Showing 18001 words to 21000 words out of 82682 words

Chapter 7 - MATAR DOCTOR COMPLT BY ESHAAT.txt

ESHAAT   

18 Jan 2025

4343

wuce masallacin dake cikin asibitin..Nafila ta dinga jerowa tana roqon Allah ya tashi kafadun matar sannan Allah ya ba su Dr. Magaji sa'a bayan ta idar ta dakko Al'qur'ani mai girma ta fara karantawa a nan ne taji zuciyar ta tayi sauki.. Ta kai kusan awa 1 a cikin masallacin kafin ta koma wajen bencin da ta zauna dazu.. Wayar ta ce ta fara ringing tana dubawa taga _Nurulqalbee_ Imran kenan. Murmushi tadan yi sannan ta dauka "Amincin Allah ya tabbata a gareka Nurulqalbee (Hasken zucia ta)" bangaren Imran wani sanyi ne ya ratsa shi "Kema amincin Allah ya tabbata a gare ki Angel"
"Da fatan kana cikin qoshi lfy"
"Alhamdulillah Angel me ya faru dake naji muryan ki so dull kamar baki lfya ko kuka kika yi ne ban sani bah cuz naji muryan ki yana cracking"
"wata patient ce ta ta bani tausayi shine nayi kuka"
"haba Angel daga fara aiki yau se kuka? Ki kwantar da hankalin ki zaki saba kinji" saida ya tabbatar hankalin ta ya fara kwanciya sannan yace "angel na kosa in je neman izini wajen Abbiey in dinga zuwa wajen ki zance bana so in fara zuwa ba tare da izinin shi ba sbd bin ka'idar addinin musulunci" tayi farin ciki sosai da jin abinda ya fada tana kara jinjina hankali irin na Imran "Allah ya baka ikon zuwa"... Yace "Ameen" Haka suka yi ta waya har tsawon wani lokaci kafin sukayi sallama..


Dr. Magaji ya fito yana share gumi da hanky bayan sun share awanni biyar a dakin theater.. Da sauri mijin matar ya tashi ya je wajen Dr. Magaji "Likita ya take? Ancire mata? Likita mata ta ta farfado? "biyo ni office" iya abinda yace kenan ya wuce.. Da sauri mutumin ya bi bayan shi.....










*Rukky Bae*😏😏😏
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: β€β£β£β£πŸ’•πŸ’•β£β£β£πŸ’•β£ *MATAR DOCTOR*❀❣❣❣❣❣❣❣❣❣










