Showing 45001 words to 48000 words out of 82682 words

Chapter 16 - MATAR DOCTOR COMPLT BY ESHAAT.txt

ESHAAT   

18 Jan 2025

4330

yace mata
Suna cikin haka Zee da Eesher suka shigo suna gaida su.
Gefen Janan suka koma suna tambayar ta jikin ta ta amsa musu da Alhamdulillah.
Ummiey ce tace Wai ya akayi haka ta faru?
Eesher tace wallahi Ummiey ni dai ban san ya akayi ba kawai dai naga an wuce da ita emergency room jikin ta duk jini Ina shiga se naji Dr. Jalal yana fadin wai Asthma din ta ne ya tashi se kuma ciwon da glass ya ji mata"
Ya Salaam! Rabon da Asthma din ki ya tashi an dade Hulwaty ya akayi har Asthma din ya tashi dan Ina kyautata zaton ruwa kika shiga!
Da kyar ta ce eh Ummiey ruwa na shiga naje siyo magani ne se ruwa ya tare ni a hanya rashin samun abun hawa yasa ruwan ya mun duka sanda na dawo asibiti kuma nazo shigowa office se jiri ya debe ni na fadi kan glass din da ban san yana wajen ba"
Yaya Khaleel yace babu masinja ne a asibitin da ke da kanki zaki je?
Bro in aka ake su shirme suke yi shiyasa naje da kai na!
Sannu Muhibbaty Allah baki lfya kin ji" Abbiey ne ya fada haka.
Saleem yace "our chef is sick wa zai dinga mana girkin?
Daria sukayi duka Abbiey yace ga Ummieyn ku nima yanzu Ummiey ta zata huta ai kai dama haka kake da son abinci gashi baka iya dafawa ba Allah dai yasa ka auri wacce ta iya girkin sbd karka dinga zuwa gidan Muhibbaty kana dan murya a san maka abinci"
Daria suka kuma yi..


Cike da mamakin Dr. Godwin ke kallon ta ganin yanda bata fada komai game da abun da ya faru ba duk ta boye fault din shi duk da ya san shine silla ji yayi wani abu na kara shiga cikin zuciyar shi har ya saukar mishi da kasala, kuma da gani ita yar gata ce a gidan su dan yaga kowa naji da ita


Ka matsa gefe Eesher zata cire min" Janan ta ce mishi
Ba musu ya matsa sbd duk ya tsargu gani yake kamar za a gane shine sillan shigan ta wannan halin..


Eesher na gama cire mata tace Ummiey kun zo mun da kaya? Ina so in yi wanka"
Bamu zo da komai ba se dai yanzu Saleem ya koma ya dakko mana duk abunda ake bukata dan ba cikin kwanciyar hankali muka fito dan duk mun damu bayan Imran ya fada mana condition din da kike ciki, ki fara cin abincin da Imran ya kawo kafin Saleem din ya dawo..
Ummiey se na yi wanka zan iya samu relief da natsuwa"


Abbiey ya miqa ma Saleem key din gida sannan ya bashi kudi yace ya siyo duk abun da ya dace
Toh kawai yace sannan ya fita..


Dr. Godwin yace kuyi hakuri da abun da ya faru da ita sannan yayi excusing kan shi ya bar dakin cike da dana sanin abunda ya aikata!


Yana fita daga dakin ya wuce inda ya ajiye motar shi ya tafi boutique ya zabo mata dogayen riguna guda 6 da towel daga nan ya wuce supermarket ya siya kayan tea se exotic carton daya da bottle water shima kwali daya ya tsaya ya siya gasassun kaji, cikin sauri yake komai sbd yana so ya kai musu kayan kafin Saleem ya dawo


Yana tafe yana tuna duk abunda ya faru tare da dukkan reactions din sa yana mamakin kan shi yanda yake ba iyayen ta respect tare da jin wani irin kunyan su!
Kwana yasha yana tuno yanda Janan ta rufa mishi asiri ko da ya tuno yanda ta fada kan glass din se yaji wani irin haushin kan shi daya biye ma Precious har hakan yaja Janan taji ciwo, gudu yake yi sosai har ya iso asibitin, dakin direct ya wuce ya ce ga shi pls kuyi managy kafin ya dawo sbd ba komai da kuke so ba na siyo da sauri ya bar dakin sbd baya so suyi mishi godia kuma yayi ma kan shi alkawarin ba zai kara hurting din ta ba koda da kallon banza ne!


