Showing 42001 words to 45000 words out of 82682 words
kwance yama rasa wani irin hukunci zai yanke mata.. Can wata dabara ta fado mishi yace "ke! Zo nan! Ba musu taje yayi rubuce rubucen shi sannan ya miqa mata hade da kudi yace kiyi sauri ki siyo min maganin nan dana rubuta kiyi sauri karki bata min lokaci.
Kin karba tayi, cikin hasala yace zaki amsa ko sai ranki ya baci?
Ka aiki masinja mana ai ni aiki na zo ba aike ba ta fada adan tsorace.. Wani mahaukacin tsawa ya daka mata wanda seda ta toshe kunnuwan ta cike da gigita.
Karba nace! kuma saura time din da na baki a cikin zuciyata ya cika baki dawo ba kiga yanda zanyi da ke! .. Jiki a sanyaye idanuwanta sun ciko da kwalla ta karba ta fita...
Jingina kanshi yayi a jikin kujera ya runtse ido hade da yamutsa gashin kanshi "I'm sorry Baby girl I don't mean to hurt u kece kika yi forcing dina na ji haushin ki har na baki aiken da zaki sha wahala cuz baa samun maganin a garin nan se a Egypt ko Lagos.. Kiyi hakuri dole ne inyi punishing din ki sbd in samu peace of mind"
Marasa lfya ne suka fara shigowa yana duba su tare da basu appointment time to time yana duba agogon dake maqale a hannun shi yanzu after 11 kuma tun tara da rabi ya aike ta har yanzu shiru, masinja ya kira yana tambayar shi patients nawa ne a waje sukayi saura?
6 ne ranka shi dade
Good! Kace musu am nt in the mood da zan iya cigaba da duba su kace musu gobe su dawo"
Masinja ze yi magana yace out! Ba shiri ya fita ya ba su hakuri ba yanda suka iya haka suka hakura..
♥♥♥🖤🖤♣♠♠♦♥♦♥
Tunda ta fita take bi shago shago duk inda taje se a ce mata babu se dai ta tambayi wasu shagunan.. Gajiya tayi da tafiya gashi bata fito da kudi ba ko wayar ta balle ta kira ta fada mishi bata samu ba ko ta hau Napepe ta dubo wasu shagunan, agogon hannun ta ta duba taga har 12 tayi ba tada zabi se kara gaba data cigaba dayi da alkawarin 12:30 nayi in bata samu ba zata koma ta fada mishi.
Kamar yanda ta alkawarta time din na cika ta juya ta kama hanyan komawa kamar da bakin kwarya aka fara ruwa ba tada wani zabi daya wuce ta cigaba da tafia ba dan tsoron fakewa take yi sbd yanda taga maza a mafi yawan gurin sun fake haka ta dinga tafia seda taji kafafunta sun kasa daukarta sbd gajia gashi nunfashin ta na wani irin daukewa.. Wani mai adaidaita ta tsaida tace ya kaita Barau Dikko ganin yanayin ta yasa be musa ba ya dauke ta, sun dau lokaci suna tafiya daga bisani suka iso, kudin shi ta bashi dakyar take daga kafa har ta kai kofar office din shi ta tura jikin ta na bari sbd dukan ruwan data sha, tana dago ido tayi mummunar gani nan take jiri ya debeta ta saki salati hade da faduwa kasa sumammiya.....
RukkyBae 😏😏😏
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: ❤❣♠❣❤♠♥♠❤❣♠♥❤❣♠❤♠♥ *MATAR DOCTOR* ♠❣❤♠♥♠❣♠❤♠♥♠❣♠❤♠♥♠
_RukkyBae_😏😏😏
Dedicated this page to one of my fan Saratuh Salisu Usman (Momy Jidderh) thanks for ur support.. Allah ya bar zumunci.
