Showing 24001 words to 27000 words out of 82682 words

Chapter 9 - MATAR DOCTOR COMPLT BY ESHAAT.txt

ESHAAT   

18 Jan 2025

4344

bai dago ba.. Kujeran da jakan ta ke kai ta koma ta zauna tana me jin dadin be mata fada bah...
Haka patients sukayi ta shigowa yana basu appointment sbd yau bazai yi ma kowa operation bah..
Lokacin sallah nayi ta tambayi permission din shi sannan ta fita.. Tana idarwa ta fita wajen asibitin.. Wani shagon snacks da drinks taje ta siyo meat pie da hollandia milk sannan ta dawo office din.. Tana shiga taga duk basa nan. Wani sanyi taji a ranta sbd sauri ko kofar bata rufe ba... Wajen zaman ta ta koma sannan ta dakko meat pie din ta bude hade da yin Bismillah a hankali ta fara ci tana sipping hollandian ta ji take kamar ba a cikin duniyar nan take ba sbd dadin abunda take ci har wani lumshe ido..
Tunda ta fara cin meat pie din Dr.Godwin ke tsaye a bakin kofa ya harde hannun shi yana kallon yanda take cin abincin.. Hannun shi yasa a aljihun ya ciro wayar shi ya seta ta daidai sanda ta saki wani murmushi ya kashe mata hoto sai da ya mayar da wayan aljihu sannan yayi gyaran murya daidai ta na cinye last bite da sauri ta dago tana kallon shi cike da tsarguwa ganin ya kafe ta da Ido da kyar ta hadiye na bakin ta har tana kokarin kwarewa.. Ciki ciki ta fara magana "ji yanda ya kafe ni da idanun shi gashi nan na kusa kwarewa"
Wajen ta ya karaso yace "me naji kina cewa"
"Am.. am.. Ni banyi magana da kai ba"
"Toh da wa kike magana in ba dani bah
"Ni bada kowa nake yi bah"
"Dago ki kalli cikin idona kice bani kike yi bah"
Gamgam ta runtse idon ta dan bazata iya kallon shi ba
Ido ya kafa mata yana kallon yanda ta runtse ido kamar taga abun tsoro ga eyelashes din ta sun sakko har ya bude baki zai sake magana kenan su Jessica suka shigo cikin office din.. Cak suka tsaya suna kallon su jin alaman an shigo yasa Dr.Godwin saurin kallon kofa ganin su Jessica ne yasa shi bata rai hade da galla musu harara sannan ya koma wajen zaman shi se da ya zauna sannan yace "baku iya knocking bane zaku shigo min cikin office anyhow?
"Sorry sir! But mun yi...
"Shhhhh surutun ku ya ishe ni haka bana san jin komai"
Wajen zaman su suka koma cike da jin haushi..
Ita kuma Janan dadi taji atleast shigowan su ya mata anfani...



_2:25pm_ nayi Janan ta fara tattara kayanta dan dama ta saba lokacin da suke office din Dr. Magaji karfe 2:30 suke barin office... wajen table din shi ta nufa dan signing out tana daukan littafin yace "hey miss! what r trying to do?
"Uhum uhumm... ina so inyi signing ne cuz it's almost 2:30pm
"U came late nd u wanna leave early huh!
Shiru tayi ta kasa magana
Ya cigaba da cewa "ba yanzu zaki tafi ba"
"Dr. Pls let me go zan je islamiya kuma bana so inyi latti"
"I said no! Ki koma ki zauna cuz babu inda zaki baki so kiyi latti shine kuma kika zo latti"
"But sir..
Be bari ta kai karshen maganan ta ba katse ta "no but! kawai ki koma ki zauna sai tym din da naga dama zan barki ki tafi kuma karki sake cewa komai as u can see na gaji da magana kin gane ko"
Jiki babu kwari ta koma ta zauna idon ta duk ya cika da kwalla dolenta ta hadiye hawayen ta dan kar ya raina nata... Wayar ta ta ciro dan buga game unlock button ta danna amma taga be kawo ba sai a lokacin ta tuna bata da chargy a waya dan jiya basu kwana da wuta bah gashi bata zo da charger ba na Dr.Godwin ne kawai manne a jikin socket kuma ita asara take ji ta tambaye shi ya bata aro ta gwammace ta zauna a haka.. gaba daya haushi ya cika ta haka tayi ta zama bata aikin komai..
Bangaren Dr.Godwin yaji dadin abun da yayi mata dan ko ba komai yasan taji haushi dama haka yake so.


