Showing 15001 words to 18000 words out of 100319 words

Chapter 6 - Masarautar Jordan Book 1 Complete Document .txt

Zarri wanda shi yasa ayi mishi dole katashi tsaye kuma ka bar kange musu arzikinsu tunda kama kana ci."
Buɗe baki Amir yayi zaiyi mgn Ra'ees yace.
"Yaki amsar tayi auren Sahela amma ya amshi tayi Adnan toh ai koda auren masa su akayi bazai zauna dasu ba dukkansu ba matansa bane, matarshi tana kusa da shi, kuma bata cikin ksbilarku. Itace zata zauna dashi babu dogon buri a tare da ita, amna shawara karku barshi ya shigo da ita dan tun kafin ya shigo da ita zata zabtare muku kimarku, sannan ka dakatar da Marhum yunkurin ganin bayan Ashraf tabbas nan gaba hukunci zata haura kanshi akwai zoɓen azurfa ka bashi ita a matsayin kyautar karin shekarar haihuwarsa ku haɗa mishi shagali ita zoɓe zatq kasance me jin umarninka ce ba tasa ba, karku sake ya shiga fadar domin idan ya taka ciki kome zai faru ciki har da abinda ya faru da iyayensa, kuma ya fahimci haka toh baki d'ayanku zaku zama baki a lahira hatta nima bazan tsira ba jiki magayi."


Yana gama faɗar haka ya ɓace daga jikin Madubin.
..........
*Hello ina son ku duba yanayin labarin da kyau gabaki ɗaya daga Jazziratul Arab ne, naso aro sunaye ganin navawa mutane wahala a cikin Abu Khadija yasa nayi amfani da sunayenmu na yau da kullum, zaku ji dai bakon sunayen ya zama dole asaka ne Musaman Rania, itace matar Sarkin Hussein Muh'd na kasar Jordan a yanzun, sai irinsu Alexandra Angela, Zoya Sahela, da sauransu arone kasancewa labarin larabawa da Yahudawa ga kuma Kabilun Urud...... Nasan kafin ni akwai marubutan da suka shiga yankuna na duniya dan labari amma Labarin masarautar jordan, dabane sabida har cikin littatafan. Tarihi irinsu Siratu nabiyyina Muh'd (S.A.W) Islam biography, Islam dictionary da sauransu nagode da fatan zaku fahimce ni.*


#MJ#HZƘ#VOTE......Ku taimaka da Vote na fara jin lalaci fa😂


Oum Muwadda....
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAƘA WRITER'S ASSO_


*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*


_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*


Page.٧
*Banu Hashim*
Watsawa Amir Ukshe wasu takardu, Amir Abu Zarri cikin mugun ɓacin rai da fusata, ya daki table ɗin gaban Amir Ukshe yace.
"Baka isa hanani rawan gaban hantsi ba, dukkanmu kabila d'aya ce kuma manufarmu d'aya ce, sannan burinmu d'aya. Taya zaka kange kome dan zalimci ka hana wasu? Raziya ta kawo takardunta kace bazaka saka baki ba, akan me? Ita kaɗai ta rage a Ashraf ya kira danginsa amma ka hanata samun kusanci da yaron meye nufinka? Ga takardun kuma dole a samata hannu itama dan dukiyar ba naka kai kaɗai bane."

