Showing 3001 words to 6000 words out of 82682 words
shi ta tashi tace ina Sandra din?? Yace cool down Mum ai na ce ta tafi... Ajiyar zuciya ta ja sannan tace masa kayi breakfast kuwa? Girgiza mata kai yayi alaman a'a kenan
Da sauri ta tashi taje ta dauki intercom tace Ruth kizo yanzu... Cikin 6secs sai gata ta karaso tace maza ki hada ma baby abinci be yi breakfast bah cikin sauri tace yes Ma.
Bayan ta gama taje ta kaima ta tace "D food is ready Ma"
Cemata tayi kawo min kan center table .. Juyawa tayi ta kawo sannan ta jere shi akan teburin zata fita kenan tace kun gyarama baby dakin shi kuwa?? Dukar da kai tayi sannan tace a'a lokacin da naje in gyara yana bacci... Tace oya wuce ki gyara mishi kafin ya gama kin san baya san kazanta... Da sauri ta wuce side din nashi taga ko datti babu amma haka sai da ta kara gyara wa ta feshe dakin da haddaddun room freshners masu kamshi ta kara karfin A.c sannan ta fita
************
Momma ta riqo hannun shi sannan ta zaunar dashi akan daya daga cikin sofas din dake dakin sannan ta jawo abincin ta fara bashi a baki har ya koshi sannan ta goge mishi baki ta bashi juice ya sha
A haka suka zauna sunata hira da shi da iyayen nashi.
Can ya mike yace bari yaje ya dan huta zuwa anjima kanwar shi ce ta mike ta bishi suka fice daga parlorn ..
Suna shiga dakin ya dakko ps4 suka fara bugawa can da suka gaji yaje ya kwanta nan da nan bacci yayi awon gaba dashi haka kanwar tashi ta haye gadon itama ta fara bacci..
Basu suka farka ba sai 4:30pm yace taje wajen Momma shi zai dan yi wanka tana fita ya shiga bayi a gurguje yayi wanka ya sake shiri cikin Blue Jeans da black shirt yaje ya dakko wani takalmi black wanda ake kira da high top ya sa sannan ya tafi sashen iyayen shi nan ya tarar da *Annabel* (Sis dinsh) sanye cikin riga da wando pink da gudu ta taso tace "babyn Momma muje garden muyi hide nd seek yace tor daddy's gal nifa shopping zanje.. Shagwabe fuska tayi tace pls kadan zamuyi sai mu je shopping din tare kayan makeup dina ya kusa karewa kuma chocolates da holandia na sun kare dad yaki sayo min... Dukkan su sukayi dariya sannan iyayen suma suka ce muje garden dukan mu
Fitowa sukayi suka nufi garden wanda yaji shukeshuken fruits iri iri da swimming pool sai liluka daban daban daga gefe wani guri ne akayi decorating din shi dark nd lemon green sai kujeru aka jera su da table wanda yake cike da fruits
Nan iyayen suka zauna suna hira su kuma yaran suka fara game dinsu na hide and seek sunata dariya cikin farin ciki da nishadi............
*Rukky Bae*😏😏
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: ❤❣❣💕💕💕❣❣❣❣💕 *MATAR DOCTOR* ❣❣💕❣❣💕❣❣❣
*Rukky Bae*😏😏
2⃣6⃣**********3⃣0⃣
***********
Ummiey ta nisa sannan tace yau harda cikakken tarihin mu zan baki sannan ta fara kamar haka..
