Showing 15001 words to 18000 words out of 82682 words

Chapter 6 - MATAR DOCTOR COMPLT BY ESHAAT.txt

ESHAAT   

18 Jan 2025

4339

zaro yace "1week is too much pls ki dan rage ko zuwa gobe ne" da kyar ta yarda nan da 3 days zata bashi amsa sannan sukayi sallama.. Bayi ta shiga tayi wanka sannan tasa kayan bacci ta hau gado tare da yin addu'a taja bargo ta fara bacci....






Sai 3:30am na dare Godwin ya farka jikin shi duk a mace ga yunwa ta addabe shi dan tun breakfast be sake cin komai bah da kyar ya tashi yana dafa bango ya shiga bayi yayi brush abincin daya siyo ya fara dubawa bai gani bah can ya tuno yana mota Key ya dauka ya nufi motar a yanda ya barta haka ya same ta ciro brief case nashi yayi da abincin gate din gidan ya kulle sannan ya shiga ciki ya yi warming abincin ciki microwave ci yake amma baya jin dadin abincin saida ya gama ci sannan yadan ji karfi amma har lokacin kanshi ciwo yakeyi sai dai ya rage ba kamar dazu bah.. Bedroom ya koma yana zuwa yaga wayar shi na haske koda ya duba sai yaga missed calls sun kai 20 ga msgs wayar ma sai warning b3 low take yi tsaki yaja ya kashe wayar ko duba waenda suka kirashi be yi ba yasa a caji.. Kaya ya cire ya shiga bayi yayi wanka da ruwa me zafin gaske a nan ne yadan ji dama dama.. Yana fito wa yasa pyjamas dinshi ya janyo laptop ya bude mails nashi har wajen 4:30 na dare yana kan laptop sai can ya kashe ya sake komawa bacci dan maganin dayasha bai sake shi bah...















*Rukky Bae*😏😏😏
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: ❤❣💕💕❣❣💕💕❤❣❣ *MATAR DOCTOR*❣💕💕💕💕❣❣❣❣💕





*Rukky Bae*😏😏😏




5⃣8⃣**************5⃣9⃣














Sai 10:00am Godwin ya farka daga bacci.. Bayi ya fada yayi wanka tare da brushing bakin sa.. Yana fitowa ya shirya cikin farar riga da bakin pencil trousers slippers irin na maza mai laushi fari ya sa sannan ya wuce parlor ya zauna tare da janyo laptop din shi yayi banciken sa.. Dakin shi ya koma ya ciro wayar shi wadda ya barta a chargy tun jiya.. Kunnata yayi ya fara dubawa missed calls ya gani rututu Momma, precious, Dad ,Lawal duk yaga sun kira shi.. Inbox nashi ya duba nan yaga msgs duk precious ce tayi mai su duk dai kan be dau wayar ta bah. Momma ya fara kira suka gaisa sai shagwaba yake zuba mata anan ya fada mata jiya ciwon kanshi yafi na kullum amma yasha magani yaji sauki.. Sun sha hira sosai kafin ya kashe ya kira Dad shima dai haka sukayi hira amma rabi akan ya riqe addinin su ne. Shidai Godwin jinshi kawai yake yi.. daga karshe ya kira precious suka sha luv.. Yaso ya kira Lawal ya kawo mishi breakfast amma sai ya fasa Dr. Magaji ya kira ya fada mishi ba zai zo asibiti bah yau cuz tun jiya yake fama da ciwon kai.. Nan Dr. Magaji yace ba matsala tunda yau short day ne ya bari Monday sai ya zo... Yana gama wayan ya shiga kitchen sbd yunwa ya fara damun shi. Rasa abun da zai ci yayi gashi be iya komai bah kuma baya san yayi break da tea nd bread.. Parlor ya koma ya dakko wayar shi wani app na yanda ake koyan girki ya shiga nan yaga girke-girke iri iri method of preparation na pancake da Quaker oat ya duba sai kuma yanda ake omelette murmushin jin dadi yayi.. Tsayawa yayi dan nan ake yinta cuz be ma iya kunna gas cooker bah.. Lebe ya cije sannan ya bude kitchen cabinet.. manual na gas din ya dakko ya duba a haka ya kunna gas din nan ya fara aiki. pancake ya fara yi duk ya qona hannu sannan omelette sai oat daga karshe kitchen din duk yayi kaca-kaca ga pancakes da omelette duk sun qone haka ya kwashe a tray ya wuce dining table ya zaune sai zufa yake yi.. Yana kai pancake bakin shi da kyar ya hadiye haka ma omelette din duk basu soyu ba gashi sun qone dan ba karamin wuta ya cika musu bah. Kasa ci yayi haka ya ture su gefa oat din ya dan sha gashi be koshi ba dan yunwa sosai yake ji. Kitchen ya koma ya dakko wayar shi ya kira Lawal yace "Lawal ka kawo min breakfast kuma akwai aikin da zaka min".....
Cikin minti 30 sai gashi ya zo dauke da leda.. Godwin ya karba ya fara cin plantain, chips da kwai saida ya qoshi sannan ya ce " Lawal ina so ka samo min masu aiki guda 2 mai gadi sai wacce zata dinga yimin girki da sauran aikace aikacen gida. U no my style nd choice". Murmushi Lawal yayi yace "yes little master ka bani daga yau zuwa gobe" "aa yanzu kaga karfe 11:30 zuwa yamma nasan zaka samo su cuz bazan iya bari sai gobe bah zan dinga biyan su 30k every month" masu tsafta nake so bana san kazamai. "ur wish is my command little master" sannan ya wuce dan nemo yan aikin...
Karfe 8 na dare Lawal ya shigo gidan tare da yan aiki guda biyu mace da namiji.. Nan yayi musu bayanin yanda za su gudanar da aiki.. Dakin kusa da gate a ka ba Iro mai gadi ita kuma Agnes aka bata dakin baya.. Harda uniform ko wani rana da kalan da za su saka...






