Showing 48001 words to 51000 words out of 82682 words
ba kina abu kamar ba kida kwakwalwa! Gaskiya be kamata ki bata ba Dr. Salma da Dr. Abraham suka ce.
Dr. Magaji dai be ce komai ba Dr. Godwin yace allow her!
Kallon shi suka juyo suna yi yace "yes allow her dama options din biyu ne either ta mutu ko Babyn ya mutu ko kuma dukkan su su mutu sbd haka let her try tunda mu mun kasa!
Dr. John yace duk abunda ya faru we will hold u responsible nt her tunda kai kace tayi ka yarda?
Yeah na yarda! Ke dauka ki bata yace mata.. Cike da tsoro ta dauka tana adduaan neman saa a wajen Allah... Dago kan matar tayi ta bata seda tasha kusan rabin cup sannan Janan ta cire daga bakin ta.. Fiye da minti 5 mata ba wani change se ma abu ya kara worst ta fara wanni irin jijjiga Dr. John yace u see! Ka ga abun da nake fada maka ko! Duk sukayi kanta da gudu
RukkyBae πππ
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBaeπππβ£β£: [9/28, 7:51 PM] RukkyBaeπππβ€β£: β₯β£β€β₯β£β€β₯β£β€β₯β£β€β₯β£β€β₯β€β₯β£β€β£β₯β€β₯ *MATAR DOCTOR* β₯β£β₯β β£β₯β£β β₯β£β β₯
RukkyBae πππ
_Aduaa itace makamin mumini kuma adduaa bata fadi kasa banza_
_Mu yawaita yin adduaa tare da neman zabin Allah a dukkan lamarin mu! za muga daidai da yardar sa_
_Tunatar wa ce_ππ»
***9β£6β£****
Duk sun tsorata ganin yanda take jijjiga da sauri Janan ta je ta daura kan matar a cinyar ta tana goge mata zufa tare da tofa mata duk adduaar
da ta zo bakin ta..
Wani irin nishi mai karfi tayi se ga baby ta fito cikin ikon Allah da sauri Dr. Salma ta cabe babyn sbd kar ta fadi tana fadin Allah Mai iko...
Wani irin ajiyar zuciya Janan ta saki tare da hamdala ga Allah shi kuma Dr. Godwin murmushi ya sakar mata tare da jinjina mataπ yace masu "I know she can do it! I told u she can make it!
Jiki a sanyaye Dr. John ya cire hand gloves din shi ya fita daga theatre room din Dr. Abraham ya saki baki yana mamaki shi kuma Dr. Magaji yace a ranshi Alhamdulillah Ala Niimatil Islam"
Gyara matar akayi amma unfortunately babyn ta mutu sbd ta jigata sannan jinin Maman da yayi mugun tashi yayi affecting din ta..
Dakin hutu aka maidata se baccin wahala take yi abun gwanin ban tausayi..
Dr. Magaji ya kira mijinta office din shi yayi mishi nasiha
Mutumin yace Matata ta mutu ko? Shiyasa kake min nasiha ko? Ya kifa kai a table yana gunjin kuka Dr. Magaji yace cool down bata mutu ba sedai ta wahala amma babyn ta mutu gata can ana goge mata jiki kayi signing se ka amsheta a kaita makwancin ta Allah ne ya baku ita kuma ya amshi abun sa Allah ya baku wasu masu albarka Allah yasa me ceton ku ce"
Ya amsa da Ameen yaji dadin maganar Dr. din ko ba komai ya samu natsuwa da wannan nasihar.. Signing yayi sannan ya fita...
Dr. Godwin yaji dadi sosai Janan na shigowa ya ji kamar ya daga ta sama sbd murna, gaban ta yaje ya tsaya yana kallon ta kafin yace "u really impressed me today ki fada duk abunda kike so I will definitely do it 4 u nayi miki alkawari"
Nothing tace mishi..