*_Rukky Bae_*😏😏😏










6⃣3⃣***************6⃣4⃣










Suna shiga office din Dr. Magaji ya zauna sannan ya ba mutumin waje yace ya zauna.. "likita Dan Allah kayi min bayani" se zufa yake yi yama cire hular kanshi sai fiffita yake duk da A.c da fankan dake cikin office din.. Remote Dr. Magaji ya dauka ya kara karfin A.c sannan yace "ka zauna tukunna se in maka bayani mana" jiki a salube ya zauna..
"Malam Adam gaskiya banji dadin abun da kuka yi kai da matar ka ba sbd ba karamar hatsari ta shiga bah domin fibroid din ya zama chronic amma munyi nasaran cire shi"
"Tor Dr. Yanzu ya take ta farfado?"
"bata yi regaining conscious nata ba sai nan da 2 hours zata farfado..Yanzu dai zaka bada ledan jini biyu mu samata cuz ta zubda jini dayawa amma b4 then kaje kayi clearing bills naka sannan muyi admitting dinta har se ta samu lfya. In an sallame ta bayan 6months zaku sake dawo wa a dubata" wani takarda Dr. ya mika mishi yace "ka kai lab in sun gani zasu gane"
"Nagode Dr. Nagode Allah ya saka da alkhairi"
"Ameen amma Dan Allah nxt tym ku kiyaye kar haka ta sake faruwa"
"In shaa Allah hakan bazai sake faruwa ba likita"
Da sauri ya bar office din yana fita daidai nan su Janan na turo matar shi a gadon marasa lfya da wani abu a bakin ta kamar matacciya.. Da gudu ya fara bin su yana hawaye "Dan Allah ku tsaya inga lfyar matata"
"Kayi hakuri bazamu iya tsayawa anan ba sbd hayaniya da kuma mutane ka bari in ta farfado sai kazo ka ganta amma yanzu ka bimu kaga dakin da zamu kaita" haka yayi ta binsu yana hawaye gwanin ban tausayi seda yaga dakin da aka kaita sannan yaje yayi clearing bills ya wuce lab din dake asibiti ya nuna musu yar takardar da Dr. Magaji ya bashi. "ka sha madara ko malt sbd jiri"
ba musu yaje ya siyo malt da peak yasha sannan ya koma wajen nurse yace "na shirya" kadan nurse ta diba a sirinji tace ya jirata wajen wani machine ta nufa ta gudanar da test dan tabbatar da bashi da wata cuta sannan tace ya kwanta a wani karamin gado aka fara diban jinin.. Seda ya kai awa 2 kafin suka bashi izinin tafiya
"babu dai wani abu ko?? Kana jin jiri? Zaka iya tafi? Akwai inda yake maka ciwo"
"zan iya kuma bana jin komai babu inda yake min ciwo nagode"
Dakin da aka kwantar da ita ya nufa yana zuwa aka barshi ya shiga sbd babu kowa a wajen ta kuma any moment zata iya farkawa.. Ya kai kusan 10 mins kafin ta fara bude ido tare da turo abinda aka sa mata a baki.. Salati ta fara yi daganan kuma ta fara sambatu "wayyo likita ciki na yana ciwo karku kashe ni ciki na yana min ciwo bana so me nake yi a nan!! Haka tayi ta ihu.. Da sauri mijin ta yaje ya riqe mata hannu yana kuka "kiyi shiru kinji a asibiti muke basa san ana ihu anan"
"Ina ruwana da asibiti? Kai waye"
"nine mijin ki Adam sannu kinji"
"bana san ganin ka ka fita a dakin nan ko in kashe ka😳 hannun ta ta fizge kafin ya ankara har ta cire drip din da aka sa mata nan da nan jini ya fara zubowa.. Wani ihu ya sake "Nurse kuna ina jini! Jini yana zuba!!" da gudu su Janan suka shigo ganin matar sukayi a kwance tanata jijjiga tana bankarewa. "Hasbunallahu wa ni'imal wakeel" abunda suka fada kenan Janan da Zee suka tafi wajen matar da gudu suka rirriqe ta ga jini se tartsowa yake yi duk fararen kayan Janan sun baci har fuskar ta sbd ita ke tsaye ta gefen da matar ta cire drip din gabaki daya ta fita a hayyacin ta.. Idanun matar suka fara qaqqafewa nan da nan suka sake rudewa gashi su ba sanin taimakon da zasuyi mata bah mijin na ganin haka ya saki wani razananne ihu ya tafi luuuuu ya fadi qasa....................














*Rukky Bae*😏😏😏
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: β€β£β£πŸ’•β£β£β£β£β£β£β£ *_MATAR DOCTOR_*β£β£β£πŸ’•πŸ’•πŸ’•β£β£β£








