Showing 42001 words to 45000 words out of 100319 words

Chapter 15 - Masarautar Jordan Book 1 Complete Document .txt

jininta karfi."

Abdul na shigowa ya mika mishi maganin, buɗe kwayar yayi ya yaye zanin da aka rufa min ya kauda kanshi ya saka min maganin a cikin jikina, sannan ya ɗago hannunshi ya kalle Abdul yayi masa bayani, janyo machine ɗin scanner yayi ya ɗiga min luquid ɗin sannan ya shiga dubawa yana musu baya yace.
"Toh cikin yafita fa!"
Cigaba yayi da dubawa karshe ya ɗaga daga jikin cikina yace.
"Dr Kyari am so sorry we lost the baby"
Gyaɗa mishi kai Abdul yayi cikin jin zafina, wanke hannunshi likitan yayi yace.
"Idan ta farka za a mata wankin ciki."
Gyaɗa kai kawai Abdul yayi, sannan ya fita, suma fita sukayi. Nana Asma'u yayi ya gaya mata halin da nake ciki, ta kira mijinta ta gaya mishi.
Ummi ya kira ya faɗa mata, ita kuma ta kira Fatima akan tazo ina asibiti kafin gobe tazo.
Gidanshi ya wucce yasami gidan yadda ya barta cire kayanshi yayi yasaka a cikin machine din wanki, ya saka Ariel. Tare da ruwa sannan ya komo ɗakina ya gyara tare da goge ko ina yasaka room fresh.
Yana fitowa yaga Sophia da kayanshi da yasaka a cikin machine ɗin wanki. Ta watsar dama a tafashe yake niman abokin taƴi yake, sai akayi dace itace ta taro match ɗin, ba faɗa ba zagi ya kwashe kayanshi ya zo ɗakinshi ya wanke sannan yaje ya shanya, ban ɗaki ya shiga yayi wanka sai cizon lips ɗinsa yake, dan ya lura hatta yaranshi ta kwashesu takai gidan iyayenta, wai kar a lalata mata tarbiyansu.
Yana gama shirƴawa ya nufi masalaci daga can ya shige asibiti. Yasame Nana da Fatima suna ɗakin jum, ajiye take away ɗin da yazo da ita yayi sannan yace.
"Bata farka ba ko?"
"Eh Baban Affan har yanzun ga abinci nazo maku dashi. Wallahi tausayi Didi take bani, daga wannan sai wannan, kasan da nacewa BABAN Sabir dukanta Abbanmu yayi,kamar ya rufe ni da duka. Karshe har kaurace min yayi wai abba bai kyauta ba,tuntuni bata lalace ba sai yanzun da kaddara ta faɗo mata, wallahi badan yana kunyar Ummi ba da ya maka abba a kotu."
Zaro ido Fatima tayi tace.
"Abban Affan da fatan cikin bai zub..."

"Na nawa kuma ai ta zibda cikin naso ta haifi yaron da Abba yaganshi, cikin safina ba gama garin ciki bane, dan cikine da yake da gata gaba da baya, akan cikin nan kuwa nasan sai Safinah ta zama abin alfahari a cikin danginmu amna dake lusara ce dan farin cikin Abba ta zubda shi."
Rike baki Fatima tayi tana zare idanunta, kafin tace.
"Amma wallahi akwai kura! Dan kuwa Anyi rigima akan cikin..."
Nan ta gaya musu aikuwa Nana Asma'u me zatayi banda dariya, tace.
"Lallai akwai wuta a gaba."

"Ai ni zan faɗa mata gaskiya Safina ce ta zubda cikin, kinsan da zata tafi me tabani, wallahi wani akwati ta bani zallar sarkoki da yan kunaye ne a ciki a na sayar na dinga saya mata abinda take so, kinga wannan alert ɗin yau da safe aka turo shi da dallar amurka zunzuruntu kaunar da takewa wancan sakarya, da abin cikinta, ɗazun sai da takirani ya take ya cikin wallahi yau sa safina kasa dani take tana tashi sai na mata dukar kawo wuka."


