Showing 36001 words to 39000 words out of 100319 words
Chapter 13 - Masarautar Jordan Book 1 Complete Document .txt
fito falour dan sun fita abincin aka bar min a ciki,, fitowa nayi nima da abincin na zauna a tsakiyar falourn, ina zama Abbanmu na shigowa.
"Ina kwana Abba!"
Zama yayi a kan kujera ya amsa da " lafiya ya jikin naki"
"Da sauki" na bashi amsa a takaice,
Nan sukayita hira da abokan aikina, ni dai bana iya dogon magana sabida amai.
..... Can suka mana sallama zasu tafi, tambayata sukayi yaushe Zan koma aiki nace musu wata sati.
...... Ga baki ɗaya wani irin kulawa nake samu daga iyayena har ƴan uwana, jikina kam da sauki babu duƙ abinda yake min yanzun wani mugun kwaɗayi ke ɗawainiya dani, musaman Nanah da Abdul.
Kuma cikin ikon Allah babu wanda ya tambaye ni, ina naje har yan uwan Ummi suka koma, aka bar Hajja kaka kuma dama tana zuwa ta huta sai ta koma.
Satina ɗ'aya na koma aikina, xuwan Anim gidanmu sau uku naki masa magana asalima bana fita sai na kwanta nayi barcin dole, yau muna gama aiki muka fito zuwa sallah, yaxo ya sha gabana.
"Feener Kyari ki faɗa min me kike nufi dani? Laifin me nayi miki da zafi?"
Gefenshi na raɓe zan wucce naji ya riko hannuna bansan lokacin da na ture shi ba, cikin ɓacin rai nace.
"Dole ne? Ka rabu dani tunda kaga naki kulaka."
Daga haka nayi wuccewata kowa na mamakin yadda na mishi wulakanci.
....... Haka nake zuwa aikina duƙda na fara fuskantar matsaloli daga Anim bai dame ni ba, dan ba zamansa nake ba.
........
Muna zaune ni da Muwaddah da Sabirah, sai tsiya suƙe min wai na gaya musu wani magani nake sha ne nayi kiba haka, dariya nayi nace.
"Shaka fashe."
Sabira ta fashe da dariya sannan tace.
"Ni kuwa yanayinki kama da masu ciki yake min."
Dariya nayi nace.
"Ba'.."
Maganarce ta makale sakamakon faduwar da gabana yayi, ina yunkurin mikewa Anim yana zuwa, da sauri na ɗauki jakata na fita bina yayi da ido, shima ya biyo bayana da sauri kafin ya iso, har nayi ribas da mugun gudu sai yanzun abubuwan da suke faruwa ya dawo min kaina, dakyar na isa asibiti dake a rikice nake, har na shiga ban tsaya tunanin inda nazo ba, asibitin da Abdul yake aiki nazo fa. Tsabar ruɗewa.
Ina kan sai share kwalla nake, har Wani abokin Abdul yazo wuccewa, yaga ina kuka shine ƴaje ya gaya mishi kaina a sunkuye, sai ji nayi an riko hannuna, dago kaina nayi naga wani sabon kuka ne ya kwace min, dago ni yayi muka wucce ofishinsa, zaunar dani yayi a kujeranshi. Ya durkusa a gabana ganin yadda nake kuka wiwi, ya kura min ido sannan yace.
"Safinah meke damunki?"
Muryana na rawa nace.
"Nazo ayi min test ne!"
"Test ɗin meye? Za a miki?"
Rufe bakina nayi da hannuna, ina girgiza kai nace.
"Kusan wata ɗaya da wasu kwanaki bangan shi yazo ba"
A ruɗe ya mike yace.
"Kwanta a wancan gadon."
Jikinshi na rawa ya kunna computer scanner ɗin, sannan ya sani ɗage rigana ya zuba min luquid ɗin, ya ɗaura abin ya hasko mishi Abinda yake son tabbatarwa, dan tunda ya ɗaura nace "wash"
A hankali ya shiga duba kwanakin cikin, sati shida cif.
"Cikin Sati shida Why Safina?"
Wani irin gigitacce kuka ne ya ƙwace min ina girgiza kaina.
Wayarshi ya ciro ya shiga niman number Ummi, ya kirata.
"Don Allah kizo karki gayawa kowa."
Juya bayana nayi, na kuma cigaba da kuka, tun daga ranar da abin ya faru nake kuka har iyau kuka nake, sallamar Ummi yasake kara kuka na, kujera ya ja mata ta zauna, zuɓewa yayi a kasa gwiwarshi duk a kasa, sannan ya ɗaura kanshi bisa cinyarta, a hankali tashiga shafawa kanshi, zuciyarta na rawa.
"Abdullah! Meke faru?"