*_Rukky Bae_*😏😏😏


*_((2016))_*






6⃣5⃣**************6⃣6⃣










"Innalillahi wa innailaihirrajiun" ana wata ga wata!! Ga mata ga miji.. Sun rasa yadda za suyi ga Aisha taje siyo musu abinci sbd tun breakfast basuci komai bah
"Zee dawo ta nan ki danne mun wajen dake fidda jinin nan ina zuwa" ba musu Zainab ta saki hannun matar ya tafi sharaf! Ya fadi kan gado.. Kallon juna sukayi ita da Janan cike da tsoro a gurguje ta koma side din da Janan take ita kuma Janan ta fita da gudu ko takan jinin dake jikin ta bata bi ba.. Ko knocking kofar bata yi ba ta shiga da sallama kamar an hankado ta "lfya Janan kika shigo haka duk jikin ki jini?
"Baba patient! Patient da mijin ta! "me ya faru da patient? Calm down nd talk to me" da sauri da sauri tayi mishi bayani.. Ko secs 2 be kara ba ya fita cikin hanzari daga office Janan na binshi a baya ya nufi dakin da matar take suna shiga yaga halin da suke ciki ita da mijin ta "Janan taimaka min mu turo gadon ta zuwa emergency room ke kuma Zainab ki yayyafa mishi ruwa yanzu zan turo wani Dr. yaga halin da yake ciki"
Gudu gudu sauri sauri haka suka nufi dakin emergency.. Oxygen aka fara sa mata domin numfashin ta yayi sama yana barazanar daukewa.. "Daughter kije ki gyara jikin ki in kin gama ki tafi gida sbd kayan ki ya baci da yawa kuma ki dena yawan kuka ke nurse ce be kamata zuciyar ki ta dinga yawan karaya haka bah"... Jiki a salube ta fito daga emergency room din daidai ta fito shima Dr. Godwin ya fito daga office din shi bata lura da shi ba.. Gefe ya koma yana kallon ta a ranshi yana fadi "ita kuma wannan meke damun ta haka duk jini a jikin ta? Ganin tayi hanyar sauka daga steps yayi sauri ya sha gaban ta "Ke! Miye haka? Jikin ki duk jini kina kokarin shiga cikin mutane kamar baki san aikin ki bah" ko kallon shi bata yi bah tace "excuse me" ganin beda niyyar matsawa ta kauce zata bi dayan gefen da sauri ya sake tare ta haka suka dinga yi har wajen sau 3 gajiya yayi da draman da suke yi ya fizgo hannun ta ya fara janta sai kokarin kwace hannun ta take amma ta kasa "miye haka wai! Ka sake ni! Ka sake ni!..be tanka ta ba kuma be seke mata hannun bah seda suka zo daidai bakin kofar office dinshi yasa key ya bude har lokacin be sake mata hannu bah.. Bayi straight ya wuce da ita sannan ya ciro hanky fari sol daga aljihun wandon shi ya fara goge mata jinin kan fuskar ta wanda har ya soma bushe wa. Be damu da yanda take ture mishi hannu bah se da ya gama goge mata fuskar tas sannan ya jawo hannun ta ya daura mata hankyn akan tafin hannun nata "goge ki fito" ya juya ya fita da harara ta rakashi sannan ta tara hannun ta a pampo ta matso hand wash ta dinga wanke hannun tana istigfari "shi wannan besan haramun bane namiji ya taba macen daba muharramar shi bace! Koda yake ba musulmi bane shiyasa yake abunda yaga dama" haka taita dirje hannun har hand wash din ya kusa karewa sannan ta barshi. A hankali ta dan goggoge jikin ta sbd kar kayan ya jike sannan ta wanke fuskar ta.. "a bayin zaki kwana ne? Seda ta murguda baki kamar yana ganin ta kafin ta bude bayin ta fito yana tsaye ya jingina da bango yayi crossing kafafun shi hannayen shi duka biyu ya zurasu cikin aljihun wandon shi yana facing kofar bayin. Dan nesa dashi ta tsaya amma bata dago bah ganin be tanka bah yasa tayi hanyan waje "Ke! Ya kirata.. Cak ta tsaya ita batayi gaba ba kuma batayi baya bah. A hankali ya tako yazo daidai gaban ta ya tsaya kanshin turaren shi na _Fresh guy_ yana dukan hancin ta. Ganin batada niyyar dago kai ya sunkuyo da kanshi daidai fuskarta yace "baki iya godia bane"
"tnx" tace a takaice ta cigaba da dosan bakin kofa. Tana daura hannu kan handle din kofan ya "ban baki izinin tafiya bah karki sake ki kara koda 1 step forward ne" fadi take a ranta "ikon Allah mutum sekace ubana se wani bani orders yake yi kamar a karkashin shi nake aiki gaskiya ya iya rainin wayau" katse mata zancen zuci yayi ta hanyar daura mata lab coat akan kafadar ta. ''wear this nd follow me" kamar kar tasa se kuma tayi tunanin gwara tasa kawai tunda batada wani zabin.. Tana cire hannu daga jikin handle din shi kuma ya bude ya fita.. Haka taita bin shi ba tare da sanin ina za su bah.. Wayar shi ce ta fara ringing yana dubawa ya Dr. Magaji da sauri ya dauka "Hello Dr."
"Surgeon G kana ina ne?
"Gani zan fita me ya faru"
"kazo emergency room yanzu pls"! Ya fada demandingly.
"OK, ok gani nan zuwa" kudi ya ciro a aljihun shi ya ya miqa mata "gashi ki hau taxi Dr. Magaji ya kira ni"
Mamaki ne ya cika ta a zuciyar ta tace "O! Dama shi a nufin shi gida ze kai ni? Tab! Allah ya kyauta in bishi ko in karba kudin hannun shi"
"ki karba kina wasting min tym" firgigit ta dawo daga duniyar tunanin da ta fada "no! Nagode inada kudin transport"
"OK, ya miki kadan koh! Let me add more 4 u" wasu kudin ya sake kara mata a kai "take"
qin karba tayi ya miqa hannu zai riqe mata hannu tayi saurin maida su baya... Ya fahimci kwata kwata bata so ya tabata wani killer smile ya mata wanda shi kadai yasan nufin shi.. Da sauri ta juya ta fara tafiya shima cikin sauri ya sake miqa hannun zai janyo ta baya wayar shi ta fara ringing dauka yayi cikin azama ya fara sauri "am on my way" ya katse wayan. Yana waigawa yaga Janan har ta bace mishi daga gani.."zaki zo hannu"
Da sauri ya karasa emergency room din ya shige.. Cikin sauri Dr. Magaji yace "stitches din da aka mata ya kwance sbd jijjigan da tayi yanzu haka wajen bleeding yake jinin ta se karewa yake yi she is suffering" ya dafe goshin shi hannun daya..
Se da Dr. Godwin ya dubata yace "aiki ya dawo baya yanzu se mun koma dakin theater" da sauri aka turata dakin theater.. Shi kuma ya canza kaya. A waya aka kira lab attendant ta kawo jinin mijin tare da wani leda biyu zuwa dakin theater da sauri ta kawo aka jona ma matar ga oxygen a hancin ta aka fara mata aikin....
_Best of luck_