_sunan Khadija Abubakar_
_Ni yar asalin Garin Gombe ce_ _domin mahaifina da mahaifiyata duk yan garin Gombe ne_ _ni kadai Allah ya basu shiyasa na tashi cikin gata da kuluwa_, _amma duk da irin gatan dana tashi dashi baisa iyayena sun sangarta ni bah_ ..... _Nayi karatun boko da islama duk a garin Gombe domin Baba na babban malami ne wanda ake ji dashi a garin Gombe sannan ya kasance jika ne a wajen sarkin Gombe_
_Mahaifiyata mai suna *janan* layin su daya da mahaifina yawan haduwan su da kuma son karatun ta yasa suka shaqu har sukayi aure_
_Tun bayan auren su mahaifiyata data samu cike baya kwari yake barewa_
_Sai bayan shekara 10 Allah yasa ta samu ciki na wanda saida ya fara girma suka san tana dauke da ciki_ .... _Murna wajen Baba na ba a magana sbd farinciki har sadaqa saida yayi kuma ya tara almajirai ya ciyar dasu_
_Bayan watanni mahaifiya ta haife ni cikin qoshin lafiya_
_Ranar suna aka rada min Nana Khadija amma anfi kirana da Nana sbd sunan kaka ta naci ta wajen uba_
_Murna sosai dangi Mama da Baba sukayi wanda saida aka yanka raguna biyu da sa biyu_ _kyautukku kuwa na same su sosai nida Mama_
_Haka iyaye na suka cigaba da kula dani har na fara girma_ _Baba kuma tun bayan haihuwata ya samu budi sosai yana tafiye tafiye_......
_Bayan shekuru muka dawo Makarfi sakamakon koyarwa da Baba ke yi_ _Anan na karasa karatuna har muka hadu da mahaifin ku wato pharouk Ibrahim Makarfi_ _wanda soyayya mai karfi ta kullu a tsakanin mu har ta kaimu ga aure_
_Barrister Pharouk Ibrahim Makarfi lawyer ne wanda yake aiki tuquru sakamakon haka yayi ta samun karin girma mun zauna a Abuja, Kano, Jigawa, Lagos dadai garuruwa da dama_
_Saida muka shekara 4 da aure kafin na haifi yayan ku Ibrahim wanda ake kira Khaleel domin yaci sunan kakan ku_
_Bayan na haifi Khaleel da shekara 3 sai na haifi Saleem_......... _Tun daga nan ban sake haihuwa bah gashi Allah ya dauramin son 'ya'ya mata amma Allah bai bani bah domin likita yace mahaifa ta is weak bazan iya daukan wani ciki bah_
_Nan na fawwalawa Allah komai kuma na gode masa domin ya bani kyautan yara har biyu_
_Kwatsam bayan shekara 8 sai gani da ciki mun yi mamaki sosai kuma munyi farin ciki lokacin muna Lagos mahaifin ku yace minene abin mamaki_? ..
_kadan daga ikon Allah kenan_
_Haka naita renon ciki na har ya girma_
_Bayan wata 9 na haifo ki sak kamata amma baki dakko haske na bah sai kika dakko kalan Baban ki inda kika ci sunan Ummata wato *JANAN*_ _nan mahaifin ki yace gaskiya 'yar nan tawa sai *DOCTOR* zata aura_...... _Mukayi dariya_
_Anyi taron suna na gani na fada domin nuna tsantsan murna da farinciki_
_Bayan shekaru 3 muka dawo Kaduna da zama anan aka saki a makaranta_ _ko ina kika shiga ana sanki_ _da muka je makarfi nan kikaji ana ce miki_ _*MATAR DOCTOR*_ _haka bakin ki ya kama sunan har makaranta duk haka ake kiran ki_ _har kika fara girma_
_Wata rana da dare kika tashi da zazzabi mai zafi kikayi ta suma numfashin ki yanata daukewa sai suma kike yi a daren muka kaiki asibiti sai kuka nake yi muna zuwa aka shiga dake emergency ashe asthma ce ta kama ki amma batayi karfi bah_
_After like 6 hours kika fardo daga dogon suman dakikayi a nan ne *Doctor* ya shigo yace za a samiki drip ayi miki allura_ _kuka kika fara ke bakya son allura da kyar akayi miki_
_After one week aka zo discharging din mu nan doctor ya shigo ya bamu sallama ya yace babu magana ne *MATAR DOCTOR* nan ta turo baki tace ni ba *MATAR DOCTOR* bace daga yanzu tunda kayi min allura bana san *doctor*_ .........