Shiru sukayi kowa da abinda yake yawo a ranshi, har Baban Sabir yazo tare da Annur.
Sai karfe tara da rabi suka tafi, aka barmu daga ni Fatima. Abdul ya koma gida.


........
Washi gari da safe Nana ta kawo mana abin karyawa, karfe goma sai ga Ummi tazo. Har lokacin ban farka ba.
Sai karfe uku da rabi na farka dishi dishi na fara buɗe idanuna, a hankali idanuna suka buɗe. Ummi da Abdul na gani a zaune Fatima ta tafi makaranta, Nana kuma ta koma gida yin abincin rana.


Gyara zama Ummi tayi cikin ɓacin rai tace.
"Zubda cikin kikayi? Duk wahalar da naƴi da rasa aurena da nayi ya zama a banza, na koma gida a matsayin bazawara Kin min adalci Safinah, laifin meye Muka miki da zaki zaɓi zub da cikin, Wallahi idan Hajiya Asma'u taji abinda kika aikata har abada bazata taɓa kallonki da kima ba, nagode da abinda kika aikata min, banda Hjy Asma'u daga ce mata cikin jikinki na D'antane har da rawan jikinta ta amshiki, toh wallahi zan gaya mata cewa cikin ba na Ashraf bane har kin zubar da shi."
Lumshe idanuna nayi, tare da komawa na kwanta. Kwalla nabin gefen fuskana, ji nake kamar na fasa ihu. Fita tayi Abdul yayi yana share kwalla, domin ina jin sautin kukan Ummi, kokarin tashi nake amma bani da karfi komawa nayi na kwanta na cigaba da kuka.


......... Sai da Nana ta kawo abinci Ummi ta koma dan tace matuƙar ta cigaba da ganina bakin cikina ne zai kasheta, Ummi da Abdul fushi suke dani, ina samun sassauci ta ɓangaren Fatima da Nana, Khalil da Khalila, Abba Lawan sau ɗaya yazo ya koma, dan Umma ta gaya mishi. Ganin halin da nake ciki ya ɗaga mishi hankali, dan sai da ya same Abba da maganata. Karshe yayi masa bibiɗi, suka rabu dutse a hannun riga.


Kwana na biyu aka sallame ni, koda na dawo gidan Abdul bai nunawa Matarsa muna rigima ba, sai dai ya ɗauke min wutane sosai. Duk sai na shiga damuwa, amma ina kokarin jan saura kimata da ta rage. Dukda naso kin biyewa Matarshi da take min iskanci, idan ina jin yunwa Atm ɗina nake ɗauka da keyn motana, tafiya gidan Abinci nake naje nasayo abincin da raina ke so.


***
Kwanaki sun haura satitika, satitika sun haura watanin, a yanzun kusan wata Huɗu babu Ashraf ba labarinsa, nayi kuka sosai gashi babu wanda ya faɗawa Nannah cikina ya zuɓe.


........ Duk iskancin da Sophia take min ban tankata ba, haka zata zo idan ina falo tayita habaici har sai na bar falourn zata hakura.
Wani abin da yake damuna, yawanci kamar jaka. Idan nasaka abinci a gabana sai naga bayan kwanu, ga kuma kwaɗayi. Idan naji kamshin girkin Sophia kamar xanyi hauka, amma dan rashin mutunci bata bani. Yau ina jin kamshin abincin da ya cika gidan na mike a hankali dan kwana biyu jikina nauyi yake min, ga ciwon jikn da bansan dalilinsa ba. Na nufi kitchen ɗinta tana fama da aiki na shiga da sallama nace.
"Don Allah Sophi abincinki zaki samin ko kaɗane"
Wani kallon banza tayi min sannan tace.
"Toh kwartonki bai kawo miki bane? Ko kuɗin da ake min burga ya kare ne."