***9⃣1⃣***
*Flashback*
Tun lokacin da Dr. Godwin yace ma masinja ya fada ma patients su dawo gobe ya tashi yake safa da marwa yana leqa window ko zai hango ta amma bata ba alamarta yana cikin haka ya juya baya ji yayi an rungume shi ta baya da sauri ya juyo da ita cikin ihu tace surprise!
Precious budurwar shi ya gani ba wani fara'a a fuskar shi yace "yaushe kika dawo daga UK din?
Shekaran jiya na dawo na sauka a Abuja jiya na biyo morning flight na kwana a Asaa pyramid hotel ban fada maka ba sbd Ina son baka surprise but naga kamar bakayi missing dina ba kuma kaman baka ji dadin gani ba..
No ba haka bane kawai am nt in a good mood kuma kema kin san hali na ai sbd haka ki zauna bana son yawan surutu, da yake tasan halin shi bata ce komai ba ta zauna shima ya zauna tace "Baby zan sha ruwa,
Ga fridge can kije ki dakko akwai cups a cikin wancan show glass din ki dauka dan ba zan iya tashi ba,
ba yanda ta iya da kanta ta dakko holandia ta zuba a cup tana sha, saman table din dayake zaune ta hau tana kallon cikin idon shi seda ta kara sipping sannan ta ajiye tace "Baby anjima zaka zo hotel din dana sauka?
Me zan zo in miki a hotel?
Wani kallo tayi mishi irin na yan barikin nan tace "haba shekaran mu nawa muna tare amma bamu taba hada shinfida ba kuma kasan Ina son hakan tun yaushe nake boyewa na kasa fada maka se dai in nuna maka amma ka kasa ganewa na gaji! Na gaji! I want to hv u I want us to... Cup din data ajiye ya dauka yayi wurgi dash ji kake tasssss! Ya fashe a kasa.
Ke wace irin yarinya ce mara kamun kai? A haka kike kiran kanki Christian? Kina bata sunan idinin ki duk da bana zuwa church amma nasan cewa Zina is prohibited domin Mary wacce kuke koyi da ita bata taba Zina ba!
Shiru tayi tana kallon shi tana mamakin hali irin nashi kamar ba namiji ba amma ta dau alwashin yau seta kauda kwadayin ta a kanshi duk da tana muamula da maza harda manyan maza amma bata bari ya sani ba sbd a sirri takeyi kuma ita burinta be wuce ta hada shinfida dashi ba sbd tana ganin hakan ze sa ya kara sonta (Waiyazubillah), tashi tayi daga kan table din ta zauna akan cinyar shi tana shafa sajen shi a hankali ta fara mishi wani sallo tun yana ture ta har ya fara biye mata sunyi nisa sosai a abunda suke yi a wannan yanayin ne Janan ta shigo ta same su abun yazo mata a ba zata kuma sabon al'amari sbd bata taba ganin haka ba fargaba da tashin hankali ga ruwan daya mata duka su suka haddasa mata faduwa kasa cikin glass din da ya fashe!
