Showing 6001 words to 9000 words out of 82682 words

Chapter 3 - MATAR DOCTOR COMPLT BY ESHAAT.txt

ESHAAT   

18 Jan 2025

4321

tuntsire da dariya kana suka miqa ma Ya Khaleel dan fadan abun da suka dauka...............










*Rukky Bae*😏😏😏
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: ❤❣❣💕💕💕❣❣❣❣❣💕 *MATAR DOCTOR* ❣💕💕💕💕💕💕❣❣




*Rukky Bae*😏😏😏






4⃣1⃣**********4⃣5⃣








Ya Khaleel ne ya karba pappern hannun su kana ya kwashe da dariya sannan yayi gyaran murya yace "bari in fara da Saleem.. Abunda zaka dafa shine tuwan shinkafa da miyan egusi then zaka yi pineapple nd ginger juice while Janan will cook jellof rice with veggies sai Chapman juice.... Yanzu dai kowa ya san me zai dafa koh??...... Janan tace "yeah" shi ko Saleem zufa ne ke tsatstsafo mashi ta ko ina hanky yasa ya share gumin fuskar shi yace "gaskiya ni ban yarda ba a sake bamu wani... Ai tuwo yayi nauyi a cishi a dinner"
Ummiey tace "mun riga munyi deciding abun da zaku dafa sbd haka baza a canza bah"....... Janan ta kalle shi ta tuntsire da dariya tace "wa yaga Ya Saleem yana tuka tuwo"
Aiko kamar Saleem zai yi kuka ya kalle ta ''yace karki damu I will surprise u".... Gwalo tayi ma aiko ya mika hannu zai chafko ta ta tsere be hakura ba ya bi bayan ta sai zagaye parlorn suke yi amma ya kasa kama ta sai can da kyar ya kamata sai nishi suke sauke wa yace "wa kike ma gwalo?? Baki ta murguda mishi hannun ta ya kara matsewa.. Arrrgh! Ta saki dan kara..
Abbiey ne yayi magana daga nesa yace "Saleem sakar mi diya ta karka jimata rauni ai ba ita tace ka dauki tuwo bah garin ruwan idon ka ne ka dakko ma kanka tuwo"
Sake ta yayi can kasa kasa "yace zan kamaki ai" gwalo ta kara yi mishi kana ta gudu ta je wajen su Abbiey..
Karfe 1:30pm suka zauna cin lunch bayan sun kammala Abbiey yace"yawwa Baba na ka dauki Muhibbaty kuje shopping kasan wata ya kare kuma gashi zata fara zuwa aiki daga nan ku biya ta wajen Sama'ila tela ku anso dinkin uniform din ta"
Saleem ne ya sosa keya yace "Abbiey ni banda ni za a shopping din? Murmushi Abbiey yayi yace "harda kai mana" sannan ya juya gun Ummiey yace"ki dakko list din abubuwan da zasu siyo miki naso in kaisu da kaina amma yau a gajiye nake"
Nan suka tashi suka shirya sannan suka je parking lot suka dau mota daya suka fice".......








°°•••••••°°••••••••••••°°••••••••
*_Lagos_*


Zaune suke dukkan su a garden suna hira Godwin na zaune sai danne danne yake a laptop dinshi... Annabelle ce ta fito sanye da blue swimming trunks wajen pool ta nufa ta yi tsalle ta fada ciki sai swimming take yi cikin kwarewa....
Godwin ne yace "dad yanzu naga wasu gidaje guda 3 but in different places daya a Unguwan Rimi GRA daya a Sultan Road dayan kuma a Governor Road kuma duka sababbi ne...... Dad yace "let me see" nan ya karkato da laptop din ya shiga nuna mishi Momma frm behind tace "ni I prefer na Governor rd it seems like yafi kyau nd will fit ur style baby"..... Dad "yace u r ryt dear"
Godwin yace "na fi son na U/Rimi cuz is more closer to d hospital" bana son inda zai dinga yimin nisan zuwa asibiti....
Nan suka ce "as u wish" kana sukayi processing komai sannan Dad ya kira wani wanda yayi aiki da shi yace mishi zai turo kudi yaje ya biya gidan da suka siya ya amso receipt da documents din gidan nan Godwin yace har renovating gidan za a sake yi mishi.... Suna gamawa ya shiga wajen furniture nan yaga wanda yake so ashe ma masu furnituren a Lagos suke order ya basu in d nxt 10 days su kai mishi gidan shi dake U/Rimi cuz yau saura 13days ya rage mishi ya tafi Kaduna yaje yaga yanda zai fara aiki...
Yana gamawa yace bari yaje yayi joining pretty a swimming pool kana ya wuce........