D'ago kanshi yayi kwalla na zuba daga idanunshi ya rike hannunta cikin kuka yace.
"Ummi! Shin bayan uwa akwai mutumin da zai iya jure zafin fitar ɗ'a daga jikinsa?"
"Babu Abdullah uwace kawai take jure zafin fitar ɗanta a jikinta"
"Ummi indai har haka ne tabbas babu uwar da zata gaza tsayawa d'anta, indai har zata iya tsaya masa tabbas ita kaɗai ce zata yarda da kaddararsa, indai har haka ne itace kawai zata iya amincewa da bukatarsa, indai har haka ne itace zata iya share masa kuka, Ummi duk duniya bamu wata bayan ke, Ummi indai har kika amshi kaddarar da tasamemu nayi.Imani da Allah bazaki taɓa ta gaiyara ba."
Shafa kanshi tayi cikin karfin hali tace.
"Ina jinka!"
"Ummi!!!!"
"Na'am!!!"
Nuna mata gadon yayi cikin kuka yace.
"Tarbiyarki ce! Renonki ce! Shekara ɗai ɗai har talatin bata taɓa saɓa miki ba bata tab'ayin abin Allah wadarai ba, sai gashi a cikin shakara na talatin da d'aya tazo miki da kaddara shin zaki amsheta."
Kallona tayi zuciyarta na wani irin bugawa,
. Sannan ya cigaba da cewa.
"Ummi baki ce kome ba"
Murmushi kawai ta iya sakewa akan fuskarta.
Goge kwalla yayi sannan cikin karamar murƴa yace.
"Cikin sati shida gareta."
Rike hannunshi tayi da mugun karfi tana ambaton sunayen Allah sai ta tayi guda ɗari ba ɗayan nan cif kafin ta iya buɗe idanunta da ta runtsa, mikewa tayi ta gyara hijab ɗinta tace.
"Tasauko muje."
Jikina ba kwari na sauka a gadon na ɗauki jakata, koda muka fita ban iya jan motana ba.
motar da ya kawo Ummi nabi kwanciya nayi a baya, idanuna suƙa cigaba da kwalla, muna isowa ana fito da kayan Anim da ya kawo na aure, aka zuba a mota.
Da sauri na shige cikin gida, ina saka kafana a falourn kunne na jiyo min........
#MJ#HZƘ#VOTE.......
Oum Muwadda......
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAƘA WRITERS ASSO_
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*
Sadaukarwa ga Ummu Sayeed naji daɗin Yadda kika tafi bincike Yasin wasu rubutun kawai suke karantawa basa bincike balle su tabbatar da labarin gaskiya ne ko karya ne,😂
Page.١٨
"Alhaji Idan karya aka mata ai gata nan ka tambayeta ba da kanka zata faɗa maka,,
"Zo nan uwata!!"
Wani irin rawa jikina ya ɗauka tare da mugun tsoro da firgici, juyawa yayi ya haura sama.
Ban taɓa sanin haka yan matan da sukayi ciƙi a waje suke fuskarta tashin hankali ba, sai yau da ya faru a kaina. Rike Ummi nake cike da tashin hankali,
"Sai anyi magana ace lokacine bai yi ba, nan kuwa ana yaudaranmu ce da cewa miji bai zo ba, ashe anje gun wani katone ya zuba nasa basirar." Inji Mame Hjy Nuratu.
Lumshe idanu Ummi tayi da gudu Abbanmu ya sauko ganinshi ni kuwa na nime guduwa D'akin Ummi, cafko ni Mamie tayi tare da falla min mari. Akan fuskana. Sam idanun Abba ya rufe kawai ya rufe ni da mugun da wayar chajin laptop ɗin, zafi da azaba da suka gaurayani, kai ko dukar da samudawan Jordan bai taɓa tsoratani ba kamaemr dukan Abba kodan akwai tsoro ne a raina yasa duk na firgice.
"Ai gwara ka daketa yarinya ta zama annobar mace, mahaifinki na zaman lafiyansa kinje kinje ki ɗauko mishi ɗan gaba da fatiha, sai anyi magana ace ai mijine bai zo ba makira kuwa kinje sun gama dake shine zaki kwaso abin kunya ki zo masa da shi wannan da nice na haife ki yau zaki bar min cikin gidana dan ba zan iya rikon asara ba.."
A yadda na fahimci Abba babba burinshi bai wucce dukar cikina ba da kafarshi, ina gano nufinshi nayi maza na k'amk'ame ummi, jikina na rawa nace.
"Ummina ki cece ni bazan kuma ba. Wayyo Allah Ummina bazan kuma ba."
"Kaji ko Alhaji! Uwarta take niman ta kareta." inji Mamie.