_3:00pm_ Ruth da Jessica suka yi signing tare da wuce nan fa Janan haushi ya kara kamata ga tsoro kuma duk ita kadai sbd bata san zama daga ita sai Dr.Godwin.. jira kawai take lokacin sallah yayi ta fita daga nan ta wuce gida abun ta... ganin ta kawo ma kanta mafita yasa ta dan murmusa...


_3:55pm_ nayi tayi saurin mikewa dama komai nata a hade yake tace "sir lokacin sallah yayi fa"
Be dago ya kalleta ba gaba daya ma ya maida hankalin shi kan laptop din dake gaban shi kamar yasan plan dinta yace "kije ki zauna bazaki fita ba har sai tym din danayi niyya"
Ido ta zaro waje tace "sir sallah ne fa!
"Yeah ai naji abun da kika ce but zan iya miki favour guda daya ki shiga cikin toilet din nan kiyi abun da zakiyi sai ki shinfida dankwalin ki kiyi a kai"
Zata sake magana ya daga mata hannu "bana san yawan surutu".. Bata da wani option daya wuce tayi haka dan bata san lokacin da zata koma gida ba kuma lokacin sallan zai iya wucewa... haka ta shiga tayo alwala ta shinfida dankwalin ta a kasa ta fara sallah.. tunda ta fara sallah Dr.Godwin yayi tagumi yana kallon yanda take sallan a nutse duk se yaji ta kara burge shi.. ya shagala da kallon ta har ta idar tana juyowa suka hada ido da sauri ta kauda kanta gefe...


_6:15_ hadari ya taso garin yayi bakinkirin ganin haka yasa Janan ta kara rudewa dan bata kaunar ruwa ya taba ta sbd babu wuya mura ta kamata..
Ganin yanda hadari ya taso yasa Dr.Godwin dago da kanshi cike da mugun ta yace "u can go nw"
Wani kallo tayi mishi ji take kamar ta fasa ihu da sauri ta dau jakarta ta fita ko kala bata ce ba..
Da sauri da sauri ta fita daga harban asibitin tana fitowa aka fara yayyafi gashi ta rasa abun hawa dan duk adaidaitan da yake zuwa acike yake duk tabi ta qagara ta ganta a gida haka tayi ta tsayuwa har ta dan fara jikewa sai faman tsaki take yi sbd haushi.. kusan minti 4 tayi a wajen sanna dan adaidaita ya tsaya da wani saurayi aciki ta fada mishi idan zai kaita gashi yayyafin ya fara karfi saurayin yace " Dallah Malam ba kudin drop na baka bah kuma inada in da zani ka tsaya a nan kana bata min lokaci"
Mai napep yace "haba dan saurayi baka ga ta fara jikewa bane? Naga kuma duk kusan hanya daya zamu bi in na kai ka sai in je in ajiye ta"
"Ni ina ruwana to! Kaga in zaka ja mu tafi gwara mu tafi in kuma ka nace sai ka dauke saidai ka bani kudina"
Hannu yasa a aljihu zai ciro kudin ya bashi Janan tayi saurin cewa "aa malam jeka kawai bari in jira wani bana so shiga hakkin kowa"
Cike da jin tausayin ta mai adaidaita ya burga abinshi ya wuce yana Allah wadar da hali irin na saurayin nan shiko saurayin ko a jikin shi..


