Showing 9001 words to 12000 words out of 100319 words
Chapter 4 - Masarautar Jordan Book 1 Complete Document .txt
Ashraf yayi mugunta yaro karami ne fa, taya zai ji tausayin mutane.
D'aga sider bag ɗina nayi naga wata farar takarda da wani kunshi.
D'auka nayi naga anyi rubutun da bazasu gaza layi shida ba.
_Barka da zuwa Masarautar jordan, a cikin jakarki akwai waya da bluetooth, sai wannan kunshin kuɗine ki ji daɗinki sannan muma zaki mana aiki idan kika ki toh zaki buɗe idanunki a lahira_
Wayyo Allah na, nashiga uku ina ne na kawo kaina, buga kofar akayi na tashi da sauri zuwa nafita, suna tsaye sun min zuru zuru. Wuccewa nayi a gaba suka rufa min baya, bansan dalilinsu na biyo ni ba. Amma ba mamaki yana nasaba da sarkinsu.
Bayan sun kawoni na wucce ciki a falon farko naji wani abin mamaki, manyan mutane fa dan akalla zasu kai shekaru sittin da ɗauriya. daya yace.
"Akwai dukiyar da nake son fitarwa daga cikin kasar nan zuwa Amurka, shine na kawo takardun yana ciki an kai, dan ma Amir Ukshe yasa baki yanzun haka takardan yana gunsa."
D'ayan yace..
"Nima manda ake hakowa a cikin kasar nan musaman mallakin masarautar akwai wasu turawa da suke sone zan sayar musu shine na kawo takardan yasa hannu, da taimakon Amir."
Hmm na iya cewa a raina, yadda suke hiransu. Muna shiga cikin gidan naji kamshin falon ya sauya. Hangoshi nayi ya naɗe kafa ɗaya akan daya, sanye yake da doguwar jallaɓiya ga wasu mutanen a tare dashi, sallamar da nayi wani daga cikinsu ya amsa. Duk mutanen sun ɗago sun kalleni banda shi. Shin dama mulki idan ya shiga jikin mutum haka yake. Tsohon da aka kaini gunshi, shine yaketa magana cikin rarrashinsa da yasa hannu a cikin takardan da yake gabansu.
Wuccewa kitchen nayi bansan ya akayi ba dan sune suketa magana, sai dai jin da nayi suna sanya mishi albarka tare da jin daɗin har da godiya,
"Anya Masarautar nan tana cikin tsari kuwa? A sani na sarki Fada yake zuwa wannan sarkin toh."
Nace a raina kar nayi gajen hakuri da saurin yanke hukunci.
***
Kwana na uku a cikin gidan kuma kullum girkina sai dai akaiwa Kare da Mage. A rana na huɗu, ne aka kawo wani balarabe, ya fara girkin sultan. Zamana da Samin yasani sake kara sanin halayar larabawa, dan ido da ido yake nuna min kabilanci da wariyar launin fata. Uwa uba, tsangwama.
Tafiya yayi nisa dan kuwa na kara fahimtar cewa Sultan Ashraf sarkine a zahiri amma a baɗɗili ba shine sarkin ba Amir Ukshe da Amir Abu Zarri, duk wani abinda zai fita daga masarautar ta hannunsu ne, sannan rayuwar Sultan Ashraf kamar a hannunsu yake dan sai yadda sukayi dashin, sannan akwai abin alajabi dan yake damuna, game da sultan duk lokacin da aka kawo mishi takardu baya buɗewa sai dai yasaka musu hannu, baya taɓa bincika meye takardan.
***
Yau na cika sati huɗu da aka kawo ni cikin kurkuku sultan a yanzun na kiyyaye abinda zaisa a zane ni sosai. Da wuri na gama abincin mage da karen. Nafita zuwa shashin bayi.
Lokacin da naje nasame Yan ɗakinmu jungun jungun. Ganin babu Zakiya yasani cewa..
"Kanena ina kanwata Zakiya."
Kuka ne ya kwace musu suka sani a gaba da kuka cikin tashin hankali nace.
"Lafiya kuke kuka."
Mujahida ce ta iya cewa..
"Kaltu Feener! Zakiya an yanke mata hukuncin zaman gidan kaso har na shekara uk."
A tsorace nace.
"Akan wani laifin?"
"Sabida ta kare kanta lokacin da Amir Sauban ya nemi keta mata haddi ta fasa masa kai da kwalb....."
