Showing 33001 words to 36000 words out of 100319 words

Chapter 12 - Masarautar Jordan Book 1 Complete Document .txt

dukiyar baitul mali, haka ba karamin d'aga musu hankali yayi ba, kuma dama Amir Ukshe yana can yana fatuttukar sai ya ɗare kujeran mulkin, duk da haka duk inda yaje maganar ɗ'aya ce bashi ba mulki sai dai ya zama jigo ga mulki.
***
Kasancewa Dr Ibrahim shine likitan masarautar, dan haka Sarki Yasir dashi yake shawara ga duk abinda yake faru a gareshi, inda yake faɗa masa abinda ke faruwa, abinda Dr Ibrahim ya ce masa shine.
"Suma kabilun ka basu shuwagabancin kabilarsu haka. Haka zaisa zasu fahimci mulkinka sannan idan da hali idan zakayi kaso a cikin masarautar ayi dasu. Kabilu guda biyun sun haɗa Banu Nazir da Kuma Banu Hussein. Dan haka suka amshi tayin abinda ya basu.


....... Bayan shekara guda da ba shi mulki, Amir Abu Zarri da Shugaban Kabilar Banu Hussein, Harris bini Hussein tare da wasu manyan Attajirai suka shirya meeting, akan basu son mulƙinsa, su shuwagabanin
Kabilun sun bada goyan baya ne dan yaki basu mukami a cikin masarautar,.Attajirai kuma ya tsawalla musu akan haraji. Yan kasuwa kuma yasasu sun karyar da kayansu sabida talakawa, abin bai tsaya nan ba tunda suka haɗa kai, basu nemi kabilar Banu nazir ba, gashi Amir Ukshe baya kasar yatafi can kasar china domin niman mulki.


A ranar da zai dawo a wannan ranar jerin shuwagabanin tare da jagorancin Amir Abu Zarri, suka kifar da mulƙin Sultan Yasir, garin ya kare kanshi suka masa kisar gilla.

Ana cikin jana'azartasa aka fara fuskartan matsaloli,


Lokacin Amir Ukshe ya shigo garin, yasamu anyi ambaliyar ruwa wanda ya kashe ɗinbun alumma, dan haka abinda ya fara an kara dashi kenan dan dama an faɗa mishi yazo ya kuma bar baya da kura, dan haka yayi maza ya koma kafin abin ya shafi kowa da kowa, koda yaxo sun gama abinda ya faru, kuma suka ɓoye mishi,
... Dr Ibrahim kuma suka sakashi a jirgi dan dole ya dawo kasarshi.


Bayan kifar da Yasir aka kuma sake shiga sabon muhawara, karshe dai Amir Ukshe ya bawa Abdullah me shekaru ashirin da uku mulƙin Jordan.


A lokacin Amir Ukshe da kanshi ya nemi Ibrahim ya dawo, sai ya turo Badar,"
D'ago kaina nayi na kalle shi, idanunshi sunyi jajjur, gashin goshinsa sun tashi ruɗa ruɗa,, murmushi nayi sannan na mike na zubda yawun na dawo inda yake na zauna sannan nace.
"Kasan waye Badar? Toh shi ɗin Mahaifina ne!!!"
Cike da mamaki yake kallona, kauda kai nayi, sannan na cigaba da cewa.
Kamar yadda suka maidaka haka suka maida Abbie ɗinka, sai da ya shekara uku suna juya shi kafin ya haɗu da Nana Asma'u, Mahaifiyarka. Tazo karatu nan, ranar da suka gama makaranta, suka haɗu da farko taki faɗa mishi ita wacece sai da yaga motar masarautar Oman, bai kuma bin takanta ba tana komawa ya tura wakilanshi, suka je masa. Ita kuma taki amincewa sai dai yaxo da kanshi.


Shiryawa yayi, ya tafi har Oman tun daga karɓan da aka masa yasan ƴa samu karɓuwa, sun zanta a tsakaninsu sannan ya koma ga iyayenta, suka tsayar da Magana.


