Showing 45001 words to 48000 words out of 100319 words
Chapter 16 - Masarautar Jordan Book 1 Complete Document .txt
Zaki haifa mim yara dozin dozin..."
Haka yayita sambatu, karshe da ya gaji yasa kai ya ficce yana share kwalla.
Zuwan wata nurse taga halin da nake cikine yasata fita takira Abdul. Yazo ya duba ni. Da yaga na farfaɗo ya saka ya fita.
.........
Bansan me kuma yan gidanmu suke bukata ba dan yanzun sun tsananta fushi dani, kowa ya kaurace min. Baki ɗaya tun daga ranar da Nannah tafita bata kuma zuwa ba. Ummi ma haka, Umma ce da Nana Asma'u suke zuwa sai dare su koma.
Na kuma shiga damuwa fiyye da kima, abinda ban taɓa tunani ba shi yake zuwa min. Zan iyayi ba kawai dai na kosa da nagan ni a gida.
Satina biyu aka sallame ni zuwa gidan Abdul.
Abinda ban sani ba kuwa, tunda na faɗawa su Ummi me cikin. Nannah taje tasame Abbanmu da maganar, dan su fahimci juna. Da fari jikinsa yayi sanyi amma lokacin da shaiɗaniyar matarsa ta saka baki a maganar sai gashi an juya maganar da cewa Ummi da Nannah suka turani Jordan, karshe dai Mamie tayiwa Nannah tijara, kuma Abba bai hanata ba, karshe dai Nannah ta basu hakuri, da kuma rokon idan na haihu zata nimawa Ashraf aurena, Mamie tace.
"Bazamu bashi aurenta ba, dan aƙwai yayana da yake da mata uku shine ya nemi aurenta kuma Alhaji ya bashi ita dan ya karɓi sadakinsa. Kije idan kun gadama ku zubda cikin."
Kan Nannah a sunkuye yake a sannu ta d'ago kanta idanunta sunyi wani irin ja. Hatta fuskarta sunyi ja murmushi tayi, sannan ta mike tace.
"Safina ta haramtawa kowani ɗa namiji sai Ashraf, ki rubuta ki kuma ajiye babu namijin da ya isa tsayawa a gaban Sarki na huɗu, Nuratu mijinki yasan gidan da nafito. Dan haka ki kiyayye harshenki, idan wani abu yasami cikin jikinta."
Dariya tasa sannan ta ficce, sai da ta isa bakin kofa. Ta juyo cikin izza tace.
"Idan wani abu yasamu jikana dake jikin Binti! Toh wallahi sai na ɗaure kaf ahalinku sai an bawa manyan kifaye namarsu ke hatta Badaru da yake Uban Binti hukuncina bazai tsallake kanshi ba, kuma koda wasa wani yayi wa Binti kallon Banza ko ya ambaci cikinta da wani kazamin suna, wallahi na rantse da Allah idan jinin sarauta ke yawo a jikina sai nasa an yanke masa harshensa ko an cire idanunsa. Idan wasa kuke ganin a gwada, zan baku nan da sati biyu kuyi yadda yayi muku, kuyi abinda ya kamaceku, zan tafi Oman kuma zan dawo dan cikin Binti."
Fita tayi bata kuma bin takansu ba taje ta ɗauki passport ɗinta, ta bar gidan tare da kiran Abdul, ya kai yata Airport. Shi da Ummi,
Dama Ummi ta koma gidan yayanta dake Suleja, Alhaji Ahmad Kamfut.
Ba sosai take zuwa ba dan ma suna fushi dani, fitowa nayi daga ban ɗaki ina ɗaure da towel. Naji an bankaɗo labulen ɗakin, Siphia ce hijab ɗina na shiga ja zan saka tayi tsaki, tare da cewa.
