaba. A karo na farko da ranta yayi mugun ɓaci, tana zuwa ta kifa mishi mari, wanda yasa bakin fashewa.


"Duk yadda akaƴi kaine kasanya Binti a gaba ta bar gidan nan wannan wacce irin masifa ce? Yarinya ta gama lalata rayuwarta a kanmu kai kuma ka biyata da haka, kai mata adalci kuwa?"


Share bakinshi yayi cikin takaici ya mike zai fita tace.
"Kazo ka ɗauki passport ɗinta ka kai mata."
Zuwa yaƴi ya ɗauka.
"Ni da bani da gata na mutu ko Ammih, Yarana fa zata tafi dasu ko sabawa dani basuyi ba, Ammih kina son kar na miki nisa amma su yarana kike son su nisance ni, ni dai wallahi bazata tafin da yarana ba"


Yana gama faɗar haka ya fita a cikin ɗakin,


....... Nayi kuka har nagodewa Allah dan ina ganin suna gargaɗi na karshe.
"Kaje kawai zanzo nan da wasu lokutar, bani da sa'a ce shi yasa kome nawa yake juyewa wata iri, Amma Insha Allah next haka bai kuma faruwa."


Jikin Dr yaƴi sanyi zuwa yaƴi zai amshi nashi suka ce yaƴi hakuri an rigada an turashi, ina ji ina gani Dr ya tafi ya barni, yaki juyowa. Balle naga halin da yake ciki.

Kaina a sunkuye ya zauna kusadani, cikin sanyin murya yace.
"Kiyi hakuri! Bazan iya rabuwa da yarana bane, kuma ina son ƙasancewa dasu har karshen rayuwata shi yasa na sace miki passport."


Yana gama faɗar haka yaje inda ake booking bansan ya sukayi ba, ya zo ya ɗauki jakata ya kai gun mota yasaka, kaf kayana ya kashe sannan ya ɗauki yaran ya kaisu mota, yazo ya zauna kusadani yace.
"Tashi zuwa gobe da safe akwai jirgin Addis Ababa, shi zaki bi kinji."


Ban ce mishi kome ba kaina a sunkuye, haka ya gama maganarshi ban d'ago kaina ba, karshe da yaga zan bata mishi lokaci sai ji nayi ya ɗauke ni, rufe idanuna nayi ban buɗe ba, har ya kaini gaban motar ya saka, sannan ya koma ma zaunin drive, yaja motar, muka wucce cikin garin Oman, wani kayataccen hotel ya kama, sannan ya kwashi yaran yakai ɗakin ya dawo yasani a gaba muka wucce dakin, tunda na shiga na zauna. Ban iya ce mishi kome ba, dan bani da abinda zance masa, yayi juyim duniya na ɗago kaina kai shi magana ma na mishi amma fir naki kaina na sunkuye, shi dakanshi ya fahimci na kai makura na bacin rai dan haka bazan taɓa cewa kome ba.
Kiran sallar asuba yasani mikewa nayi alola nazo na fara sallah, sai a lokacin abinda ya tokare min wuyana ya sauka, na fashe da wani irin kuka.

Inayin sallar amma kuka yaci karfina, dakyar na idar, sannan na cigaba da kuka sosai. Dake ya fita zuwa masalci. Dawowa yayi ya same ni a zaune, ina kuka.


Zama yayi ya buga tagume, yana kallon yadda na lalace, a cikin kwana biyu da zuwanshi, har yaran suka tashi, yayi musu wanka. Sosai sannan yazo ya shiryasu. Ina zaune aka kawo abincin yaje ya amsa sannan yazo ya ajiye min, ko kallon abincin bany ba, zuwa yayi ya haɗa min ruwan wankan.


"Ko zaki shiga wnk ne! Karfe tara jirgin zai tashi."


