Showing 30001 words to 33000 words out of 82682 words

Chapter 11 - MATAR DOCTOR COMPLT BY ESHAAT.txt

ESHAAT   

18 Jan 2025

4328

bata koma office ba tasan yau ba karamin wulakanci zata sha wajen Dr.Godwin ba... zunbur ta miqe dan gaba daya tama manta da warning din da yayi mata da sauri tayi ma su Zee sallama ta wuce suka ce "ki jira mu tafi tare mana
tace "aa karku damu sauri nake yi"
Gudu-gudu sauri sauri ta doshi office din seda tayi Addua'a ta shafa sannan ta bude kofar a hankali tana sa kafa cikin office din sukayi ido hudu da Dr.Godwin gaban ta ya bada darammm!!














*_Rukky Bae_*😏😏😏
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: [12/18, 12:38 AM] Rukky Bae😏😏😏❣❀❣: ❀⚜❣⚜❀⚜❣⚜❀⚜ *MATAR DOCTOR*⚜❣⚜❀⚜❣⚜❀⚜❣⚜❀⚜❣⚜❀⚜❣⚜❀❣⚜❀⚜❀⚜❣❀⚜






*Rukky Bae*😏😏😏








_Dedicated this page to all my primary and secondary sch frnds and classmates.._ _my unforgettable_😍
_One love to u guys_✌





7⃣8⃣






Suna hada ido da Dr.Godwin gaban ta ya bada darammmm!! Kasa motsawa tayi daga bakin kofar ganin haka yasa shi dauke ido a kanta ya cigaba da danna laptop..
Yar siririyar ajiyar zucia ta saki sannan ta taka a hankali ta koma wajen zaman ta.. Duk abun da suke yi idon su Jessica yana kai sedai basu kawo komai a ransu ba...
Haka suka zauna shiru babu me cewa komai..




2:20pm Se lokacin Janan ta tuno bata ci komai ba se ruwan shayi gashi har ya kare duk da ba wani yunwa take ji ba amma tana so ta dan ci wani abu ko zata ji dadin bakin ta.....
Da sauri ta bude jakarta ta ciro wafer sticks din da Eesher ta basu ta miqawa su Jessica suka ce basu ci.. Bude abunta tayi tana ci har ta gama sannan ta dakko bounty chocolate shima tana ci... Wani irin kara suka ji daga wajen da Dr.Godwin yake da sauri suka kalli direction din suka ga se buga kanshi yake yi akan table ga jini a gefen girar shi a rude duk suka miqe suka yo kanshi Jessica da Ruth sukayi saurin riqe shi a tsawace yace "take off ur filthy hands frm my body" da sauri suka dauke hannun su daga jikin shi suka ce "sorry sir"
Ganin haka yasa Janan komawa baya dan tsawan ya razanata...
Da hannu biyu ya riqe kanshi sbd juyin da yake yi ga jini yana diga a kayan shi damma kayan baki ne.. Gabaki daya duk ya canza fuskar shi tayi jajawur.. Janan na kallon shi taji ya bata tausayi a hankali ta nufi first aid box dake cikin office din ta dakko hydrogen, cotton wool da plaster cike da tsoro ta karaso bakin table din ta tsugunna...Tunanin ta tsaya yi can dai ta daure cikin rawar murya tace "ex...cuse me" jin muryar ta a kusa dashi yasa yayi saurin bude ido tare da sauke hannu daya yana kallon ta amma be ce komai ba ganin kayan aiki a hannun ta yasa ya fahimci inda ta dosa... A hankali ya cire hannun shi.. Cike da mamakin yanda be yi gardama ko tsawa ba Janan ta fara goge mishi jinin... Hydrogen ta zuba jikin auduga ta shafa a kan ciwon..
Arrrrrgggghhhh ya saki kara sbd zafi da sauri ya ture hannun ta ya kwanta akan table din dan yaji zafi sosai...