*************
*_Kaduna_*
Sun je wajen tela sun amsa dinkin sannan suka wuce Mangal plaza don yin sauran siyayyan sun sayi abubuwa da yawa Janan ta dauki takalma da jakunkuna... purse dinta ta duba bataga list din Ummiey ba, ta tambaye su suka ce "baya wajen su" key ta amsa ta nufi mota dan dubawa.... Ta dakko tana sauri ta shiga cikin plazan sbd ta barsu Ya Khaleel na ta jiranta ji tayi sunyi karo da mutum kayan hannun shi duk sun bare "Ya Salaam" ta fada tare da dafe goshin ta da sauri ta durkusa tana kwashe mishi kayan sai sorry take fada ta zuba kayan cikin leda shiko mutumin kallon ta kawai yake yi kafin daga bisani shima ya duqa yana tayata kwashewa har suka gama
Tashi tsaye tayi tare da mika mishi ledan cikin muryar ta me sanyi take fadin "am sorry pls sauri nake yi mistakenly na bige ka da fatan ka hakura" Bakin ta kawai yake kallo yanda kalmomin ke fita sai murmushi yake mata gashi ya kafeta da idanu... Hannun ta tadan yi waving wajen fuskar shi tana fadin "hello"
Firgigit ya dawo daga duniyar tunanin daya fada ya fara magana cikin inda inda am......meee... Kika ce? Mamaki ne ya cikata a ranta tace "is this guy serious at all? Be ma ji abun da nake ta cewa ba kenan" dan tsaki taja mara sauti kana ta sake maimaita mishi abunda tace murmushi yayi yace "no prob" ya amshi ledar shi bata jira komai ba tayi shigewar ta cikin plazan ko waigowa bata sake yi bah...
Suna gamawa da plaza Janan tace "luvly bro mu biya Mr. Biggs pls daga nan sai muje wannan shagon chocolates wallahi na gida saura kadan.....
Saleem yayi karap yace"bakin ki kamar chocolate sai hakoran ki sun koma na tsofaffi sbd shan zaki" baki ta turo sannan tace "ba abun da zai yi ai ina brushing hakora na sau 2 ko 3 kullum"
Dariya suka yi sannan Ya Khaleel yace" oops! Naso in manta jiya da nake dawowa daga wajen aiki na siyo miki sweets da chocolates amma yanzu zamu biyawa mu karo wasu" kiss ta manna mishi a kumatu kana tace "that's my swt bro sannan suka tafa" haka suke yi duk sanda daya yaba dan uwan shi support ko ya sashi farin ciki.....
Suna zuwa Mr. Biggs duk suka shiga suka kwaso kayan kwalama su ice cream, cup cakes, burger, shawarma, pizza da dai sauran su...... Suna fitowa suka hadu da guy din dazu da Janan ta bige a plaza ido ta zaro a ranta tace"ko dai be hakura bane" gani kawai tayi yana nufo wajen su sai zuba murmushi yake hannu ya miqawa Ya Khaleel kana suka rungume juna Ya khaleel yace "Dr. Imran ashe kana duniya dariya yayi sannan yace " Engineer Khaleel kwana biyu...... Nan da suka gaggaisa tare da tambaya juna bayan rabuwa
Khaleel ne yace "meet my siblings Saleem nd Janan"
Hannu ya miqawa Saleem kana ya juya wajen Janan yace "so she is ur sis! Khaleel yace "yeah! Ka santa ne? Murmushi yayi sannan yace Nasan ta mana..... Ido Khaleel ya zaro yace "a ina kasan ta?
Imran yace tunda sis dinka ce ai na santa kuma dazu mun hadu a Plaza" Murmushi Khaleel yayi kana yace "Maza har yanzu kana nan da halin barkwancin ka"
Janan ce ta gaishe shi sannan Khaleel yace "muna kan hanya ne zamu koma gida" nan sukayi exchanging numbers kafin suka sake shaking hands suka wuce"
Shagon chocolates suka nufa nan fa Janan ta jidi chocolates iri iri Ya Saleem nata mata tsiya....
Sai 4:oopm suka koma gida a gajiya..... Masallaci direct su Khaleel suka nufa ita kuma Janan ta wuce gida.... Tana shiga da sallama taga ba kowa a parlor dakin Ummiey ta leka taga tana sallah nata dakin ta wuce ta watsa ruwa sannan itama tayi sallah... Tana idar wa ta fito parlor nan ta tarar da Ummiey ta fito su Ya Khaleel har sun dawo daga Masallaci harda Abbiey ma ya dawo... Sannu da gida tayi musu kana suka fara firfito da kayan... Har 5:00 suna zaune suna hira kana Ummiey ta daga kai taga time cewa tayi "ya lbrin daura abinci ne? Lokaci ya fara wuce wa"
Ya Khaleel yace "haka ne yanzu 5:00 na baku 15mins ku shirya 5:15 zaku fara girki zaku tsaya karfe 6:45 r we good to go? Nan suka tashi suka nufi kitchen Ummiey taje ta dakko musu apron da hula irin na chefs din nan ta basu sanna aka nunawa kowa wajen da zai yi nashi girkin duk wanda apron da wajen shi is rough za a rage mishi marks su Ummiey ne zasu dinga inspection...........
5:15 on dot Ya Khaleel ya danna wani dan bell dake hannun shi yace start"
When is exactly 6:45 zan danna bell din again ina dannawa u guys will stop! Kun gane? Suka ce "yes"......














