Showing 57001 words to 60000 words out of 82682 words

Chapter 20 - MATAR DOCTOR COMPLT BY ESHAAT.txt

ESHAAT   

18 Jan 2025

4324

ta lallaba ta shiga gida..


Da Sallama ta shiga parlor nan ta tarar da Ummiey a zaune tana kallon Sunna TV seda ta zauna sannan Ummiey tace "ya akayi? Anyi gwajin? Me Likitan yace?
Nunfashi Janan taja sannan tace "an deba jinin mu amma Likita yace ze kira Daddy ya fada mishi yanda ake ciki"


"Toh Allah yasa muji alkhairi" inji Ummiey.


Janan ta ansan da Ameen tace Ummiey bari in shiga ciki...






Da yamma Abbiey ya dawo bayan sun mishi sannun da zuwa Janan tace Abbiey naga yau duk ka gaji bari in kawo maka abu me sanyi kadan sha sbd naga yau Garin anyi rana"


Yace ''yawwa Yar Albarka"


Zobo ta kawo mishi me sanyi ta ajiye akan center table sannan ta zuba mishi a cup ta mika mishi, tas ya shanye tare da fadin Alhamdulillah sannan ya kara da fadin dazu Mahaifin Imran ya kira ni yace zuwa bayan Isha'i zasu zo harda Likitan sbd ayi komai cikin yarda da aminci, toh da dai nace musu ai duk daya muke babu wani matsala se naga sun fi son ayi komai dalla dalla sbd aba kowa hakkin shi se nima na amince da shawarar su yanzu dai ku shirya zuwan su"


Ummiey tace Toh ba matsala Allah ya kawo su lfya"








Ummiey , Abbiey, Daddy, Imran, Janan da Likita duk zaune suke a cikin Parlorn baki suna jiran bayanin Likitan duk sun kagara sbd ko Daddy be san komai akan result din ba ..


Murya Likita ya gyara sannan ya fara bayanin shi "kamar yanda kuka sani wannan gwaji anyi shi sbd sanin kwayoyin hallitan Janan da Imran kuma anyi haka ne sbd gudun fadawa hatsari tare da gujewa cutar sickle cell, sakamako ya nuna za su iya aure kuma su samu iri amma fa kaso mafi yawa daga cikin yaran zasu kasance masu dauke da sickle cell domin kwayoyin hallitar su dayane maana genotype din duk su biyun AS ne wanda a kimiyance akwai Babban hatsari idan AS da AS suka auri juna,
Amma wasu sukan dauki risk din yin haka wanda kuma daga karshe suke regretting abun da suka aikata.. Yanzu dai ku a matsayin iyayen su ku zaku yanke hukunci..
Ya koma ya zauna.
Shiru parlon ya dauka kamar babu masu rai a ciki domin gaba dayan su hankalin su ya kai kololuwan tashi... Zufa ne ya fara ketowa Imran frm no where ita ko Janan wani irin kyarma jikin ta yake yi kamar me fama da fever....


Har yanzu dai babu wanda yayi magana can dai Abbiey yayi karfin hali cikin dashashshiyar murya ya ce "Likita munji bayanin ka kuma mu bamu isa muja da hukuncin Ubangiji ba muna adduaar Allah yasa haka ne mafi alkhairi kuma mun yarda da kaddara me kyau ko mara kyau sbd dukkan mu nan Musulmai ne suma Yaran Allah ya basu hakuri da Juriyan rashin da suka yi"


Daddy yace "nayi bakin ciki kuma nasan munyi babban rashi domin samun irin Janan se an tona kuma samun iyaye irin ku masu mutunci da dattako se a tona amma haka Allah ya tsaro mana kuma ya fimu sanin dalilin haka"


Abbiey yace babu komai hakan kuma ba yana nufin ba zamu dinga zumunci ba da yardar Allah yanzu ma muka fara fatan mu dai Allah ya musanya musu da mafificin alkhairi..


