Showing 51001 words to 54000 words out of 100319 words

Chapter 18 - Masarautar Jordan Book 1 Complete Document .txt

cikin mugun kewar rashin kunyarta, juya bayanshi yayi, yana tuno abubuwan da ya shiga tsakaninsu, musaman lokacin da yayi mata fyaɗe. Da zaran ya tun kareta zata sume mishi. Ba karamin tausayi ta bashi ba, dan yayi imani idan ba ita ba baya tunanin akwai macen da zata ɗauke shi, sai ita kuma baya jin sha'awar wata mace, tun bayan faruwar kome. Shi yasan sha'awarta yake a yanzun dan haka koda yayi nisan kwana, bazai tirsasa mata ta zauna dashi ba, amma zai nemi alfarma kodan albarkacin ɗansu ko yarsu ta zauna dashi idan taki kuwa zai kwace abinsa, yazo ya reni shi da kanshi yadda.


"Ashraf!!?"
D'ago kanshi yayi a hankali sannan ya mik'e.
"Lauyanka na jiranka!"
Mikewa yayi daga gadon, sannan ya fito zuwa inda Lawyer yake, zama yayi yana kallon lawyer, har lawyer ya. Buɗi baki zai magana. Ashraf yace mishi.
"Ghaniyu! Kodan na rayu da abinda ke cikinta."
Sunkuyar da kai Lawyer yayi cikin mutuwar jiki, yace.
"Yallaɓai! Ina me baka hakuri da abinda zance, a halin yanzun an nime Safeenah an rasa, dan an saceta."
Lumshe idanunshi yaƴi sannan ya gyara zamanshi, kauda kai yaƴi sannan yace.
"Idan Ghaniyu yaki baka haɗin kai ka sace kanwarsa sannan ka shiga ɗakina ka buɗe Computer makulinsa shine Baiwata (My Slave.) dashi number zai haɗa maka da hotunanrta sai ka kajerasu yadda zai bada harufar baiwata."
Yana gama faɗar haka ya mike yabar gun. Yaki bawa lawyer daman ya tambaye shi, sabida kar ya hango tashin hankalin da yake cikin kwayar idanunsa ne.

***
*Atlanta Ocean*
Sati biyu da satoni, ina kwance nayi wani irin kumburi na fitan hankali idanuna sun shige cikin fuska, hakan ya farune sakamakon tunanin da nake yawanta yi, tashi nayi na jingina da gadon. A hankali na sauke kwallar dake cikin idanuna. Na sauko a gadon fitsarin da ya cika min mara naje nayi sannan na dawo. Tare da zama a kasa. Kurawa guri ɗaya ido nayi hawaye nabin fuskana, da mugun gudu.
Murɗa kofar akayi, na juya ina kallonshi sannan na kauda kaina.
"Tashi muje ga likita can na jiranki."
A sannu na mike dan nima ina son ganin likita yau kwana uku yaron cikina baya motsawa yadda ya dace.
Ina fita likitan ya fara min tambayoyi, ina bashi amsa. Sannan ya gwada jinina nan yaga hawansa 199 saukar shi 180, kallon Anim yayi cikin damuwa yace.
"Idan ba akaita asibiti ba za a iya rasa Uwar da abin cikinta, dan jininta ya haura sosai. Kuma kaji cikinta bai kai Bakwai ba balle muce zata iya haihuwar prematura."
"Kawai ka bata magani amma batun kaita asibiti bai taso ba."


