Showing 57001 words to 60000 words out of 100319 words

Chapter 20 - Masarautar Jordan Book 1 Complete Document .txt

yaran, ta wucce dasu ɗakin kula dasu, ni kuwa suka rufa min dan cito rayuwata.
Idan ka rayu babu jarabta a rayuwa ka binciki imaninka, Aslhamdulillah nagodewa Allah da yake jarabta rayuwata, kuma bana bakin ciki da haka sai godiyar Ubangiji. Da nake ba dare ba rana.
........
"Hmm kagani ko! Ai na gaya maka Maryam ta rabaka da yaranka musaman wancar karuwar, tunda ai ba yau ta fara cikin ba. Sau nawa tana zubda cikin a ɓoye daga ita sai wancar munafukar balarabiy..."
Wani mugun kallo ya bita dashi wanda yasata haɗiye maganarta, cikin fushi da ɓacin rai yace.
"Balarabiyar mutum ce! Daga cikin mutanen kirki ita tankar waliyiyya ce, domin zuciyarta takai kololuwar kyautatawa, duk abinda nake bata min magana sabida dalilai guda biyu ne. Dalili na farko tabani dukiyarta ina kuma cin gajiyarta, ko sau ɗaya bata taɓa saka idanunta akai ba, Dalili na biyu sabida, sadaukar da rayuwata da nayi sabida ita, wannan dalilin Yasa Gimbiya Asma'u bata da kataɓus akaina, dan tana gudun kar tamin magana nace dan taga ta tallafi rayuwata shi yasa tayi min magana, ban taɓa jin kunya a rayuwata irin na yau ba, da Abdullahi yace zai take ni da mota, sabida yar uwansa, idan na cigaba da tsawallawa. Wata rana zuciya bata da kashi zasu tanka min, dan ma Allah ya basu jarumar Uwa, wacce duk abinda nayi mata bata duba a bisa laifi sai dai ajizancin ɗan Adam."

