Showing 12001 words to 15000 words out of 82682 words
dau hanyar Kaduna... Sun shigo Kaduna ana ruwa..direct gidan Godwin Lawal ya kaishi gidan shi wanda ya matukar tsaru ba kadan bah idan na tsaya baku lbrin haduwan gidan Godwin sai hannu na ya qage u guys should jst imagine yanda gidan ya tsaruπ.. Har ciki suka shiga Lawal ya kara nunnu na mishi kayan gidan.. Nan ya ciro kudi a jakar shi yace aje a siyo mai kayan kitchen da food stuffs. Sake ciro wasu kudin yayi yace "gashi ka kara mai a mota". Godiya sosai Lawal yayi sannan ya tafi da alkawarin gobe zai kawo mishi saqon daya aike shi. Dakin shi ya wuce yaga komai yayi yanda yake so fadawa yayi kan gadon yana sauke numfashi sai da yadan huta kafin ya tashi ya shiga wanka. Bayan ya fito ya gyara jikin shi sannan ya haye gadon tare da jan bargo ya soma bacci..
******************
Janan zaune a kasa kan pillow ta daura kanta a kafar Abbiey yana tsefe mata kalaban da Ummiey tayi masa last week. A hankali Abbiey ke mata tsifan ita kuma tana buga farm heroes a wayar shi. A tare Khaleel da Saleem suka shigo da sallama suka gaishe su sannan suka sami waje suka zauna. Ummiey na daga gafe tace "Wallahi kai kake kara shagwaba yarinyar nan kaida Khaleel... Kiri-kiri yarinya bata yarda kowa ya tsefe mata kai sai ku!! Murmushi Abbiey yayi yace in ban shagwaba ta ba wanake dashi dazan shagwa.. Kafin ya karasa wayar shi dake hannun Janan ta fara ringing da sauri ta miqa mishi tace "Uncle Justice Abubakar ke kiran ka Abbiey". Daukan wayan yayi ya kara a kunnen shi tare da yin salllama... Sun dan dau lokaci suna wayan kafin Justice Abubakar ya kashe" miqewa Abbiey yayi yace "an kirani a office munada wani case.. Addua'a suka yi mishi sannan ya tafi.
Khaleel ne ya dauki kibiyan ya cigaba da tsefe ma Janan kitson. Ummiey ta tashi ta wuce daki shi kuma Saleem ya tabe baki yace " ke wai auta koh? Har tsifa ma yi miki ake yi. Idan kinyi aure ai sai muga me yi miki caraf Khaleel ya amshe yace "mijin ki zai dinga yi maki koh princess? Tashi tayi da gudu ta bar wajen sbd kunyar maganan da Ya Khaleel yayi mata.. Saleem ne ya daga murya yace kunyar karya ne.. Duk suka tuntsire da dariya Khaleel yace "kaga kasa taji kunya koh? Ko tsifar ma bamu gama bah anjima ma karasa..
*Rukky Bae*πππ
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBaeπππβ£β£: β€β£β£πππππππβ£ *MATAR DOCTOR*β£ππβ£β£β£β£β£ππ
*Rukky Bae*πππ
5β£4β£**************5β£5β£
*Waye Imran*
Imran Mahmoud Sambo d'a ne ga Alhaji Mahmoud da Hajia Firdausi... Su 6 ne a gidan shine Namiji daya a gidan kuma first born sai kannen shi mata 5.. Yayi pry da sec sch duk a Lagos sai yayi karatun likita a ABU Zaria.. Matashi ne mai jini a jika kyakkyawa asalin dan Zaria... Yanada tsawo amma ba sosai bah komai dai nashi moderate.. Ma'abocin tsafta, hakuri, ladabi,biyayya da riqon addini,fara'a.. Saidai be iya fushi dan ba karamin shakkar shi kannen sa keyi bah.. yanada kimanin shekaru 28 a duniya aboki ne wajen Khaleel Yayan Janan domin tare sukayi ABU inda shi ya karanci Likitanci while Khaleel ya karanci Engineering... Yanzu haka shi cikakken Medical Doctor ne....Wannan kenan..