Girgiza kai nayi cikin tsananin bukatar abinci nace.
"Dan girman Allah ki bani koda kaɗane kika ce na biya zan biyaki."


Dariya ta fasa tare da tafa hannunta tace.
"Wow kice kwartonki yana sake miki kuɗi, ok ga Acc numberna naji 50k"
Jikina na rawa na koma ɗaki ma ɗauko wayata na tura mata, tsabar wulakanci kuɗin na shiga tace.
"Zan baki amma sai kin min wanke wanke, ki wanke min kayana sai nima nasaka miki."


Sunkuyar da kaina nayi tabbas duk macen da ta zubda kimarta sai an wani gari sa'an kaninka shi zai sakaka aiki, murmushi nayi tare da cewa.
"Bani wankin, na fara dash.."


"Bazaki wanke ba! Ni Sophia kika ciwa mutunci yayata kikewa haka? Ba damuwa Didi jeki ɗaki zan kawo miki abincin da kuɗinki."


Kamar zanyi magana sai na fasa, shiga kitchen ɗin yayi itama ta ɓata rai tace.
"Ai nayi kokari tunda Uban da ya haifeta ya kor..."


Abincin ya ɗiba har yazo bakin kofa yace.
"Ki ajiye mata kuɗinta, sannan kuma ki haɗa kayanki idan zan koma zanyi ajiyeki a gidanku, aai kuma ina miki albashir da next week zanyi aure idan na kaiki ki musu bayani azo a kwashe kayanki.........


**** Ban kar zo man ba ...🏃
......
*(Ina kira gareku ban manta Ashraf ba, ina sane dashi babu yadda saudia zata yanke mishi hukunci har sai ta sami shaidu da kwarara akanshi ku biyo ni cikin labarin me cike da ban haushi da ban tausayi sadaukarwa soyayya, makirci hassada kiyayya rashin fahimta kyashi mugunta,munafuci zalunci, yaudara cin Amana)*

#MJ#HZƘ#Vote....




Oum Muwaddah....... 😎
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAƘA WRITERS ASSO_*


*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*






Page.٢٠
"Waye shi? Waye zai min iyaka da muradina? Na rantse sai na kashe su."


Tura kekensa Amir yayi tare da barin ɗakin, da gudu ya riko keken Amir Yace.
"Waye shi?"

"Ko waye ne baya bukatar gabatarwa, idan lokaci yayi zaka ga kowaye."


Yana gama faɗar haka ya tura keken yayi gaba abinsa.
Wato wani irin rikici ya ɓarke a kasar jordan, dangane da mulki wanda yakai duk wanda yayi tari akayi akan mulkin sunanka matacce. Tsabar mulkin zalimci kuma kujerar gata nan amma ta haramci mutane dayawa.
Dan haka sai aka fara samun yan hatsaniya da yamutsi. Wanda ya kuma sabunta rigima a tsakanin mgadarar masarautar suna tankawa junarsu. A gefe guda kuwa Banu Nazir da Banu Hussein suna nan suna nasu shirin..
.....
Sati biyu kenan da Ghaniyu ke niman Ashraf bashi ba labarin,, ya damu sosai da rashin samunshi a waya.
***
*Nigeria*
Abuja.....
Kwana na goma kenan laulayi ya sani a gaba, bana iya cin kome sai ruwa aketa ɗaura min, magana me tsawo ma bana iya yinshi sosai. Ga zubda yawu amai kam ba a magana. Bani da karfi a jikina sai yadda akayi dani.
Ina matukar jin wahala, har na tsani cikin da me cikin dan wallahi da zanga Ashraf a gabana zan iya mishi abinda ban tsammani ba. Dan ya gama lalata min rayuwata da kuma farin cikina.
....... Dafani Nannah tayi , ajiyar zuciya na sauke sannan na k'akaro murmushi tare da sunkuyar da kaina. Dan yanzun ina matuƙar jin nauyinta,
Ledar hannunta na kalla naji yawun bakina yatsinke, agwalimace a cike da yar karamar bakar ledan nan, gyara zama nayi ina jin wani mugun daɗi ya cika ni.