Ban gama jinsu ba na fita daga gidan, da gudu. Sai gidan Sultan raina a ɓace na shiga yana zaune a falo. Kai tsaye na nufi inda yake cikin kuka nace.
"Shin kai wani irin sarkine da baka samawa talakawanka adalci?"
Idan dutse zai amsa min toh Sultan Ashraf ya tanka min.
"Wato ku kanku kuka sani, daga ku sai danginku, ta rasa ahalinta a yakin siriya tazo nan dan rufawa kanta asiri."
Ji nayi an fizgo min, fita dani suka fara yi cikin ihu nace.
"Kayiwa kanka Adalci."
Tunda suka kaini ɗakin suke zane ni, sai da suka na daina numfashi sannan suka kyale ni. Sai da nayi kwana uku a ɗakin duhu sannan aka fito dani. Tunda aka fito dani hasken waje ya ɗauke min gani na.
Sai da nayi awa uku sannan ganina ya dawo dai dai.
...... Koda na shiga kitchen Samin na kallona ya kauda kanshi, yace.
"Sorry Feener! Kiyi a hankali dayiwa Sultan Magana kai tsaye, dan zaki iya rasa rayuwarki baki ɗaya, ai da sai kinyi sati za'a fidda ke toh dabobin da kike musu abinci an kai musu abincina sunki ci shine suka fara niman mutuwa shine mai kula da Arduwan yace a fidda ke in ba haka ba mutuwa zasuyi. Sultan naji da kare da magen kamar rayuwarsa."
Gyaɗa kaina nayi kwalla na zuɓo min, haka nasa hannu nayi girki aka kai musu. Na fito zanje shashim bayi aka hanani. Wai ance kar na kuma fita daga shashin har sai sultan yabar kasan, dan saura kwana uku zai bar kasan.
Kamar na daka tsalle zai tafi zan koma cikin gidan gun bayi Yan uwana.
Haka na koma kitchen dan anan nake zaune bani da inda yafi nan.
Tsabar na kagu ya tafi bansan ya akayi nayi Mansaf yayi yaji ba, ranar sai da naci duka bayan an sani sabon abinci wai kare da mage hauka sukayita musu dake suna can gefen gidan ta baya, shine aka kira likitan dababobi ya gano yajin da na cika a cikin abinci Sultan da kanshi yace.
" ku mata kaman yadda tayi musu."
Wato su bani abinci me yaji kamar yadda na musu
Kare mishi kallo nayi bai wucce sa'an Abdullah kanina ba wai shine yake bada umarni a zane ni, ina da matukar zuciya da fushi, shi yasa ban cika shiga tsabgar kowa ba, sai na yaba da halinka. Bansan lokacin da nace masa.
"Na zata sawa zakayi a kashe ni kamar yadda kasaba sawa ana kashe mutane."
Bai taɓa tsayawa ya kalle ni ba, sai yau, kaɗa kai yayi yace.
"Ku jiyar da ita azaba wanda gobe ko hango ni tayi zata sauya hanya."
Lumshe idanunshi yayi aka suka fita dani, zuwa ɗakin azaba. Wato wani irin wahala suka bani wanda yasa ko tsayuwa na gaggari yi sai kwalla kawai.
***
*Banu Hussein*
Yake shi da kabilarsa, kowannensu sai shawara suke badawa yadda zasu kwace mulkin Jordan, da karfin cin tuwo har suka gama sannan ya zauna cikin izza yace.
"Na bawa Sultan Ashraf Rania!"
"Amir Adna kasan abinda kayi kuwa? Ka ɗauki Y'arka kabawa."
"Shakur! Mulkin jordan muke so! Idan Rania tashiga tasamu ciki ta haihu da Ashraf tankar mulki ya dawo cikin kabilar Banu Hussein ne kuje kuyi nazari."
Yana gama faɗar haka ya bar musu falon baki ɗaya.
***
*Gidan Amir Ukshe*
"Abbie!"
Gyara zama mutumin yayi cikin girmamawa yace.
"Abbie! Sahel ta amince da zaɓinka! Amma meye kasonmu idan Ashraf ya aureta?"
Kura mishi ido Amir Ukshe yayi sannan yace.
"Me kake tunani akan mulkin Jordan bayan bamu kaɗai bane muke kwadayin mulkin, akwai Kabilun Banu Nazir da Kabilun Hussein, ko da wasa bazaka taɓa samun koda taki ɗaya ne na mulki tunda Yasir ya sadaukar da karagar babu wanda ya isa ɗarewa da karfin tsiya ka cire ranka a cikin sha'anin mulkin gidan nan. Zaka iya tafiya"
Jikin Amir Marhum ya mike zuciyarshi cike da haushin Mahaifinsa.