Haka tayi ta tsayuwa amma ta kasa samun abun hawa cikin lokaci kadan har ta fara rawan sanyi gashi ruwa yayi karfi wani dakali ta hanga sbd babu inda zata fake da sauri ta nufa dakalin ta zauna tare da tusa kanta cikin cinyoyin ta ruwa na dukan bayan ta so take tayi kuka amma ta kasa.. Tana zaune a haka taji horn din mota kin dagowa tayi dan yanda zuciyar ta ke zafi... A hankali ya bude motar tare da fitowa riqe da lema a hannun shi har ya iso gaban ta tare da durkusawa jin an sa mata lema ruwa ya dena dukan ta ga kuma kamshin turaren shi yasa ta dago suka hada ido ya sakar mata wani murmushi mai sanyi.......










*_Rukky Bae_*😏😏😏
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: [11/15, 10:10 PM] Rukky Bae😏😏😏❣❣💋: ❤⚜❣⚜❤⚜❣⚜❤⚜❣ *_MATAR DOCTOR_*⚜❣❣❤⚜❤❤❣❤⚜❣❣❣⚜❣❣❣⚜⚜❣❣⚜⚜❤⚜❣⚜❣⚜❣⚜⚜❤❣








*_Rukky Bae_*😏😏😏




*_wannan page din na sadaukar dashi ga duk daukacin masoya na nagode da soyayyar ku agareni da kuma kwarin gwiwan da kuke bani Allah ya bar zumunci.. soyayyar da kuke nuna ma wannan littafin shi ke kara bani courage wajen cigaba da rubuta muku shi_*
*_Jazakumullah bi khayr_*
*_i luv u lodi lodi_*
😘😘😘😘😘😘😘😘😘




7⃣3⃣




Hada ido suka yi ya sakar mata da wani murmushi mai sanyi wani kallo ta watsa mishi tare da kauda kanta gefe haka yasa jikin shi yayi sanyi ga ruwa na jika shi white sleeve din shi ya jike har singlet dinshi na nunawa haka gashin kanshi ya jike sajen shi ya kwanta lub a gafen fuskar shi.. ganin bata sake kallon shi ba yayi gyaran murya sannan yace "hey! Ki tashi in rage miki hanya danna ga baki samu abin hawa ba in kuma bazaki ba gud nd fyn dan ni bana taimako balle tausayi kema ba wai ina tausayin ki bane kawai naga dama ne"..
Yi tayi kamar bada ita yake yi ganin yanda ruwa ke jika shi yasa tadan ji dadi ita ma ko ba komai shima ya dandana yaji..
Sake magana yayi yace "baki ga ruwa na jika ni bane? Ki tashi in kuma baki so inyi tafiyata"
Tasan sarai in ya tafi bazata samu abun hawa ba amma ita gani take bazata iya bishin ba dama gashi shi yaja mata har ruwa ya jika ta.. ganin bata da niyyar mishi magana yasa yayi tunanin bari ya fada mata magana hala taji haushi ta bishi yace "kina wani pretending kamar baki so ki bini bayan can karkashin zuciyan ki kina jiran irin wannan opportunity kuma karki manta opportunity comes but only once sbd haka ni zan wuce mota na baki minti daya tak ki gama gulman ki sai ki shigo mu tafi" da sauri ya miqe tsaye dan baya san ta samu damar yin magana sannan ya jingine mata leman yanda ruwa bazai jika ta ba ya juya ya fara tafiya wajen mota ruwa na kara jika shi...
Ba karamin haushi maganan ya bata ba amma ta daure dan bata so ya gane taji haushi ko kallon shi bata yi bah.. shikuma a tunanin shi tunda ya gaya mata magana kuma ya juya zai shiga mota hala tayi saurin biyoshi har ya bude motar se ya juya ga mamakin san ko motsi bata yi ba sai ma lemar shi daya gani a kasa ta wurgar
Murmushi yayi sannan yace a ranshi "komai tayi yana mata kyau when she gets angry she looks cute in tayi murmushi she looks more cute... zan so in ganta in tana kuka nasa zeyi fitting dinta" a hankali ya kara komawa inda take amma beyi mata magana ba se dai ya tsaya a gaban ta yana kallon ta yafi minti 2 a haka yaga alaman bata da niyyar tashi balle tayi magana hakan yasa shi yinkurin riko hannun ta dan ya daga ta da sauri ta sake dukunkune kanta abun yaso ya bashi daria se ya dake yace "ki tashi nifa na gaji in kuma baki tashi ba i swear with my life sai na dauke ki kamar baby na saki a mota if u think am joking ki tsaya ki gani" hannun sleeve dinshi ya fara rolling sama ganin da gaske yake yi yasa tayi saurin mike wa tana turo baki amma bata tafi ba ya sake cewa "ohh bazaki iya tafiya ba ko? Shikenan lemme carry u" dayan hannun rigan ya sake nadewa sama ai bata jira komai ba tayi saurin wucewa jikin ta sai digan ruwa yake... gwalo yayi mata sanna ya bita shima sai diga yake yi abun ka da dagon mutum har ya wuce ta ya bude mata kofar gaba a hankali ta shiga cikin motar wani sanyi da kamshi suka doki hancin ta bata san sanda ta lumshe ido bah.. zagayawa dayan side din yayi ya shigo ganin tana rawan sanyi yasa shi kashe A.c sannan ya miqa hannun shi bayan seat din ya dakko suit dinshi daya yi hanging ya sa mata da sauri ta kankame suit din duk yana kallon ta amma beyi magana bah.... Kunna motar yayi suka fara tafiya se sharara gudu yake yi babu me cewa wani uffan shi be tambayeta ina ne gidan su bah itama bata fada mishi hanyar bah jin shirun yayi yawa yasa shi kunna wakar _patoranking na my woman my everything_ lokaci zuwa lokaci yana bin wakar haka sukayi ta tafiya.. agogon motar ta kalla taga 7:30pm ido ta zaro amma kuma ita bata so tayi mishi magana ga ruwa ya kara karfi ganin ya dau hanyar Zaria yasata yin saurin cewa "ba nan bane hanyar gidan mu fa"
"Aww ashe kina kallo se yanzu kika ga daman yin magana? Na riga na dau hanya duk inda na kai ki nan zan ajiye ki"
Baki ta tabe amma can kasar zuciyar ta tsoro ne fal daurewa tayi tace "Hmm ko dai kidnapping dina zakayi ne shiyasa ka bi hanyar nan?......