*Thursday*
*7:30am*
Janan, Aisha, Zainab duk zaune suke suna jiran a kira sunan su..Messenger yace "Zainab da Aisha likita daya zai musu interview while Janan ita wani Dr. zai mata nata interview din sbd office dinshi aka kai nata file din.. Zainab aka fara kira daga ita sai Aisha duk a office daya inda aka rubata Dr. Magaji a jikin tag ... Sai zaman jiran ayiwa Janan suke yi sbd Dr. din da zai musu bai dade da zuwa bah kuma ga layi dan itace ta kusan 14 kuma da wuri ta zo.. Sai wajajen 2:55pm aka kira Janan duk bata cikin walwala sbd an raba musu office dasu Zee ga zaman jiran da sukayi tayi.. Da kyar ta tashi idon ta duk ya ciko da kwalla sbd bakin ciki haka ta dinga tafiya kamar kwai ya fashe mata a ciki.. Knocking kofan tayi tafi 2mins kafin daga ciki aka ce "come in" a takaice.... Gaban ta sai faduwa yake yi cikin rawar murya tace "As..sala..mu alai..kum".. be dago ba bare yaga wacece sbd muryar ta ta haifar mishi da wani mummunan faduwar gaba a take kanshi yayi masa nauyi.. Rubutu yake yi amma ya kasa cigabawa gaba daya jikin shi ya dauki rawa.. A zuciyar shi yace "what d hell is wrong with me" gaba daya natsuwa ta gagare shi.... Janan kanta a kasa sai tsayuwa take gashi be dago bah bare ya bata wajen zama. Sun fi 3mins a haka can dai ya dage ya dago a hankali dai dai nan itama ta dago "Ya Salaam! Abunda tace a hankali kenan sbd tsoro bata manta fuskar shi ba shine dai same guy din daya watsa mata cabalbali ranan Monday.. Bangaren Godwin kuwa zufa ne yafara keto mishi ta ko ina ya rasa dalili.. ido ya kafeta dashi Allah yaso shi sanye yake da bakin sunglasses idan ba haka ba da sai taga yanayin shi.. A kasalance yace "sit" da sauri ta zauna a wani kujera dama duk ta gaji da tsayuwa... Karfin A.c ya kara sannan ya cire suit din jikin shi ya rage sai shirt din ciki.. "What's ur name? Abunda yace kenan.. Janan Pharouk Makarfi tace mishi... File dinta ya dakko ya miqa mata ba tare da ya kalleta bah yace "am tired I can't attend to u nw. U can come bck tmrw" ranta ya baci sosai bayan jiran da tayi zai ce mata ya gaji.. Hannu ta mika a hankali zata amsa.. Fasa bata yayi can yayi wani tunani sannan yayi rubutu a yar paper ya miqa mata hade da file dinta ba tare da yayi magana bah.. Fushi tayi ko tambayen shi me zatayi da paper'n bata tsaya yiba kuma bata san ya zatayi bah.. Har ta kai bakin kofa tasa hannu kan handle din kofa yace "HEY((Ke))" tsayawa tayi ba tare da ta juyo bah shima bai damu ya dago bah yace "kiba messenger paper'n"..... Ko tanka mishi batayi bah ta fita... Tana fita taba messenger yar paper sannan ta juya ta kalli tag din dake manne a saman office din taga an rubu *Surgeon "G"* tsaki kadan taja ta wuce wajen su Zee ta fada musu abunda ya faru.. Ba karamin haushin shi suka ji bah da sukaji shine wanda ya bata mata kaya rannan ga wulakancin da ya sake yi mata yau.. Har sun tashi za su tafi messenger yace ta shiga office din Dr. Magaji kallon juna sukayi dasu Aisha sannan ta wuce.. Tana sallama ya amsa cike da fara'a kafin ya bata wajen zama yace " kece Dr. Godwin ya aiko nan ko? Mamaki ne ya kamata bayan yace ta dawo jiya ashe nan ya turota wani murmushi ne ya subuce mata tace "Eh nice Baba" a hankali Dr. Magaji ya dago ya kalleta sbd yaji dadin sunan data kirashi dashi. Nan yayi mata tambayoyi da yawa ta bashi amsa yanda ya kamata "smart gal