Jin haka yasani mikewa ɓa wucce shi naje nayi wankan, ina fitowa nasamu baya ciki shida yaran zama nayi na shirƴa. Kaman yasan na shirya sai gashi ya shigo, da yaran zubasu yayi sannan ya wucce ban ɗaki ya shiga wannan, fitowa yayi daure da towel. Hannunshi rike da karami yana goge kanshi.
Sunkuyar da kaina nayi, yana jin an buga kofar ɗakin yaje ya buɗe,jakar takarda ya ansa har guda biyu, yazo ya zazzagesu, riga ce Fari me guntu hannu sai wando, jeans dark blue. Da takalmi fari,sai man shafawa.
Sai a lokacin na lura da wata hegiyar gyaran gashin da yayi, a raina nace.
*Yaranta na yawo da Ashraf shi yasa baya jin kome dan ya cusguna min*


Kauda kaina nayi, dan ya kamani ina kare mishi kallo.
Yana gamawa ya fidda kayana. A hankali nace.
"Wahalalle"
Haka ya kwashe kayan sannan yazo ya ɗauki yaran, sannan nabi bayanshi, muna zuwa ya min kome. Yana kara rungumar yaranshi, ya sumbaci wannan ya sumbaci wannan, d'agowa yayi idanunshi sunyi jajjur. Har kana hango kwalla cikin eye ball ɗinsa, suna maiko, mun jima muna kallon juna. Kafin na kauda kaina, yana gama min kome ya rakani har cikin jirgin yaga yadda muka zauna, sannan yace min.
"Kice min wani abu mana"
Shiru na mishi haka ya gaji da tsaƴuwa ya juya zai fita sai da naga ya kusan fita nace.
"Thank you"
Juyowa yayi dan bai tsammaci godiyata ba, kauda kai naƴi ina kallon waje, ta window.
Fita yayi, nabishi da ido. Jingina kaina naƴi da jikin kujera. Zuciyata tayi min sanyi tunda nasamu nayi kuka tun ina sallah naji tayi min sanyi.


Ban sami nutsuwa da ƴarda da kai ba, sai da naji ance mu ɗaura belt nasamu nutsuwa, jirginmu na tashi ina sauke ajiyar zuciya.


........ Daga airport kamar zai wucce gida, sai ya nufi hotel ɗin da muka kwana, yaje ɗakin. Ya zauna. Can ya shiga dubawa ƙo nayi mantuwa, yana shiga ya sami pant ɗina da na wanƙe, ɗauka yayi ya matse sannan ya saka a cikin ledar hular wankan da yasaka a cikin aljuhunsa, ya fita ya duba babu kome.


Sannan ya sauko ya basu key ɗinsu ya fita, gidan ya ƙoma yasamu Nannah tanata fushi, sunkuyar da kanshi yaƴi kasa, bata ce mishi kome ba, ta wucce ɗakinta, shima ya wucce ɗakinshi ya zuciyarshi cike da kewar Yaranshi.
Zama yayi sannan ya fidda pant ɗin ya ɗaura akan pillow ɗinshi,
(Mayye kawai😡😒😞)


......... Ranar ko Natasha da tazo ba ganewa kowa tayi a gidan ba, dan dukkansu kewan yaran na damunsu, baran ma Ubansu dayafi kowa shiga damuwa sukusuku, yake. Abinci ranar bai iya shaba sai
Coffee, har dare bai kurɓi komd ba sai coffee ɗin koda dare yayi ɗakin da nasauka yaje ya zauna a tsakiyar gadon ya jingina bayanshi da allon gadon, zuciyarshi ba daɗi.


***
Kun isa Addis Ababa karfe biyar na yamma, mukayi hutun awa guda sannan muka bi jirgin Abuja, tunda muka shiga jirgin naji wani farin ciki ya kamani, karfe d'aya na dare muka iso, amma banyi gigin niman gida ba, dan kar tsautsayi ya faɗa kan yarana, sai yanzun nake jin wani shegen tsoro ya kamani, domin zuciyata ta tuno min da chakwakiyar da na tafi na bari, rungume yarana nayi, sakamakon kallon da wasu mutane ke min, fuskarsu babu annuri.
A iya sanina mutane biyu ne dan tsigar jikina na tashi, bansan lokacin da bakina ya fara ambatar.
"Hasbiyallahu La'ilalaha ilahuwa Alaihi tawwakallatu wa huwa arshin Azim"
(Don Allah idan nayi kuskure a cikin addu'ar ku ankarar dani.)