Abu kadan ne babu a kayan da Dr. Godwin ya kawo, Saleem na dawowa ta shiga tayi wanka a bayin ta shirya, kwata kwata taki anfani da kayan da Dr. Godwin ya siyo abincin da Imran ya kawo tun dazu shi taci se ruwan gora da Dr. Godwin ya kawo shima dan Yaya Saleem ya manta be siyo ruwa ba shiyasa tasha..




Se can yamma Imran ya dawo kuma dai dai da lokacin da Dr. Jalal yayi discharging din ta shi kuma Dr. Godwin ya bata hutun 1 week ko hakan ze kara sata farin ciki kuma yasa ta huce daga fushin daya ga tana yi dashi duk da yasan zeyi missing din ta sosai..
Tunda ya shigo be kalla Imran ba har ya fita sbd yama tsani ganin shi balle har su tsaya a inuwa daya dashi...
Godia su Abbiey suka yi musu sannan suka kwashe kayan su suka tafi gida...




Get Well Soon JananπŸ˜πŸ’‹πŸ˜˜








RukkyBae 😏😏😏
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: β™₯♠❀♣β™₯β™ β™₯♣❀♠♣β™₯♣❀♣β™₯♠❀♣β™₯♣β™₯♠❀♣β™₯β™ β™₯♣β™₯ *MATAR DOCTOR* ♣❀β™₯♣β™₯♠♣β™₯❀♠♣β™₯




Alhamdulillah! Alhamdulillah! Kamar wasa yanzu ya zama gaske babu abunda zan ce se dai Godia ga Allah daya daukaka wannan littafi!


Wannan shafin naku gaba dayan ku yan grp din *MATAR DOCTOR'S NOVEL ONLY*! Ngd da yanda kuke bani hadin kai kuma kuke son wannan littafin! Allah ya bar zumunci Ameen!








_RukkyBae_😏😏😏








***9⃣4⃣***








Tun lokacin da Precious ta bar asibitin hotel din data sauka ta koma tayi wanka ta fito daure da towel se ga chief din ya kirata ta fada mishi room numb din ko knocking be yi ba ya shigo ganin ta haka yasa ya fara mata wani kallo kasakasa tana ganin haka tasan me yake nufi nan suka fara aikata masha'ar su(Allah ya kare mu daga saba maka)








Haka kwanaki yayi ta tafiya kullum Dr. Godwin na hanyar gidan su Janan siyayya kala kala yake ma ta se dai ya aika yara su shiga dashi amma ya kasa shiga ciki sbd kunya su da yake ji yana son ya ganta a rana na 4 daya je be aika yara ba shida kanshi ya shiga ciki a tsakar gidan ya tsaya ya rasa ta ya zai yi su san ya shigo se ga Saleem nan ya shigo da mamaki ya miqa mishi hannu suka gaisa sannan ya ce yana zuwa
Yana shiga parlor ya tarar dasu zaune suna kallon TV Janan na shan fruits yace "Black Sis ga wannan Doc. din wanda kike taya shi aiki yazo, a tsakar gidannan na ganshi a tsaye"
Ummiey tace Ikon Allah ka bude mishi dakin baki ya shiga mana ka barshi a tsaye kamar wani soja"


Kai! matsala ta da waenda ba musulmai ba kenan basu san su nemi izini ba kafin su shigo gidan mutane ko an ce mishi nan a garin Jahilai ne da ze wani shigo mana gida ba izini oho"


cike da mamaki Ummiey ke kallon ta tace ke kuma lfyar ki ke fadin haka yanzu idan ya ji ki fa? Yaushe kika zama haka?
Ta turo baki to ai gaskiya ne Ummiey..
Allahu yahadeeki (Allah ya shirye ki) tashi ki kai mishi ruwa da danbun nama da drinks ai bakon annabin ka Ina laifi ma yazo duba ki ga dawainiyar da yake yi dake sbd a karkashin sa kike amma kike fada haka maza ki tashi ki kai mishi..