❤♠❤♥♠❤♠♥♠♥♠❤
Faduwar ta ne ya dawo dasu daga duniyar da suka lula cikin sauri ya hankadeta gefe "oh no! Damn it! Ya fadi yayo kanta yana girgiza ta, ke! Ke! Ke! Ki tashi mana ki tashi nace! Ki tashi! Ya rude bema lura akan glass din da yake ba har jini na fita a hannun shi itama jini ya bata mata kaya se malala yake yi a kasa kamar an yanka rago.. Precious ce taja tsaki cike da jin haushin bata mata plan da Janan tayi bata damu da halin da suke ciki ba ta dau jakar ta ta fice tana laluban numb din chief dinta yazo dan yau in bata samu abun da take so ba zata iya mutuwa..(Allah ka kare mu daga Zina! Ameen)
Idon shi ya kada yayi jajur gaba daya ji ya ke kaman ze haukace da sauri ya dauke ta cak gaba daya duk jikin ta ya saki, kara tsorata yayi dan gani yake kamar ta mutu.. Da gudu ya nufi emergency room da ita akan gado ya ajiye ta ya fara danna kirjin ta se zufa yake yi duk da sanyin garin, Baby girl ki tashi mana pls open ur eyes daurewa yake yi amma kuka ne fal a cikin shi.. Ganin taki motsi yasa ya sa mata oxygen kwatakwata nunfashin ta yaki zuwa abun ma yaki motsi zama dirshan yayi a kasa yana fadin "pls karki mutu karki tafi ki barni in kika mutu I will definitely kill myself"
Bude kofan akayi Dr.Jalal ne da Dr.Magaji suka shigo dan suna ganin lokacin da Dr.Godwin ya wuce da Janan a hannun shi, da sauri Dr.Jalal yayi kanta yana dubata yace "Ya Salaam! She is an Asthmatic patient sanyi ya shiga jikin ta sosai kuma zuciyar ta tayi sanyi kamar taga wani abun tsoro ko na tashin hankali nunfashin ta yayi nisa gashi kafanta da hannu suna bleeding ta zubar da jini haba Dr. Godwin me yasa baka tsaida jinin ba? Dr. Godwin kasa magana yayi..
Suna cikin haka se ga Dr. Imran ya shigo a gigice sanye da lab coat be bi ta kan su ba ya nufeta yana danna kirjin ta jin nunfashin yaki kawowa ya hada bakin shi da nata yana hura mata iska yafi minti 10 yana haka se abun ya fara reading alamun nunfashin ta ya fara dawowa can ta saki ajiyar zuciya, Dr. Imran da Dr. Godwin suma suka saki ajiyar zuciya lokaci guda.. Dr. Imran yace "I'm sorry banyi introducing kaina ba na shigo without ur permission sunana Imran a Doc. frm Sefa specialist hospital kuyi hakuri da shiga cikin muku aiki amma dole ne inyi haka sbd bana so inyi loosing dinta cuz she is my wife to be in shaa Allah.........
_RukkyBae_😏😏😏
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: ❤♣♠♥♣♥♠❤♣♥♠❤ *MATAR DOCTOR* ♥♣❤♣♥♠♥♣♥♠❤♥♣♠❤♥♠❤
_RukkyBae_😏😏😏
Ina godia a gare ku masoya na kun nuna kulawar ku a gare ni tare da bani kwarin gwiwa.. Allah saka muku da alkhairi ngd da shawarwarin ku kuma in shaa Allah zan yi anfani da shawar ku!! ILYSM😍
Wannan shafin naku NE _YAN MUTAN JOS NOVELS GROUP_! U guys deserve a dedication frm me! Thanks for the love nd the support u always make me happy🤗😃😄 Allah bar soyayya!
***9⃣2⃣***
Wani irin razanannan kallo Dr. Godwin ya ke ma Dr. Imran a ranshi yace "His wife to be? Ta yaya? Wannan shi ake kira Impossible! Gaba daya wani irin haushin Dr. Imran yake ji ko don yanda ya hada bakin shi da na Janan.. Ji yake kamar ya tashi ya shaqe shi
Fatan alkhairi su Dr. Jalal suka mishi tare da taya shi murnan samun yarinya mai tarbiyya irin Janan! Murmushin jin dadi yayi hade da yi musu godia... Wajen ta suka koma Dr. Jalal ya cire mata glass din da suka ji mata ciwo ya goggoge jinin yana mamakin irin yanda glass din ya ji mata ciwo dan harda dinki yayi mata , maganar shi ta dawo da Dr. Godwin daga dogon tunanin da yake yi, hankalin su duk ya koma kan Dr. Jalal din yana cewa gaskiya ta zubar da jini sosai yanzu dole za a kara mata jini..
Eesher ce tayi knocking sannan ta shigo cike da tashin hankali ganin halin da kawarta take ciki! Gaishe su tayi Dr. Jalal yace yawwa kije lab ki ce ta su bani jini leda daya.