Monday zaku fara zuwa aiki" ... Godiya taimishi sannan ta fita tana jin dadi straight wajen kawenyata ta nufa ta rungume su tace "office din Dr. Magaji zamuyi aiki" suma duk sunyi farinciki sannan suka fito bakin gate.. Zee ce tace "ku tsaya yanzu za a zo a dauke mu" a tare Janan da Eesher suka ce wane? Imran ta basu amsa Aisha tace "ni ko in tambaye ki mana" Zee tace "inaji" mene ne alakan ki da Imran ne wai? Murmushi Zee tayi sannan tace cousin dina ne.. First born din Uncle Mahmoud Yayan Daddyn mu" jin jina kai sukayi... Basufi minti 5 sai gashi yazo sai da yakai Zainab da Aisha kafin ya dau hanyan gidan su Janan sai hira yake mata ita kuma kunya shi take ji duk ta kosa su kai gida.. A daidai kofar gate din su ya tsaya zata fita ya waigo yace "Dan Allah ki bani aron minti 2 a lokacin ki zan dan yi magana dake" kai kawai ta daga alaman ta yarda... Jingina yayi da hannun motar yana fuskantar ta sannan yace "Janan tun randa muka hadu a plaza kika shiga raina Dan Allah ki bani dama in nuna miki irin son da nake miki kece mace ta farko dana fara so a rayuwata"... Sai da ya kashe mata jiki da kalaman soyayya sannan yace "ki bani numb dinki zan kiraki da dare in na dawo aiki inji hukuncin da kika yanke Allah ya zaba mana abunda yafi alkhairi" a hankali tace "Ameen" bashi numb din tayi sannan ta wuce gida cike da kunya ga wani farin ciki da take ji a ranta"
*Rukky Bae*πππ
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBaeπππβ£β£: [10/13, 7:12 PM] Rukky Baeπππβ£β£π: β€β£πππβ£β£β£β£β£πβ£ *MATAR DOCTOR*β£β£β£β£ππβ£β£β£
*Rukky Bae*πππ
5β£6β£**************5β£7β£
Janan na shiga gida ta tarar Ummiey harta gama girki.. Sannun da gida tayi mata tare da gaisheta da aiki.. Ummiey ta shafa kanta sannan tace "da alama Hulwaty yau kin gaji" murmushi Janan tayi kafin tace "wallahi Ummiey na gaji ga kuma yunwan da nake ji".. Cemata tayi "ai na gama girki kije kice"..."Jazakillah Khairan Ummiey" sannan ta wuce kitchen ta debo abincin... Tana fitowa zata zauna Ummiey tace "duk yunwan da kike ji iya abincin da zaki ci kenan??koma ki karo dan nasan wannan bazai ishe ki bah Kallon abincin tayi ganin ya kai rabin plate tace "Ummiey ni gani nake kamar ma bazan iya cinyewa bah" da mamaki Ummiey ke kallon tace "Hulwaty har yau baki san cin abinci ko? Wannan abincin ne zai ishe ki? Kamar wani dan yaro zai ci?murmushi Janan tayi tace "Ummiey zai ishe ni Inshaa Allah" ni bana so inyi qiba kamar Mmn Hafiz"(( matar cousin dinta ne Mmn Hafiz)) dariya Ummiey tayi sannan tace "aka ce miki abinci ne kawai kesa qiba? Ko kaci abinci ko baka ci ba indai jikin mutum na qiba ne zeyi " dariya Janan tayi sannan ta dau cokali hade da yin "Bismillah" ta fara cin abincin da kyar taci dayawa sannan ta kora da ruwa tace "Alhamdulillah" Ummiey dake zaune tace badai har kin koshi bah? Tace wallahi Ummiey na koshi dayawa har naso inyi over feeding" Ummiey dai sai kallonta take har ta wuce kitchen ta rufe sauran abincin data rage" parlor ta dawo suka danyi hira da Ummiey sannan tace "Ummiey bari inje indan watsa ruwa in kwanta kaina yana so ya min ciwo" Paracetamol ta bata... Karba tayi zata wuce daki Ummiey tace "tsaya a nan kisha nasan in kika je daki ba sha zakiyi bah" kai tadan sosa sbd Ummiey ta gano ta karban maganin tayi tasha sannan ta wuce dakin ta tayi wanka ta kwanta dama tana fashin sallah........