*_Rukky Bae_*😏😏😏
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: ❣❣⚜⚜❣⚜❤❤⚜⚜⚜ *_MATAR DOCTOR_*⚜❣❣❤⚜❤⚜❤⚜❤❣⚜⚜❤❤⚜❣







*_Rukky Bae_*😏😏😏





7⃣4⃣








[11/16, 7:04 PM] Rukky Bae😏😏😏❣❣💋:
Wani irin daria ya fashe dashi wanda shi kanshi be san ya iya irin ta ba sannan yace "akan wani dalili zanyi kidnapping dinki? After all ni bama san ganin fuskar ki nake ba da ace dai sonki nake yi watakila da nayi kidnapping dinki yanzu dai ban san in sake cewa komai sbd tun dazu kike ta sani surutu kuma ze iya sani rashin lfya ki dinga kwatan ta mun gidan ku kuma bance ki nuna min hanya da hannu ba da baki zakiyi magana sbd ki biya ni maganan da nake tayi tuntuni har sai na kaiki kofar gidan ku in kuma kika ki gida na zan wuce dake in kuma kina tantama ki gwada"
Ido ta zaro waje cike da tsoro a ranta tace "nasan zai iya gwara kawai in mishi kwatancen" da wannan shawaran ta ce "a wurno rd muke"
Yace "Ban san gurin ba sbd haka aikin ki yafara yanzu"
Haka tai tayi mishi kwatance har suka kai kofar gidan.. ko gama parking be yi ba ta murda hannun kofar ta fita da sauri ta shige gate din gidan su ko waigowa batayi bah.. girgiza kai kawai yayi tare da cewa "zamu hadu gobe ai zaki sani ne" sannan ya wuce gida shima..
Tana shiga tsakar gidan su ta tuno da suit din shi a jikin ta da sauri ta fita amma bata ganshi ba haka ta dawo ciki ta cire suit din ta nade shi ta sa cikin jakan ta sannan ta bude kofar parlor'n da sallama ta shiga ganin su Ummiey tayi a tsaitsaye sai kai komo Ya Khaleel ke yi da waya a hannun shi.. jin sallamanta yasa su juyowa da sauri suna tambayan ina ta tsaya har karfe 8:00pm kuma wayar ta a kashe?
Lbr ta basu na rasa abun hawa amma bata fada musu komai ba game da Dr.Godwin.... se a lokacin hankalin su ya dan kwanta..
Daki ta wuce tasa wayar ta a chargy sannan ta shige bayi tayi wanka da ruwa mai zafi hade da wanke suit din Dr.Godwin da kayan ta ta shaya a bayin tana fitowa tasa kayan bacci ta fito daga dakin ta wuce kitchen ta debo abinci ta ci tana gamawa Abbiey yace ta je tayi bacci sbd karta makara ga kuma gajiyan yau...
Sallama tayi musu sanna ta shiga daki.. Imran ne yazo ranta da sauri ta kunna wayar nan taga text msgs daga Imran iri iri wanda yake nuna yanda yayi missing dinta da kuma rashin samun ta a waya.. Murmushi tayi a fili tace "Allah sarki Nurulqalbee nima nayi missing dinka" dialing numb din shi tayi taji number busy tana kashewa ya kirata nan tace "naji number busy ne"
"Ke nake kira ai kin san tun yaushe nake trying layin ki ne"
Hakuri ta bashi tare da fada mishi wayar ce babu chargy.. sosai suka sha hira sannan yace "yau ni zan miki addu'a se ki shafa ki kwanta kinji Angel"
"Yawwa Nurqalbee ina jinka"
Adduo'i sosai yayi mata sannan ta shafa daga bisani sukayi sallama ta juya ta kwanta cike da nishadi....