Sau bakwai na karanta, ina d'ago kaina na nimesu na rasa, ajiyar zuciya na sauke, sannan na cigaba da addu'ar, shi wannan addu'a yana kariya sosai babu mugu ko shaiɗanin da ya isa cutar maka, sai in Allah yaso faruwar haka.....


(Jazakillahu Alkhair Ummyn Aiman)


*Masoyana na Nijar ga number da xaku mata magana idan kuna son Book ɗin Wanda yake a dalla 100 +227 96 51 58 05 Maman Fareesah*
*Ga masu son biyan Book 2-3 zasu iya turo kuɗinsu sai nasakasu a Paid grp idan ta bank ne 150 ne idan kuma Kati ne Transfer 200 ne, Mtn, ga number bankinaAcct: 0472282105...*
*Gtbnk Ramlat Abdulrahman Manga. Ga number da za asame ni 08130269641 nagode saura 14 pages Insha Allah*


Oum Muwaddah......
[2/5, 9:24 PM] Raghad💃🏻: _HAZAK'A WRITERS ASSO...._


*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*


_Jordan Historical_


*©2020*
BOOK ONE....


Page.٤٧-47
Sosai nake Addu'a jikina ya gama sanyi fatana Allah ya kaimu gida lafiya, ina zaune a gurin har akayi sallar asuba, gari na fara wayewa na duba jakata, na ciro wayata na na cire layin Oman nasaka Mtn ɗina, yana hawa kan wayata sakonin suka fara shigowa, a hankali na shiga niman numbers Number Dr na fara cin karo dashi dan haka na kira.
Cikin muryan barci ya d'aga kiran nace.
"Baby! Kayi sallar Asuba ma kuwa dan naga kamar baka tashi ba ma"
"Beauty!!!" ya kira sunana da karfi, cikin zolaya nace.
"Malaminsu ba ita bace! Mrs Zaki ce"
"Kina ina yanzun!?"
"Baby Ina airport, kuma gaskiya ina jin tsoron bin mota."


"Ki zauna gani nan zuwa kiyita Addu'a nan zuwa."


Yace min, ya kashe kiran nima na kashe,
Ina gurin zaune ina addu'a sai gashi sanye da jallabiya, ash colour. Mikewa nayi tsabar farin ciki, fuskana ɗauƙe da murmushi
Yana zuwa ya hura min iskan bakinshi. Dariya na saka tare da saukar kwalla,
"Baby! Ina farin ciki sosai."
D'aukar kayan yayi. Sannan yace,
"Sai ma kin zama tawa, nan ne zaki yi farin ciki ranar da na mallaki wannan ɗan bakin."


Lumshe idanunshi yayi sannan ya buɗe, yana bina da wani shu'umin kallo, irin kallon zaki shiga hannuna idan muka jone.
Tura baki nayi gaba ina cewa.
"Wallahi kabar min irin wannan kallon, dan tsoro yake bani jifa sai kace wanda ya tsinci dami a kala."


Wani kallon kurilla yayi min, wanda yasani sunkuyar da kaina tare da wasa da Aanih. Fita yayi yana girgiza kanshi, a ranshi kuwa cewa yake.
*Ya Allah ka mallakamin Safinah badan na isa ko na kai ba.*
(Ni kuwa nace Amin😎 Team Ashraf ya dason life finku)


Ina tsaye ya dawo sannan ya amshi yarinyar muka fita, muna hira dukda safiya ce hira muke sosai, yana tuki ina bashi labarin yadda na same Passport ɗina, dan ce masa nayi na manta akan gado.
Murmushi yayi hankalinshi nakan hanya yace.
"Safinah kenan! A kalla nasan na baki sama da shekaru sha uku! Ba tantama ne, kuma abinda yasani sonki gaskiyarki, dukda bana son jin kome amma yana da kyau ki nutsar da zuciyarki guri guda, idan nine toh lokaci yayi da zan mallakeki, idan kuma Babansu Maryam ne ni bani da matsala da haka."