***********
Da kyar Godwin ya kammala abunda zai yi ya wuce gida.. Disney chicken ya biya yayi take away kafin ya wuce gida. Gaba daya ya kasa samun natsuwa.. Tuki yake amma hankalin shi baya kan titi saura kadan ya kwashe dan adaidaita.. Waka ya sa ko zai dan sami natsuwa amma ina ya kasa wakar ma tamkar tana kara mishi zafi ne hannun shi ya buga da karfi a kan steering motan yace "damn it!!... Idon shi duk sunyi ja ga wani ciwo da kanshi yake mishi na fitar hankali.. Da kyar ya karasa gida. A gigice yayi parking.. abincin da brief case dinshi duk a motar ya barsu ko kofar be rufe bah jikin shi sai rawa yake yi.. Key ya ciro ya bude kofa.. Dakin baccin shi ya wuce straight gado ya haye ko cover shoes nashi bai cire bah bargo yaja ya rufe duka jikin shi har kai sannan ya rufe ido da niyyar yin bacci amma ina.. Daya rufe ido sai yaga Janan ga kunnen shi yaki daina amsa kuwwar muryarta da take mishi Sallama. Noooooo!!ya saki ihu hade da toshe kunuwan shi sannan ya miqa hannu wajen bedside table da kyar ya dakko sleeping pills din da yake sha da rarrafe ya shiga bayi ya kunna pampo ya dauki maganin har guda 5 yasha instead of 2.. Yau ko takan bottle water bai bi ba ..Kanshi ya tara a bakin pampan har saida gashin kan ya jiqe sharkaf sannan ya sake rarrafawa ya haye kan gadon tare da sake rufa da bargon baifi 40secs da kwantawa ba bacci mai nauyi yayi awon gaba dashi...
Se wuraren 5:30pm ta farka hade da yin salati a gurguje ta fada toilet ta kuskure baki sannan ta wuce parlor tana zuwa ta ga ba kowa dakin Ummiey ta wuce da sallama ta shiga taga bata nan motsi taji a bayi alaman akwai mutum a ciki.. Kitchen ta wuce ta dan daura musu dinner.. Ta rasa me zata dafa. Tana tsaye Ummiey ta shigo tace "har kin tashi? "na tashi Ummiey.. Me zamuyi dinner dashi ne? Tace "nima na rasa abunda za a dafa amma ki dafa ko mene ne"... "Tor" ta amsa tana dariyar mugunta.. Dafa dukan Couscous tayi mai kayan lambu yaji hanta gidan sai kamshi yake yi.. Zobo ta dafa mai kayan kanshi da abarba sai da ya huce sannan ta hada ta fasa kan-kara ta zuba a ciki.. Karfe 7:30 ta kammala girkin sannan ta wanke komai ta goge kitchen din.. A tray ta daura kayan ta kai inda suke cin abinci.. Plates da cups ta kwaso ta ajiye.. Sai bayan sallan isha'i su Abbiey suka dawo.. Wajen cin abincin suka nufa Janan na bude cooler kamshi ya fara tashi nan ta zubama kowa... Saleem bai lura da abinda Janan ta dafaba sbd hankalin shi nakan wayar shi. Saida ya gama sannan ya karaso ya zauna ba inda idon shi ya sauka sai kan plate din da aka zuba musu abinci.. Ido ya zaro waje yace "black sisi me nake gani kamar couscous" dariya take san yi amma ta basar dama tasan Saleem ya tsani couscous shiyasa ta dafa.. Bata bashi amsa bah ta cigaba da cin abincin ta.. Saleem ko kamar zeyi kuka yace "Ummiey kinga abunda black