Be ce mata komai ba ya wuce ya bude locker ya dakko check da biro yayi signing yace ki rubuta amount din da kike s"
Bata rai tayi tace I don't need it nayi ne sbd Allah kuma sbd ni musulmace addinin mu ya hore mu da taimako a duk inda muke kuma she ze bani lada so ka ga no need in amsa kudin ka ka ajiye su kaima ka taimaki wasu dashi "
Tace excuse me ta wuce waje sbd ta gyara kanta toilet din Nurses ta nufa tayi duk abunda take son yi..
Bangaren Dr. Godwin kuwa ta soso mishi inda yake mishi kaikayi nan da nan idon shi ya kada yayi ja a rayuwar shi in akwai abunda ya tsana to a kira mishi taimako gani yake duk Dunia ba kalmar daya tsana kamar ta. Kanshi ne ya fara juyawa ya fara wani tunanin, wajen zaman shi ya koma ya zauna dafe da kai yana fadin No! No! No! Ya watsar da takardun kan table din sannan ya janyo drawer ya dakko maganin bacci ya zuba a baki yana tauna su ko daci bayaji sbd da dacin yake ji a zuciyar shi ya ninka dacin maganin ninkin ba ninkin..
Cikin mintunan da basu fi 2 ba bacci ya kwashe shi.. Tana shigowa taga yana bacci kallo ta karshe mishi taga baccin shi yayi nisa ga takaddu nan yashe a kasa seda ta kwashe su ta ajiye akan wani table sannan ta tattara kayanta dama karfe 5 saura ta wuce gida abun ta...
β€β€β£β£β€β£β€β£β£β€β€β£β€β β β₯β₯β₯
Haka lokaci yayi ta tafiya Janan da Dr. Godwin suyi fada wata Rana kuma ya mata kirki in yaga dama se dai ta lura baya so a ambaci kalmar taimako ko
menene dalili oho!!
Yanzu bikin su da Imran saura watanni uku se faman shirye shirye ake yi daga dukkan bangare... Imran duk ya kosa se dai kullum ya kwanta se yayi wani mugun mafarki amma ya rasa dalili kuma baya gane kan mafarkin...
Wani dare bayan ya gama mafarkin daya zama kamar dole a gare shi ya tashi da ciwo mai zafin gaske tun yana daurewa har ya kasa jure, sakkowa yayi daga gadon ya kwanta flat a kasa nan da nan ya fara rawan sanyi da kyar ya jawo bargo ya rufe jikin shi amma be ji saukin ciwon ba haka yayi ta murkususu har aka kira sallan asuba ya kasa tashi balle yayi sallah nunfashi ma ya fara gagaran shi..
Yau shiru Imran be zo yayi knocking kofar kannan shi ba alaman su tashi sallah Daddy ma be ganshi a masallaci ba dan kusan kullum shine a gaba gaba baya wasa da bautan Allah.. Ana idar da sallah Daddy ya shigo ya tarar da Maman su Imran din tana sallah ya jirata ta idar yace lafiya banga Imran a masallaci ba?
Tace inaga ba lfya ba kasan baya fashin sallah toh ko dai ya makara ne?
Muje dai mu duba mu gani inji Daddy, a tare suka fita dan zuwa dakin Imran din suna shiga suka ganshi kwance a kasa da bargo a lullube, Subhanallahi Imran lfyar ka? Inji Mommy tana yaye bargon, sallati suka saki ganin Imran kwance ba nunfashi babu alamar nunfashi.......
RukkyBae πππ
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBaeπππβ£β£: [9/30, 6:29 PM] RukkyBaeπππβ€β£: β€β£β₯β β€β£β₯β β€β£β₯β β€β£β₯β β€β£β₯β β€β£β₯β£ *MATAR DOCTOR*
β£β₯β β€β£β₯β β₯β£β₯β β₯β£β₯β β₯β£β
_RukkyBae_πππ
_Mutuwa bata sanar da lokacin zuwanta se dai kawai ta dauke mutum idan lokacin shi yayi.. Mu aikata aikin kwarai domin mu samu tsira gobe Qiyamah_!