*Rukky Bae*😏😏😏
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: ❤❣❣❣💕❣❣❣❣❣💕💕 *MATAR DOCTOR* ❣❣❣💕💕💕❣❣❣❣❣❣❣❣










*Rukky Bae*😏😏😏




4⃣6⃣************4⃣7⃣








***************
Nan su Janan da Saleem suka fara girki. Saleem sai zufa yake yi... Su Ummiey ne suka shigo don yin inspection duddubawa sukayi kana suka koma parlor sai dariya suke ma Saleem sbd da gani har ya fara gajiya
Miya Saleem ya fara daurawa nan yayi ta soya miyar har tayi baki ta fara kauri.. Janan ce ta bude fridge ta dakko ruwan sanyi ta dan kora sbd kaurin miyan Saleem ya fara damun ta... Bude nata girkin tayi gani tayi ya kusa nuna sai kamshi yake yi murmushi tadan sake kana ta rufe tukunyar..
Saleem dai yaga cewa lallai Janan zata riga shi gamawa sai yace" black sisi mudai kar ayi mana half done mu kasa ci ko kuma cikin mu ya baci naga sai wani sauri kike yi"
Dariya take son yi amma ta daure tace" don't worry bazan muku half-done bah"
Kallon ta yayi sai can yayi noticing ashe miyar ta fara konewa maggi kusan guda 10 ya zambada da half spoon na gishiri.....
Janan ce take son yin dariya sai tace "bari in danje inyi fitsari" tana zuwa dakin ta ta zauna a qasa sai kwasar dariya take har da hawaye fuska ta wanke a toilet kafin da kyar ta tashi ta koma kitchen din tana shiga taga Saleem na kokarin rage gas cookern... Tsayawa tayi tana kallon shi taga dai da gaske zai rage kuma zai sa shinkafar tayi ciki biyu.. Da sauri ta karasa tace "aa! Ya Saleem ya haka kuma? Keya ya fara sosawa yana fadin" dama...dama naji kamar abincin na kauri ne" baki ta murguda mishi tace "nidai ka barmin abuna
Sun ci 1hr acikin tym dinsu Saleem bai dade da daura tuwon shinkafan bah.. Itako Janan saura kadan abincin ya nuna.. Chapman drink ta fara hadawa sannan ta fasa kankara ta zuba a cikin Saleem kuwa dama shinkafar ruwa kadan ya samata yana budewa ya tallatso mishi a hannu da sauri ya wurgar da murfin auuuchhh!!! Ya saki kara yana yarfe hannu... su Ummiey ne suka shiga suke tambayar shi lfya?? Ruwa ya debo a bowl ya tsoma hannun shi sannan yace "am OK na dan kone ne" fita sukayi... Suna fita ya sa dakko muciya da gari yana tuqa tuwo!!! ((imagine yanda Saleem ke tuqa tuwo hahhhha)) duk ya bata wajen da gari gashi sai zubawa yake yana tuqawa.. Ya Khaleel ne ya shigo yace " 40mins left 4 u guys" u better start rounding up"Janan tace "am almost done".......
Hango Saleem yayi yanta fada da muciya me zeyi in ba dariya bah!! Sai faman dariya yake can yace "well-done bro!! Saleem ko iya kuluwa ya kulu bai ce komai ba ya cigaba da aikin shi... Khaleel ne ya shiga binciken wayan shi bai gani bah can ya hango na Janan dauka yayi ya fara daukan Saleem video yana tuqin tuwo Janan na daga gefe ta riqe cikin ta sai dariya take yi aiko Khaleel sai video yake musu.
Yana gama tuqawa ko sulala bai bari tuwon yayi bah ya dakko mara da kula ya fara kwashewa duk yabi ya qona hannun shi!! Da sauri ya gama kwashewa sbd saura musu 20mins a kada bell.... Tashi yayi ya dakko pineapple ya fara ferewa sai zabtarewa yake sannan ga baki bakin jikin abarban bai cire bah citta mai uban yawa ya kwaso a fridge ya wanke ko kankarewa bai yi bah ya hada ya fara blending...