sisi tayi min koh"? Tasan bana cin couscous shine ta dafa" Ummiey ma bata amsa shi bah sbd ka'idar su ne ba a magana in ana cin abinci ... Haka ya zauna ya zabga tagumi gashi gwani ne wajen cin abinci kuma yau ba karamar yunwa yake ji bah... Can ya tashi ya nufa kitchen indomie guda biyu da kwai biyu ya dauka ya dafa duk ya kosa yaci dan cikin shi sai qugi yake masa.. Yana kammalwa ya juyo duka a plate sannan yaje ya zauna a kan kujera ko wajen su Ummiey be koma ba sbd yanda bai son ya sake hada ido da couscous.. Suna gama cin abincin Janan ta kwashe kayan ta kai kitchen sannan ta wuce gun Saleem tace "Ya Saleem inzo muci tare? Harara ya dalla mata sannan yace "me zaki ci? Tace "indomie" yace "ji bakin ki kamar indomie ta bazaki cishi bah ai kin san bana cin couscous amma kika dafa sbd haka bazan bada bah" "oops! Sorry Ya Saleem na manta baka cin couscous" yace "yanzu ai kin tuna" kin tafiya tayi ta zauna tana kallon shi saida ya ci kusan rabin plate kafin yace "zo muci kafin kisa in kware duk kin kafe ni da idanun ki" da sauri taje ta dakko fork ta zauna suka fara ci loma 1 tayi ta dauke kwan guda daya daya rage ta ruga da guda daki sannan ta daga murya tace dama na koshi kwan nake so inci.. Abbiey, Ummiey, Ya Khaleel saida safen ku" da gudu Saleem yayi hanyar dakin ta tana ganin shi tayi saurin rufe kofar harda sa key.. Jikin kofar ya tsaya yace "idan na kamaki sai kin gane ruwa shayi ne"... tace Ya Saleem gudnyt".. Kwafa yayi sannan ya koma ya cigaba da cin indomien shi duk sai yaji indomien salap.. Badan yunwan da yake ji ba da bazai ci bah.. Abbiey yace "ina zatan Tom and Jerry sunyi halin nasu" Ummiey da Ya Khaleel suka tuntsire da dariya....
Wayar ta taji tanata ringing a cikin jakar data dawo dashi dazu daga asibiti.. Kafin ta ciro har ta tsinke.. Dubawa tayi taga 8 missed calls da txt msgs guda 2 miss calls din ta fara dubawa taga bakuwar numb sannan ta bude txt din ta fara karantawa kamar haka
_Angel da fatan kin shiga gida lfya.. tunda muka rabu nake kewar ki na kira baki dau wayar bah_
Na biyun ta bude ta fara karantawa kamar haka
_Angel pls ki dau wayar inaso inji muryar ki na kasa samun natsuwa Allah dai yasa ba wani abu bane ya same ki_
_Ur husband 2 be in shaa Allah_
_Imran Mahmoud Sambo_
Murmushi tayi kamar zata kira sai ta fasa..niyyar ajiye wayan tayi sai ga kira ya shigo tana duba taga Imran ne a hankali ta daga tare da furta "Assalamu alaikum" saida ya lumshe ido sannan ya sake ajiyar zuciya yace "Waalaikumussalam Angel kin wahalar dani tunda na dawo nake kiranki baki dauka bah me yasa? Ko abinci na kasa ci" hakuri ta bashi tare da fada mishi tana kitchen ne bata san yana kira....hira sosai sukayi yana kara jaddada mata yanda yake santa.. Ya tambayeta shin ta karbi kokon barar shi kokuwa?? A kunyace tace ka bani 1 week in yi shawara" ido ya