"Ok!"
Magani ya rubuta sannan yace.
"Ayi kokari a nimo sannan aƙwai yunwa sosai a tare da abincin."
Fita likintan yaƴi Anim ya bishi da ido, sannan ya sauke a kaina. Zai magana, nace.
"Ina haɗaka da Allah badan ni ba, dan sonka da Annabi kabarni na tafi Mahaifiyata da abin cikina kabarni na koma cikin dangina, idan kai min haka tabbas zan iya amincewa kana kaunata amma idan kaki amincewa. Zan maka kallon baka kaunata, Amma zan gaya maka wani abu kasani hakan da kaƴi baxao taɓa baka ni ba. "

"Idan naki maidaki fa?" ya tambaye ni,
Murmushi nayi sannan nace.
"Tabbas zaka wayi gari ka tsinci gawata."
Ina gama gaya mishi na mike a hankali nabar falon ina kuka, dan iya cutuwa na cutu. Ni yanzun wallahi tsoron maza nake, kai hatta Ubana tsoronshi nake dan shima da girmansu tsofai tsofai yasake mana Uwarmu, tunda na shiga ɗakin nake kuka me cin rai, ga jagwalgwalani da yake son ranshi, ga muguntan da yake min. Zan iya cewa cikina rashin kuzarinsa ya faru ne tasanadin matseni da yayi a ban ɗaki, indai haka ake soyayya har abada zance nayi retire. Dan niso bai kareni da kome ba sai tulin takaici. Tunda gashi ina cin azaba a gun Anim, wanda bansan ranar karewarta ba, *Allah sarki Ummina*
Abinda nace kenan a raina, ina matuƙar kewarta da kuma kowa nawa, *Ayya ko ya Nannah zata ji*
"Da kike cewa mahaifiyarki, lokacin da kika tafi yawon tazubar kin tuna da ita? Ko yanzun da kike son ki juye mata abin kunya yasa kike tunata, Safina nifa abin arziki na miki bana tsiya ba, amma kike niman rabuwa dani, toh kome zakiyi kiyi amma bazaki bar nan ba sai da igiyar aurena, dan ko yayya nayi sake dake nayi mugun asara, tunda naji labarin Uwar kwartonki tana can ana bincike bata san mu yan Naija zuwa ɗaya mukewa abu mun mun gama ba, sannan ina son ki sani wayarki ma na wurgar da ita..........


*_Duk wani fararre abu zaka samu yana da dalili da kuma hujja, nasan ban kyauta muku ba amma iya adadin kuskurena zaku duba da kuma kyautarawata zaku ga akwai rata me tarin yawa,karku sake jikinku ga wannan alamarin dan bana son cin amanar zuci ya faru tsakaninmu ina muku fatan alkhairi........._*


Oum Muwaddah..
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAƘA WRITER'S ASSO_*


*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*


*_Wai me akayi tukun bamu gama book one ba har kun fara gajiya hmm da naso da Rayuwar Safeena zan kira book ɗin amma sabida shiga Ahalinta Masarautar jordan yasani ambatar labarin haka duk abinda ake a nan ba kome bane idan zaku iya hakuri ku bini toh bismillah dan labarin ba takaitacce bane kamar sauran shi yasa nace muku ya sha banban da sauran👏_*

YAUSHE NAYI ALLAH YA ISA A BOOK Ɗ'IN MJ😏.....
Page.٢٦
"Kuma wallahi bazan fasa kudirina ba" ya faɗa yana zare idanunshi, kura mishi ido nayi ina jin ba daɗi yau Abbana shi ya juya min baya mutumin da yake kokarin saya min farin ciki da hannunshi da dukiyarsa, yau shine yake juya min baya.