Reaction dinshi yaso ya bata daria amma ta daure ta sake matsowa da hydrogen din da sauri ya riqe mata hannu yana mata kallon karki sa akwai zafi ta fahimci kallon amma se ta kalli hannun daya riqe mata alaman ya saketa da sauri ya cire hannun shi yana kallon fuskarta...a haka ta samu ta karasa har ta sa mishi plaster din sannan ta tashi zata wuce da sauri yace "auush" komawa tayi ta durkusa dan bata san me yasa yace auush ba... Ganin ta tsugunna yasa yace "baki bani magani ba"
Tace "oops! Ina yake?
ya mika hannu daidai gefen bakin ta ya ciro karamin chocolate din daya maqale a wajen yasa a baki tare da lumshe ido sannan yace " wannan ne magani na''
Janan kasa magana tayi se ma tashi da tayi ta maida kayan cikin first aid box din dan alamarin shi ya fara ishen ta...


Su Jessica dake tsaye tuntuni suka kalli juna cike da mamakin abunda ya faru tsakanin Dr.Godwin da Janan... Wani tari Ruth tayi wanda ya tuna mai suna office din yace "zaku iya tafia se gobe as u can see am sick sannan kuma ba muda aiki daya rage ganin ku makes me fall sick again and again"
Jiki a sanyaye suka dau bags din su suka fita suna ta maganan su Janan a haka har suka samu abun hawa kowa ta wuce gidan su...


Bangaren Janan kuwa ganin ya ce su Jessica su tafi itama ta dauki jakar ta tana jiyowa taga yana rawan sanyi remote din AC ta dauka ta kashe ta dakko suit din shi da yaki amsa ta daura mishi a jiki.. A hankali ya fara rufe ido tace "can i go? Tunowa yayi da itama tana fama da mura kuma yaji dadin taimakon da tayi mishi duk da be nuna mata ba.. kai kawai ya daga mata alamar eh zata iya tafia...
Cike da murna ta fara tafia se taji yace "hey come"
Dawowa tayi tace "gani"
Yace "ki dau wayata ki kira mun Lawal yazo ya wuce dani gida I can't stay here all alone"
A ranta tace "ni ina nasan wani Lawal ma?
Kan table din ta duba bata ga wayan ba ta duba side drawers duk bata gani ba tace "nifa banga wayan ba"
Cikin muryan jin jiki yace "yana cikin aljihu na ki ciro"
Wani irin zare ido tayi tace "whattt! ni zan ciro daga aljihun ka??












*_Rukky Bae_*😏😏😏
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: [12/20, 4:38 PM] Rukky Bae😏😏😏❣❀❣: ❀⚜❣⚜❀⚜❣⚜❀⚜❣ *_MATAR DOCTOR_*⚜❣⚜❀⚜❣⚜❀⚜❣⚜❀⚜❣⚜❀⚜❣⚜❀⚜❣⚜❀⚜❣⚜








*_Rukky Bae_*😏😏😏








7⃣9⃣








Wani zare ido tayi tace "whattt! Ni zan ciro wayar daga aljihun ka??
Yace "yea ke zaki ciro"
Tace "no gaskiya bazan iya ba ka ciro da kanka ni kuma se na kira in fada mishi yazo ya dauke ka"
Yasan sarai bazata ciro ba shi kuma ya fara gajia da magana dan jin shi yake very weak
Jikin shi na karkarwa ya sa hannu a aljihun ya ciro hannun shi se rawa yake yi yana miqa mata wayar ta subuce a hannun shi da sauri Janan ta taro ta kafin ta karasa kai wa kasa..
Unlock button ta danna se taci karo da wayar an sa mata password
Kallon shi tayi cike da kosawa tace "what's d password"
Yace *"Momma*"
Tana sawa ya bude to her greatest surprise taga hoton ta a wallpaper na wayar.. Kasa motsi tayi sbd mamaki kwatakwata bata taba zaton zataga hoton ta a wayar shi ba ita bata ma san lokacin da ya dauke ta hoton ba da sauri ta shiga gallery dan ta goge hoton namma dai akwai password Momma ta fara sawa yaki buduwa ta rubuta Godwin nan ma yaki buduwa duk abun da ta zata a matsayin password ta sa hakura tayi sbd tayi trying passwords daban daban amma yaki yayi... Numb din Lawal tayi dialing tasa a hands free ringing daya ya dauka tare da fadin "hello liltle master"
Janan tace "ehmm... Ba shi bane nurse ce shi yace in kiraka kazo ka dauke shi cuz bazai iya driving ba"
Lawal yace "OK gani nan zuwa nan da 5mins"
Kwantawa yayi akan table ya riqe kan shi da hannu.. Har ta juya kamar zata wuce se taji yana fidda nishi da kyar da sauri ta karasa kusa da shi ta ce "meke damun ka?
Da kyar ya bude baki a hankali yace "kaina!kaina!!kaina ze tsage"
Gaba daya ta rasa me ya kamata tayi se can ta tuno da addua'ar da ake yi ma me ciwon kai a cikin ruwa
( _Suratul Fatiha kafa 7_))
(( _Ayatul kursiyyu kafa 7_))
((_Falaq, Nasi da Ikhlass kafa uku uku_))
_se ayi Bissimillah a shanye sannan a shafe fuska da ragowan.. Bi'iznillah za'a samu sauki daga ko wacce irin ciwon kai_......