Dr. Godwin ne yace haba dai taya za a amso jinin wanda ba a sani ba a sa mata bari in je a diba nawa, be jira abun da za su ce ba ya fice daga dakin, Dr. Imran cikin ranshi yace "ikon Allah! Taya za ayi Ina nan a sa mata jinin wani? Wanin ma Christian?
Bayan Dr. Godwin ya bi ita ma Eesher ta bi Bayan su!
Dr. Godwin na shiga Imran da Eesher suka shigo, sun tarar da Dr. Godwin har ya bada order a diba jinin shi, Nurse din tace "Sir jini na zuba daga hannun ka kuma se an duba jinin ka in zaka iya donating!
Wani tsawa ya daka mata yana fadin ba kida hankali ne? Ni zaki fada ma abun da ya kamata? Kin fini sanin kaina ne ko kin fini sanin blood grp dina ne ko kuma aiki na? In baki sani ba toh ki sani ni A+ ne sannan ni donor ne zan iya donating jini ga kowa!
Sorry Sir! Ta fada dan ta san shi tun zuwan shi asibitin.
Ki riqe sorry din ki dan ba zai mun anfani ba...
Cike da jin tsoro tace
Sir pls ka bari a cire glass din dake hannun ka kuma a tsayar da jinin dake zuba daga hannun ka kafin a diba jinin, kallon hannun yayi dan shi gaba daya ma be lura da ciwon da yaji ba kuma kwalban ya shiga sosai, ba musu yace ma Eesher ke zo kiyi dressing min hannun na kuma make it fast cuz bana son a bata mun time.. Se a lokacin Imran yayi magana da fadin ni yafi dacewa da in bata jini na sbd already jinin ta yana yawo a jiki na nima kuma nawa yana yawo a nata karka damu kanka ni zan bada na hutashshe ka..
Hey! Mr what so ever u call ur self nan asibiti ne kuma baka da iko a kanta sbd she is under my custody inji Dr. Godwin.
Kizo kiyi aikin ki yace ma Eesher, kamar tace ba za tayi ba amma hakan be dace ba ta bude first aid box din dake wajen ta fara cire mishi kwalban.. Kallon shi kawai Imran yayi ba tare da yace komai ba abun ka da mara son hayaniya! Wajen wata Nurse musulma yaje dan ya ga dayar kamar tana tsoron Dr. Godwin yace mata ki diba jini na ki gwada in yayi ki zo ki diba Dan girman Allah kiyi sauri akwai patient da za a sama jinin kuma shi is unconscious!
Ba musu ta diba tare da fadin bani 5 min in duba in gani.. Dr. Godwin be ma san abun da ake ciki ba sbd se yanzu yake jin zafin ciwon ashe kwalban ya shiga sosai zufa kawai yake yi yana jin zafin sosai tausayin Janan ya darsu a zuciar shi yana tuno yanda ta fada akan kwalban dai dai minti 5 din da Nurse ta dawo dai dai lokacin Eesher itama ta gama gama dinke mishi hannun tare da nadewa da bandeji, Nurse din ta dawo wajen Imran tana fadi i'm so sorry Sir ba zaka iya donating jinin ka ba cuz kai ba donor bane, karap a kunnan Dr. Godwin wani irin sanyi yaji ya sauka har cikin kashin shi,
shi kuma Imran gefe ya koma ya durkusa tare da dafe kai dan har wani irin jiri jiri yake ji Innalillahi wainnailaihirrajiun kawai yake nanatawa a zucian shi yana wajen Dr. Godwin ya zo ya wuce shi ya kwanta saman Gado tare da miqa ma Nurse din hannu bata tsaya bata lokaci ba ta fara diba..
Ana gama diba ya dan tsaya minti 2 kafin ya tashi sbd kar jiri ya kwashe shi ya karba ledan jinin yayi ficewar sa.