_Tunatarwa ce_ππ»
****9β£7β£****
Cikin sauri Daddy ya fito dauke dashi a hannu yana cema Mommy ta dakko key akan drawer, bada bata lokaci ba suka sashi a mota suka nufi family hospital din su *Garkuwa*
Da shigar su Likitoci suka yo kan su da sauri aka dakko gadon tura mara lfya aka daura shi ana tura shi likita yana shafa mishi ruwa a fuska nan da nan nunfashin shi ya dawo suka shiga dashi wani daki aka bar Daddy da Mommy a waje suna ta safa da marwa suna adduuan Allah bashi lfya
bayan kusan minti 40 se ga likitan ya fito da sauri Daddy yaje gurin shi yana tambayar jikin yaron shi, likitan yace "ku kwantar da hankalin ku in shaa Allah ze samu sauki yanzu ma ya dawo normal se dai za a diba jinin shi a tabbatar da abunda ke damun shi..
Godia ya mishi sannan yace za su iya shiga su ganshi, da sauri suka shiga, a kwance suka ganshi idon shi a bude se karin ruwan dake hannun shi, a tare suke tambayar jikin shi ya amsa da Alhamdulillah!
Yau tun da Janan ta tashi gaban ta ke faduwa gashi Imran be kirata ba nan zuciyar ta ta fara raya mata babu lfya tunda be saba mata haka ba.. Wayar ta ta dakko tayi dialing numb din shi amma no answer bata hakura ba ta dinga kira seda ta kira sau 7 ana 8 ne aka dauka gab da zata tsinke, muryar Hammeda taji kanwar Imran wacce za su kusa saa da ita suka gaisa a mutunce sannan take fada mata ai ankai Imran asibiti suma yanzu zasu shirya su tafi a rikice Janan tace wani asibitin? Ta fada mata sannan sukayi sallama
Dakin Ummiey taje ta fada mata Imran ba shida lfya yana asibiti,
Subhanallah maza tashi ki daura abinci a kai asibitin Yayan ki ya kaimu tunda yau weekend
jiki babu kwari ta wuce kitchen parpesun kayan ciki tayi da paten dankali se kunun tamba bata sa sugar da madara ba sbd kar ya tsinke..
Tana kammalawa taje tayi wanka ta sa riga da skirt ta dau dogon hijjab me hannu ta saka babu komai a fuskar ta, tana fitowa ta tarar da Ummiey har ta shirya, Janan ta koma kitchen ta kwaso kayan dama ta hada komai a basket tare suka fita sbd khaleel ya fara musu horn..
Suna zuwa asibitin suka tarar da har kannen shi sun zo, har kasa Janan ta duqa ta gaida Mommy da Daddy cike da jin kunya, Ummiey da Yaya Khalee suka gaida su tare da tambayan jikin Imran din, idon Imran a kan Janan ji yayi wasu hawaye sun ciko mishi ido ya rasa na menene, da kyar ta karasa kusa dashi ta gaida shi da jiki ta fita waje sbd gaba daya ta kasa sakewa a dakin tana fita su Hameeda suma suka fito suka zauna tare da ita suna mata hira nan Ameerah karamar su dake kusa da ita tace wallahi Anty Janan kina da kyau Ina sonki sosai, murmushi Janan tayi tare da ja mata kumatu tace kema kina da kyau sosai
Wow! Yawwa ngd miki dama su Yaya Hameeda na cewa nice mummunar gidan mu yau kin wanke ni tayi musu gwalo duk suka kwashe da daria....
Se yamma suka shirya tafiya Mommy nata jin dadi sbd Imran yaci abincin da su Janan suka kawo dama tuntuni take fama dashi yaci yaqi se yanzu..
Har gaban mota Mommy ta rako su sannan tace "Angel yaushe zaki zo gidan mu?
Cike da jin kunya ta sunkuyar da kanta qasa sbd sunan data kirata dashi bata taba zaton har yan gidan su Imran sun san sunan da yake kiranta dashi ba... Mommy ta kara cewa shikenan tunda kunyata kike ji ni dai ba yar kunya tsakanin mu sbd na dauke ki tamkar su Hammeda, Ummiey dai tana gefe bata ce komai ba..