Wajen su Zee ta koma amma bata basu lbrin abunda ya faru bah se dai tace musu ta bar matar a emergency room. Rakata suka yi inda aka kwantar da mijin matar wanda ya farfado amma an bashi gado ya huta..
Wayan Ya Saleem ta kira yana dauka yace "black sisi ya akayi ne"
"Ya Saleem pls kazo ka dauke ni a asibiti bazan iya dawowa da kaina ba jinin wata patient ya bata mun kaya"
"jini kuma? Bari in juyo dama yanzu na wuce asibitin ku naje refilling gas kawai ki fito bakin gate" sallama tama su Zee sannan ta wuce.
Tana fita ta ganshi.. A mota ta bashi lbrin duk abunda ya faru da matar.. Ba karamin tausayawa matar yayi bah. A haka har suka kai gida. Tana shiga daki ta wuce tayi wanka ta sa dogon riga mara nauyi tayi sallah. Dakin Ummiey ta leqa taga tana barci. Kitchen ta koma ta deba abinci taci tasha ruwa seda ta bari abincin yadan fada mata ta koma dakin ta ta kwanta dan huce gajiya.

****
Da dare bayan sun gama cin abinci Abbiey ke tambayar ta ya aikin. Nan ta labarta musu komai suma dai duk sun tausayawa matar addu'a sosai suka mata Allah ya bata lfya.. Daga nan kowa yaje ya kwanta............