Cup ta dauka dakko da ruwan gora ta zuba tayi mishi addua'an durkusawa tayi ta miqa mishi tace "take this"
kasa amsa yayi sbd jikin shi ba karamin rawa yake yi ba ganin bazai iya amsa ba yasa ta runtse ido tare da istigfari tace "open ur mouth"
Kamar karamin yaro ya bude baki tayi Bismillah sannan ta bashi seda ya kusa shanyewa sannan ta cire kofin daga bakin shi ta zuba a hannu hade da sake yin Bismillah ta runtse ido ta shafa mishi a fuska..


A hankali ya fara rufe ido tare da sauke nannauyan ajiyan zucia cikin dan kankanin lokaci bacci me nauyi ya dauke shi...
Waje ta samu ta zauna tana jiran Lawal ya zo ta wuce... Ta kai kusan 7mins sannan taji ana knocking kofa zuwa tayi ta bude wani ta gani suka gaisa sannan yace "nine Lawal nazo wajen little master ne" se a lokacin ta gane muryan shi tace "awww! come in yana bacci ne"
Tana gaba yana baya suka karaso cikin office din suna shiga Lawal yaga kanshi kan table yana bacci yana sauke nunfashi a hankali tare da ajiyar zucia...
Jakarta ta dauka tayi ma Lawal sallama sannan ta wuce.. Shi kuma ya tsaya jiran Dr.Godwin ya farka...


Bayan like 30mins ya farka yana bude ido yaji kanshi ya dena ciwo da sauri ya miqe sbd wani kuzari yake ji yana waigawa gefen shi yaga Lawal yace mishi "where is she?
Lawal yace "ta tafi"
Shiru yayi hade da dafe kanshi yace "Lawal let's go home I need to rest nd hv a shower".......
Lawal ya taimaka mishi suka fito suka rude kofan tare da wucewa...












*_Rukky Bae_*😏😏😏
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: [12/26, 7:13 PM] Rukky Bae😏😏😏❣❀❣: ❀⚜❣⚜❀⚜❣⚜❀⚜ *_MATAR DOCTOR_*❀⚜❣⚜❀⚜❣⚜❀⚜❣⚜❀⚜❣⚜❀⚜❣






*_Rukky Bae_*😏😏😏






8⃣0⃣








*_Washe gari_*




Cikin nishadi da kuzari Dr.Godwin ya tashi tun da yake be taba jin dadin jikin shi irin yau ba.. Farin suit ya yasaka da farin sleeve se red neck tie da farin cover shoes ba karamin kyau yayi ba... Suman kanshi me yawa ya taje sannan ya dau brief case din shi ya fito har ya kai tsakiyan parlor Agnes ta fito da sauri daga kitchen ta tsugunna har kasa tace "good morning oga!
Kai kawai ya daga ba tare daya amsa ba Ya cigaba da tafiya tace "ehmmm oga u nvr chop ur breakfast is ready I don put them on d table"
Be kalle ta ba ya cigaba da tafiya har ya kai bakin kofa ya waigo yace "yau bazan yi breakfast ba ku cinye keda me gadi" be jira abun da zata ce ba ya wuce...