***
*Banu Nazir*
"Zoya! Naji Ashraf zai koma Germany ki shirya na nima miki masters a can, kafin ku dawo ki tabbatar da kin shawo kansa, inta kama ma kanki ne ki mika mishi dole na ruguza Daular banu Hashim da hannuna.......
*Ku nutsu labarin cike yake da sarkakiya karku min korafi akan duk abinda zai faru idan kuka duba sunan labarin kunsan kome zai faru no more any korafi*
#MJ
#HZƘ
#Mai_Dambu
#VOTE MJ...
Oum-Muwaddah.....
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAƘA WRITER'S ASSO_
*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*®2020*
*BOOK ONE*
Page.٦
"Yaro!!"
*Samin Ni zan faɗa maka Ashraf Yarone."
Abinda yayita kai da komowa kenan a ranshi, baji haushin Samin kamar yadda yake jin haushin wancar bakar fatan, kallon kanshi yayi a madubi. Girman jikinshi ya kalla, da irin yadda Allah ya masa kira irinta lafiyayyun maza, matashin me ji da kuruciyarsa, wato Ashraf dogone me matsakaicin jiki, yana da dogon hanci wanda ya karawa fuskarshi kyau, sai idanunshi an dai-dai, yana da cikar gashin gira. Sai kayataccen sajen da zagaye fuskarshi, me haɗe da gemu ɗan cass. (Da zaku san crown prince Muhammad Bini Salman, wato yarimar saudiya me jiran gado, toh haka Ashraf yake)
Takaicine ya turnike shi bai san lokacin da yakaiwa madubin naushi ba har sai da kome ya tarwatse, kalamar Yaro ne yake yawo akanshi, babu wanda ya taɓa masa kallon Yaro sai wancar bakar fatan, haka ya tarwatsa kome sannan ya danna wani karfe sai ga masu kula dashi sun shigo..
Dafe yake da goshinsa yace..
"Ku ɗaukota."
Fita sukayi dan cika umarninsa, ina kwance sai ji nayi anyi sama dani, kafin na wartsake an dire ni a cikin fasassun kwalaɓe, dan suna shiga yayi musu nuni da cikin kwalbar dan haka suka cika umarninsa. Suna dire ni cikin kwalbar na sake kara da.
"Auuchhhhh Ya ilahi"
Fesa turarenshi yayi yasa kai ya ficce a ɗakin, kuka ne ya kwace min. Duk yadda na motsa kwalabe ke shigewa cikin kafana, na ruɗe na kiɗime. Ga baki ɗaya nayi danasanin shigowa Rayuwarshi. A gigice nayita taka kwalaɓen har na fita a cikinsu na zuɓe a gefe guda ina jawo kafafuna, ina dubawa manyan kwalaɓe da kananu dakyar na ciresu. Ga jinin dake fita a kafar.
Bansan iya adadin lokacin da na ɗauka ina cire kwallar da kuka ba, ina gama cirewa na rarrafa na ficce daga ɗakin.
Ina fita na mike ina dangala kafata a kasa har na isa kitchen na, ban ɗaki na shiga na zauna dirshan tare da fashewa da kuka, wanke kafar nayi na saka cikin ruwan zafi ga uban azabar da nake ji, haka na gasa kafar. Ina nufar gun kayana na fahimci an taɓa min side bag ɗin, ina buɗewa nasamu takarda a saman anyi rubutu haka.
_Zamu fidda ke daga masarautar ki tabbatar kin zuba mishi wannan gubar a cikin abin shansa baya kisa farat ɗaya, sai ya gama cin jikin mutum_
Hannuwana biyu na ɗaura akai na fashe da kuka, tare da cewa.
"Na shiga uku na lalace."
Mikewa nayi na ɗauki jakar na sakala. Dai daita tsayuwata nayi, na shiga takawa a hankali sabida ciwona.
Cikin sanɗa na fara tafiya har na isa bakin falo, ba a kashe ba haske . Saka hannuna nayi naja kofar abin mamaki a buɗe take, ina zura kaina zan fita. Naji motsi a bayana alamun an buɗe kofa.
A sannu na juya Sultan a tsaye sanye da kayan barci dogon wando da rigar me guntun hannu farare kwal, kallo ɗaya zakawa kayan kasan asalin auduga ne, yana tsaye harɗe da hannunshi a kirji, Mujahidah ce ta faɗo min a raina, gashi ya zuba min ido ni ban fita ba ban kuma shiga ba. Lokaci ɗaya na shiga tattara inda ya bayyana a jikina, musaman kirjina ina karesu takowa ya fara, kallon shi nayi naga inda nake yake zuwa.