.....
Bayan wata uku da dawowanshi kayi bikinsu, tunda Nannah tashigo masarautar ta fahimci sunan Abbienka sarkine a baki a zahiri kuma Amir Ukshe da Abu Zarri sune sarakin.


Dan haka tashiga faɗi tashi har ta samu damar maida mijinta me cikakken iko, ganin abubuwa sun fara faruwa Abbana yasamu a jirgi muka dawo maiduguri.
A lokacin shekaruna huɗu a duniya,tun da muka dawo. Duk bayan wata shida Abbana yana zuwa.


Bayan an haifeka kome ya kuma jagulewa dan kuwa, sun fara nuna halinsu nakin mulkinsa, dan har sun fara masa barazana. Bai fasa abinda yayi niyya ba, Amir Ukshe yana nunawa a gabanshi yana sonshi a bayan idanunshi kuwa shi yake kara rura wutar rigimar da yake faruwa.


Ranar da zasu kashe shi, ya haɗa kayanka da kuma Nannah, ya mikawa Abbana yace.
"Badar ga Ahalina! Don Allah karka bari wani ya cin maku, ya zauna a hannunka karka taɓa barinshi ya dawo."


Jin Ana dukar kofar yajasu zuwa wani kofa, ya turasu.


....... Suna barin gidan, suma mutanen na shigowa, suka same shi a kujeran da ake bala'i akanta, murmushi yayi sannan yace.
"Daga kaina bazaku kuma kashe wani sarki ba, bazanyi fatan jinina ya mulkeku ba. Am...."
Rufa mishi sukayi da sara har sai da suka ga baya numfashi, abinda yabasu mamaki shine ganin murmushi akan fuskar gawanshi, suna fitowa suka sami Amir Ukshe da Sauran manyan fadar, har da Amirah Raziƴah, murna suka fara Guru Ra'ees ya bayyana musu cikin shiga na alfarma fuskarshi a murtuke yace.
"Kun kashe maciji baku sare kai ba, kuƴi maza ku dawo da yaron nan biyan bukatarku yana ga yarone ku mai dashi kan kujeraaa"
Daga haka ya ɓace ɓat.


Umarni Amir Ukshe ya bada akan a dawo da Yaron,
***
Gudu sosai suƙe Abbana yana rike da Kayanku, Nannah tana ɗauke da kai, faɗuwa tayi tare da kai. Dawowa da baya abbana yayi cikin haki da gajiya yace.
"Uwar gijiyata, ɗaure ki tashi mu tsira da rayukarmu."
Cire kanta tayi cikin sarewa tare fidda tsammani ga rayuwa tace.
"Badar kuje kawai. Nagode kabarni a nan."
"Ba zan iya ba, ki daure muje zan ɗauki yaron ma."
Haka ya ɗaukeka ya kuma ɗauki jakarka, ya kuma riko hannunta suka fara gudu. Dukda gudun ba wani sosao bane. Duk tagaji basu kai ga barin cikin garin Amman. Suka cin masu. Basu musu kome ba yaron suka amsa bayan sun wurga mata jakar kuɗin dallar U.S, sannan suƙa mata gargaɗin da karsu kuma ganinta a kasar ko kuma su kasheka, domin kai ka rayu ita ta bar kasar baki ɗaya, domin kai tabar mahaifarta, dan tasan matuƙar ta koma kasarta zasu abin zai zama kamar yak...."


Mikewa yayi yana me zuba hannunshi cikin aljuhun wandonshi, ya kalle ni a sace sannan yace.
"Meye ya kawo ki.?"

"Tausayin Nannah da irin son da take min, yasani jin zan iya kome dan tayi farin ciki, dukda ta gargaɗe ni da zuwa nan ɗin." sunkuyar da kaina nayi tare da fashewa da kuka, nace.
"Nagama aikina. Amma na rasa tawa farin cikin, na rasa abinda zai cire zargi a zuciyar duk wanda zan au..."