_6:50am_
Yana zuwa asibiti ya fito sanye da bakin glasses cikin takun shi na kasaita ya dinga wuce mutane nurses nata gaishe shi amma be amsa ba sedai yau fuskan shi na dauke da murmushi ga wani annuri dake fita daga fuskan...Yana shiga office din shi yaga babu wacce tazo a cikin su... Yasha ko su Jessica sun zo hakan be dame shi ba se rashin ganin Janan da wuri da beyi ba... Har aka fara shigo da files babu wacce tazo se can yaji knocking yace "yes"
Su Jessica ya gani duk daukan shi Janan ce wani gutun tsaki ya saki suna gaida shi ko kallon su be yi ba suka ce "hw is ur health sir?
Yi yayi kamar be ji su ba
Jiki a sanyaye suka zauna... Sunyi zaton ze musu abun da yake ma Janan in tazo latti ne sbd su samu shiga a wajen shi se suka ga yayi banza dasu.... Tunda suka zauna suke kallon shi sbd kyan da yayi kamar ance ya dago aiko ya kamasu suna kallon shi wani irin banzan kallo ya watsa musu wanda yasa sukayi saurin sauke kansu kasa.....




_7:15am_ ta yi knocking yace "come in" Janan ce ta bude kofan ta shigo as usual kanta a kasa bata dago ta kalle shi ba tace "good morning"
Be kulata ba jin yayi shiru yasa ta dago daidai nan ya sakar mata wani murmushi wanda ya kara fito da ainihin kyaun shi da sauri ta kauda kai shi kuma ya amsa da "morning"
Ta gaisa dasu Ruth sannan ta zauna su ko se faman hararanta suke yi bata ma san sunayi ba


7:30am patients suka fara shigowa can wani mutumi ya shigo dauke da matar shi yana zufa yace "Dr. Matata na bleeding pls Doctor ka taimaka min"
Seda ya cire glasses din dake idon shi yace "kaje kayi clearing bills dinka sannan zamu karbeta"
Hular kanshi ya cire yan firfita yace Doctor labour ne yazo mata da garda Dan Allah ka taimaka kar baby da matata su mutu"
Dr.Godwin yace "bana amsan patient se anyi clearing bills ka gane?
Kamar mahaukaci haka mutumin ya fita ya ajiye ta akan wani kujera dake wajen ... Da gudu yaje wajen biyan kudin nan fa aka fada mishi nawa ze biya mutuwar tsaye yayi sbd bashida kudin kuma be san inda ze samu ba... Komawa office din Dr.Godwin yayi yace "Dr. Bani da kudin amma zan biya half in yaso kafin a gama zan nemo sauran..
Dr.Godwin yace "if u r not ready u can go outta my office as u can see I hv lots of patients waiting 4 me"
Mutumin yace "Doctor ka taimaka min pls help me kaji tausayin matata"
Kamar ya watsa ma Dr.Godwin garwashi haka yaji maganar cikin tsawa yace "kar ka kara cewa in taima ke ka cuz ni bana taimako a rayuwata sannan kuma tausayi!! Bani da tausayi kuma bashida muhalli a waje na domin ban san mene ne tausayi ba sbd haka pay or leave kuma asibitin nan bana taimako bane koma na taimako ne to ni bana taimako"
Janan dake zaune daga gefe ganin yanda matar ke nishi ga jini duk ya bata kayan mijin yasa ta fashe da wani irin kuka da sauri ta taso taje gaban Dr.Godwin tayi kneel down tace "Dr.plsss ka karbeta wallahi in be biya kudin ba ayi deducting a salary dina"
A razane mutumin ya juyo yace "aa kar ki fadi haka bana so in sa kowa a cikin matsala"
Tace "karka damu in shaa Allah babu matsala"
Dr.Godwin yana kallon su ga Janan na zubda hawaye ji yayi zuciyar shi na daci tana bugawa da sauri amma baya jin ze iya amsan wannan patient din sbd in ya tuno wasu dalilai nashi
Yana cikin tunani yaji Janan ta riqe kasan wandon shi tana kuka me tsuma rai...
Gaba daya kanshi yayi zafi be san lokacin daya daka mata tsawa yace "stay out of this or else.....
Cikin kuka tace ''or else what?