Juyewa tayi a wani bowl ɗin da Ummi ta kawo min salat, ta wanko min A banɗaki ta kawo min,
Dake ɗakin da muke VIP Ward ne, mu kaɗaine a cikin ɗakin. Tunda na amshi agwalimar nake mata wani irin kallo, sannu na fara sha kamar nasami tuwo. Har wani lumshe idanuna nake, shigowar Abdul yasani buɗe idanuna tare da sakar masa murmushi. Dan ya zame min jiki bana magana sai murmushi, shida wata mace yaki ya matsa min naga wacece.
Sai lekata nake ina son ganin wacece, karshe matsawa yayi.
"Ummina ce"
Wancakalar da bowl ɗin nayi tare da dira da karfi naje na rungumeta, kuka ne ya kwace min. Rungume ni tayi tana buga bayana, cikin mita Abdul yace.
"Yanzun dan girman Ubangiji meye haka, baki san akwai abu a tare dake bane, wallahi wannan tsalle kamar a zuciyata kika yishi. Kuma ina kishi, kuma ina taya babyna jin b...."


Wani irin kallo na masa, dan duk abinda ake bana kaunar maganar cikin, kauda kaina nayi cikin kuka nace.
"Wallahi idan bai zo ba zubda cikin zanyi dan cikin y."


"Wallahi kika taɓa lafiyar cikin nan sai kin kare rayuwarki cikin bakin ciki da nadama,, kuma na rantse wani abu ya faru da cikin ni dake ne, nonsense."
Haushi yasashi ficcewa,
Kukane ya kwace min, Nannah ta maidani bakin gadon, cikin damuwa zatayi magana na dakatar da ita.
"Nannah! Meye laifina dan nace zan zubda cikin nan, Ummina nifa taimako naje. Na gaji da ganin Nannah tana zubda hawayenta, Ummi nasan keda Nannah zaku fahimceni. Wallahi ba yadda kuke tsamani bane na same shi tunda yazo a haka me zai hana na zubda shi."


"Waye me cikin?" Inji Ummina.
Kaina a sunkuye, na ɗago shi cikin rawan murya nace.
"Ba zakiyi fushi dani ba? Idan na gaya miki."
"Akan me zanyi fushi dake? Ai da zanyi da ban saurareki ba kamar Yadda Abbanku yayi miki haka zan miki."


Kallon Nannah nayi cikin kuka nace.
"Am sorry Nannah!"
Girgiza kai tayi tare da nuna min tana ji na.
Shigowa Abdul yayi yace.
"Ummi naga kiranki."
Bata bi tankashi ba, kallonshi nayi tare da mika mishi hannuna, zuwa yayi tare da rikewa, ya zauna a kusadani. Daura kaina nayi a bisa kafaɗarshi kwalla nabim fuskana lumshe idanuna yayi tare da fashewa da kuka sabida hango ranar nake a idanuna, da yadda nayita rokon Ashraf yakyaleni amma abin yaci tura, haɗiye kukan nayi amma naki buɗe idanuna nace.
"Cikin..."
Shiru nayi tare da mugun fargaba ya cika min zuciya, matse min hannuna Abdul yayi cikin kwarara min gwiwa yace.
"Faɗa Safina, kina inda baza'a kalubalance ki ba. Karki ji tsoro mun yarda da kaddara me kyau ko mara kyau muna tare dake,"


"Na Sultan Muhammad Ashraf bin Abdullah Alhashmiyya."