Fita yayi daga ɗakin, na kuma rushewa da kuka, sabida son nagyarawa wasu zuciyarsu ni tawa zuciyar ta lalace. Taya zan fahimtsar da Anim, wallahi yasan halin da na jefa kaina ciki har abada bazai kuma haɗa hanya dani ba,


***
Ƴau kwana biyu kenan tunda ya tafi nake cikin damuwa, ga ciwon kullum yake, sam ban taɓa kawo wani abu a raina ba, kawai bar haka a matsayin typhord. Ranar da aka mai dani fada ina tsaye aka gabatar da laifina. Suƙa nemi nace wani abu amma naki magana, shima yace wani abu yaki magana, haka suka mai dani tare da masa caaaaa kuma dama sun sami labarin yaje gidan yarin dan haka Marhum ya faɗawa Amir Ukshe, sun tattauna akan Sultan.


***
Ina zaune ya shigo tare da mika min password ɗina, gyara tsayuwarshi yayi sannan yace.
"Nasamu a cikin kayanki, sannan nayi miki booking ɗin jirgi wanda zai tashi karfe sha ɗaya na rana zuwa jakarta na kasar Tunis, sannan ki rubuta min address ɗinki da Number wayar gidanku. Idan nagama abinda naƙe zanzo naga Ammina."


Jikina na rawan sanyi na rubuta mishi number Nannah sannan na mika mishi, garin karɓa ya shafi hannuna da sauri ya d'ago kanshi yana kallona yace.
"Baki da lafiya ne?"


"Fever ne, amma nasha magani, idan na isa gida zanje Abdul ya duba ni."
Tsare ni da ido yayi sosai, sannan ya taɓe baki yace.
"Waye Abdul? Ko shine zaki au."
Girgiza kaina nayi cikin gajiƴa nace.
"Kanina ne?"


Fita yayi daga ɗakin, kwanciya nayi a gadona wani irin farin ciki na cika min zuciya,
........ Washi gari aka mai dani, kamar da yadda aka saba naki magana, shima bai ce kome ba.
"Idan na fahimta Sultan Ashraf na kare mai laifi, bayan kuma shi ya saka doka...."
Bai kai aya ba Ashraf ya mike, daga kujeran ya cire duk wani abinda ya shafi na sarauta ya ajiye musu, sannan yace.
"Ni Muh'd Ashraf na ajiye muku mukamin ku, sannan zan tafi karku taɓa sakaƙancewa, dan dole wata rana ku nime ni."


Yana gama gaya musu maganar ya dawo inda nake ya riko hannuna muka fita, inda aka ajiye motarshi muka nufa Ghaniyu yaja motar, Zuwa Airport, naso muyi sallama dasu. Amma ban samu halin haka ba.


...... Tunda muka isa na zauna sukayita zirga zirga, sannan ya dawo da wata jaƙar takarda ya mika min sannan yace min.
"Kije ki sauya kayanki kowa kallonki yake."
Mikewa nayi jiri ya tafi dani. Da sauri ya tare ni, na zuɓe a kirjinshi ajiyar zuciya na sauke, ina rungume a jikinshi ya nufi gurin sauya kaya, shigar dani yayi sannan ya fito nasaka kayan na fito dakyar, dawowa yayi ya sanya hannuna a kafaɗarshi yana rike da k'uguna muka fito, dake ticker VIP. Ƴa saya min, muna fitowa ya kaini can. Zama yayi kusadani yana ce min sannu, zuba min ido yayi ganin yadda nake share kwalla. Ajiyar zuciya ƴa sauke sannan yace.
"Da zan tafi Madina ne karɓo takarduna, amma ganin halin da kike ciki yasani zan biki zuwa Nigeria, Naga ƴanayin j.."


Da sauri na katse shi ta hanyar gyara zamana nace.
"Lafiyata lau, kawai ciwon jikin dukar da nasha a hannun samudawarka ne."

Kauda kanshi yayi sannan ya mike yace.
"Insha Allah zan zo nan da wata biyu."