"Aikin banza karuwar banza kawai, ba a gidana xaki haifa min shege ba wacce ta zamewa Iyayenta bakar kaddarar "
Saka kayana nayi ban kulata ba, na cigaba da saka kayana. Ina son zan fitane ina gama shiryawa na ficce a gidan sanye da bakaken kaya, na nufi wani shagon saida magani. Dukda ina tsorace amma haka na mika musu kuɗin suka bani, juyo tare da dawowa gida, kitchen na shiga zan ɗauki ruwa, ta hanani ta hanyar ce min.
"Nan gidan tsaftattatun mutane ne, ba masu kazamta ba. Masu zuwa aikata zina yanzun ma an dawo daga gu..."
Tsinka mata mari nayi cikin ɓacin rai nace.
"Kin isheni, gwarani tsautsayine ke kan bansan me zai faru dake ba nan gaba bana miki fata."
Na tureta sannan na ɗauki goran ruwa na fito cikin d'aga murya tace.
"Karuwa kawai."
Tsabar ɓacin rai ina shiga ɗakin maganin guda uku na ɓalla tare da haɗiyesu lokaci guda. Sannan na ɗauki abin maganin nasaka a cikin bahaya na sake mashi ruwa ya tafi.
Dawowa nayi na kwanta, dukda ina kokarin ɓoye tsorona amma a haka nake bawa kaina kwarin gwiwa.
Barci me karfine yayi gaba dani, har na minti talatin kafin maganin ya fara aiki, wani mugun murɗane ya taso min, na buɗe idanuna dakyar, tashi nayi naga yadda jini ke malala a bakin gadon, wani masifaffen tsorone tare da mugun ciwon ciki. Wanda yana murdamin jini yana ketowa da mugun karfi, har wani fuuuu yake.
Maida kaina nayi jikin gadon, nasake yunkura zan tashi wani jiri ya dawo dani tare da tsinkewar Jini tsuuuu. Sharaf na koma idanuna suna masu kafewa...............
*Toh burinku ya cika ciki dai ya zuɓe kowa ya huta kar naji any korafi😎😏*
Wallahi ku bar tambayata daga farko😭
#MJ
#HZƘ
#Vote
Oum Muwadda......
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAƘA WRITERS ASSO_
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*
GA KYAUTAR SHAFI NAN NOVELLA Ku kaɗanku...
Page.٢٣
Bansan iya adadin lokacin da na ɗauka ina barci ba, ni dai yunwar cikina da kuma wutsilniyar yaron cikina yasani na tashi, mika nayi tare da addu'ar tashi daga barci. A sannu na kebin ɗakin da kallo hannuna dafe da cikina, a karon farko da naji tausayin yaron cikin ya cika min zuciya, sunkuyar da kaina nayi ina shafa cikin a raina nake cewa.
*Kai ma kashiga cikin kundin kaddarata ko? Gashi tun baka zo duniya ba na fara wahalar da rayuwarka daga wannan sai wannan*
D'ago kaina nayi cikin nutsuwa ina karewa ɗakin kallo, kome na cikin ɗakin farine. Hatta kayan jikina fari ne, *Waye ya sauya min kayana?"*
Tambayar da ban same amsarta kenan, murɗa hannun kofar akayi. Da sauri na ɗago kaina ina jiran shigowar wanda yayi nasaran kwamusheni.
Turo kofar yayi ɗan karamin bakinshi ɗauke da sallama. Mikewa nayi jikina na rawa, haka ma bakina ya kasa furta kome, sai nuna shi nake da yatsa kamar mareniya nace.
"Anim Kamil Matawalle! Meye nayi maka ne da zafi? Wa...."
"Anna shigo min da abincin."
Take wata baturiya ta turo abincin a keke. Raina a ɓace tsiwa nacina nace.
"Uwar me na maka da zaka satoni? Nd ina nan?"
Bangaje shi nayi na fita banga hanya ba, dan naga kamar hotel ne. Zan iya cewa na manta da ciki a jikina na zura a guje, nayita ratsa kofifi da manyan faloka har na sauko kasa, ganin kofar karshe yasani karawa da gudu, ina tura kofar na zaro idanuna. Fisgoni yayi baya.na kwace kaina na fasa ihu nayi tare da zubewa lokaci guda na fashe da kuka me tsanani. Ina hango inda nake wani bakin cikine ya kamani. Na tun kari kofar yayi maza yasha gabana cikin tausassiyar murya yace.