Itako Janan har ta gama nata girkin sai kamshi yake yi ta wanke komai tayi mopping wajen sannan ta jere abincin a katon tray har tayi hanyar fita sai ta juyo taga yanda Saleem ke zufa gashi ya bata wajen da yake aiki ga uban kwanuka sai taji tausayin shi ajiye trayn tayi akan wani table sannan ta nufa wajen shi tace "Swt bro bari in tayaka koda wanke plates ne" kallon ta yayi sannan yace "babu ruwan ki dani kawai ki tafi nima na kusa gamawa, ina da 20mins kuma nasan zanyi covering up b4 d tym" tari ne ya sarke shi itama zatayi magana kawai sai tari sbd gingern da Saleem ke blending yayi over.. da kyar ta lallaba ta kwashe kayan ta ta wuce dining area ta ajiye nan Ya Khaleel ya duba tym sannan yayi rubutu a wajen sunan Janan.
Saleem sai tari yake yi amma ya toshe bakin shi kar a ji shi... Bai gama blending bah ya tsula ruwa a ciki kawai ya dakko rariya ya tace sannan ya zambada sugar a ciki... Cokali ya dauka ya dan dana da sauri ya zubar a cikin sink hade da kuskure baki sai yamutsa fuska yake sbd dacin da juice din yayi!!
Kwankwason shi ya rike tare da dafe kai da hannu daya yana kallon shirgin wanke-wanken shi tsaki yaja yace "dama na bari tayi min gashi ni ba wani iya wanke-wanke nayi bah" gaban sink din ya nufa ya fara wanke-wanke gashi da manja yayi amfani da kyar suke fita sai zufa yake gogewa duk ya bata wajen da ruwan kumfa... Ya gama wanke na kan sink din saura na kan table juyawa yayi dan ya dakko sauran kwanukan santsi ya debe shi tiiiimmmm!!! Ya fadi a kasa baya ya riqe yana cije lebe yafi minti 2 ahaka
Khaleel na daga bakin kofa yana video taping dariya yake son yi amma ya daure
Da kyar Saleem ya iya tashi yana daddafa jikin bango har ya isa wajen plates din yana kwaso wa Khaleel ya danna bell din yace" time up!! Saleem kamar ya daura hannu a ka ya saki ihu.. Haka ya kwashe abincin ya fita dashi.... Su Ummiey ne suka shiga kitchen din sannan suka dudduba wajen Janan very clean nd neat while portion din Saleem very rough rubutu sukayi kana suka fito zuwa dining area.. Nan aka kira su... Umma ta kalli Saleem tayi rubutu tana rubutu tana dariya sbd apron din Saleem yayi kaca-kaca sannan ta juwa wajen Janan ta kalleta sannan tayi rubutu ita kuma apron din stains kadan kadan ne a nata ba kamar na Saleem bah daya cabe yayi baki bah.. Tana gamawa ta mika ma Abbiey ya duba.. Sannan yayi gyaran murya ya fara magana kamar haka "Saleem kayi kokari sosai amma baka gama aikin ka akan lokaci bah kuma ka duba neatness dinka dana environment din dakayi girki gaba daya babu tsafta a ciki".. Wajen Janan ya juya sannan yace "Muhibbaty kinyi kokari kema sannan kin gama akan lokaci, environment dinki is neat sannan apron dinki is neat but not very neat sbd akwai stains a jiki.. Yanzu mun gama da bangaren nan saura bangaren tasting abinci amma shi ba yanzu zamu dan-dana bah sai bayan mun dawo daga sallan Isha'i sannan za a dandana aba kowa marks din shi.. Gaskiya kunyi kokari sosai.. Yanzu kuje kuyi wanka ku sake shiri kai Saleem ka taho masallaci ita kuma tayi a dakin ta.. Nan kowa ya tashi ya wuce dan yin sallah