Mikewa Amir yayi ýa tawo inda Amir Abu yake, hannunshi yakai zai taɓa Amir Abu Zarri, cikin sauri yaja da baya, yana nuna shi da d'an yatsa yace.
"Macuci baka da bakin gaya min kome nasan kai waye, kuma dole ayi kashe muraba. Ka duba jaridar can da na kawo maka karka manta yarjejeniyarmu na bawa juna goyan baya maciyi amana."
Yana gama gaya mishi haka ya juya tare da barin ofishin.
Idan ran Amir Ukshe yayi dubu sai da suka ɓaci. Fuskarshi har ja tayi tsabar ɓacin rai, danna wani karfe yayi sai ga masu kula dashi sun shigo, nuna musu takardun yayi, suka tattara sannan suka zuba a kwandon shara suka fita.
***
Wani irin rikicine ya taso daga cikin kabilun Hashimiyya, wanda yaja hankalin, sauran kabilu guda biyu suka zuba ido suna kallon yadda wasan zai kayya, kuma abin takaici ba kome yaja wannan rikicin ba, sai dukiyar masarautar da suke watandarshi, karshe dai wasu daga cikin familyn Yasir sune suka, shiga alamarin inda aka dai daita ba tare da sanin Sultan Ashraf ba.
........ Takardun da zaisa hannun suka, na kalla suna kan wani table na daban, dake Allah ya ɗaura min karambani, zama nayi a kujeran table ɗin, na shiga ɗauƙar takardun ina dubawa, a hankali na shiga duba abubuwan da takardun ya kunsa, mamakine ya kamani sakamakon ganin zunzuruntun dallolin american da zasu cire daga baitul mali. Masarautar, jin motsin yasani mikewa nabar gun, kitchen na shige. Ina hango shi ya fara samusu hannu ko duba takardun bai yi ba. Mamaki ne ya kamani na fito daga kitchen ɗin tsoro da fargaba dake raina bai hanani fitowa ba nuryana na rawa jikina na ɓari nace .
"Sultan!!!" bai ɗago ba kuma bai fasa abinda yayi niyya ba, na cigaba da cewa.
"Allah ya baka mulki ne dan ya gwada imaninka bawai ka zama azzalumi ba, wannan sa hannun da kake yi ka duba meye ya kun..."
D'ago kanshi yayi idanunshi sunyi jajjur, takanta fuskarshi tayi ja. Ainun balle kuma ace meye a zuciyarshi, kura min ido yayi sannan ya danna ɗan kararawar. Sai da naji cikina ya murɗa, shigowa suƙayi idanuna cikin nashi, bai janye ba nima kuma haka, cikin kasa kasa da murya suka ce.
"Umarninka muke jira"
"Ku tafi da ita, taji a jikinta." yace, idanunshi cikin nawa,
Lumshe idanuna nayi cikin karfin hali nace.
"Me yasa bazaka fahimc..."
Juyar dani suka fitar dani, cigaba yayi da aikinshi.
Wato idan akwai mugayen mutane bayan larabawa ne, suna fita dani, suka wucce dani wani ɗakin ruwa. Suna shigar dani suka kifa kaina cikin ruwan sai da naƴi minti uku zuwa huɗu suka fidda, kuka nasaka ina jin numfashi dakyar naja numfashina, kafin na daidaita an sake tsumbulani cikin ruwan, har kusan minti biyar, bansan yadda zan muku bayani irin azabar da nake ji, amma bari na muku misali da kwarewa, idan wani kware da ruwa ya kuke ganin yake ji balle ni da ake tsuma kaina cikik ruwa bana jan iska, sai ruwa zalla nake ja.
Kusan minti ashirin suka ɗauƙa ana horani da ruwa, nayi laushi na masifar gajiya, suna ciro ni suka jefani gefe guda ina sauke numfashi ga kwallar wahala da nake fiddawa.
....... Bayan awa guda suka mai dani cikin gidan suka watsar a kasan kitchen ɗin da sauri Samin yazo inda nake ya ɗaga ni, kuka na saka mishi, coffee ya haɗa da sauri ya bani nasha, ina kuka, ganin yana juye ruwan coffee a cikin wani butar shan shayi, ya jera kofuna biyu. Zai fita dashi nayi maza na amsa, dan haka kawai naji ban yarda da coffee ɗin ba, dan a madadin ya bani na cikin tukunyar, a'a sai ya dafa min wani a cikin wani tukunyar ga kuma wanda ya dafa. Olready cikin siyasa na mike tare da cewa.
"Bani na kai mishi."

Ba musu ya bani, ina fita falon, da gayya nasake tiren ya faɗi a kasa, kome ya zube. Da gudu Samin ya fito bai yi wata wata ba ya tsinka min mari, dai dai fitowar Sultan ga kuma masu tsaronshi sun shigo, sakamakon jin karan fashewar abu. Cike da jin haushi ya kuma d'aga hannu zai mare ni, Ghaniyu ya dakatar dashi. Ƙasa ƙasa yayi da murya yace.
" Kina da dangantaka da bakakken aljanune, yanzun aka dawo dake daga ɗakin horo amma har kin kuma wani laifin, ke ko tsoron sul...."
Bai kai karshe ba na tsinkawa Samin Mari, duk suka zaro idanu. Hatta Sultan ɗin mamakine ya kamashi, dukda a tsorace nake. Nace,
"Bani da lokacinku idan kun damu da abinda nake wanda kuke kira da Sultan yayi magana."
Zasu yi magana ya d'aga musu hannu, takowa yayi har inda muke ya kalle su gabaki ɗaya suka fita daga falon takowa yayi gabana, d'ago kaina nayi naganni yar karama a gabanshi, tsaki yayi ya min sannan ya bar falon, komawa nayi kitchen. Ina shiga Samin na finciko ni, haɗani yayi da bango, tare da toshe min baki da hannunshi cikin zafin rai yace.
"Ina kyale kine sabida, baki cikin tsarina, wannan ɓarnan ƴa zams nakarshe da zaki min in ba haka ba zaki mutu. Dan ni an biyani kuɗin aikina ke da baki da rabo kita zama matsiyaciya."