_Tun daga lokacin kika tsani a kiraki *MATAR DOCTOR* har yanzu_........
*Rukky Bae*
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: ❤❣❣💕💕❣❣❣❣❣❣❣ *MATAR DOCTOR* ❤❣❣❣❣❣❣❣❣💕💕💕💕❣❣❣
*Rukky Bae*😏😏
3⃣1⃣***********3⃣5⃣
***************
Ummiey tace kin ji tarihin mu kuma yanzu kinji dalilin kiran ki da sunan koh??
Murmushi tayi sannan ta goge hawayen ta tace "Swt bro ai ka dena cemin *MATAR DOCTOR* koh??
Shida Ummiey duk suka sa dariya sbd yanda tayi maganan kaman me neman gafara.....
Gira daya ya dage sannan yace harda wani 'sweet" dan kiyi min dadin baki koh??.... Tace "a'a ba haka bane ai dama u r my swt bro"...
Ummiey tace "ni kunga kar ku ishe ni da surutu kuje kuyi sallah".... Baki dayan su suka tashi dan sauke farali......
*7:30pm*
********
*Lagos*
Sun gama shopping suna hanyar dawowa.... Zaune suke a cikin mota kiran Camry gabaki daya glasses din motan tinted ne ko ina a rufe yake ya kunna A.c gashi ya kure karan speakers din motan sai over speeding yake yi haka al'adar *Godwin Williams Albert* yake....
Wakan Mr. Romantic kawai ke tashi daga motan inda yake bin wakan tiryan tiryan yana kada kai alamun wakar na mishi dadi... Haka ma Annabelle sistern shi tana daga gefe tana rawa abun ta har suka iso gida a haka.....
Horn ya dannawa aka wage musu gate din katon mansion din su.... Ma'ikata sai sunnu da zuwa suke musu amma duk cikin su ba wanda ya amsa.... Sai can Godwin ya bude baki kamar bazai yi magana bah yace "Moses get d stuffs out of d car" yana tafiya yana maganar...
Suna shiga parlorn suka tarar da iyayen su na jiran su har rige rige suke su karasa suka manna musu peck a goshi da kumatu sannan Momma tace "time 4 dinner" "shall we?? Nan suka ce "yes" sannan suka wuce dining area inda cook tayi serving din su fried rice with chicken Kiev sai pineapple nd coconut juice nan suka fara ci suna hira(babu table manners) a nan ne Godwin ke fada ma iyayen shi cewa asibitin da yayi housemanship sun turo mishi da request suna son aiki dashi sai Teaching hospital Kano, Asibitin ABU Zaria, Teaching hospital Abuja, Barau Dikko Kaduna, prvt hospital Lagos.....
Momma ta ijjiye spoon tace "wanne ka zaba aciki? Yace mata "Barau Dikko Kaduna" a tare duk suka ce "what?? Yace "yap" Annabelle ta marairaice tace "haba babyn Momma me yasa zaka tafi KD" y nt ka karbi offer din prvt hospital na Lagos din??
"Momma tace ko Abuja! Amma Kaduna is far frm here we can't let u go cuz we gonna miss u a lot" murmushi yayi yace I will miss u more" amma Kaduna really need me cuz yanzu ake gyara hospital din basu da qualified doctors especially *surgeons* sannan kuma nurses din wajen basa aiki da kyau ana complain sosai da asibitin kuma that will be d best hospital where I can show my skill nd my profession"
Ajiyar zuciya suka ja sannan suka ce shikenan tunda kayi insisting akan Kadunan kake so! Wish u all d best!
Nan suka cigaba da cin abinci har suka gama.....
Godwin yace zai je daki ya kwanta sbd kanshi ya fara ciwo kuma zai yi research akan wani ciwon..... Nan ya manna ma dukkan su gudnyt kiss kafin ya wuce daki....
Yana zuwa ya watsa ruwa sannan yasa pyjamas ya hau gado tare da jawo laptop ya shiga dube dube bayan like 30mins ya ja bargon shi ya fara bacci.......