"Bar kallona da kifi-kifin idanunki kamar na yan matan ɓera, shaiɗaniya kin rabani da mata ta da d'ana har mutanen arzikin baki bar min su ba, Anya Safeenah ba canza min ke akayi ba a can inda kika je yawon banzanki." Allah tijarar da Abba yayi min ba sauki dan nayi kuka sosai nayi danasanin tafiya jordan yafi sau dubu, wancan makaryacin kuwa na mishi Allaj ya isa yafi sau ɗari, ga Anim wanda banda kar ace min zararriya da ina tashi rufeshi da duka zanyi mugu azzalumi.
Ahankali barci me nauyi yayi gaba dani.
....... A iyakar rayuwata bansan meye kunci ba sai da nasaka kafata a kasar jordan, tun daga ranar da Ashraf yayi tarayya dani kome nawa ya wargaje, na rasa farin cikina na rasa duniyata kome na rayuwata. Ya lalace, ji nake kamar na gudu na bar kowa naje naƴo rayuwata ni ɗaya.
Dan rashin kunya Anim har gida yaje ya sami Abba, suka gaisa sannan yayi kasa da kanshi kafin yace.
"Abba dama akan Safeenah nazo kayi hakuri da abinda ya faru da ita, babu wanda ya isa ya tserewa kaddarar sa, indai haka ne kaddarar. Ni naji na gani ina sonta dan wannan rabon cikin ya kaita can kuma nasan wacece ita bazata taɓa watsi da tarbiyanku ba, tunda ba yau tasaba zama wani waje, da halintane tabbas da tun tuni ta tarama jikoki sama da haka don Allah ka dubeta da idon rahama ka sassauta mata, ni ina sonta kuma zan kula da abin cikinta idan ta haifa,"
Da wannan maganar Anim ya gama kashe Abba, ya kuma dinga amayarwa Abba yadda ya hau bishiyar kace, a kaina suna cikin haka Mamie tazo tana ganin Anim ta shiga ɓara ɓare tana jin abinda yakawo shi take ta shiga masa kamfe, da zai tafi ya ajiye mata kuɗi me mugun yawa, ai kuwa baki yaki rufuwa, bayan tafiyarshi ta dubi Abba tace.
"Gaskiya yaron nan d'an gidan albarka ne kaga zuwan yau kawai ya ajiye min dubu ɗari biyu, nan gaba bansan me zan samu ba, Allah yasa kar Maryam ta mata bakin ciki dan naga bata gaji arziki ba sai tantagaryan tsiya da talauci."


"Hmm! Ai ina ɗaga musu kafane sabida Uwargijiyata in ba haka ba abinda zanwa maryam sai garin Abuja ya ɗauka toh babu yadda na iya ne, basunce cikin na Ashraf bane bari muga abinda zata haifa, tana haihu babu batun shayarwa zan ɗaura AURENTA da Anim."