A hankali na shiga ja da baya, jikina na rawa. Abin dariya yana zuwa ya ficce daga falon, ajiyar zuciya na sauke dole na koma naje na kwanta. Ban runtsa ba a daren sai kusan asuba. Barci ya ɗauke ni, saukar ruwa naji a kaina na mike firgit, na zauna tafin kafana sun kumbura tam.
Haka kawai nake jin na ɓata jikina, dan ina lissafin kwanakina na har da kusan sati ɗaya. Kallon basamuden da ya watsa min ruwa nayi cikin raunaniyar murya nace.
"Kai baka da imani ne? Idan shi ya baku umarnin zalinci sai ku aikata, yanzun daka watsa min ruwa meye ribarka?"
"Eyye! Bakar fata da maganar banza a cikin masarautar larabawa." yace min.
Cikin jin haushi nace.
"Zaka iya sauya rubutun alkur'ani zuwa farin tawada?"
Kura min ido yayi cike da mamaki bakinshi buɗe yace.
"Lallai zaki wayi gari a barzahu. "
"Idan na wayi gari a can kai kayi gad..."
Dake ɗaga muryana nake, kusan masu kula da lafiyar Sultan sunji mu. Kafin na karasa sun shigo amadadin su tambayi ba asi. Sai suka shiga zane ni. Da gayya na fara ihu. Yana can ɗakin hutawarshi yaji hayaniya dan sun daina dukana kokari suke nayi shiru, sai ga Amir Ukshe tare da d'anshi Marhum da kuma Amir Abu Zarri. Tare da Wata mace sun shigo gidan, jin hayaniyanmu yasasu leko kitchen ɗin. Cikin kasa kasa da murya Amir Ukshe ya rufesu da faɗa, har ya dakatar dasu. Ni kuma aka kira likitan masarautar da nurse suka zo aka duba kafana sai da suka min dress sabida akwai kwalaɓe.
Ana gama min, nurse ts rike ni muka koma can shashin bayi, ranar da muka ga juna munci kuka babu Zakiya. Kwana goma nayi ina jinyar kafar a lokaci kuwa Azrah tazo yakai sau goma akan lallai ina warkewa na koma bakin aikina dan sabida jinyata gashi karen da Sultan ƙe kiyo ya mutu, dan kwana uku ana kai mishi abinci yana kin ci har dai ranar da yunwa ta buwaye shi, ana kai mishi abincin yafarwa mutane garin a san yadda za'ayi dashi ya zarge kanshi, a take ya sheka. Nayi Imani da Allah sai Sultan ya azabtar dani akan haka. Ina zaune na buga tagumi dare yayi su Hindu sun tafi gun rawansu. Dauke wuta kwan ɗakinmu yayi, jakata na shiga lalluba zan kuna torch ɗin wayar da aka saka min naji karan buɗe kofa. D'ago kaina nayi dan har waje baka ganin haske sai duhu.
Komawa nayi da baya na hantsila kasan gadonmu cikin sauri na shige kasar gadon.
"Ki fito!"
Aka ce min, shiru nayi na ɗauke numfashina. Amma ina saukewa a hankali. Ko ya aka san ina kasan gadon sai ji nayi an finciko ni, ihu nasaka akayi maza aka shafa min abu a hancina ban kuma fahimtan komi ba....
***
"Alexandra! Na faɗa maka karku taɓa barin a nima masa baiwa indai ba daga Yankin nan tafito nan gaba babu wanda ya isa raba Larabawan nan da mulki sabida shigowarta cikisu zata ankarar dashi abinda yake ɓoye, dukda ba kai ɗaya kake bibiyarshi ba, ina jiye maka ranar da zai fito zahirin sarkinsa dan larabawa suna da kishin kansu balle kuma d'an kabilarsu, kuma bazaku taɓa cin nasaran kifar dashi ba, sai dai ku addabi rayuwanshi ita kaɗaice bata da mugun nufi akanshi ban sani ba ko tazo amma zata zo ɗin. Sai dai kuma shi muslimin kwarai ne babu ta inda zaku kuntattashi ba tare da Allah ya warware mishi ba, sai dai zan baka shawara ɗaya karku nuna sai kun hamɓarar dashi, mafi alkhairi kunemi mafita."