Bayan sallan isha'i Abbiey ya fito daga masallaci ya hadu da wani makocin shi Malam Yusuf suka gaisa anan M.Yusuf ke tambayan ina yaron shi Saleem nan Abbiey yace yawwa M.Yusuf bismillah muje gidan nawa sai ku gaisa daga nan ka tayamu judging kada danka yace anyi masa sankai.. M.Yusuf yace name fah? Nan Abbiey ya fada mishi komai dariya M.Yusuf yayi yace "dan nan nawa akwai rigima"
Gaba daya suka dunguma sukayi gidan su Saleem din.. Suna shiga kowa ya hallara a wajen cin abinci kafin aka bubbude aka zuzzuba a plates.. Abbiey ne yayi magana yace"tor ga M.Yusuf nan sai tayamu judging yanzu dana wa za a fara?? Na Saleem ko na Muhibbaty? Ya Khaleel ne yace a fara dana Saleem sbd shine Babba kowa a wajen yace gaskiya ne. sannan aka bude na Saleem ba abinda ke tashi in banda kauri... Cokali suka dauk dan dan-danawa lomar farko da kyar suka hadiye sbd maggi da gishiri yayi over ga tuwon danye ko dahuwa bai yi bah gashi yayi tauri.. Pineapple nd ginger drink din suka dauka dan sha ko zasu ji dan sauki sauki aiko suna sawa a baki har rige rigen zubar wa suke acikin wani dan bowl sbd tsabar dacin da drink din yayi gashi yayi baki Abbiey da Ummiey suka kalli juna sukayi ya mutsa fuska a tare... Kan Saleem a kasa sbd yasan beyi abun kwarai bah
Na Janan suka bude ba abinda ke tashi sai kamshi a hankali suka sa cokali suka fara dan-danawa sai da sukayi wajen loma 5 sannan suka dan-dana drink din lumshe ido

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login