Finciko ni yayi Ummi ta rike ni gam, cikin hargagi da kuma ingiza me kantu ruwa, yace.
"Maryam! Saketa ko kuma ranki ya ɓaci"
"Rayukarmu ne zasu ɓaci, ban hanaka hukunci ba, amma idan zakayi ka fara aiki da hankali yafi aiki da agogo, a cikin shekarun da tayi. Bata taɓa yin abinda zai ɓata maka ba, tun tasowarta take kare kanta, da sunanka. Shin d gangan haka ya sameta ko kuwa karfi aka gwada mata, yarinyar da ka ɗauketa zuwa ghana dan tayi karatu yau dan tazo maka da akasin kaddara sai ka juya mata baya, ka nunawa Ubangiji bai isa ya jarabeka ba, kanunawa Ubangiji baka da karfin Imani, kai Uba kenan ina kuma ni da nake Uwa."
"Wannan matsalarki ce! Alhaji idan baka ɗauki mataki ba hatta fita waje sai yafi karfinka, cikin shege taɓ ɗan gaba da fatiha fa. Da sakel an ba wa me kaza kai."
Gabaki ɗaya sake haukacewa. Abba yayi cikin tashin hankali da ɓacin rai yace.
"Nuratu! Ɗauko min wuka a kitchen idan ban kashe Safinah ba nayiwa kaina karya bani."
Abin nima ya samu, da gudu Mamie ta shige kitchen, sai da tayi rawa💃💃💃💃💃 "Shegiyar yarinya ta hanani rawan gaban hantsi yau dole ki bar gidan nan."
Da gudu ta ɗauki wukar tafita zuwa palour, karɓa yayi yayo kaina. Na fasa ihu tare da rike Ummina, kamar zata faɗi.
"Zaki faɗa min uban da ya miki ciki ko sai na miki yankan rago?"
Ya daka min tsawa, duk na kara rikicewa, jin ihuna yasa Umma da Hajja kaka suka fito da sauri, Nannah ta rufa musu baya. Finciko ni yayi yasa min wukar a wuya. Cikin kuka nace.
"Ummina karki tafi ki tsaya."
Cak ta tsaya ita batayi gaba ba, ita batayi baya ba. Taki kuma juyawa ta kalle mu, Nannah ce tasaka hannu ta amshi wukar, cikin ɓacin rai tace.
"Banda ina ganin girmanka, tabbas da na mareka wallahi."
Wurgar da wukar cikin zafin rai Hajja kaka tace.
"Yau naga jakar uba! Yo da kaɗauki zungureren wukar nan wata uwar zaka yi da ita"
"Hmm! Ai da zaku ji abin kunyar da yar gwal ɗinku tayi da bazaku ga laifinsa ba, domin d'an gaba da fatiha ne a kwance cikin mahaifarta." Inji Mamie ta faɗa tare da kumbura fuska tana hura hanci.
Tsaki Hajja Kaka tayi cikin ko in kula tace.
"Sai me dan tayi cikin shege! Ai gwara ita, wasu asalinsu idan kaji har duniya tatashi bazaka haɗa iri da suba, amma da kaddarar rabo ya haɗa aiki gashi ana zaune lafiya, wai kura na cewa kare mayye, yo wani dare ne jemage bai gani ba, ai sai daren mutuwarsa, abin kunya gaba ta bashi ba baya ba, kuma ba kanta farau ba, kuma ba akanta karau ba, wasu nasu kazantar ko kuda bazai so hawa kai ba. Balle yarinyar da tayi zaman a wata duniya na tsawon shekaru, dan yau ta dawo sai a nemi kashe min ita, don Allah yankata dan kwal ubanka, wato dan bani ce na haifeka ba, ka nuna min dan ban taɓa haihuwa ba shine zaka kashe yarka ko shawara dani bakayi ba ai da na gaya maka hanya mafi sauki da zaka kasheta. Ke Amnah ɗauko min igiya ya ratayeta ina ga irin wannan kisar ba a ciki tsananta bincike ba ko."
Wani katon harara ta masa sannan ta dawo kaina riko hannuna tayi, tare zaunar dani jikina bai fasa rawa ba, ta kalle ni cikin jin haushi tace.
"Yar banza da shege idanu kamar yayan kurna, taya kika bashi ya ɗirka miki ciki, yo yanzun da duniya ta cigaba, aiko wannan kororon roba yasaka, codan yako ko me." (Just for fun😂 Hajja kaka wooo)
Sunkuyar da kaina nayi dan na lura yau barikancin hajja kaka ya motsa,
Taɓe baki tayi cikin ko in kula tace.