Sororo nayi ina kallon Samin kenan zuwa yayi ya kashe D'an Nannah, bansan lokacin da nace masa.
"Sai dai in bana numfashi matukar ina raye sai dai ka mutu. Amma ba Sultan ba yarda yasa ya daukeka aiki ko dan wannan yarda bazaka taɓa cuta...."


Shake min wuya yayi cikin mugun ɓacin rai yace.
"Na lura baki iya da harshenki ba, zan baki mamaki."


Daga haka Bai kuma kulani ba ya koma bakin aikinshi, tun daga ranar nasaka ido sosai akan abinda yake, karshe idan yayi girki kifarwa nake, sultan yasa a zane ni. Tafiya tayi nisa inda na shiga renawa kowa hankali musaman masu zane. Idan suks ɗauƙe ni zasu ciks umarninsu, sai nayi tsagal nace.
"Kunga ni karku kaini wancan ɗakin wannan zaku kaini."
Ko sai an shigar dani nace.
"Gaskiya nan bai min ba can zaku mai dani."
Haka xasu dawo dani. Karshe dai sai an fasa hukuntani sabida renin hankalin da nake musu, sam na manta da mutanen da suke bibiyar alamarin. Ashraf kawai burina nasami shiga jikinshi.
***
Yau kwana uku kenan da bana ganinshi tawani fuska naji sauki tunda babu wanda zaisa a zane ni, tunda na fahimci har Samin baya nan take naji hankalina bau kwanta ba, tambayar ghaniyu nayi yace min ai sultan ya tafi dashi Germany, kamar zararriya haka ns koma. Burina na maidawa Nannah ɗanta gashi ya tafi da makashinsa.
***
*Germany*
Kofin Coffee da Samin ya kawo ya ajiye a gaban Ashraf, yayi nisa a karanta jarida. D'ago kai yayi yana kallon kofin, sannan ya juya ga Samin da yake tsaye, sannan ya juya ya kalli kofin.
Mikewa yayi ya fita can sai gashi rungume da yar magensa, zama yayi ya ɗauki kofin ya kai bakinta ta lashi coffee ɗin,


Tasha kaɗan sannan ya kalle Samin, da sauri ya ɗauki kofin yana jin haushin abinda ya faru. Yanzun ya fahimci wani abu wato tsabar rashin yarda irin na Ashraf ko abincin kowa baya ci ya gwamace ya ajiye kayan zaki a ɗakinshi yayita ci, dake shima ba me yawan ciye ciye bane dan tunda aka kai mishi hari sau biyu yake gudun cin abin hannun kowa.
***
*Bayan wata uku*
*Middle easth club*
Wani haɗaɗɗen club ne dake cikin garin Amman, shiga gun sai yaran wane da wane. Club ɗin ya cika makil da matasan larabawa da turawa kai har da tsirarun, gefe can yarima Nu'yam ne zaune tare da yan matansa, babban jikan Amir Ukshe, d'an Amir Marhum. Yana zukar shisha, wata yar kabilar Banu nazir tazo wuccewa ta bayanshi dake ya jima yana kwaɗaituwa da ita. Musaman shigar da tayi wani ɗan mini skirt da farin shirt, sai wata baby top da ta ɗaura kana ganinta kaga ma'aikaciya a cikin club ɗin, tazo wuccewa ya kai mata duka akan tuwaiyarta(bombom)
Juyawa tayi cike da kunya, dan yana kai mata duka mutanen gun suka fasa ihu da sowa dake larabawa sunfi yawa a cikin club ɗin, bakin ciki yasa ta kife shi da mari. Shiru gun ya ɗauka, sakamakon marin da aka mishi,ture yan matan da suka zagaye shi yayi, ya tunkareta inda ya rufeta da duka kamar mahaukaci. Ganin haka yan kabilarta suma suka rufawa Nu'yam, basu kyale shi ba sai da suka kashe shi, sannan suka fita da gudu. Cikik club ɗin duk aka watse.
Kafin kace me har larabi ya shiga cikin masarautar, Amir Ukshe da Marhum sai Amir Uzaifa. Kanin Marhum suka je club ɗin anan suka sami gawar Nu'yam, a yashe kamar gawan mara galihu.
Dake Yan sanda sun iso da wuri, ɗaukar gawan akayi zuwa Asibiti ana gama bincike aks basu. A daren suka kira Ashraf.

Dole aka jinkirta yiwa Gawar Nu'yam sallah.
Karfe sha biyu na rana. Sultan ya iso, sannan aka sallaci gawar aka kaita gidanta na gaskiya. Bayan sun dawo aka fito masa da file ɗin abinda ya faru, matasan sun gudu sai Yarinyar, dan haka an kamo yarinyar dan har an yanke mata hukuncin kisa, umarnin Sultan ake jira.
Dukda bansan zai zo ba na gyara gidan, tunda ya hana a barni na koma shashin bayi.
Kuma dama kaman jiranshi sukr kowa ya ɗauko cuwa cuwarsa, ya kawo Sultan yasa mishi Hannu.