........ Gyaɗa mishi kaina nayi, tare da janyen idanuna akanshi,.yau ce rana tafarko da nake jin ba dad'i rabuwa da wani, shima ban san dalilinshi nakin tafiya ba, zuba min idanu yayi ya sauke a jiyar zuciya sannan ya fita, ina zaune can sai ga wata ma'aikaciyar jirgin tashigo rike da wani takarda mika min tayi, na amsa buɗewa nayi, zoɓe ya faɗo. Tare da wani ƙaramin rubutu aka ce.
*_Nasan bazan biyaki abinda kika rasa ba, bansan me yasa haka ya faru ba amma ina me baki hakuri da ki yafe min dan na zalince ki na rabaki da kimarki na Y'a mace ina kara baki hakuri , idan kin isa ki sumbaci goshin Ammina ina nan zuwa gareta_*
Lumshe idanuna nayi, zuciyata na min ciwo. Ainun ina jin sa,ada jirgin ya tashi,


....... Bayan tashinm ya kalle Ghaniyu cikin damuwa, yace.
"Yarinyar can bata da lafiya"


"Eh ranka shi daɗe, gaskiya Safinat bata da lafiya, tana da hakuri da juriya ne kawai, amma kana kallonta kasan bata da lafiya."


Haka sukayita tattaunawa har lokacin tashin jirgin Ashraf yayi.
Suka yi sallama da Ghaniyu, sun rabu cikin jimami.
***
*NIGERIA*
Abuja.....
Shakar iskar kasata yasani lumshe idanuna, a hankali naƙe saukowa daga matakalar jirgin. Har na iso arriver, ɗan jakata na ɗauka tare da fita daga cikin gun, ina fita nasame taxi, na gaji ga jirin dake damuna.


Sunan unguwarmu na faɗa mishi a gajiye, yace min.
"Madam 1.5₦" gyaɗa kaina nayi na shiga, tsoro da farga duk suƙa ciƙa min Zuciya.


......... Tafiyar awa ɗaya ya kaimu, ƴana tsayuwa a kofar gidanmu Khalilah tana fitowa zata taka kawayenta da suka zo jajjen ɓata na, yayinda Abdul ya zo zai shiga gidan. Na fito a hankali,


"Addah Feener!!!"
Wani irin kwalla ne ya zubo min, fitowa da gudu Abdul yayi lokacin na mike tsaye ya karaso guna, faɗawa jikinsa nayi tare da fashewa da kuk.......


_A ɗauri kashine ko a ɓata igiya😎_





MJ#HZƘ#VOTE....


OUM MUWADDA😇
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAƘA WRITERS ASSO_*




*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*
*_Maidambu ki zubda cikin nan na tsani cikin, Oum Muwadda don Allah a cire cikin Maman Walid don Allah karta samu matsala da family ta.....Chaiiiii ina kuke so na cusa kaina... Bari na ware muku wani abu da tunda ya shige Muku duhu Kaddara da Rabon dake tsakaninta da Sultan, haka kawai dan taga halin da mahaifiyarshi take ci taxo, sai kaddarar Ubangiji, aurenta aka saka amma aka fasa sabida karfin rabo, da anyi auren tabbas Anim Mutuwa zai yi ko kuma aje auren ba daɗi, Shi alamarin Ubangiji babu ruwanshi idan ya shirya ya shirya kenan har ranar da duniya zata tashi.... A ranar da abin zai faru taso komawa amma dake Allah ya nufa haka sai ya faru sai ya kasance tabbas wannan bangare na labarin ya tuna min kanwata Ya Allah ka bamu ikon cinye Jarabawarmu.....Shin A matsayinki na Uwa ya zaki amshi Feener Shawarar da zaku bada tayu Ummi ta fahimta ko kuma Abba Nagode👏_*


Page.١٧
Numfashi nake sauƙa da sauri da sauri, rike rigarshi nayi kuka ya ƙwace min, ɗauƙa na zai na girgiza mishi kaina, raɓani yayi a jikinshi muka nufi cikin gidan, me taxi ɗine yace.
"Kuɗina fa!"