"Pls ki saurareni!"
D'ago jajjayen idanuna nayi, a sannun na lumshesu. Nace,
"Anim! Why me? Nayi chanchanci haka daga gareku ko? Me yasa duk wata damuwa sai nice zaku ɗaurawa, a bisa tsautsayi na tafi can kaddara rubta dani, yau gashi dan son kanka karabani da iyayena, kai ma jikin nawa kake bukata ko? Ince jikine yake ruɗarku kuke ganin wani abin arzikine, ya ɗauki nashi kason kaina muje na baka, tunda haka Allah yayi ni kowani namiji ya ɗibo dattinsa ya zuba a kaina, muje na baka."
Tunkara shi nayi raina a ɓace, sai masifa nake.
"Kyari!!! Ni..."
"Me zaka gaya? Ehhe meye zaka gaya min?
"Amma ya dace ki saurareni" ya faɗa da sigar lallashi.
"Wallahi Allah sai yasaka min mugu azzalumi, macuci."
"I heard that daga bakin Rabi'atu."
Tsaki nayi na juya zan koma ɗakin, yana biye dani sau biyu ina ɓata kafin na amince yayi min jagora zuwa ɗakin, ina shiga na fara niman wayata nasameta a kasar pillow, ɗauƙa nayi naganta a kashe, ina kunna wayar naga babu service, fita nayi na koma har hanyar ɗazun babu service babu alamarshi.
"Ai bazaki taɓa samun service ba sai ini ne naso ki samu, ki bani."
"In baka wata uwar? Lallai Anim baka da kunya da mutunci nice zan baka kain..."
"Ke ni bana son hauka! Ki bani lokacinki muyi magana na gaskiya, Step Mother ɗinki ce taje gidanmu ta faɗawa Innata, kome ina shirin na tambayeki gaskiya na kuma jin irin haka a bakik abokan aikinmu, nifa ban taɓa kallonki da sigar sha'awa ba sabida nima Ubane ina da nawa yaran bazan so.."
"Don Allah get out" na nuna mishi hanyar kofa..
Murmushi yayi sannan ya shiga ɓalle rigarshi, dafe cikina nayi a tsorace nace.
"Na haɗaka da Allah karka cutar da Yaron da bai san waye shi ba."
Murmushi yayi cike da kwarin gwiwa yace.
"Toh zaki saurareni?"
Gyaɗa kaina naƴi kwalla na zubo min,
"Ok zauna kici abinci!" yace min.
Ba musu na zauna tare da wurga mishi tambaya nace.
"Ina ka kawo ni?"
"Atlanta Ocean muna cikin jirgin ruwa ne" yace min a takaice, tausayin kaina ne ya kamani. Me yasa rayuwa take wasan kwallo dani.
Zama yayi ya shiga zuba min sannan ya fara ɗiba zai bani na kauda kaina yace min.
"Hmm"
Babu wasa a fuskarshi, amsar abincin nayi a sannu yayita bani, har naci kaɗan, sannan nakauda kaina nace.
"Yaushe zaka maidani gun Ummina da Duduna"
Taɓe bakinsa yaƴi sannan yace.
"Sai lokacin da naƴi niyya."
Kura mishi ido nayi jikina yayi mugun sanyi,
"Duk akan me?"
"So!!!"
"Cuta dai! Matawalle wannan ba so bane cutane."
Shafa fuskana fuskana yayi fuskarshi cike da damuwa yace.
"Cutie sabida so na ɗauko ki, naga mutane zasu min shamaki ne dake, Dudu, Innata, Rabi'atu. Zasu min katanga dake suna shirin min bakin ciki. Kinga yadda ciki yayi miki kyau, ina son ganinki a haka shi yasa na kawo ki nan, pls ki barni na taɓa ki."