Janan da Imran kuwa ji suke kamar rayuwar su ta kare, dan a wajen suka zauna suna kuka kamar ransu ze fita dukkan su sun kasa controlling hawayen su babu wanda be tausaya musu ba, Ummiey ta janyo Janan jikin ta tana shafa mata baya alaman rarrashi da kyar Daddy ya lallaba Imran ya tashi amma ya kasa tsayawa balle ya yi tafiya haka Daddy da Dr suka sa shi a tsakayi suka bashi support dan da alama ba zai iya tafiya shi daya ba...
A haka suka bar gidan ranan dai sunga tashin hankali dan Janan seda Ummiey da Abbiey suka dinga bata baki suna mata nasiha ita dai binsu kawai take yi da ido,
har daki Ummiey ta rakata tayi mata adduaa sannan ta rufa mata bargo ta fita..


Gefen Imran kuwa sambatu ya dingayi tun suna ganin ze dena har suka fara tsorata, Mummy ce ta debo ruwa a cup tayi mishi adduaa ta bashi yasha sannan ya dan yi shiru cikin yan mintuna kadan bacci ya dauke shi..


Can cikin dare kamar hadin baki suka farka lokaci daya se a lokacin abun ya kara dawo musu sabo daidai lokacin da Janan ta dauka wayarta kiran Imran ya shigo da kyar ta iya hada wayan da kunne ta dan kwatakwata bata jin karfi a jikin ta.. murya can ciki tayi mishi sallama shima cikin mutawar jiki ya amsa seda suka dau kusan minti 2 suna sauke nunfashi kowa yana tausayin dan uwan shi can dai Imran yayi karfin hali yace "Angel shikenan yanzu Ina ji ina gani zan rabu dake? Duk tsawon lokacin da muka dauka muna gina soyayyar mu me tsafta yanzu duk ya tashi for nothing? Ban san wani hali zan shiga ba na rashin ki bazan taba jin dadin rayuwa ba tare da ke ba pls kice min mafarki ne ya fashe da wani irin kuka itama dai Janan din kuka take yi sbd bata taba zaton wani abu ze rabata da Nurul Qalb din ta ba amma yau gashi sun rabu rana tsaka.... Ita kuka shi kuka babu me lallashin wani a haka har bacci ya sake awon gaba dasu ba tare da sanin su ba.....






Tsayawa fadin irin tashin hankalin da Masoyan suke ciki abu ne me matukar wahala... Daka gansu kallo daya zaka musu kasan zuciyoyin su na azabtuwa da rashin juna kwata kwata Imran ya dena fita ya dena zuwa aiki kullum yana daki daga massalaci se daki abinci kuwa ba a magana Dan ko kallo be ishe shi ba tun su Daddy da Mummy suna fada har suka koma lallashi da ban baki tare da adduaa...


Ita ko Janan ta zama kamar mutum mutumi daga ido se ido be fi tayi magana sau 4 zuwa 5 ba a rana... Saleem da Khaleel kullum suna janta a jiki sbd su rage mata damuwa amma abun yaci tura..




_Hmmm! Ciwon so ba shida magani_






RukkyBae 😏😏😏
[11/10/2017, 10:33 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: [11/10, 8:21 PM] RukkyBae😏😏😏❀❣: ❀♣β™₯♣❀β™₯♣❀♣β™₯♣β™₯❀β™₯♣β™₯❀♣β™₯❀♣β™₯❀♣β™₯❀♣β™₯❀β™₯ *MATAR DOCTOR* β™₯♣❀β™₯♣❀β™₯❀♣❀♣❀❀♣❀♣β™₯❀








_RukkyBae_😏😏😏






🌐 *HAJOW*🌐
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*✍🏻✍🏻✍🏻








_Mutuwa, Aure, Arziki, Haihuwa, Daukaka.. Duk na Allah ne kuma lokaci ne.. Ya Rabbi ka cire mana son Duniya da abunda ke cikin ta_