Janan na dakin ta tana gyaran wardrobe dinta wayar ta ta fara ringing Zee ta gani a jikin screen din da sauri ta dauka suka gaisa nan Zee ke ce mata "ai rannan Imran yazo gidan mu muyi hira sosai kan ki nan yake fada min yanda yake sanki wallahi na tayaki murna samun saurayi irin Imran sai an tona Dan Allah kema ki so shi sbd kun dace kuma wallahi dagaske auren ki zai yi mudai muna roqan ki ki so shi cuz bai taba soyayya bah.. Ai ni tuwo na mai na.. Allah dai ya nuna mana tym din biki" dariya sosai Janan tayi kafin tace "sannu yar campaign kin zo kiyi mai campaign ne koh? "aa ba wani campaign wallahi kun dace can't wait to see ur cute babies" "lallai Zee ke har kin fishi zaqewa"... Sosai sukayi hira kafin suka yi sallama



******

Yau kwana 3 dai dai Imran ya kira Janan dan jin kota amince! Kasa bashi amsa tayi dan kunyar da take ji nan ya gane ta karbi soyayyar shi amma saida ya takura mata sai ta fada mishi.. cikin jin nauyi ta fada mishi ta karbi soyayyar shi.. Hamdala yayi daga nan suka sha soyayya saida waja jen 9:00pm ya barta.. Juyawa tayi tana addu'a taji Alamar txt ya shigo wayar ta. Saida ta kammala addu'an sannan ta dauka ta duba kamar haka
_My Luv 4 u is natural, u r my soul mate, my hrt desire u just d perfect blood in my veins.. I can't explain hw much I luv u but I promise to luv u till eternity.. Gudnyt my Angel_ _I so much luv u_
Ta karanta msg din yafi sau a qirga kafin ta kwanta bacci cikin jin dadi da kwanciyar hankali..










*Rukky Bae*😏😏😏
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: ❤❣❣💕💕❣❣💕💕💕❣ *MATAR DOCTOR*❣❤❣❣❣💕❣❣❣💕