Kawar Khalilah ce ta tambaye shi ya gaya mata ta ciro a cikin jakarta ta mika masa, sannan yaja motarsa yayi gaba.
Kai tsaye Abdul ya shige dani falourn Ummi inda Yan uwanta daga maidugurin suka zo mata jajje, ga wasu danginsu Abbanmu. Kakarmu Hajja Kaka kanwar Baban Abbanmu, tana zaune kanta naɗe da laffaya, casbi ne a hannunta,


Ganin Abdul rike da mace yana shigowa yasa duk suƙa mike, kwantar dani yayi a kan kujeran falon, yace.
"Ummi! Alhamdulillah Allah ya dawo mana da ita, Khalilah jeki cikin motana zaki ga memo ɗin Asibitinmu ɗauƙo min maza."


Da gudu tafi, Mutanen da suke falon suka haɗa baki suka ce.
"Allahu Akbar! Allah maji roƙon bawansa, Allah mun gode maka da kadawoma da ita gida lafiya."


(Wai nace Hmm)

Nan suka shiga hidima akaina, karshe dai Hajja kaka ta matso cikin kulawa tace.
"Bawan Allah ko zaka wucce da ita asibitine?"


Lokacin har Khalilah ta shigo da takardan rubutu yayi har dasu magunguna ya fita da sauri.

Ummi kam tunda ta zuba min ido bata ɗaga ba, sam taki cewa kome kallona kawai take, Shigowar Hajiya Amna da Hajiya Nuratu wato Mame da Umma yasa duk suka ɗaga kansu, cikin alhini Umma tace.


"Barka da Arziki Safinatu, sannu Allah ya baki lafiya."

"Amin Amnah," inji Hajja kaka,


Zama Hajiya Nuratu tayi, tana kallona taɓe baki tayi sannan tace.
"Nikam ba makaranta kika tafi bane? Ko wani kika bine? Ya miki halin Yan dun..."


Zama hajja kaka ta gyara, tare da rike tasbinta tace.
"Nuratu kenan! Ai ba awa motar gawa dariya, idan bai ɗaukeka ba ya ɗauki Uba nai ko uwatai! ehtoh a bakinki muka fara ji, tsalle ɗaya ake a faɗa rijiya, sai anƴi dubu ba a fito ba, harshenka kamaninka"


"Ayya Hajja daga tambaya sai ya zama laifi"
"Oho ke kika ji gun ai hannun hagu ba bakon wanƙe kashi bane.,"


Shiru falour ya ɗauka, shigowar Nannah wacce Anas yaje ya gaya mata na dawo, kamar zata kifa cikin farin ciki da murna ta riko hannuna tace.
"Bint!!! Alhamdulillah, sannu bint"


Ga baki ɗaya duk ta rud'e sai kiran sunana take, tana share kwalla. Shigowar Abdul yasata mikewa daga inda nake ta koma gefe, ruwa ya samin tare da allura,


Har aka kira magrib ban tashi ba sai karfe uku na dare na farka, Ummi da Nannah na gansu zaune akan abin sallah tashi nayi na zauna, ina kallonsu. Zare karin ruwar nayi na shiga wanka, dan zafi nake ji.


Ina fitowa na buɗe wardrob ɗin Ummi na ɗauki.Hijab da doguwar riga na saka, sannan na tadda sallar dake kaina ina idarwa masalci suna sallah.

Mikewa nayi na gabatar da sallah, sannan na fara addu'a. Ina idarwa barci yace gani nan nazo...
Kallon Nannah nayi tare da sakar mata murmushi nace.
"Nannah kafa suna min ciwo musaman nan."


Na nuna mata gun kaina na ɗaura a cinyar Ummi, nace.
"Ummi don Allah sosa min kaina."
Zare hijab ɗin nayi ita kuma ta shiga sosa min kai Nannah na matsa min kafar, kafin kace minti biyar barci yayi gaba dani.


......... Suna ganin nayi barci Nannah ta ɗauko pillow tasa min, hira suka taɓa sama sama,, sannan suƙa kwanta.


...... Ina farkawa naga abokan aikina na gidan radio duk sun zuba min ido mikewa nayi ina murmushi yawu ya cika min bakina, zubda yawun nayi tare da ɗaukar sabon brush a locker ban ɗakin, na wanke bakina sannan na fito nasamu sunyi min kunun tsamiya, da kosai. Murmushi nayi na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login