Haka sukaita tattaunawa har lokaci yaja sannan Abba ya bar gidan.
***
Wani shishigin da Anim yake a cikin Yan uwana ya wucce misali dan tsakaninshi da Allah yake nuna kulawarsa A kaina. Muna cikin wannan halin aka kira Nannah daga Oman babu dogon shiri ta haɗa kayanta ta koma can.
A yanzun hankalin Ummi ya kwanta da Anim sabida irin hidiman da yake min, ga baki ɗaya. Da zaran yazo Ummi zata fita tabarmu, tana fita zai zo ya sani a gaba da iskanci. Kamar zan mutu dan bakin ciki sai dai bani da yadda na iya tunda ba gane maganata ake ba, babu abinda ke kara min takaici kamar yadda ya takurawa nonuwana, da zaran Ummi ta bamu guri toh zaija kujera yayita murza min so, na gaji sosai yau ma kamar kullum yana zuwa Ummi tana bani abinci suka gaisa, rike mata riga nayi. Kwalla ya fara sauka min, wanan na sauka wani na koro wani.
Ganin zatq mike na maza na rike zaninta ina girgiza kaina, dawowa tayi ta zauna, na ɗaura kaina a jikinta ina sauke wani irin kuka mara sauti, ajiye filet ɗin tayi ta shiga shafa kaina har nayi shiru. Kallona yaƴi yana min kallon kasa kasa, ni kuwa na tura mishi bakin dake gefe guda. Lashe lips ɗinsa yaƴi sannan ya sunkuyar da kanshi. Sama sama yaƴi hiran sannan ya tafi gidanshi dama zuwan dare yake.
Yana fita na sauke ajiyar zuciya, kallona tayi cikin nutsuwa tace.
"Baki son zuwansa ne?"
Gyaɗa mata kai naƴo, idanuna akan abarban data yanka min da gwanda da kuma kankana,, tashi tayi ta ɗauko ta fara bani ina sha ina kallonta, a hankali na motsa bakina nace.
"Am sorry Ummina"
Kallona tayi sannan tace.
"Kince wani abune!"
Rike cokalin nayi na ɗiba itama na bata, girgiza kanta taƴi sannan ta shiga bani.
"Eyye ɗaurewa bariki gindi! Tayo shegen ma ana riritata, kai Ni naga duniya ni Nuratu Alhaji yaron nan Anim yaƴi kokari da Jahadi dan ni ina tsoron kar a lakatawa ɗan uwana damuwa, Uwa da y'a sun zauna suna soyawa. Kagani ba ita murna take dan yarta ta ɗauko magana."
Take fuskar Abba ya koma tankar red emoji, sai hura hanci yake, yanawa Ummi wani kallon hadirin kaji. Irin lallai ma kun renani.
Daga ni har Ummi shiru mukaƴi zai fara tijarar sa, Dudu ya shigo Ajiyar zuciya na sauke, kallonshi Abdul yayi sannan yace.
"Meke faru?"
"Kaniyarka ce ke faru! Kaji min mara mutunci yaushe rabonka da kazo gaishe ni wato an muku ingiza me kantu ruwa, an rabani da y'ay'ana da a nuna min sanabe toh kayi maza ka dawo da yar mutanen da ka tura gidansu, dan iskanci akan wancar abar wallahi Abdullahi ka fita idona na rufe"
Shiru mukayi har ya gama sauke buhun masifarsa sannan ya ficce shi da jelarsa.
D'ago kai Ummi tayi tana kallon Abdul, wanda ya sunkuyar da kanshi. Jikinshi yayi masifar sanyi yace.
"Ummi Am sorry! Naso na gaya miki amma kuma.."


"Karka damu, ai tayi laife ne kuma ko zaman gidan da tayi yaci ace tasan laifinta kayi kokarin dawo da ita in ba haka ba yadda naga Abbanku ya koma zai iyawa kowa rashin kirki bavu ruwansa. Kuma ba damuwarsa bane yayi maka a gaban kowa don Allah ku kiyayye abinda zai ja muki rigima da shi."


"Thank you so much."
Ya faɗi haka tare da ɗaura akanshi a kafaɗar Ummi yana min gwalo.
Murmushi nayi nima na masa gwalo.
***
Yau ma kamar ko yaushe idan yaje yawonshi zai dawo yaƴi wanka a cikin gidanshi, tana zaune a bakin gado ya fito ɗaure da towel a kugunsa hannunshi ɗaya rike da karamin towel, yana goge kanshi.
"Zargina ya zama gaskiya! Kana zuwa waje kayi lalata da yan mata sannan ka dawo min gida kana wanka sabida rashin adalci Anim meye na rageka dashi? Da har ka gwammaci kaje waje kayi lalatarka sannan ka ɗibo min datti zuwa gidana."
Dan wulakanci irin na mijin bahaushiya. Ya Kare mata kallo yana kuma dubata sama da kasa sannan yace.
"Dukda tafiki a shekaru, amma nonuwarta kullum a tsaye suke kamar zasu tsone maka idanu, idan ka taɓasu tankar audiga. Laushin fatarta kuwa ya wucce ayi misalinsa, bakinta kuwa idan kana sumbatarta kamar alewa aƙa saka maka a ciki, ban taɓa ganin macen da ciki yayi mata kyau irinta ba, ga sura kamar ita ta zaɓa tayiwa kanta, dukda kinfita kyau ita kuma tafiki cikar halitta."
Kura mishi ido tayi bata san lokacin da hawaye ya fara zubo mata, cikin kuka tace.
"Wacece haka ?ka gaya min ita wani irin tsafi tayi maka da kake da na roketa ta faɗa min inda taje nima naje a karya ko zaka kalle ni a matsayin mace."
Tsaki yayi tare da zama a kan stool ya ɗauki cream ɗinsa ya fara shafawa, kaman bazai magana ba yace.
"Safeenah"
"Safeenah!!!?" banza yayi da ita kankamce idanuta tayi cikin zallar kishi da bala'i tace.
"Wallahi ba zaka taɓa auranta ba sai dai ayi babu kai."