*Rukky Bae*😏😏😏








6⃣0⃣








*Monday morning*






Janan shirye cikin fararen kayan nurse riga da wando se dan karamin hijjah tayi kyau sosai a gurguje ta karya tayi ma Ummiey sallama ita kuma Ummiey se addu'a take zuba mata.. Horn din Abbiey ne ya sata fitowa da sauri sbd shi ze yi dropping dinta.. Dai dai bakin gate ya ajiye ta sannan ya bata 500 na abinci da transport godia tayi mishi tare da daga mai hannu har ya wuce tana kokarin shiga ciki sai ga Zee ta sauka daga adaidaita tare suka shiga cikin asibitin.. Kokarin shiga office din Dr. Magaji sukeyi se ga Eesher nan da sauri sai faman haki take yi tace "Gud morning babes" dariya sukayi kafin suka amsa mata suna tambayan "lfya kike haki kamar wacce a ka biyo da gudu? "ba dole inyi haki ba ina ta faman kiran wayan ku be shiga bah gashi ina tunanin nayi latti ko kyakkyawan breakfast ban yi ba na fito sai uban sauri nake yi, Alhamdulillah na hadu daku sai mu shiga".. Knocking kofar sukayi daga ciki a ka ce "come in" da sallama suka shiga cikin office din sannan suka duqa suka gaida Dr. Magaji da fara'a ya amsa musu yana me jin dadin yanda suke girmama shi.. Kujera ya nuna musu duk suka zauna.. Bayani ya fara musu kamar haka "Alhamdulillah yau ta kasance Monday wato tushen aiki a yau zaku fara aiki ina fata zakuyi aikin ku tsakani da Allah kuma ina so in ja hankalin ku akan hakuri tare da juriya sbd wannan aikin naku saida hakuri sbd aikin taimako ne sannan ina so ku kasan ce masu sympathy(tausayi) akan marasa lfya ko mai girma ko kankantar patient koda ba addinin ku daya ba ta haka ne zaku cimma burin ku kuma zaku sami lada mai tarin yawa daga wajen Allah (SWT) sannan ku girmama duk wani wanda ya girme ku kar ku kasance daga cikin nurses masu dakawa duk wani mara lfya tsawa da fatan za kuyi anfani da wannan shawara dana baku"
A tare suka hada baki wajen cewa "In shaa Allah zaka same mu masu gaskiya da riqon amana a wannan aikin namu tare da jajjircewa wajen bawa duk wani patient kulawa har in da karfin mu ya kare" Dr. Magaji yace "Allah ya albarkaci rayuwar ku ya taimake ku" "Ameen" duk suka amsa.. Mai kawo katinnan marasa lfya ne ya shigo da files masu yawa a hannun shi saida ya gaishe da Dr. Magaji su kuma su Janan suka gaida shi kafin ya ajiye files kan table din Dr. Ya fita.. Daya bayan dayan marasa lfya suka dinga shigowa suna fadawa Dr. Matsalolin su duk su Janan suna kallo.. Wata mara lfya ce ta shigo bayan ta gama yiwa likita bayani ya juyo ya kalle su Janan yace " 'ya'yan albarka wa zai fada min matsalar matan nan? Shiru suka yi se can Aisha tace " tana fama da matsalar appendix" jin jina kai yayi yace haka ne.. Kirji matar ta dafe tace "appendix kuma? "Yau na shiga uku likita kana nufin sai an fede ni? kuka ta fashe dashi.. Zainab ce ta tashi ta matsa kusa da ita tare da dafa kafadar ta tace "ki kwantar da hankalin ki ba lallai bane ayi miki operation wannan fargaban da kike sawa kanki zai iya haifar miki da hawan jini" a hankali matar ta goge hawayen ta tace "tor likita yanzu mene ne abun yi? Shiru yayi yana kallon su Janan yana jiran amsa daga bakin su.. Janan tace "dubaki za a fara yi idan har appendix din beyi kwari bah ma'ana beyi girma ba tor za a baki magunguna waenda zasu narkar dashi amma idan yayi girma to dole za ayi miki operation a cire miki shi sbd in ya fashe a cikin ki ze iya damaging miki hanji da kuma kayan cikin ki" "Excellent" inji Dr. Magaji. Wani gado ya nuna mata yace ta kwanta a kai haka ta kwanta ya gama gwaje-gwajen sa sannan yace "be yi girma ba zan rubuta miki magunguna sai kije pharmacy ki saya bayan wata 2 sai ki dawo idan ya narke shikenan idan kuma be narke ba sai anyi operation" yar paper ya miqo mata rubuce da magunguna.. Godiya ta mishi tare da sama su Janan albarka.. Tana fita mai kawo katinan marasa lfya ya shigo da sauri yana fadin "likita ga wata mata an kawo rai a hannun Allah" da sauri Dr. Magaji ya tashi yace dasu Janan su dakko gadon da ake tura marasa lfya su biyo bayan shi.. Cikin sauri suka dakko suna binshi a baya.. Suna zuwa suka ga patient din a sume sai bleeding take yi.. Janan na ganin jini ta runtse ido jikin ta ya fara rawa gabaki daya ta rude ta kasa natsuwa babu abinda take furtawa sai "innalillahi wa innailaihirraji'un"..waenda suke tare da ita sai kuka suke yi. Da sauri Dr. Magaji yace su Janan su dauketa su azata bisa gadon.. Gefe Janan ta koma tana kuka ko ina a jikinta rawa yake yi.. Ganin haka Dr. Magaji yace su Aisha da 'yan uwanta su dauke ta su daurata a kai.. Haka suka daura a kan gadon suna turata da sauri Dr. Magaji na gaba suna binshi a baya.. Straight dakin theater suka wuce... Inda yake ajiye files ya fara dubawa Janan na tayashi amma ya kasa ganin file din matar "ya salaam!! Abunda ya furta kenan ga matar kwance hopelessly gashi babu file dinta kuma kafin su bude sabon file wani aiki ne. Da sauri yace "Janan jeki store room inda muke a jiye files din marasa lfya ki nemo min file din Halima Adam in baki gani ba ki kwaso duka files din dake gefen "H" ki taho min da su.. Yana gamawa Janan ta fita cikin sauri tana zuwa ta dinga dubawa bata gani bah haka ta kwaso files din da suka fara da "H" ta fito sai faman sauri take yi idonta duk kwalla sbd ta tsorata da yanayin patient din gaba daya hankalinta baya tare da ita ga files din sun rufe mata hanya.. Bata ankara ba tayi karo da mutum duk files din suka warwatse gasu da uban yawa... Dagowa tayi da niyyar masife ko waye tace " are u blin......daidai nan shima ya bude baki yana fadan "what the... A maqogaron shi sauran maganan ya maqale ita ma haka ta kasa karasawa........