*_Rukky Bae_*😏😏😏
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: β€β£β£β£πŸ’•β£β£β£β£πŸ’•πŸ’• *_MATAR DOCTOR_*β€β£β£πŸ’•πŸ’•πŸ’•β£β€β€


(( *_2016_*))






*_Rukky Bae_*😏😏😏








6⃣7⃣****************6⃣8⃣








Alhamdulillah! Anyi operation lfya kuma sun fito lfya.
A hankali matar ta fara samun sauki.. Kullum likitoci da Nurses suna duba ta.
Tun daga lokacin Dr. Magaji ya dau nauyin ciyar dasu Janan kullum daga gidan shi ake kawo musu abinci.. Yana jin dadin aiki dasu suma suna jin dadin aiki a karkashin sa..
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya. Inda yanzu Janan ta fara sabawa da yima patients alluran anesthesia da kuma sa musu drip. Tunda suka fara aiki da Dr. Magaji kullum 2:30pm yake sallaman su sbd Islamiyan da suke zuwa har yana cema Janan da Aisha "lallai lallai idan saukan ya rage 2 weeks ku fada min kar in manta"
suka ce "in shaa Allah za mu fada maka".....
Gefe guda kuma ita da Imran soyayya na kara karfi inda yayi mata alkawarin yana dawowa daga seminar daya je a London ze zo wajen Abbiey neman izini...
Ashirin da biyar ga wata aka biya su albashi. Ba karamin farinciki suka yi bah. A ranan Janan ta shiga kasuwa bayan sun tashi daga aiki ta siyo ma Ummiey atampa karamar _Sheraton_ ta saima Abbiey agogunan fata guda 2 baki se kuma light brown Ya Saleem da Ya Khaleel ta siyo musu takalma na maza se kuma Nurulqal dinta tasai mai turaren _Gentle guy_... Har ta fito se ta hango wani shagon Arabian perfumes karasawa tayi ta siya guda 2 _Ameer oud da Alharamain Madina_ tana gama siyayya ta tsare adaidaita ya kaita gida...


***Da dare bayan sun gama cin abinci taje ta dakko kayan data siyo tare da canjin daya rage seda ta ba kowa nashi suna ta murna hade da yaba hankali irin na Janan cuz she is jaz 18yrs zata shiga 19 amma tayi abunda wasu 'yan 25yrs baza su iyi bah Ummiey da Abbiey sun samata albarka sosai Ya Khaleel da Ya Saleem se godia suke mata murmushi tayi sannan tace "kun cancanci fiye da haka"... Canjin daya rage ta ajiye a gaban iyayen ta tace "Ummiey,, Abbiey ga sauran canjin daya rage kuyi anfani da shi.. Kanta Abbiey ya shafa yace "Muhibbaty babu abinda za muyi dasu kinga ki ajiye a wajen ki sbd in bukata ta taso miki kinji! Ummiey tace "kwarai kuwa ki riqe ai naki ne Mamana Allah dai yayi miki albarka tare da yayyin ki baki daya" "Ameen" suka amsa.. Janan bata ji dadin haka ba amma bata san yin jayayya da iyayen nata haka ta hakura.. Hira suka dan yi kafin kowa ya wuce makwancin sa.. Tana shiga ta dauki turaren da ta siyo ma Imran ta shaqa tare da lumshe idon sannan ta bude drawer ta ajiye da niyyar in ya dawo ta bashi as a gift.. Har ta sa kayan bacci ta kwanta wayar ta ta fara ringing ko bata duba ba tasan Imran ne sbd wakar _Aashiqui_ ta sa mai.. Sunyi hiran soyayya sosai har yake fada mata nxt week ze dawo kuma cikin week din zai zo wajen Abbiey.. Tayi murna ba kadan bah se da ta fara hamma sannan yace "gwara in barki ki kwanta kar ki fara min sambatu" murmushi tayi kamar yana ganin tace gudnyt nd swt drmz" shi kuma yace "gudnyt nd chocolate drmz I luv u" da sauri tace "bye" ta katse wayan sbd tasan halin Imran yanzu se yace itama sai tace tana son shi.....


~A week later~


Imran ya dawo Nigeria cike da farin ciki ji yake kamar ya tafi gidan su Janan ya ganta sbd ba karamin missing dinta yayi bah amma se ya fasa yafi son se an bashi izini sannan ze je wajen ta su hadu... Bayan ya koma gida ya kirata ya fada mata ya dawo tayi murna sosai tare da mai Allah huta gajiya...




Ranar Thursday da yamma Imran ne tare da Faisal yayan Zee

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login