Jiki a sanyaye Imran ya tashi gaba daya se yaji kamar kafafun shi ba zasu dauke shi ba sbd halin da yake ciki, Eesher ce ta ba shi baki sannan ya dan daure suka koma emergency room din suna zuwa suka tarar har an sa mata karin jinin har lokacin idon ta a rufe suke se nunfashin ta da yake sauka a hankali!
Special room aka maida ta wanda se special mutane ake ajiyewa a nan, se a sannan suka samu natsuwa Imran ya kira Khaleel ya fada mishi abun da ke faruwa..
Ba suyi kyakkyawan mintuna 40 se gasu a asibitin suna zuwa kafin su shiga suka hadu da Imran a hanya shima an kirashi da gaggawa a asibitin su dama lunch din Janan yazo kawo mata ya dinga kira amma wayar bata shiga ba dalilin da hankalin shi ya daga kenan ya zo asibitin yana zuwa ya kira Eesher yana tambayar ta Angel din sa nan take fada masa bata lfya sbd taga an shigar da ita Emergency room..
Har kasa ya durkusa yana gaida Ummiey da Abbiey sukayi musabaha da Khaleel da Saleem sannan yayi musu jagora zuwa dakin, har yanzu bata tashi ba Imran ya koma mota ya kawo abincin da ya taho mata da shi su Ummiey suna ta fadi baka gajia da dawainiya?
Yana sosa keya yace Aa babu komai Ummiey sannan ya fada musu ze je ya dawo an kirashi a asibiti
Fatan alkhairi suka mishi sannan ya wuce..
Suna nan zaune na tsawon lokaci Saleem yana gefen gadon ya zaune se ga Dr. Godwin ya shigo ko ba a fada mishi ba yasan Family'n Janan sbd duk sun yi kama wani irin kwarjini suka mishi be san lokacin daya duqa har kasa yana gaida su Ummiey ba shi kan shi yayi mamakin kan shi sbd be taba duqawa ya gaida kowa ba har iyayen shi tun da yake se yau! Suka amsa mishi sannan ya ba su Saleem hannu suka gaisa Abbiey yana mishi kallon sanni haka ma Khaleel yana mishi kallon sanni amma sun kasa tuno inda suka san shi..
Dai dai nan ta farka hade da yin salati da sauri suka yo kanta in da a tare suke tambayar me ke mata ciwo, da kyar take iya magana tace babu ko Ina ku kwantar da hankalin ku in shaa Allah zan samu lfya....
Kina jin wani pain a jikin ki? Akwai inda yake miki zafi? Dr. Godwin ne ke mata waennan tambayoyin yana kokarin hada ido da ita, ita kuma taki bari su hada idon kuma taki bashi amsa...
RukkyBae 😏😏😏
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: ❤♣♥♠❤♣♥♠♣♥♠♥♣♥❤♥♣♠♥♣♥♠❤♥♣♠♥❤♣♥ *MATAR DOCTOR* ♥♠♥♣♥♠♣♥♣♥♠♣
I specially dedicated this page to u Little Eesher u r no more Little Eesher but Bigger Eesher and also a Mrs to Engineer. Idrees Kabo! Ngd miki sosai sbd kin min abunda bazan taba mantawa ba Allah ya biya miki bukatunki na alkhairi! Allah ya baki lfya! Kece ta farko da kika dawo min da novel din lively kika turo min daga page one nayi murna sosai! ILYSM😍😘
RukkyBae 😏😏😏
Idan kuka duba MATAR DOCTOR za kuga page 89 wanda na rubuta _few days to my birthday_ se kuma wani page 89 din wanda na rubuta _continuation_ karku zama confused duk cigaba ne kuma dai dai ne se kun karanta zaku gane me nake nufi! Ngd sosai da sosai❤♥
***9⃣3⃣***
Ganin da yayi bata da niyyar kallon shi yasa duk jikin shi yayi sanyi, ya fara kokarin cire mata karin jinin da sauri matsar da hannun ta a hankali tace don't touch me with this ur dirty hands"
Stop all this drama and lemme do my work"