Zaro ido nayi ina ja da baya tare da girgiza kaina, bakina na rawa nace.
"Karka min haka, Anim wallahi ni ba mazinaciya bace."
Ina matsawa yana matsoni, sai da muka kure gadon, rufe idanuna nayi. Kwalla ya shiga zuba min. Hannunshi naji a kan cikina yana shafawa a slow, tsigar jikina ya mike. Kwalla masu zafi suka shiga zuba da mugun gudu. D'ago kanshi yayi yaga yadda kwalla suke wasan tsare akan fuskana, abinda najine yasani buɗe idanuna,
*Allah sarki Sultan banda wannan abinda ya faru damu bai taɓa kuskuran taɓa ni ba*
"Anim!!" na kirashi a hankali,
"Hmm! Cutie."
Girgiza mishi kai nayi, hannunshi naji a bayana, kuka nake wiwi ina tureshi haka Anim ya cigaba da, bin jikina.
"Ashraf!!!"
Na ambaci sunanshi, d'ago kanshi yayi da jajjayen idanunshi Jijjiyar kanshi yayi raɗa raɗa, yace.
"Uban cikinki ko? Safina meye yasa?"
"Wayyo Allah na! Nace da karfi, ina rike hannunshi. Mugunta zalla ya min, danne cibiyata yaƴi.
"Idan kika kuma kiran sunanshi sai na illata wannan abun domin kuwa shi ya hanani ke shi ya rabani dake,"
Bansan wata irin rayuwa nake ba, daga wannan matsalar sai wannan. Ji nake ina ma banq cikin duniyar nan, sai da yayi da kanshi ya kyale ni, anan na kwanta na cigaba da kuka.
***
*Suleja*
Kallon agogen falon Ummi tayi. Karfe biyu saura na rana Safina babu dalilinta, mikewa tayi ta fito har part ɗin Mama ta zauna cikin damuwa tace.
"Maman Abideen har yanzun Yakolo bata dawo ba, kuma karfe goma take dawowa. Kinga har biyu fa."
"Maman Safinah kina da hankali kuwa, yarinya tun goma bata dawo ba, shine baki faɗa ba yau da ita ɗaya ne ai da sauki mace da ciki fa."
Kamar zata rufe Ummi da duka haka take ji, ta shiga kiran Abideen yana ɗauka ta gaya mishi sannan ta kashe.
Shima asibitin yaje akace bata zo ba, tashin hankali wanda ba asa masa rana. Ummi takira Abdul ta gaya mishi halin da ake ciki, shi kuma ya faɗawa su Nana da Abba.
Lokacin da Abba yaji labari, tsabar tsoro ɗaukar takai mishi yayi ya ɗaura akanshi, hularsa a hammatarshi. Yakira Abdul yace.
"Gimbiya Asma'u tasani ne?"
Abdul yace.
"A'a bata sani ba."
"Shi kenan takare min, dan mutuwa zanyi tace bata kyale kowa."
Hankalin kowa a tashe yake, Mamie kam gani take kamar wasa Nannah take, kuma tana da masaniyar sace Safinah dan yayita bin Abdul ya gaya mishi inda take amma fir yaki, da yaga tana bautawa kuɗi sama da kome shine yayi amfani sa kuɗin ya tambayeta tace bari ta tambayi khalil. Zuciyarshi ɗaƴa Khalil tana tambayarshi ya gaya mata, tana Suleja. Jim kadan takira Anim ya gaya mishi.
Shi kuma yayo hayar kwararru a kidnapping suƙa kwamushe. Baiwar Sultan mamar magajin gobe (😥😹😂)
***
*OMAN*
Kallon ruwan dake gudu a lambusu take jikinta na bata akwai wani abu, dake dab da faru. Kawai ta ɗauki wayarta ta kira Abduƙ bugu biyu ya ɗauka,kamar ya kifa yace.
"Nannah! Akwai matsala."
Tashi tayi kamar zata zuba da gudu tace.
"Ba dai wani abu yasami Binti ba."