A zuciyar tace Ummiey baki san waye shi ba ne shi yasa kike fadan haka ba karamin dan wulakanci bane ga rainin wayau da dan banzan mugunta"


Dogon hijjab tasa sannan ta jera kayan a kan tray ta fice ba dan ranta yaso ba.. Tana shiga ta ganshi zaune suna hira da Saleem ta fada a hankali "ji be shi kamar na kirki se iskanci fal ciki me qaton kai kawai"
Sallama tayi sannan ta shiga idon shi qyar a kanta gani yayi tayi mishi wani irin kyau amma ta dan rame har wani lumshe idanu yake yi, a gaban shi ta ajiye tray din sannan ta juya zata tafi Saleem yace ke haka ake yi ma baqo a garin ku? Ko gaishe shi ba kiyi ba kin wani dungura mishi abu zaki tafi kin dai san shinfidar fuska tafi ta tabarma ko? .
Bata so haka ba dan ita haushi yake bata sbd bata son wani alaka ya dinga hada ta da dan iska, dawowa tayi ta zauna gefen Saleem, "Ina wuni" ta fada a daqile kamar ba magana take yi ba,
Shiru yayi yana wani shan kamshi irin shi a dole be ji ba din nan Yaya Saleem yace ko ni da nake kusa dake ban jiba balle shi da yake nesa.


Cikin qosawa ta sake gaida shi amma wannan karan da karfi tayi
Ze yi magana kenan aka kira wayar Saleem yace bari ya amsa waya yana zuwa, kamar jira Dr. Godwin ke yi Saleem na fita ya dawo kusa da ita yana mata kallon nayi kewar ki ta kawar da kai gefe tana jin haushin irin wannan kallon tace a hankali ni dai ba yar... Bata karasa ba yace ba yar me ba?
Ba komai tace a takaice
Yasan cewa yayi mata ba dai dai ba amma shi a ganin shi ba komai bane dan ta gansu a wannan halin shida Precious sbd haka be ma sa wannan a matsayin laifi ba shi dai laifin daya da ya aike ta har aka samu matsala


*JANAN* ya kira sunan ta!
Ya Salaammm! Ta fadi a ranta tana lumshe ido cike da mamakin yanda ya iya kiran sunan kamar shi ya rada mata kuma in zata tuna yau ne first time daya fara kiran sunan ta tunda suke! Ya katse mata tunani da fadin "kina gani kamar nayi miki laifi ne bayan kuma kece da laifi sbd ke kika ja komai ya faru ya kamata kizo office da wuri amma kika ki shine ni kuma nayi punishing din ki sbd nxt time karki sake haka"
Wani kallo tayi mishi irin na ka raina min wayau bata ce komai ba ya cigaba "ki manta da komai kuma ya kamata ki bani hakuri a matsayina na Boss din ki"


Tabb! Ka dade kana min laifi ban taba cewa komai ba ka ja Asthma na ya tashi wanda ni kaina na manta Ina da shi sannan na shigo naga kuna iskanci da wata ka fasa glass a kasa na fada a akai naji ciwo harda dinki aka min amma kace wai ni ya kamata in baka hakuri" niyyar tashi tayi amma yasa hannun shi ya danne kafar ta


Miye haka kuma ni ka dena taba ni sbd ni ba yar iska bace"


Killer smile din shi ya mata yace to waye dan iska?
Shiru tayi sbd yanda ya tsareta da mayun idon shi ba zata iya cewa komai ba


Anyway! Tunda ba zaki bani hakuri ba shikenan ya tashi ya koma mazaunin shi yace zo ki zuba min ruwa in sha"