1⃣0⃣4⃣








Yau tun 12 na rana su Eesher ke gidan su Janan suna ta jan ta da hira suna da ban baki. Sosai taji dadin zuwan su ko ba komai sun rage mata wani radadi da take ji a zuciyar ta dan in tana tare dasu dole su sata farin ciki.. Zee ta kwashe da daria harda hawaye Eesheer da Janan suka kalli juna hade da daga gira suna juya yatsansu a setin kansu alamar 'notin kan Zee ya kwance' can ta dakata tana ce musu ku dena mun kallon nan kamar kun ga wata mahau .."
Suka hada baki da fadin "kaciya cuz we see za example" (kalan turancin da suke yi in suna tare wanda su kadai suke ganewa)
Tare suka yi daria wannan karan sannan Zee tace "kun tuno lokacin da muka sama Mr. Jolly mayen mata bawon ayaba ya zame? Daria suke kaman sun sha laughing gas da sun tsagaita se su cigaba.. Janan tace secondary school memories Allah dai ya yafe mana amma mun tsula tsiya.. Nan fa suka dinga tuna rashin jin da suka yi.. Se yamma likis suka tafi gida..


****


Ummiey da Abbiey na zaune Janan ta fito daga daki duk ta rame a yan kwanakin nan sbd tun randa suka yi waya da Imran ta cire SIM card din ta dan ba zata iya cigaba da jin muryar shi ba tunda kaddara ta riga fata sbd jin muryar shi na kara dagula mata lissafi tare da fama mata ciwukan da warkewar su ba nan kusa ba..


Zama tayi tana fadin "Ummiey, Abbiey barkan ku da hutawa"
Tare suka amsa mata cike da kulawa.. Ganin tayi shiru tana wasa da yatsun ta suka gane akwai maganar da take son fada., Abbiey ne yayi saurin cewa "Muhibbatie bakin ki kamar akwai magana, ki fadi abun da ke ranki idan muna da iko zamu miki maganin shi da yardar Allah"
Har yanzu dai wasan take yi da yatsun ta sannan tace "dama Ina so ne in ajiye aikina" ta karasa maganar muryan ta na rawa..


Haba Hulwaty kina so ki dinga zama kina tunani ne? Ni a nawa ganin kamar zaki fi sakewa in kina wajen aiki tunda ga su Aisha suma sa debe miki kewa ga kuma aiki zaki dinga yi ba kida lokacin tunanin wani abu" Ummiey tayi maganar..


Abbiey yace haka ne amma bari mu gani zuwa nan da 2 weeks din da aka bata a wajen aiki ya cika tukunna kin san na fada miki suna so suyi min canjen wajen aiki daga nan zuwa Abuja"


Ummiey ta jin jina kai tana fadin "Toh Allah ya zaba mafi alkhairi mu fara shiri kenan..






An tabbatar ma dasu Abbiey maganar komawan su can din bayan ya dawo gida ya fadi ma su Ummiey Janan kuma ya tayata ta rubuta takardar barin aikin amma can kasan zuciyar ta tana jin ba dadi dan ko ba komai za tayi kewar fadan su ita da Dr. Godwin the mighty kamar yanda take ce mishi...


Su Zee sun sha kuka sbd za suyi kewar ta shi kuma Dr. Magaji yayi mata fatan alkhairi amma shima ya san za suyi rashin Nurse me tausayi da sanin makamar aiki..


Cikin kankanin lokaci aka gama komai aka kai takardan ta Ministry of Health suka buga stamp me tabbatar da ajiye aikin nata..




********


Wuse zone II nan sabon gidan su Janan yake gidan me kyau ba wani babba bane amma komai daidai su har BQ inda Ya Khaleel da Ya Saleem zasu zauna tunda sunki aure... Allah yasa sun yo takeaway suna zuwa suka baje suka ci abinci dama tun a hanya sukayi sallah hutawa kadan suka yi sannan suka dan yi gyare gyaren su...