Janan cikin jin kunya tace zan zo in shaa Allah
Mommy tace "Toh Allah ya kaimu sannan tace ma Ummiey "Hajia mungode Allah huta gajiya...
A ba komai ai Allah ya bashi lfya, suka amsa da Ameen sannan Khaleel yaja mota suka tafi
Likita ne ya shigo ya kara duba shi sannan yace ma Daddy yana son ganin shi a office, tare suka tafi bayan ya bashi wajen zama se yake ce mishi "anyi gwaji malaria da typhoid ke da mun shi se kuma baya samun isheshen bacci yanzu ga takardan maganin da za a siya mishi gobe da safe in Allah ya kaimu za a sallame shi sedai wani hanzari ba gudu ba a kwajin da mukayi akwai abun da nake so mu tattauna a kanshi da fatan zaka bani hadin kai...
_Kuyi hakuri da wannan_
_Ku sani a adduoin ku Dan Allah_
RukkyBae πππ
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBaeπππβ£β£: [10/2, 7:35 PM] RukkyBaeπππβ€β£: β€β£β₯β β£β₯β€β£β€β β₯β£β₯β β€β£β β€β£β₯β β€β£β₯ *MATAR DOCTOR* β£β€β β₯β£β₯β€β β₯β£β€β β₯β£β€β β₯β£
Rukkybae πππ
*Ya Rabbi ka bawa Baba na lfya da tsawon kwana.. Allah ka sa kaffara ce a gare shi we love u Baba*πππ’
*Ya Allah duk waenda ba su da lfya gida da asibiti Allah ka basu lfya mai anfani.. Ameen*
****9β£8β£****
Daddy yace in shaa Allah ba matsala ai duk mun zama daya"
Likita yace ka san abunda ake nufi da sickle cell?
Daddy yace eh"
Likita ya cigaba da fadin bayan gwajin da muka yi mun tabbatar da Imran idan ya auri mace wacce genotype din su ya zo daya toh akwai high probability za su haifi sickler
Daddy yace ban gane ba menene genotype din nasa kuma mene ne risk din dake ciki in ya auri me genotype irin nashi?
Likita yace AS ne genotype din shi kuma idan AS da AS suka auri juna toh za su sami yara masu dauke da cutar sickler wacce a yanzu ta zama ruwan dare shi yasa asibitoci da wajajen bauta, gidan radio da telebijin suke fadakarwa akan ayi gwajin jini sbd cututtukan zamani da kuma sanin kwayoyin hallitan juna sbd ana samun yawan macece a cikin alumma sbd wannan cutar
da yanzu zan kai ka inda ake basu magani za kayi mamakin yawan su shiyasa nake so ku tabbatar in zai yi aure a kawo matar domin duba jinin ta sbd lfyar su da kuma kwanciyar hankalin su..
Daddy ya gyada kai tare da jinjina abun a ran shi kuma shima ya sha ganin yanda mutane ke fama da wannan cutar a lokacin ya tuno da yarinyar abokin shi yanda suke fama kullum asibiti gata ta girma amma har yanzu ta rasa wanda zai aure ta sbd wannan ciwon nata, seda ya nunfasa sannan yace ma Likita in shaa Allah ni da kaina zan kawo su dama yanzu bikin su kwata kwata be fi wata 3 ba zan je in samu Baban ta sbd mu fahimce juna sbd mu gudu tare mu tsira tare..
Dr. Yace shikenan Allah yasa a dace.. Suka sake musabaha sannan Daddy ya fito daga office din..
Washe Gari aka sallame su Likita yace kar ka manta da maganan da mukayi!
Daddy yace in shaa
Allah...
Bayan sun koma gida Imran yayi wanka sannan ya ci abinci ya sha magani ya kwanta amma ba bacci yake ba Hammeda ta turo kofar ta shigo tare da gaishe shi da jiki sannan ta miqa mishi wayan shi tace Yaya gashi na ajiye maka ne sbd kar a dinga kiran ka a asibiti..
Ya karba tare da fadin good girl ngd sosai..
Ta fita tare da rufe mishi kofan.