*Rukky Bae*😏😏😏
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: ❤❣❣💕💕💕❣❣❣❣ *_MATAR DOCTOR_*❣❣💕💕💕💕❣❣❤










*_Rukky Bae_*😏😏😏








6⃣1⃣~~~~~~~~~~6⃣2⃣












Kasa karasa maganan sukayi sakamakon ganin junan su .. Godwin da karfin hali shine ma ya iya bude baki yayi magana "nxt tym in kina tafiya ki dinga duba hanya bawai ki dinga tafi anyhow bah" kallon shi kawai take yi sbd tsabar haushi "am nt in d mood" iya abinda tace kenan kawai ta fara tattare takardun bata sake kallon inda yake ba balle magana ta sake hada su.. Har ya duqa zai tayata kwashewa sai kuma ya fasa kawai yayi wuce war shi ko waigen ta be sake yi bah... "wannan wani irin mutum ne? Shi kullum haduwa dashi babu wani alkhairi? Gashi da shegen girman kai.. Me ya dauki kanshi" Mitchww ta ja tsaki haka tayi ta mita cikin ranta tana kwashe takardun.. Wasu mata da suke zaune a gefe suka zo suka fara tayata kwashe files din "baiwar Allah kiyi hakuri wasu haka suke sun san kirikiri suke da laifi amma basa daukan laifin su.. Shifa ya bige ki sbd yana tafe yana amsa waya amma ya daura miki laifin".. a haka har suka gama kwashe mata files din "muje mu raka ki dan naga files din sun miki yawa" "Nagode sosai Allah ya saka muku da alkhairi" har kofan dakin theater suka raka ta ta shiga ciki ta ajiye na hannun ta sannan taje ta karbo na hannun su ta kara musu godiya "babu komai ki kara hakuri kinsan komai na duniya dan hakuri ne" "Allah ya biyaku" "Ameen" suka juya suka wuce ita kuma ta koma ciki..


Da kyar aka lalubo file dinta duk yayi kura sbd ta dade bata zo asibitin ba. Fada Dr. Magaji ya fara ma mijin ta "meyi haka? Tun yaushe ya kamata ace kun dawo asibitin nan baku dawo ba se yau kasan halin da take ciki kuwa? Se da nayi muku kashedi ku dawo akan lokaci amma baku ji bah. Na ja muku kunne har kai na kira na fada maka amma a banza. Baka damu da halin da take ciki kenan ba. Kasan sharrin fibroid kuwa? Har ya kai da tana bleeding" tabur ya buga yace "I will get back to u" office din shi ya wuce ya bar mijin matar a tsaya ko motsi ya kasa kamar ruwa ya cinye shi.. Dr. Magaji ya dawo cikin saurin sanye da kayan operation bayan yayi alwala a office din shi, hand gloves yake sawa ko kallon sashen mutumin be sake yi bah ya shige ciki.. Da sauri da sauri ya fara fiddo kayan aiki.


Dr. Magaji se sai specialist wanda ke hada alluran anesthesia sai kuma wata likita guda daya mai suna Dr. Salma sannan su Janan. Duk tsaye suke a gaban gadon matar bayan an canza mata kaya zuwa na operation kwata-kwata bata san inda kanta yake bah.. Dr. Salma ce ta fara sterilizing wukake da karafunan da za ayi amfani dashi.. Dr. Magaji ya karbi alluran anesthesia ya miqawa Janan yace "kiyi mata sbd kar muna cikin aiki ta farka tunda suma tayi zafin operation zai iya sa ta farka".. Jikin Janan ya fara rawa idon ta yayi raurau.. Ganin haka Dr. Magaji ya fasa bata ya miqa ma Aisha aiko ta karba tayi ma matan ita kuma Zee ta sa mata drip. Duk da likitoci basa ba nurses su sama patient drip ko suyi musu anesthesia amma shi ya basu sbd yaga they r very intelligent kuma suna da natsuwa.. Duk suna tsaye aka kunna fitulun operation nan da nan suka fara aiki Janan ta kasa jurewa sai kuka take yi.. Alama yayi mata da hannu taje waje sbd yanda hankalin ta ya tashi.. Kamar dama jira take yi ta fice da sauri.. A benci dake waje ta zauna tare da daura kanta a cinyar ta tai ta faman rusar kuka.. Ganin kuka bazai mata magani bah ta tashi ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login