Mikewa Nannah tayi jikinta na rawa, ta riko hannuna cikin wani yanayi, tana kallona kawai sai tasa sake hannuna tabar ɗakin baki ɗaya, tasowa Ummi tayi tazo inda nake ta kifa min mari, Abdul zai tare ta daga mishi hannu, ta kuma ki faɗa min mari,
"Ummi"
"Hmm" tace mishi.
Sake kifa min marin tayi na sake wata gigitacciyar kuka nace.
"Na tuba nabi Allah da manzonsa na biki."
Iska taja sannan ta kare min kallo, tace.
"Ko yanzun na rage nauyin da yake dankare cikin zuciyata, da kika san jordan zaki me yasa baki gaya min ba, shine marin farko da na miki na kigane rashin gaya mana zaki tafi. Mari na biyu, da kika tafi da kin kira kin shaida mana halin da kike ciki da bazamuyi kasa a gwiwa ba, zamu cigaba da miki addu'a har Allah ya dawo dake ya kuma kareki dagq duk wani mugun abu. Mari na uku, shirun da kikayi bayan Abdul ya gano kina da ciki da tun lokacin kik gaya mana cikin waye, ba maƙawa Abbanku bazai fusata ba gaki kin girma amna har yanzun tunaninki irina Anas ne, shashashar banza shashashar wofi, kawai kin jefa zukatarmu cikin fargaba, kinsan yadda nake kwana kuwa, idan na tuna cikin jikinki. Ji nake kamar ana cenawa zuciyata wuta, ina son nayi barci cikin salama abu yaci tura da zaran na kwanta kukanki ne yake hanani rintsawa gani nake kina fama da ciwo a rayuwarki, sabida ke yau har sake ni Badaru yayi dan na nuna mishi ke nake so sama da kome, kin barni ina tuninan baki san waye Uban cikinki ba, tunda ance mana kin shiga yanki Syria, ashe Safinah bakinki cike yake da magana kike kallon kowa ganga ba rufe, wallahi kin ɓata min fiyye da kima, kin sani cikin zulumi. Kinsani naji na tsani kome raina, Ya Ubangiji karka ka mata da laifin wahalar da zuciyata ya Allah ka kawo mata karshen wahalarta Allah ya shirya mana Zuri'a alummar musulmi baki ɗaya. Sakarya kawai."
Tana gama gaya min haka taficce Abdul yabi bayanta, komawa nayi na kwanta, hawaye nabin gefen fuskana, sosai nayi kuka tare da ɗan da nasanin abinda na aikata.
Na jima kwance ina kuka, jin kaman wani na kusadani, yasai buɗe idanuna, Anim nagani zaune idanunshi sun kaɗa jajjur.
Tashi nayi na zauna tare da takure kaina guri guda, domin yanzun idan ba Abdul ba bana kaunar na keɓe da wani namiji.
Tashi yaƴi yaje ya rugo kofar, ya shiga tawowa yana ɓalle botton ɗin rigarshi, ja da baya nake. Cike da tashin hankali na fara girgiza masa kai cikin kuka nace.
"Karka min haka Anim! Wall.."


Zame wandonshi yaƴi ya kuma tun karoni, juyawa ɗakin ya fara min kafin wani lokaci duhu ya rufe min ganina baki ɗaya, gyara wandonshi yaƴi tare da rigarshi ya share kwallarsa. Zuwa yayi ya zauna yana kallon yadda na kara kyau, kwalla ne ya zubo mishi daga idanunshi. Shafan fuskana yayi cikin raunanniyar murya.
"Wani irin kaddara ce ta rabani dake? Me yasa cikin bai zo a kaddararmu ba yazo a kaddararki ke ɗaya, yau kwana goma barci ya kaurace min, bana jin daɗin kome sai tunaninki, matata da ta dame ni korarta nayi, Why Kyari? Ban kai irin namijin da kike buƙata bane da zaki samu. Nasan nafi wanda yayi miki wannan illar kome, dan nayi imani ina da makamin da zata cika miki kugunki ba sai kinyi tunanin wani namiji ba, sannan na miki Alkawarin zama dake har da yaron cikinki dan Ina sonsu Allah ya nufa a can zasu fito dan haka y'ay'ana ne daga wannan na cikinki har wanda zai zasu zo bayan aurenmu.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login