❣⚜❤⚜❣❤⚜❣


Dr.Godwin na koma gida ya wuce dakin shi towel ya dauka sannan ya shiga bayi ya hada ruwa mai zafin gaske ya dade kafin ya fito ya shirya cikin yellow pyjamas.. dining ya wuce yaci abinci yana gamawa ya koma kan kujera ya kalli kwallo sai wajen 10:00pm ya koma daki nan ma seda ya gama danne dannen shi a laptop yana rufewa yaji kanshi ya fara ciwo nan ya tuno yau through out be sha maganin shi bah da sauri ya ballo yasha har yaja bargo ya kwanta ya tuno da hotan da yayiwa Janan zumbur ya tashi ya dakko wayar shi ya zubawa hoton ido yanda tayi murmushi yasa shi shafa screen din wayar a haka bacci ya kwashe shi....
















*_Rukky Bae_*😏😏😏
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: [11/22, 5:38 PM] Rukky Bae😏😏😏❣❣💋: [11/21, 6:43 PM] Rukky Bae😏😏😏❣❣💋: ❤⚜❣⚜❤⚜❣ *_MATAR DOCTOR_*❣⚜❤⚜❣⚜❤⚜❤⚜❤⚜❤⚜❤❤⚜⚜❤❣⚜❤⚜❤⚜❤❣









*_Rukky Bae_*😏😏😏


_Dedicated this page to_
_Hadiza berrish_
_Pheenerh fulani_
_and all the members of Hauwa Slim Small group_






7⃣5⃣






*~_washe gari_~*


Da asuba Janan na farkawa taji hancinta ya toshe alamar mura kenan dama tayi tunanin haka... bayi ta shiga tayi alwala sannan tayi sallah bayan ta idar tayi daily adhkar dinta se wajen shida saura sannan ta shiga bayi ta dakko suit din Dr.Godwin ta goge har lokacin kamshin turaren shi na jiki kamar be dade da fesawa wa ba a ranta tace "gaskiya wannan ya iya cika turare na wanke riga amma har yanzu kamshin yana nan"
Tana gama gogewa ta wuce kitchen dankali ta soya musu da kwai sannan ta dafa ruwan shayi me kayan kamshi da na'a na'a ta zuba a babban flask se karamin flask kuma wanda zata tafi dashi asibiti sbd mura 6:30am ta gama hada komai na breakfast sannan ta koma dakin ta tayi wanka ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login