Ta so tace ai kana da hannu kuma ni ba yar aikin ka bace se dai kawai ta fasa sbd ta gaji da magana da shi..
Cup ta dauka ta zuba mishi ya fara sha se ga Saleem ya dawo yana cewa "baka ci komai ba se ruwa? Pls Kaci danbun naman nan I knw u will like it"
Kadan ya diba yasa a baki wani irin dadi da gardi ya ji ya mamaye ilahirin bakin shi ji yake kamar ya dau bowl din ya tura a baki ganin kar ya bada kanshi ya zubda class din shi yasa ya miqe yana fadin "zan tafi ngd sosai"
Hanyar waje yayi Saleem yace ma Janan ta dakko bowl din ta bashi sbd ya lura Dr. Godwin naso yaci sosai amma yana jan aji!


Foil paper ta koma ciki ta dakko sannan ta rufe ta bishi dashi, a bakin kofar gate ta same su sukayi sallama da Saleem ya koma cikin gida ita kuma Janan taje wajen motar shi dan ta bashi danbun.. Jikin motar ya tsaya ya harde hannayen shi a kirji yana kallon ta tana tahowa a hankali har ta karaso, miqa mishi tayi yaki amsa ta zagaya dayan bangaren ta ajiye mishi akan kujeran motan ta juya tayi tafiyar ta..
Girgiza kai yayi yace "ke kadai ce kike min abunda kika ga dama ba wanda naga dama ba,"
ya shiga motar shi ya wuce yana jin dadin ganin ta da kuma abunda ta bashi...


Dakin bakin ta koma dan tayi clearing komai kawai se taga ledoji guda 2, daya chocolates da sweets dayan kuma turarruka ne masu kyau baki ta tabe sannan ta kwashe ta kaima Ummiey, zuciyar Ummiey ta fara raya mata wasu abubuwa amma se ta share tana fadin it's impossible! A fili kuma tace gaskiya Yaron nan akwai kokari ga kirki"
Saleem yace wallahi kuwa baki ga yanda muka sha hira da shi ba"
Hmm! Dan baku san halin shi bane shiyasa kuke fadin haka" Janan tace
Ummiey tace mu dai abun da muka gani shi zamu fada"
Shiru Janan tayi bata sake cewa komai ba sema ta canza hiran...














RukkyBae 😏😏😏
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: β™₯♣❀♠❀♣❀♠β™₯♣❀♠♣β™₯♠❀♣β™₯♠❀♣♠β™₯❀ *MATAR DOCTOR*
♣❀♠β™₯♣♠♣❀♣β™₯♠❀♣♠β™₯♣❀♠β™₯♣β™₯♠❀♣








Rukkybae 😏😏😏






A piece of advice! Duk sanda period din ki yazo ki karanta wannan adduaar *Alhamdulillahi Ala kulli halin wa ana astagfirullah wa atubi ilaihi*
Sannan ki yawaita istigfari domin neman gafaran Allah kuma ki kasance kullum cikin alwala sbd neman tsari daga Aljanu da kuma Sihiri domin lokacin da mace bata cikin tsarki toh Asiri da aljanu za suyi saurin tasiri a jikin ta! Wallahu Aalam!








****9⃣5⃣****








Yau sati dayan da Dr. Godwin ya daukar wa Janan har ya cika ba da son ranta ta koma asibitin ba se dan taimakon jamaa..


Tana shiga ta gaishe shi ta zauna tana hada rai sau daya ya kalleta ya kauda kai sbd yaga alaman yau fada take ji.. Marasa lfya suka fara shigowa yana duba su can wajen 12 se ga kira nan ya shigo da zumudi ya dauka cikin shagwaba yace "Momma nayi fushi dake yaushe rabon ki kira ni? Kallon shi Janan ta tsaya yi ganin yanda yake shagwaba kamar wani yaron goye!
Momma daga daya bangaren tace Baby muna missing dinka sosai ka kunna laptop din ka muyi video call inga yanda ka zama.