********************
*kaduna*
*8:30pm*
Janan ne da iyayen ta da yayyin ta bayan su idar da sallan isha'i zaune a wani gefe na dakin inda akayi decorating dinshi tamkar wajen da za ayi kamu suna cin abin ci kowa yayi shiru sai cin abincin sa yake inda Janan ke ci tare da Abbiey da Ummiey a plate daya while ya Khaleel da ya Saleem ke ci a plate daya(cin abinci tare da yan uwa yana kara ma mutum tausayi da kuma son dan uwan shi sannan abincin yana kara albarka)
Suna kammalawa Janan tayi saurin tashi ta kwashe plates din sannan ta tawo da ruwa a bowl tare da liquid soap ta je wajen Abbiey din ta ta durkusa tare da kamo hannun shi tana wankewa har ta gama sannan taje ta wankewa Ummiey nata hannun sai wajen yayyinta suma ta wanke musu (haka take yi aduk lokacin da suka gama cin abinci har sun saba da haka) wuce wa kitchen tayi ta dauraye plates din sannan ta fito dauke da glass jug nd cups acikin tray...
Kunun ayan ta zuzzuba kana ta mika musu sannan ta dau nata ta zauna tana sha......
Abbiey ne ya kurbi kunun ayan tare da lumshe ido wani dadi yana ratsa shi a haka har ya shanye kana yace Allah yayi miki albarka *Muhibbaty* tace ameen Abbiey....
Ya Saleem yace "my black sisi an iya aiki" Janan ta turo baki tace "am nt black" Ya khaleel yace "rabu dashi he is jealous princess, u hv a beautiful nd glowing skin" murna ya cika ta tace "that's my luvly bro high five" nan suka tafa aka cigaba da hira.... Anan ne Abbiey yake ce mata "ya lbrin exams ne? Tace "Alhamdulillah"
yace "yaushe result zai fito?
Tace "in d nxt 2 weeks in shaa allah" duk suka ce "Allah ya kaimu "
Haka sukayi ta hira har zuwa 9:30pm sannan Abbiey yace"time to sleep "duk suka mike kowa ya wuce dakin shi.....
Janan na shiga daki taje tayi wanka kana ta sa wani pink riga da wando na bacci...
Gado ta fada tare da jan bargo tayi addu'an bacci ( Falq, Nas, Ikhlass, Aayatul kursi, sannan tace"Bismikallahumma ahaya wa bismika amuut "( da sunan ka Allah nake raye kuma da sunan ka zan mutu) ta shafa sannan ta juya gefen dama ta fara bacci........
*Rukky Bae*😏😏😏😏😏
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: ❤❤❣💕💕❣❣💕💕❣💕❤ *MATAR DOCTOR*❣❣❤❤💕💕💕❣❣
*Rukky Bae*😏😏😏
3⃣6⃣************4⃣0⃣
Washe gari tunda Janan ta farka sallan asubah bata sake komawa bacci bah... Zaune take tana adhkar bayan ta gama adhkar din ta kunna karatun Alqur'ani.. Qira'ar Sheikh Shureim kawai ke tashi cikin suratul-Furqan haka tai tabin karatun cikin kwarewa tanayi tana murmushi domin tana matuqar son qira'ar gashi ta iya sosai ga muryar ta mai zaqin sauraro dalilin haka yasa yan Islamiyan su ke san karatun ta kusan kullum sai tayi karatu idan suna rehearsal din karatun saukan su..
Karfe 7:30am ta kammala karatun sannan ta rufe Alqur'anin tare da kashe karatun... Direct kitchen ta wuce domin yi musu breakfast.... Tsayawa tayi tana tunanin abunda zata dafa musu can tace "yes na tuna me zan dafa"
Pancakes da chelsca buns tayi sannan ta dafa ruwan shayi mai kayan kanshi harda na'a na'a ta saka gidan sai kamshi yake yi.... 8:30am on d dot ta gama hada breakfast din sannan ta fitar dashi inda suke cin abinci.... Kitchen din ta koma kana ta gyara shi ta wanke duk abinda tayi amfani dashi...