"Kenan.."
"Don Allah fita ki bani guri bana son damuwa gabaki ɗaya kin chaxa min kai da wanne zanji da naki ko da na yarana, zaki iƴa fita."
Ya nuna mata hanya, fuuuuu tayi waje.
***
Sun kai awa biyu kafin likitotin suka fito, babban cikinsu wanda zai kai kimanin shekaru arba'in ya fara fitowa cikin ɓacin rai yace.
"Dr Kyari! Sam baku kyauta ba, wani irin abune haka, ban da Allah ya takaita wallahi mutuwa zatayi, kun bar mace a cikin mugun yanayi, ina ma mijinta yake?."
Shiru duk sukayi, "Oh sorry bansan ya mutu ba, kunga kodan tunanin mijinta zaisata cikin damuwa, don Allah a kiyayye gaba."
Gyaɗa kai sukayi kaman wasu dolaye, suna tsaye aka turo ni zuwa ɗakin hutu, shafa kaina Ummi tayi cikin juriya tace.
"Allah ya baki lafiya ya shirya zuri'arki."
"Amin" Umma da Abdul suka ce, tafiya Abdul yayi gun biyan kuɗi, aka ce masa Dr Hameed Zaki Katagum ya biya, kome har na yaran sannan zuwa an jima za a maidata ɗakin VIP. Mamaki ne ya kamashi, dan yasan Dr Hameed Zaki Katagum, mutum ne da babu abinda yasa a gaba sai aikinshi baya shiga rayuwar kowa, sannan baƴa kyautatawa kowa, ga tsananin masifa, kowa shayinsa yake sabida mutum neda yatsaya akan gaskiyarsa, baya karya duk abinda ya faɗa iya gaskiyar ce. Basi jima da rabuwa da matarsa, Zuwariyya ba, sabida ta zubda masa cikinsa dan tana shayarwa a cikin asibitin yayi mata tijara, Murmushi Abdul yayi sannan yace.
"Mungode."
Ya bar gurin, dawowa gun Ummi ya faɗa musu abinda ke faru, godiya sukayi tare da sanya mashi albarka.
"Ummi bari naje gida na dawo."
"Allah ya tsare a dawo lafiya." suka ce mishi, da sauri ya tafi.
........
Sophia ta gama abincin rana tana saka kayanta ya shigo gidan, kallon jikinsa tayi a tsorace tace.
"Baby lafiya ? Waye yaƴo a tsari."
"Kwantar da hankalinki Honey, Feener muka kai asibiti ta haihu, amma ba lafiya, babys ɗin suna ɗakin kula da jarirai."
A ruɗe ta kalle shi, "Nikam bari nasa kaya ka kaini."
Ganin yadda duk ta ruɗe yasashi riko hannunta yace.
"Honey! Tana lafiƴa fa muje ki yi min wanka, sannan wai yaushe zaki fara sallah ne na gaji wallahi bayana da marana daurewa nake kawai amma..."
Rufe mishi baki tayi da nata, sannan ta zare towel ɗin ya faɗi kasa, shigewa jikinshi taƴi tare da ɓalle botirin rigarsa, daga nan suka zube gado,
( toh ina zan iya wannan kallon🏃🏃🏃)
........ Bayan wani lokaci suna rungume da juna, sai mita take masa shi kuma yana, shafa bayanta.
"Baby jikina ciwo! Yake min."
"Meye yasa kikayi tsarin iyali? Kuma da zakiyi baki gaya min ba ko baki san zan fiki sanin wani tsari zaki yi ba, gashi ina zaman lafiƴa kin janyo min duƙ wata sai kinyi jini sau uku, plss duk abinda zakiyi ki faɗa min, sabida ni likitane, kuma ina da hanyoyin da zan kiyayye dan ɗauƙar ciki, nima kuma ina son ki huta."
"Kayi hakuri bazan bazan kuma ba."ta faɗa mishi a raunane, tasa mijinta yana da yanayi da mabukatar maza kuma tasan hakuri yake mata, in wani namijine tuni ya tsunduma bin matan layi, tare sukayi wanka sannan suka fito.
Ta ɗauki babban flask ɗinta ta cika da ruwan zafi, kana ta haɗa da manyan kofina guda biyu, sai abincin da tayi tasan bazai ci wani abu a halin yanzun ba. Ta haɗa kome sannan suka fita, can gida yaje ya ɗauki kayanmu a cikin wata karamar akwati ya fito daga gidan.


A bakin get ya haɗu dasu Batul da Khalila, da kuma Khalil ya gaya musu haihuwa,, Batul na shiga cikin gida ta kira Nanah Asma'u ta gaya mata na haihu.
........
Suna isa ana canza min ɗaki, sannan, suka nufi ɗakin. Har dasu Ummi, ajiye kayan yayi zai fita sai ga Masijan ofishin Dr H.Z Katagum, ya kawo kaya niƙi niki, ya shiga dashi, sannan yafita ya sake shigowa da wasu kayan. Bakinsu Ummi a buɗe suke kallon wannan abin mamaki, yana gama shigo da kayan yace.
"Inji Dr Zaki Katagum."
"Mun gode."
Yana fita, Umma ta shiga buɗe kayan. Ledar farko kayan tea ne danginsu Madara ovalti, milo bournvita, cornflas, goldenmo, sugar me iyali, garin coffe, leda na biyun, kuma madaran jarirai ce, da pampas, wipes sai set na kayan sanyi, da kuma kayan jarirai irinsu Overolly, pink nd purple, da kuma wasu yan kananun safarsu. Leda na uku gashashiyar nama ce, wacce taji yankankun kabeje da albasa da tumatir gashi yasha yaji.(😎😏 saura naga cutar kwadayinku ya tashi ni dakune )