No! No! Not now yanzu Ina cikin aiki ne when i'm free I will call se muyi video call din"
Momma tace yanzu nake so in ganka kuma Ina jiranka na baka 2 mints" tayi hanging call din.. Yasan tayi fushi ne ba yanda ya iya haka ya jawo laptop din yana kunnawa se ga call din ya shigo da sauri yayi connecting daga bangaren ta tace "wow baby naga ka kara girma ne kayi fresh wato ka barmu kana can kana jin dadin ka menene sirrin! Janan ya kalla da gefen ido yaga shi take kallo murmushi yayi yace "Momma ba wani fresh ni da nake missing din ku wani jin dadi kuma"


Fada min me kaci yau da safe? Rolling idon shi sama yayi kamar me tunani yace "no bazan fada ba kiyi guessing!
Tayi daria tace " Garri ba sugar"
Daria ya kwashe da shi harda kyakyatawa yace haba Momma yaushe kika dena sona ban sani ba how on earth za ace in rasa abun breakfast se garri kuma wai ba sugar" ya sake kwashewa da daria, tunda kin kasa guessing kuma kin manta favorite dina toh I ate sandwich nd oat"
Tace wow! Dole ka dinga qiba.


Haka sukayi ta hiran su yana zuba mata shagwaba Annabell da Dad shigowar su kenan suma sukayi joining hiran..


Duk sun yi farin cikin ganin junan su..
Mamaki ne ya cika Janan ganin yanda Family'n nashi suke son shi kamar zasu hadiye shi..


Dad yace hope dai kana zuwa church"
No Dad bana zuwa kasan aiki na bazai barni ba"


Stop dodging nasan halin ka I knw ba zaka dinga zuwa ba since u aren't interested!
Kai kawai ya ke sosawa alaman rashin gaskiya
Momma tace Precious ta zo tace min kayi mata wulakanci"
Yamutsa fuska yayi yace forget abt her Momma I don't wanna talk abt her"
Annabell sister'n shi tace "Babyn Momma yaushe zaka zo?
Soon Princess don't worry kin ji?


Wayar office din sa ce ta fara ringing yasan emergency ne sbd dalilin haka aka ajiye wayar a office din, da sauri yace Momma urgent call ne ana nema na a emergency inna samu time I will call u I love u all yayi musu kiss suma suka ce we love u more sukayi kissing din shi da sauri ya kashe yace ma Janan let's go! Ya zari lab coat din shi.. Ba musu tabi bayan shi..


_Labour Room_


Tun safe aka kawo matar amma ta kasa haihuwa da kanta sbd BP din ta yayi high kusan awa 3 da rabi kenan duk ta jigata har ta gaji da nunfashi da karfi ta koma a hankali..


Takardan yarjejeniya akan za'a mata operation aka ba mijin ta ya cika..


Kan gado aka daurata cikin gaggawa aka shigar da ita dakin theatre..


Kwararrun Likitoci ne har 5 a kanta amma sun kasa komai duk iya kokarin su sun kasa se kai kawo suke yi amma abu yaci tura! Dr. Godwin yace ohhh my God! This is serious!
Duk suka hada baki suka ce very serious!
BP din yaki sauka balle a mata operation kuma akwai tabbacin da zaran sun mata theatre jinin be sauka ba zata iya rasa ranta so dole ne ita da kanta ta haihu but how?
kwata kwata dabara ta dauke musu..


Da sauri Janan ta fita ta koma office ta dakko ruwan gora ta zuba a cup jikin ta se rawa yake yi ta tofa adduaa a ciki sannan ta karanta _thummassabila yassara_ ba adadi sannan ta koma dakin yanda ta tafi ta barsu haka ta dawo ta same su, inda matar take kwance ta wuce seda ta ajiye cup din akan wani table tace "pls ku bani dama in bata ruwan nan by the Grace of Allah zata haihu da kanta" Wani irin kallo suke mata Dr. John yace "ya za ayi mu barki ki bata ruwa bayan kin san ba zai yiwu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login