β™₯


Yau ta kama Lahadi su Dr. Godwin suka dawo daga Garin Makarfi in da aka tura su dalilin bude wata Babbar asibiti cike da Nasara da jin dadi suka dawo Garin Kaduna babu ma kamar Dr. Godwin wanda yake jin shi kamar wani sabon halitta yanzu ya fara sanin dadin rayuwa da kuma abubuwa da dama daya rasa a shekarun baya masu yawa.. Allah Allah yake Gobe tayi ya koma office ya ga Janan din shi wacce yake matukar missing ga kuma labaran da yake son bata, kwanakin baya ya sha trying numb din ta amma baya shiga ya dan damu amma kuma se ya basar yace ko ma dai mene ne ai ze dawo... A gajiye ya koma gida seda yayi wanka yaci abinci sannan ya kwanta bacci duk ya kosa gobe tayi.. Ya farka yafi sau 3 duk a tunanin shi safiya tayi amma gani yayi Daren ya mishi tsawo....












_RukkyBae_😏😏😏
[11/18/2017, 5:14 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: [11/14, 7:15 PM] RukkyBae😏😏😏❀❣: ❀♣β™₯♠♣β™₯♣♠β™₯β™₯β™₯β™ β™₯β™₯♣β™₯♠♣♠♣β™₯β™₯♠❀♣β™₯♠❀β™₯ *MATAR DOCTOR* ❀β™₯♣♠❀♠♣β™₯❀♠♣β™₯❀♠♣β™₯❀β™₯










_Rukkybae_😏😏😏








🌐 _*HAJOW*_🌐
*_HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS_*✍🏻✍🏻








_Wannan shafin na sadaukar da shi ga duk wata UWA da ta rasa Ya' ko Da' ubangiji Allah ya baku juriya da hakuri, Allah yasa ma su ceton ku neβ™₯❀_....

_FROM ALLAH WE ARE AND TO HIM WE SHALL ALL RETURN_😭😭






1⃣0⃣5⃣






β™₯






Kiran sallan farko Dr. Godwin ya tashi yayi wanka yasa wani yadi sky blue mai laushi wandon pencil ne ita kuma rigar bata karasa gwiwar sa ba da sauri da sauri yake saka links din rigan agogon shi baki dake kan mirror ya dauka ya fito parlor yana zuwa yaga har Agnes ta gama jera breakfast akan dining table.
Ba ya jin ze iya tsayawa ya karya sbd tsabar zumudi.. Tea ya hada da sauri ya sha sbd be son ya bar cikin shi empty dan ma ya san anfanin breakfast a jikin Dan Adam if nt ba zai ci komai ba..




Bakwai saura kwata ya karaso asibitin, da izzan shi yake tafiya da ganin shi zaka san yana ji da samartaka yana tafiya ma su aikin wajen na gaida shi ga mamakin su yau da fara'a ya dinga amsa su a haka har ya shiga office din shi, tas ya ganshi komai a gyare se kamshin air freshener ke tashi a hankali ya lumshe idon shi yana shakan kamshin kafin ya bude ido, kujeran shi ya zauna ga takardu himm a kan table din yace ''huh akwai aiki" daya bayan daya yake duba takardun can wani takadda ya fado cikin envelop cike da gajiya ya duk'a ya dakko har ya ajiye a gefe. se can zuciyar shi tace ya bude, hannu yasa ya jawo ya bude, abun da ya gani ya bashi mamaki kwata kwata ya kasa yarda da abun da yake karantawa,
jingina yayi da kujeran a hankali yake ma kanshi magana "calm down, take a breath, ba gaskiya ba ne"


Ido ya budewa ya kara karantawa kusan sau 5 sannan ya fara fadin "why Janan? Why? Me yasa za kiyi min haka? Me yasa zaki ajiye aiki ba tare da dalili ba ba tare da kin tambayi shawara ta ba, ba tare da sani na ba? Ya kike so in yi? Me yasa? Me yasa zaki tafi ki barni bayan yanzu nake bukatar ki d most? Oh My God!
Wani daci yaji bakin shi nayi mishi, kamar an tsikare shi ya tashi da takardar ya bar office din..


Office din Dr. Magaji ya nufa sbd ya mishi karin bayani dan shi ya bar ma amanan Janan kuma yaga sa hannun shi a cikin takardar wato harda amincewar shi akan barin aikin ta...