....... Mamaki ne ya kamasu Dole Abdul ya fita, zuwa ofishinsa. Koda yaje yasamu baya nan, dole ya dawo. Yana shiga yasami Nanah Asma'u tazo.
"Abban Affan muje ka nuna min jariran."
Karban kayan yayi suka tafi, suna shiga Nurse ɗin da take kula dasu. Tace,
"Dr Zaki yazo ya duba yaran sannan yace za a kawo kayansu,"
Mika mata kayan yayi, ta amsa, sannan ta mika musu safar hannu, ta kaisu har inda yaran suke, kura musu ido yayi an mannasu da juna, suna jin ɗumin junansu. Abin gwanin sha''awa, karewa yaran kallo Asma'u tayi, sannan tace.
"Dukda bansan Babansu ba Dudu yaran nan kamar an raba gardama ne. Domin babu abinda suka ɗauƙa na Didi, hatta farcensu irin ɗaya ne da na Nannah, duba sajensu mana."


Juyawa yaƴi ya kalle nurse ɗin yace .
"Maza ne ko mata?"
Murmushi taƴi sannan tace.
"Dukkansu Matane, Dr ban taɓa karɓan yara kyawawa irinsu ba, kyansu kamar yaran laraba"


Me karatu kayi nazarin kyau irin na Ashraf, asalin balarabe ne dan haka kyan yaran ya zarce ayi bayaninshi a rubuci kalleshi da mahangarka, yaran sun haɗu wai dama bakwaini ne........




Oum Muwadda.....👏👏👏
[2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZAƘA WRITERS ASSO_


*_MASARAUTAR JORDAN!!!_*
_Jordan Historical_
*©2020*
*BOOK ONE*


Page.٢٧


"Kayi hakuri Baby bazan kuma ba insha Allah zan bata hakuri Baby ka maidani ɗakina. Bazan kara ba ka maidani ɗakina kaji baby." ta karshe maganar cikin kuka, jawota yayi gabanshi yana kallon fuskarta a sannu jikinshi na kara sanyi wani irin kewarta yake ji, d'ago haɓɓarta yayi suna kallon cikin idanun juya yace.
"Ina jin tsoron kar na mai dake ki hanani aikata alkhai."
Rufe masa bakinshi tayi da hannuta tare da girgiza kanta.
"Wallahi tallahi bilahi Azim, bazan cuce koda kiyashi ka kawo cikin gidan da sunan naka, bazan taɓa cutar dashi ba dan Allah ka yarda dani."


"Toh irin wannan dadumar kin manta a gidan surukaina nake, don Allah sake ni kafin ki kayardani kin min fyaɗe."
Murmushi tayi tare da kifa kanta a kirjinta, tace.
"Baby I miss u"
"Ke dai faɗi gaskiya, daga ganin ɗ'an Ummi kanin Didi Feener kin gigice" duka ta kai mishi irinta masoya tace.
"Sai na gayawa Didi kana gulmanta,"
Raɗa mata abu yayi a kunne, ta ɗago kanta da sauri tana kallon fuskarshi, gyaɗa kanta tayi tare da ɗaura kanta a tafukan hannunshi. Janye hannunsa yayi ya riko hannunta suka fita, har sun isa gun motarsa.
"Affan fa?"
"Kyaleshi Baby muje kaji."
Murmushi me sauti yayi sannan yace.
"Ban gane ba sai wani rawan jiki kike, ina tsoron karki cinye ni ɗanye."
Dariya tayi sannan tace.
"Ai in danye ne da sauki, if i catch."
"Yarinya ki bi a hankali sau nawa ina win ɗin ki yau ma muje a sake gwada."