"Nannah an saceta."
Mikewa tayi wayar ta subuce a hannunta, zama tayi jikinta kamar wacce bata da karfi.
Zubur ta mike ta nufi cikin gida........
A ranar ta baro kasat zuwa nigeria
***
Duk inda ake tsamani zanje an duba bana gun jikinsu yayi sanyi, da farko sun zata kamar yadda nayi wanca tafiya, sai da aka je har airport aka duba, gabaki ɗaya, hankali kowa sai da ya tashi kwana biyu tsakani sai ga Nannah. Abin ba a cewa kome dan kuwa Nannah tana isowa batabi takan kowa ba, aka shiga bincike da lokacin........
Kuyi hakuri, Waleed ba lafiya jiya kwana mukayi bamu runtsa ba yanzun ma ina rubutun kamar wacce aka sani dole in Barar Addu'arku........
#MJ
#Vote
#HZƘ.....
Oum Muwadda....
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAƘA WRITERS ASSO_
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*
Page.٢٢
Tawowa yayi ya kawo min abincin, sannan ya ajiye min kallonshi nayi zai fita nayi maza na rike hannunshi, cikin rawar murya nace.
"Kayi hakuri Dudu."
Murmushi yayi min kaɗan sannan yace.
"Kici, idan bai isheki ba a karo miki."
Girgiza kai nayi, nasaka abincin a gaba na fara ci, har zai fita nace mishi.
"Abdul! Don Allah ka kaini suleja ina kewar Ummina."
Gyara tsayuwarshi yayi, sannan ya shafe kwantaccen gashin kansa yace.
"Ok ki gama sai na kaiki in yaso jibi sai ki dawo."
Gyaɗa mishi kai nayi, shi kuma ya fita.
Sosai naci abincin sannan naje ban daki na wanke bakina bayan nayi wanka, na shirya cikin bakakken kaya, doguwar riga da bakin gyale, sannan na ɗibe kayana sosai. Sannan na fito na same Madam sophia a tsaye. Yana fitowa ya ɗauki jakana, muka fita, gaba ya buɗe min na zauna yasa jakar a baya itama tashiga yajamu muka tafi.
........ Har gidan iyayenta ya kainta wanda yake kusada gidanmu, kallonshi nayi zanyi magana muryarta ƴa katsemu tace.
"Karuwa hankalinki ya kwanta, kin rabani da mijina. Muguwa azzaluma baiki aure ba harkin kashe auren kaninki, a haka zaki kare."
Ji nayi kirjina yayi min nauyi, dakyar nake jan numfashina, tabbas an taɓani amma ba kome. Bai damuwa yaja motar muka bar layin. Tunda muka ɗauki hanya bai ce min kome ba. Nima haka muna dab zamu shiga suleja naga masu fura da nono..
"Dudu! Zansha fura."
Sauka yayi a gefen hanya sannan ya fita, yaje ya sayo min. Yana shigowa ya mika min, naji jikin goran yayi matuƙar sanyi, buɗewa nayi na fara sha, wani sanyi daɗi tare da garɗi me shiga rai ya gauraya furan ina kurɓa tare da lumshe idanuna, komawa yayi da baya yasake sayo min gora biyu, dan tun bamu bar gurin ba na kusan shanye goran.
Kafin mu isa gidan Uncle Ahmad na shanye goran farko na kuma buɗe na biyu shima sai da naga bayan rabinsa naji cikina ya cika, kwanar da zai kaini gidan. Muka hango mai sayarda gashen masara, tare da ayaba a gashe. Bani manta lokacin da na gama karatu aka turani Imo naci ayabar da gyaɗa.
"Dudu! Ayaba da Masara,"
Tsayawa yayi yasaya min sannan muka wucce gidan, Yaran gidan suka taremu da murna gasu da tarbiya, karɓan kayan sukayi tare da kai mana ɗakin Ummi, Gaida Mama Saratu mukayi tayi mana yar nasiha sannan muka wucce, ɗakin Ummu tana zaune akan abin sallah