Tana fita ya kira Janan sbd yaga text mssgs din ta da missed calls din ta..
Sun ji dadin jin muryar juna seda suka rama hiran kwanakin da basu yi sannan suka yi sallama...
Mommy da Daddy na zaune a parlour ya kwashe duk yanda sukayi da Likita ya fada mata tare da neman shawaran ta akan yanda zasu tunkari Iyayen Janan da wannan zance..
Ajiyar zuciya ta sake tana fadin gaskiya nima na rasa yanda za muyi sbd nima naji abun banbarakwai ballatana su...
Daddy yace wallahi kuwa amma da yardar Allah zan je in same shi kin san yanada ilimi ba zai kasa fahimtar magana ta ba dadin muaamula da mai ilimi kenan..
Mommy tace gaskiya ne Allah dai yasa mu dace..
Ya amsa da Ameen..
Wayar shi ce ta fara ringing ya dauka, yana gamawa yace kinji wai zamu tafi Istanbul wani seminar se bayan wata daya zamu dawo..
Mommy tace Toh fa! Allah ya bada saa yasa kuje a saa ku dawo a saa Allah kuma ya kare min kai yaushe za ku tafin?
Gobe wai morning flight za mu bi so yanzu dole zan je office in ji yanda ake ciki ki hada min kaya na Bari in je in dawo..
Da asuba Daddy ya gama shirin shi sbd Mommy ta kasa taya shi duk tayi wani iri idonta ya ciko da kwalla..
Daddy ya dawo gefen gadon ya zauna yana fadin "ohhh Darling bana son inga kwallan ki ya zubo ko kadan ne.
Kuka ta fashe dashi tare da fadawa jikin shi tace bana so ka tafi sbd zanyi missing dinka sosai..
Nima zanyi missing din ki babu yanda zanyi ne da tare dake zamu tafi amma kinga su Ameerah na zuwa sch babu yanda za ayi mu barsu su kadai ki dena kuka kin ji My Wifey yasa hannu yana goge mata hawayen tare da fadin ki dena mun asaran hawayennan sbd yanzu kin girma..
Tace in dai a wajen ka ne bazan taba girma ba am still a Baby..
Daria yayi yace toh shikenan zan kawo miki pampas da feeder tunda u r still a Baby... Duka suka kwashe da daria ta ce tashi muje kar kayi latti tayi mishi goodbye kiss shi kuma ya ce hau in goya ki ba musu ta hau seda ya kaita parlor sannan tace Toh ya isa haka sauke ni
daria yayi sannan ya sauke ta... Yaran ne suka fito daga dakin su suka gaida su
Mommy tace ku kwaso sauran kayan Daddy mu raka shi da sauri suka kwaso kayan Imran ne ze kaishi office sannan motan office din su ya kaisu airport.
har bakin mota suka raka shi yana daga musu hannu ya bar gidan su kuma suka koma ciki...
Yau ta kama Friday Dr. Godwin ya shigo sanye da fararen kaftan ya sa wani black slippers irin na maza se black agogo se bakin glasses ya gyara gashin kanshi se faman kanshi yake yi ga wani annuri dake fita a fuskar shi alamun yana cikin farin ciki tun daga kan masu gadi ya fara rabon kudi harda nurses duk ya basu rabon su..
Kowa se mamakin shi yake yi dan tunda yake be taba shigowa cikin farin ciki ba kullum cikin shan kamshi da jijji da kai...
Yana shiga office yace ma masinja yau Ina off babu patient din dazan duba ka tura su office din Dr. Magaji jiya nayi mishi bayani..
Masinja yace an gama ranka ya dade sannan ya fita...
Janan ta shigo ganin Dr. Godwin cikin kaftan abun ya bata mamaki a ranta tace "wow gaskiya yayi kyau kamar ba Christian ba"
Kallon ta yayi yace ya dai kike kallo na ko nayi miki kyau ne?
Gefe ta kauda kanta kafin tace no baka yi kyau ba
A hankali ya taho yazo dab da ita ya hura mata iska a fuska har seda eye lashes din ta suka motsa kamshin turaren shi da sweet din