"Wayyo Allah ni banja muyi haka da kai ba."
Haka suka isa gidansu sosai suka shirya tsakanin miji da mata ya tabbata.
***
*SAUDI*

"Abisa hujjojin da kotu ta haɗa, mun sallame Sultan Ashraf akan zargin da muke masa, tare da bashi hakuri sai kuma muna gargaɗinsa da kar yakuma yin shiru akan gaskiyarsa, dan haka kotu ta ɗaure shi har na tsawon wata goma babu tara dan ya zama gargaɗi da izina ga mutane irinshi, sannan a gefe guda Mun mika Marhum ga Hukumar kasarshi kamar yadda jami'in jakadar Kasar Jordan ya bukata, alkali na gama bayanin ya mike, nan mutanen cikin kotun suka ce kotuuuuu.
***
Nigeria.
Yau aka sallame ni a asibiti bansan ya akayi ba, sai ganin Dudu naƴi ya wucce damu gidan Abba, kallon Ummi nayi itama ranta a ɓace yake, kana ganinta kasan ranta yakai kololuwar ɓaci, lumshe idanunta tayi taki magana. Kwantar da kaina nayi a kafadarta a hankali kwalla ya shiga sauko min, daga idanuna riko hannuna tayi cikin rarrashi tace.
"Kiyi hakuri kome na duniya me wuccewa ne,Insha Allah wata rana sai labari."
Gyaɗa kaina nayi dan na kasa cewa kome har muka isa gidan.
..... Abinda ya faru kuwa, kwana biyu da suka wucce Anim yaje gun Abba dan ya fahimci da zaran aka sallame ni, Suleja zamu koma da Ummi shine munafuki ya sami Abba da cewa ya maida Ummi wannan ba darajarshi bane ace yar shi da uwargidanshi basa gidanshi kuma ai haka zai zamewa Safeenah abin gori, kuma a matsayinshi na babba me mutunci ya kamata ya kankaro darajarshi a idanun jama'a kar ya bari mutane su fahimci matsalar gidanshi.
Nan Abba ya amince, sannan yaje har Suleja, ya sami Yayan Ummi sukayi magana yace yaje ya same Babban yayansu dake Maiduguri, dan haka yana dawowa. Suka tafi da Anim inda aka maida Auren Ummi da Abba ba tare da izinta ba. Koda suka dawo Sheik Hayatudeen Kamfu ya kira Ummi yayi mata nasiha sannan ya gaya mata,abinda sukayi. Hankalin Ummi yayi mugun tashi data gayawa Abdul kwantar mata da hankali yayi sannan yace karta bari nasani dan ya fahimci ina ganin laifin kaina akan faruwan kome, parking da yayi ya dawo dani daga duniyar tunani. Na kurawa gidanmu ido, gashi nan na sake dawowa. A hankali Ummi ta fita, bangarena Ummi tazo ina fitowa ta miko min hannu na riketa sannan na fito a sannu, ganin Umma tafito ita da bakuwarta ya sani juyawa cikin mota da dan sauri, Ummi ta rike ni tare da girgiza min kai tace.
"Duk wanda yayi miki dariya ko habaici bai san kan rayuwa bane, idan kasan kan rayuwa baka dariyar motar gawa."
Riko ni sosai Ummi tayi, har muka iso gunsu Umma kaina a sunkuye.
"Hajiya Maryam! Ya me jikin dai? Kuyi hakuri ban zo muku jajje ba, sabida ina gudun kar nazo ace gulma ko wani abu na daban, dan kinsan duniya ba a iyar mata."
Murmushi Ummi tayi sannan tace.
"Hajiya Barakah ai duk wanda yazo gulma ko ganin wani abu toh zan iyacewa bai san me ake kira da kaddar bane, amma idan kasanta toh babu ruwanka da kalubalartan nawani."


"Hmm! Hajiya Maryam abar kasa a cikin gashinta, nima kamar yadda ya same ki nima ya taɓa samuna, domin kuwa Rashmar ta taɓa kinkimo min magana, wanda sanadinsa tunda muka rabu da Alhaji har yau bamu dai-daita ba, amma ni na zubda cikin gaskiya sabida damuwar zata min yawa ina zan kai damuwa dan a lokacin ji nayi ina ma bana raye."

Riko hannuna Dudu yaƴi muka shige, yana ce min.
"Kin tsaya bin nasu Ummi, da wancar maganarniyar matar sam magana baya damunta, da kuma suka zubda cikin ai gashi Rashmar ɗin haryau bata sake samun ciki ba, da sun bar mata cikinta maybe da tana da ɗanta na kanta."