Daki ta koma ta cire kaya tare da daura towel ta wuce bayi don yin wanka... Tana fitowa ta nufi wajen mirror tare da zama kan stool din dake wajen... Comb ta dauka ta taje kanta man gashi ta shafa sannan ta yi parking gashin a tsakiyar kanta.... Lotion dinta ta dauka ta shafa sannan ta shafa humra da turarurrukan ta har a kai ta shafa ( wasu na cewa shafa turare akai yana kawo furfura amma ni ban yarda bah sbd furfuran wasu baiwa ce ta wasu kuma tsufa ne ta wasu kuma wahala ce ta fiddo musu furfuran).. Tana gamawa ta wuce wajen wardrobe din ta ta fiddo wani atamfa riga da zani ta sa zani ya zauna cas a jikin ta hips din nan sun fito gwanin ban sha'awa dama gata ta iya daura zani ( mata da yawa basu iya daura zani bah sai skirt koh wando wanda ba al'adar mu bace..... Mace ta daura zani shine al'adar Mutan Arewa) komawa tayi ta sake peshe jikin ta da turare sannan ta daura dankwali tana kokarin fita kenan wayanta ya fara ringing wajen bedside drawer ta matsa ganin suna Aisha Bashir rubuce kan screen din yasa ta daka tsalle jikin ta har rawa yake ta dauki wayan ta haye gadon sannan suka fara magana....
Waya sosai sukayi sannan Eesher take tambayan Janan "yaushe za a manna musu result? Tace sunce "in 2 weeks time" sannan sukayi sallama da juna suna masu farin ciki
Daga kai sama tayi taga past 9 da sauri ta fito.. Wajen cin abinci ta nufa taga ita suke jira hakuri ta basu sannan ta zauna suka fara cin abincin....
Suna kammalawa Ya Khaleel yace " princess D food taste very good " haka ma Ummiey da Abbiey suka ce.. juyawa tayi wajen Ya Saleem tace "kai fa baka ce komai bah tadan murguda baki"..... Cewa yayi "naji duk suna wani koda ki kin iya girki ne bayan baki kai ni iyawa bah"..... Ummiey "tace ai gaskiya ne ko ka fita iyawa ne? Yace "Eh yau ni zan mana dinner na huttashshe ki black sisi"
Ya Khaleel ne yayi magana yace "tab! Gaskiya mun yafe haka kawai mu kwana da yunwa? Me ka iya in banda dafa indomie sai jagwalgwalo??......
Saleem yace "karfa ka manta bording skul nayi kuma Bayero Uni nayi babu mai dafa mun abinci" babu abinda ke burgeni a girki kaman soya miya "
Dukkan su suka fashe da dariya sannan Abbiey yace munji amma mu bamu san ka iya girki ba sai yau".. Ko kayi catering skul ne bamu sani bah?? Anyway munji ka iya amma baza mu yarda ka mana dinner bah gaskiya"......... Saleem ya marairaice yace naji amma ku bari muyi competition tsakanina da black sisi aga wanda zai cinye" Janan tace "wow! A very good idea" na yarda muyi...
Khaleel yace nine time keeper while Ummiey da Abbiey sune panel of judges... Agree? Suka ce "yes" yace "good amma balloting zakuyi sbd kar wani yace anmasa san kai"
Nan ya dakko paper da pen ya mika ma su Ummiey su rubata abun da zasu dafa
Ummiey da Abbiey suka yi kuskus sannan suka yi rubutu a papern sannan aka ce Saleem shine Babba ya fara dauka hannu yasa zai dauka sai ruwan ido yake har ya dau daya zai bude Janan ma tazo daukan dayan sauri yayi ya ajiye wanda ke hannun shi karap ya dauke wanda Janan ke shirin dauka Ya Khaleel yace "maza dai garin ruwan ido kadau wanda yafi karfin ka" yace "oya kowa ya bude nashi" Saleem na ganin nashi yayi popping idon shi waje ita kuma Janan ta