*_Rukky Bae_*😏😏😏
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: [12/28, 12:04 PM] Rukky Bae😏😏😏❣❀❣: β€πŸ”…β£πŸ”…β€πŸ”…β£πŸ”…β€πŸ”…β£πŸ”…β€πŸ”…β£πŸ”…β€πŸ”…β£ *_MATAR DOCTOR_*πŸ”…β£πŸ”…β€πŸ”…β£πŸ”…β€πŸ”…β£








*_Rukky Bae_*😏😏😏








8⃣1⃣






Cikin kuka tace "or else what??
Shiru yayi yana kallon ta gabadaya bai ji dadin tsawan dayayi mata ba kuma batayi deserving haka daga wajen shi ba cuz shima jiya ta taimake shi amma bazai iya mata godia ba kuma baya jin ze iya karban patient din sbd abun da ya faru dashi wanda bazai taba mantawa ba har abada amma kuma yana ji a cikin ranshi ze iya karban patient sbd Janan amma bazai bari ta gane sbd ita zeyi hakan ba....
Gyaran murya yayi sannan yace "kina so kisa kanki cikin matsala baki san su ba basu sanki ba zaki daukan ma kanki bashi anyways ko sun gudu ke baki isa ki gudu ba sbd haka dole za a rubuta agreement kin yarda?
Da sauri tace "eh na yarda"
Paper da Biro ya dakko suka rubuta agreement din harda phone number da signature..
Dr.Godwin ya kara da cewa "duk abun da yaje ya dawo don't blame anybody blame ur self.....


Se lokacin ya kalli matar gani yayi kamar bata nunfashi a hankali ya tako yazo gaban mijin ya durkusa tare da daga hannun matar yabass! hannun ya dawo abun duba bugun zucia ya dakko ya gwadata nan yaga zuciarta na bugawa alaman tana da sauran rai cikin sauri yace ma Janan "ki shirya ta kema ki shirya ku biyoni dakin theatre.. Kai kuma kaje ka bada half payment din kace _'Surgeon G'_ ne ya aiko ka" be jira komai ba ya wuce don shiryawa.... Mutumin ya kalli Janan yace "Allah yayi miki albarka kuma na miki alkawari bazan taba disappointing dinki ba"
Jiki a sanyaye ya mike yana share hawayen dake kan fuskar shi a haka ya bar office din...




_2hrs later_


Dr.Godwin ya fito daga dakin theatre yana cire hand gloves ita kuma Janan da wata nurse suka turo matar zuwa dakin hutu... Tunda aka fito da matar Janan ke trying number'n mijin amma switched off.. Hankalinta ba karamin tashi yayi ba sbd any moment from now matar zata iya farkawa kuma ana bukatar abubuwa dayawa kamar su pads kayan sawar matan da kuma na babies da dai wasu abubuwan da bazaa rasa ba..
Tana cikin tunanin abun yi ne taji ance "me yasa kike tunani? Number'n shi yaki shiga ko?
Lokacin da nake fada miki u should stay out of this matter kinki ji gashi tun yanzu kin fara shiga tension kuma kin san yanzu dole a samu wanda ze zauna da ita ko kece zaki bar aikin ki ki zauna da ita cuz naga tausayin ki yayi yawa"
Shiru Janan tayi dan bata san me zata ce ba kanta a kasa tace "nagode da taimakon daka mata"
Dr.Godwin yace "taimako? Ba taimako bane wannan naga dama ne kawai cuz I don't hv d heart to help, I don't help anyone in my life kuma I don't want anyone to help me sbd komai nake so I will do it my self ko banyi da kaina ba I can use my money cuz I hv money kin gane?
"u r mistaken cuz money cannot buy everything!
Wani irin murmushi yayi me kama da na yake yace "money is life!!
Zata sake magana ya katseta da fadin "shhhhh ya isa haka.. Ya wuce abun shi......


Jiki a sanyaye ta koma cikin dakin da aka bar matar dan hutawa ta kira dayar nurse din suka kai ta dakin da akayi admitting dinta.. Har ta juya zata koma dan dakko babies din taji matar tana fadin "ruwa!ruwa!! a bani ruwa! a bani ruwa! Karku kashe ni ku maida min baby marainiya!
Salati Janan ta dinga yi sbd batayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login