"Nima da na rasa wannan babyn maybe har na koma ga Allah bazan rike ɗan kaina ba."
Matse min hannu yayi sannan yace.
"Karki damu Allah ya tsare."
Jingina kaina nayi a hankali nace..
"Dudu! Maganata ta dawo."
"Kuma munata binki ki gaya mana waye yasa a sace ki kinki faɗa sau nawa yan sanda na zuwa sai kice baki sanshi ba."

Bansan me yasa naki gayawa Mutane cewa Anim ne ya sace, kodan yadda ya nuna kulawarshi akan ciwona ne ban sani ba, amma wallahi na tsani Anim fiye da kome a duniya dan bana raba ɗayan biyu yana cikin sawun munafukai, sabida yadda yake pretending a gaban dangina da yadda yake cewa idan ya kama wanda ya sace ni sai yasa an minshi wulakanci da bakar izaya, sai na buɗe baki nayita kallon ikon Allah, mutum ya zama annamimi.


***
Jordan.....
Yau jumma'a bayan sallar Abu Zarri yazo zai shiga mota aka, kuskuran harbinsa. Bobyguard ɗinsa suka ture shi ya faɗi, daga nan aka shiga musayan harbi. Dakyar yan bindiga daɗin suka ware bayan an harbi mutum ɗaya a cikinsu. Koda suka koma gida jikinshi rawa yace.
"Ukshe!!!"
Ya kira da karfi, ɗauka rigarshi yayi. Ya fita da sauri sai gidan Ukshe yana zaune akan keken guragu, cikin zafin rai yakaiwa Ukshe tokari. Cikin izza irinta larabawa yace.
"Duk wanda yayi niyya ya fasa shege ne, idan na kyaleka Wallahi ba jinin Banu Hashim ke bin jikina ba. Wallahi tallahi Ukshe mu fara daga yau har ranar da duniya zata tashi."


"Abu Zarri! Na rantse da Ubangiji sai na hanaka farin ciki, Abu Zarri."
"Idan ka fasa kai shege ne. Banza mara mutunci. Banza kawai wallahi sai dai muga bayan juna."


.......
Banu Nazir..
"Alexandra!! Nazo maka Da tayu me gwaɓi, tsakanin Ukshe da Abu Zarri yayi tsamari, idan muka amshi mulkin kaga jordan ya dawo hannunmu, kuma zan ka goyan."
"Adnan! Kaje babu ruwana da haɗakar kowa, idan ina bukatar mulkin da kowa, iya ni zan kurmushe kowa."


"Zanyi murna idan ka nemi goyan bayanka ɗari bisa ɗari."

"Bana niman goyan bayan kowa Iyani kaɗai gayya. Zaka iya tafiya."
.....
Wato wani zazzafar bala'i ya ɓarke a jordan ga arziki ga mulkin babu sarki, sannan ga kaiwa juna harin bazata dan kowa yunkurin kashe junansu. Kuma duk wannan bala'in babu wata hukuma da tayi yunkurin shiga rigima, sabida an bar abin akan iyakar zuri'a guda suke wannan tashin hankali.
Ammar da Uzaif an barsuna matsayin sune masu, sulhu idan ka gansu sai sun baka tausayi sabida tsabar tashin hankali da ya addabi masarautar, kuma a wannaj yanayin Marhum ya dawo dama duk shirin Ukshe ne, idan yasa aka dawo dashi zai san yadda zai fito dashi, a cigaba da fafatawa.
***
Mikar da kafafuna nayi Anas yana matsa min, ni kuma ina rike da magarya, sai tsotsa nake ina gyaɗa kaina, dan ina sauraron kira'ar sheik Abdul Basi. Cikin suratu Maryam, shi kuma yaron ya dage dai matsamin kafar yake, a lissafina dai wata bakwai kenan, cikin yayi wani mugun girma, idan Abdul yazo zama yake yana min dariya, yace.
"My Mom Babys! Kinga hancinki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login