***
*Banu Nazir*
Zubewa a gaban Alexandra wani farin tsoho yayi yana kuka sosai yace.
"Ya Shugabana! Angela itace kaɗai ta rage min, kuma matukar aka kasheta bani da kowa a duniya, asalima yaron shi ya fara mata rashin d'a'a har yakai da ya rufeta da duka, badan su Thomas sun taimaka ba da gawarta zasu kawo min kuma babu yadda na iya."
Shiru falon yayi sai kuka Tsohon yayi, mikewa Shugaba Alexandra ya ficce daga falon yayi ya nufi can masarautar yaje dan su fahimci juna abun bakin ciki sam suka ki barishi ya gana da Ashraf. Karshe haka ya dawo da bacin rai wanda ya kuma tunzura zuciyarshi ga dole sai ya hamɓarar da Sultan Ashraf. Dan tsakani da Allah Ami Ukshe ya nuna musu kabilanci...
Kuma idan baku manta ba tun shafin farko na faɗa muku yadda Larabawa suke da nuna kabilanci......


















*😂 "Anyan Kuna Fahimta kuwa Zauren Mai dambu nasan sunfi Yan Wattpad fahimta Musaman Fatima Da Maman Abba Kd jiya na hango ku Laaaa Sister Meeshaz da Queen Hafcy ku bar Harara na ko na tsuma kanku cikin ruwa😹"*


#MJ#Mai_Dambu#Vote&Share
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAƘA WRITER'S ASSO_*


*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*


_Fatan alkhairi gareku yan team ɗin A koyar da ita yadda ake magana😂 Wato Sultan Ashraf....Sister Meerah Uwar ɗakin Sulfeena, da Kuma Yar ɗakin Ashrafeena Rukayya Abdul.... Ga kyautarku nan_


Page.٩
Gabaki ɗaya ji yayi hankalinshi yayi mugun tashi, ranshine yayi masifar ɓaci. Badan karya saɓawa Ra'ees ba da..... Sai kuma ya mike daga zaman da yake yasaka kayansa dan dama zaune yake daga shi sai wani jan kwarjalle, (Wato kwarjalle daga yanki Asia aka amfani dashi zaku sai danfarin kyalle da yan kudancin india suke amfani dashi a film ɗinsu) shine a jikin Amir.
Yana gamawa yafito, ta cikin uwar ɗakinshi. Waje ya fito tare da wasiwasin abinda Ra'ees ya faɗa mishi, kawai sai yaji bai amince da maganar Ra'ees ba karo na farko a rayuwarshi, mikewa yayi ya koma ɗakin ya buɗe inda Ra'ees yake ajiye masa abu nan yaga zoɓen ɗanyen azirfa. Dauka yayi yana kallon zoɓen wanda aka zagaye samanshi da jan Diamond, dan kyau zoɓen ya haɗu. Dauka yayi yasaka a cikin aljuhunsa sannan ya dawo falourn inda yasami Uzaif yana xaman jiranshi,
Kallon Uzaif yayi sannan ya zauna tare da mai da hankalinshi ga baki ɗaya kan Uzaif.
"Abbie!"
D'aga mishi hannu yayi cikin tsukewar fuska yace.
"Kacewa Marhum ya dakatar da abinda yake, in ba haka ba duk abinda ya dawo mishi yayi kuka da kanshi."
Gyaɗa kai Uzaif yayi, sannan yace.
"Abbie maganar fidda kuɗin nan Sultan ya nemi hujja"
Kurawa Uzaif ido yayi kafin ya janye, kamar bazai ce kome ba.
"Me kace masa?"

"Abbie wallahi bansan me bakina yace ba dan Yaron akwai wani ɓoyayyen sirri a tare dashi."

"Ba tambayar da na maka ba kenan me ka gaya mishi nake son sani.
Shiru yayi sannan ya faɗa mishi yadda sukayi da Sultan.

"Hmm" kawai Amir ya iya cewa, sannan ya sallame Uzaif.
Bayan fitar Uzaif juya alamarin Sultan, yake tabbas akwai matsala, matuƙar ya bari su Raziya sukai galaba akanshi har abada bashi da ikon akan Masarautar dan itama bata ki abata mulkin ba.
......
Fitar Uzaif gidan Marhum ya wucce, gaisawa sukayi sannan ya gaya mishi sakon Amir, riƙe yake da kofi me ɗauke da taceccen inabi, bai san lokacin da ya maka kofin da kasa, sai da ya tarwatse baki ɗaya.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login