"Toh haka ma yayi koma me nene, duk ciki Yaran maryam kece me shegen taurin kai kamar ganda, baki jin ko fiɗis, da wasu soyayyun idanunki nan kamar soyayyer gyaɗa, kik cika fitina bana wasa ba, gaji duk hakurin irinta Badaru sai da kika sashi yaƴi miki biɗibiɗi, haka kawai kin zauna ana jibgarki kamar wata lusara. Shashashar wofi"
B'antara goronta tayi cikin nutsuwa tana taunawa, Umma tace.
"Wallahi Alhaji ka bani mamaki yadda, ka ware karfinka akan safinatu, yarinyar da tun tasowarta muke zargin aljanu ne da ita, shine zaka ware karfinka akanta dan wannan abun ya faru. A cikin gidan nan har kake zargin yarka dan kaddara ta faɗo mata, toh kasheta."
Ummi kan falon ta bari, bai kulasu ba ya nufi dakin Ummi, wacce ta fito ban ɗaki zatayi sallar azhar, cikin bala'i yace.
"Kice ta bar min gidana kafin na dawo."
Ko kallo bai isheta ba tasaka hijab ɗinta ta tadda sallah,
"Na gaya miki ta fita tabar min gidana"
Banza tayi da shi, har ya fito ya dawo cikin zafin rai yace.
"Idan kika fita, dan kareta ban yaf."
Mika alamuranta tayi ga Ubangiji ta cigaba da sallarta, tana idarwa ta shiga zuba kayanta a cikin babban a kwatinta, sannan tafito zuwa falon ta kalle ni yadda nake kwance na takura guri guda ina kuka, tace.
"Ki shiga ɗakinki ki kwaso kaƴanki."
Mikewa nayi na kalleta naga ta kauda kanta, girgiza kai nayi cikin tashin hankali nace.
"Ummi!!!"
Yatsar hannunta ta ɗaura bisa bakinta alamar nayi shiru.
Mikewa nayi naje nayi yadda tace,
Ina gama hada kayana najanyo akwatin na fito dashi, dai dai shigowar Nannah, a firgice tace.
"Ina zaki Binti"
Sunkuyar da kaina naƴi nace.
"Ummi ce tasani na fito da kayana!"
Riko hannuna tayi, na ɗago tare da kallonta, kwantaccen gashin dake gefen fuskarta sak da nashi, har ɗakin ta kaini tace.
"Maryam lafiya?"
Murmushi me ciwo tayi sannan tace.
"Yace tabar mushi gidansa, toh meye amfanin zamana a gidanshi tunda bai yarda da kaddara ba. Ni yanzun damuwata Safinatu ce, ko zata gaya min cikin waye."
Jingina a jikin bango na zame a hankali tare da sake kuka mara sauti nace.
"Allah na na cuce kaina ko na gaya muku cikin waye bazaku yarda b.."
Ji nayi an shure ni da kafa, tare da ɗago ni a zafaffe akayi waje dani, har bakin get ya cillani na zuɓe a gun.
Ummi naga itama tafito tare da Nannah, sam Abba kamar wanda ya fita hankalinshi, ranar wanda bai san meke faruwa ba ya sani, a gaban ɗinbu mutane Abba yace min.
"Kisaka a ranki ke matacciya ce, kin jima da mutuwa a cikinmu, bamu da ke a cikinmu, karki kuma takowa cikinmu kije duniya ta isheki riga da wando, kamar yadda kika kwarar min da mutuncina naki sai yafi nawa zuɓewa, kuma idan baki bar min kofar gida ba yan sanda zan kira miki, bana son ganinki."
Yana gama gaya min haka yasa key ya rufe gidanshi, ya kalle Ummi yace.
"Idan kika saka kafarki kiƙa tsallakw bakin get ɗin nan a bakin aurenki."
Zuwa nayi nayita buga get ɗin ina kuka tare da cewa..
"Don Allah Abbana karka kore ni, daga gareka don Allah ka rufa min asir..."
Ji nayi an riko hannuna, na juya a sannu Abdul ne idanunshi sunyi jajjur, yaja hannuna a har cikin motarshi, zanyi magana ya rufe min bakina da yatsar hannunshi.
"Ya isa muje gidana."
Gidanshi muka nufa wanda yake can doctors quarts, muna shiga get ɗin gidan Matarshi Sophia, ta fito fuskarta a murtuke ta tare kofar shiga gidan, wani irin kallo take mishi. A sani na Abdul yana da matuƙar hakuri da rashin son magana, kuma ban taɓa tsamani a kaina zai iya zarta da hukunci har haka ba sai da naji yace.
"Ko ki bani hanya na shige ko kuma ki wucce gidanku na sake ki sa..."
"Abdul!!!"
Na kira sunanshi a raunane, na girgiza mishi kai cikin kuka nace.
"Don Allah karka ka rasa, ni na hakura zan nime wani gurin