Tsaki yaƴi cikin ko in kula yace.
"Fita min a ɗakina barci zanyi."


Fuuu ta fita abin na masifar kona ranta, wato ta hanashi ya aurota shine yanzu suke baɗalar a waje. *Kai Allah ya isa min* tace da muguɓ karfi kallon hoton aurensu tayi ta ɗauki wani turarenta ta jefi hoton saida glass ɗin ya tsage tare da zubowa.
Kuka ne ya kwace mata tanayi tana fasa kome na ɗakin ga alwashin da ta ɗaukarwa kanta matukar tana raye.
***
Daga Asibiti Gidansu Sophia Abdul ya nufa, tunda yayi sallama. Aka ce ya shiga falo ya zauna yana jiransa aka kawo mishi ruwa bai taba ba ya cigaba da jiranta can sai gata tafito rike da Affan kauda kanshi yayi daga kallonta ya mikawa Affan ɗin hannu da gudu yaron ya shige jikin babanshi. Cikin sanyi jiki ta zauna a kujeran dake kallon nashi, dukda yana cikin matsanancin kewarta haka bai sashi jin tausayinta ba, zamewa tayi daga kujeran ta fashe da kuka sosai, yana jinta kamar bazai kula ba , ya mike yacewa Affan..
"Jeka gurin kaka ta baka bobo."
Da gudu yaron ya fita, maida dubansa yayi gareta sannan yace.
"Kin sani a gaba da kuka zan tafi fa."
D'ago manyan idanunshi yaƴi ganin yadda ta rame yasashi tambayar lafiyanta kuwa.
Nan take bashi labarin bata da lafiya, amma da sauki.
"Hmm! Me yasa kika saka a ka kirani"
"Ina so zan koma ɗankina ne don Allah "
Kura mata ido yaƴo yana kallon yadda take motsa bakinta yayi, ɗauke kanshi yai tare da jan wani mugun iska tare da fesar da iskar bakinshi, yana matukar kewar matarsa da ɗanshi amma baya jin zai maidata cikin sauki, kauda kanshi yayi sannan yace.
"Kin manta keda bakinki kika ce na zauna da yar uwana ta maye gurbinki, ina ga kin mantane ƙuma gashi na tuna miki, duk ranar da kika san yadda zaki gayawa mutum magana zan dawo dake, ko kuma kije ki roki wacce kika wulakanta, idan ta yafe miki maybe zanyi tunani akanki da kuma makomar rayuwarmu."
Yana dire mata aya yq mike zai fita da gudu taje ta rungume shi ta baya, tana kuka tare da cewa....🏃🏃🏃🏃😂




*Kuna nan kun zuba ido muna jira.... Anya nan gaba bazaku juya min baya ba😢😭*
















Oum Muwaddah.....
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAƘA WRITER'S ASSO_*


*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*



*_Labarin daban yake da sauran._*



_FATAN ALKHAIRI ZAINAB MUSTAPHA nagode da kauna🌹_


ZAUREN MAI_DAMBU KU BAR KULA UMMU MUH'D.... Dan na lura da ita duk sai ta mannawa kowa hawan pure water😂 Ina gaida uwar dakin Anim bayan My Zahra yau ga wata me kare yan ta'ddan novel😹
Page.٢٥
Kwanciya nayi tare da juya masa baya,zuciyata na zafi ji nake numfashi na kamar ina kokuwar dawo dashi, cikin ikon Allah da ambatonsa, duk yadda naso kuka na kasa, haka na cigaba da kwanciyar ina jin ɗan motsi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login