Cike da mamaki na kalle shi, bakina na rawa nace.
"Hmm! Kana zargina kenan?"
"Ko d'aya bana zarginki! Sai dai ina da karamin kokwanto ne, Passport a jakarki ace ya faɗi a gado kodai Uban yaranki ya ɗauka dan karyayi nisa dashi, hmm. Taya ma zaki auri lebira irina, wanda baya samun hakkinsa sai karshen wata, bayan kin baro inda arziki yake, Safinah ban yarda ni kike so ba, ima ni kike so toh tabbas, kin jefani cikin kokwanto."


Bakina da idona da hancina duƙ asake ina ƙallon Dr yadda yake karyata son da nake mishi.
"Nagode"
Iyakar abinda kenan matuƙar nace zanyi magana toh ba makawa kuka zanyi, lumshe idanuna naƴi burina mu isa gida lafiya, ina jin ya tsaye tare da danna horn nayi maza na ɓalle murfin motar na fito hankalina kwance, na ɗauki yarana. Na shiga gida dai dai Abba zai fita daga gidan ya ganni na shigo ai tsayar da motar yayi. Yafito da sauri ya amshi, Aamih tare da sauke murmushi yace.
"Yanzun airport zani, Sultan Ashraf ya kira yace mana kin taso. Amma yana tsamanin saukar cikin dare zaki yi."


Maida kwallar cikin idanuna nayi nace.
"Abba na iso cikin dare! Toh ina tsoro kar wani abu ya samemu yasani zama har gari ya waye. Mun sameku lafiya,"


"Lafiya lau."
Nayi gaba dan naga Dr na karasowa, ni kuwa raina yadda yake ɓace zan zabga mishi wulakanci iya ganin idona.


Nan yake gayawa Abba ai kiranshi nayi ga kayanmu a cikin motar, ina shiga cikin gida ya kaceme da ihu, da farin ciki.


Take yaran suka shiga makale min, da zaran an ɗaukesu sai su fasa kuka, nan suna kiuya.


"Ina yar shamurmurar take, lange lenge me ramar keta. Wannan Y'a mijin da ya aureki ai shine za a kira a ɗauri kashi ko a ɓata igiya sam babu kayan mora."


Basu Ummi da Umma ba hatta Abba da yakawo Aamih, sai da ya direta da sauri ya fita, taɓe baki tayi cikin ko in kula irin ko a jikina ɗin nan sannan ta cigaba da cewa.
"Taya wancan Malohon ya tawo ya barki a can"


*"MALOHO???"*
Bakinmu a haɗe muka zaro idanu. Gyara zama nayi ina son sanin sanin Waye malohon da Maloho. Zumbura baki tayi gaba tare da watsa hannu gaba irin jaraba da masifa nacin ranta ta zabga mana harara sannan tace.
"Waye kuke tambaya ya wucce wancan gabjejjen tsohon da ya makelewa Safinah."


"Lallai ma kuwa! Na rantse kika kuma kiran Baby da wannan sunan sai na zuba miki shinkafar ɓera kinci kowa ya huta da batsar da kike mana nan, haba kin ishemu da maganar banza."

Ina gama balbaleta na mike tare da barin falon na nufi ɗakin Umminmu, alola nayi dan nabar sallah a kaina. Sai da na gabatar dashi sannan na kwanta dan dukkanmu duk mun gaji. Tuni barci yayi gaba dani.
***
Karfe biyu saura na muka farka nida yaran, fitowa Ummi tayi daga ban ɗaki tace.
"Nikan a cikin wata huɗu ne yaran nan suka ɗauko mugun kiuya haka. Tun kafin ki tashi naso

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login