Ko knocking be yi ba ya tura kofan, a rufe ya ji ta se yanzu ya tuno irin sammakon da yayi, da karfi ya buga kofan yana fadin "shit!


Kai komo ya dinga yi lokaci zuwa lokaci yana duba agogon hannun shi gani yake kamar time baya gudu..


Se karfe takwas saura sannan Dr. Magaji ya shigo asibitin sbd hold up da ya rutsa dashi a hanya.. Cike da sakin fuska suka gaisa da ma'aikatan wajen sannan ya bude kofar office din..
Dr. Godwin dake jingine da bango ya dafe kan shi be lura da zuwa shi ba,
Karan rufe kofa kawai yaji da sauri shima ya tura kofan ba tare da yayi knocking ba.. Yana shiga Dr. Magaji ya juyo da sauri dan ko kaiwa da zama be yi ba yaji an hankado kofar ba tare da anyi knocking ba,
Cike da mamaki yace "a a Surgeon G yaushe a gari?
Ba tare da fara'a ba ya dan yamutsa fuska yace a takaice "jiya"


"have a seat" yace mishi lokacin yana kokarin zama a nashi kujerar..


"No, thanks ba zan zauna ba ina so na koma office akwai aiki sosai dama ina so muyi wata magana ce"


"Uhum am all ears"


Takardan ya mika mishi ba tare da yace komai ba..


Hannu Dr. Magaji yasa ya amsa ya bude se a lokacin ya tuna ba su yi maganar da shi ba yace "Ya Salaam! Ka ga na manta koh! thou dai na tura maka through email din ka naga kuma baka yi replying dina back ba"


Ba karamin kimar Dr. Magaji yake gani ba shiyasa yake kokarin controlling temper din shi,
a hankali yace "ni ban gane komai ba kaina ya kulle I need more explanation yanda zan fahimta"


Nan ya bashi lbrn yanda tazo ta fadi mishi zata bar aiki duk da yayi kokarin ya fahimtar da ita kan aure baya hana but tayi insisting akan tana son ta bar aikin maybe mijin ta ne baya so shiyasa kawai na sa hannu Ministry of Health suma suka amince suka buga stamp!


Gaban table din ya karasa tare da dafawa yace "excuse me! Kamar aure naji kace!


Dr. Magaji yace "yea aure za tayi gama IV din bikin'' ya jawo drawer din shi ya ciro katin yana mika ma Dr. Godwin


Jikin shi na kyarma ya karba da baya da baya ya fara tafiya seda ya kai kan wani kujera dake can nesa yayi zaman yan bori yana jin iskar wajen na ko karin dena kaiwa inda ya kamata duk da AC dake kunne...
Zazzare ido yake yi yana kokarin karantawa dan gani yake size din idon shi sunyi kanana wajen karatun yafi minti 2 kafin kwakwalwar shi ta fara aiki sannan ya fara gane abun da yake karantawa, yi yake yana karawa ya gane komai amma ya kasa hana kan shi karantawa, wani irin zufa me zafi ya fara karyo mishi, hannu yasa yana balle botiran rigan shi ko zai ji iska amma ina! Kamar ma yana karama kan shi zafi ne...


Dr. Magaji dake gefe ya zuba mishi ido cike da mamaki, duk da shi ba malamin soyayya bane yana ganin kamar Dr. Godwin yana son Janan din...


Ji yayi Dr. Godwin ya ruko hannun shi duka biyu yana fadin "Ba da gaske bane ko? Kace min wasa ne, ka ce min idona ba su gani da kyau, kace min ba au... Ya kasa karasa maganar dan ba zai iya fadin wai Janan din shi zata auri wani ba, idon shi yayi jajawur zuciyar shi na zafi so yake yayi kuka ko zai samu relief amma ya kasa...!


A hankali Dr. Magaji ya fara bubbuga bayan shi har zuwa lokacin be yi magana ba sbd be san abun da ze ce mishi ba kuma ba zai iya yi mishi karya ba... Ganin da yayi ba shida niyyar magana yasa shi wani irin murmushi wanda gara kuka a kan shi sannan yasa kai ya fice daga office din ba tare daya kara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login