Showing 54001 words to 57000 words out of 82682 words

Chapter 19 - MATAR DOCTOR COMPLT BY ESHAAT.txt

ESHAAT   

18 Jan 2025

4333

tursasawa a addinin ku! ma'ana ana tilasatawa mutum shiga addinin kuma dole ne yayi alkawari akan bazai bar addinin ba?






Zama Janan ta gyara sannan ta fara da fadin "zan baka amsar tambayoyin ka daidai abun da na sani sbd shi ilimin addinin musulunci yanada zurfi..... Kamar yanda yazo a cikin littafin tauheedi _Mulunci shine miqa wuya ga Allah da kadaita shi which means yarda da Allah shi kadai ba tare da hada shi da komai ba_..


Yace ban gane ba ki kara min haske"


Zan maka misali da Christian yanda zaka fi fahimta kun yarda da Allah amma baku kaida ta shi ba u believe in trinity ( Father, Son and d Holy spirit) kun yarda kuma kuna fadin Annabi Isah 'Dan Allah ne (Wa'iyazubillah) mu kuma munce Annabi Isah Manzon Allah ne, kuma ita maihaifiyar Annabi Isah ayace ga mutane baki daya domin mutane su tabbatar da Allah can do d possible frm impossible nd d impossible frm d possible kuma ze iya tashin rayayye daga matacce sannan matacce daga rayayye...
Sannan dole ne Imani da Allah,
da Manzonin shi,
da Mala'ikun sa,
da littafan sa (Attaurah, Injila wato Bible, Zaburah da kuma Al'qur'ani mai girma)
Imani da ranar tashin alqiyama sannan Imani da Kaddara me kyau da mara kyau..
Sannan kalmar da yake tabbatar da mutum ya zama cikakken musulumi shine _Laiha illallah Muhammadurrasulullah (SAW)... (wato Shaidawa babu abun bautawa da gaskiya se Allah kuma Annabi Muhammad Manzon Allah ne)_..


Kamar yanda yazo a cikin Hadisin Annabi Muhammad (SAW) an gina Musulunci akan abubuwa guda 5


1. Shahadatain (shaidawa babu abun bautawa da gaskiya se Allah kuma Annabi Muhammad (SAW) Manzon Allah ne


2. Ikamatussalah (tsaida sallah maana kiyaye sallah akan lokacin ta)


3. Saumu Ramadan (azumin watan Ramadan)

4. Eeta'uzzakah (Bada zakkah)


5. Hajj (aikin Hajji ga wanda Allah ya bawa ikon zuwa)




Ajiyar zuciya Dr. Godwin yayi sannan yace kuma kun yarda da Bible kenan?


Tace eh mun yarda da Bible domin kafin zuwan Annabi Muhammad (SAW) lokacin Annabi Isah da Bible ake amfani amma bayan zuwan Annabi Muhammad (SAW) se aka umurce mu da anfani da Al'qur'ani me girma domin duk wani abu dake cikin dukkan littattafan da suka gabata a kwai shi a cikin Al'qur'ani me girma shiyasa duk wani Musulumi ya dena anfani da Bible sbd a halin yanzu babu old testament wanda yake na ainihi se new testament wanda a ko wani lokaci ake cikin caccanza abubuwan dake ciki waenda suka sabawa koyarwar Annabi Isah..


Shiru yayi ko me yake tunani oho! Ya sake cewa shin Christian ze iya auren Musulumi?


Tace eh akwai aure tsakanin Ahlul kitab da Musulmi amma ba a cika yin haka ba sbd yawan matsaloli da ake samu sannan hakan yana jan rabuwar kan yara sbd kowa ze so subi addinin sa, sannan Musulumi baya cin gadon Christian...

Ya Kuma cewa toh idan addinin ku daya amma ba yaren ku daya ba fa?


Za su yi auren su mana sbd babu tribalism a Islam domin Allah Madaukakin Sarki ya fada a cikin Al'qur'ani : _ya ku mutane lallai Allah ya hallice ku Maza da Mata, kuma ya hallice ku qabilu daban daban domin kuyi tarayya da juna, babu wanda yafi wani se wanda ya fiku tsoron Allah_

Mene ne tsoron Allah?


Shine gujewa duk wani abunda yayi hani dashi, kaji tsoron shi kamar kana ganin shi, idan kai baka ganin shi to shi yana ganin ka.. Sbd duk wanda ya aikata aikin kwarai ze sa shi a cikin Aljannah wanda kuma ya saba mishi ze shiga wuta"




Yace "na yarda Shi ya hallice mu with different structure akwai wani anfani da surorin mu za suyi wajen shiga Aljanna ko wuta?


Tace "tace aa babu wani anfani da za suyi domin bayan mun mutu duk tsutsotsi ne zasu cinye jikin kuma Hadisin Manzon Allah yana fadin " "! _"lallai Allah baya dubi zuwa ga jikkunan ku, ko zuwa ga surorin ku, se dai shi yana dubi zuwa ga zuciyoyin ku da kuma ayyukan ku_

Kallon ta kawai yake yi yana kara jin wani irin sonta na shigar shi...




Yace sannan se tambayar da na miki akan cewa akwai tilastawa a cikin addin ku?


Janan tace babu tilastawa a cikin addinin Musulunci domin fadar Allah (SWT) a cikin Al'qur'ani me girma cikin Suratul Baqarah Aya ta 256: _Babu tilastawa a cikin addini, hakika shiriya ta bayyana daga bata, duk wanda ya kafurcewa gumaka kuma yayi Imani da Allah toh lallai yayi riqo da igiya me karfi wacce bata tsinkewa, kuma Allah Mai ji ne, Masani_:


Hawaye ne ya fara kwaranyowa daga idon Dr. Godwin....


Cike da tsoro Janan take kallon shi dan tunda take bata taba ganin hawayen shi ba se yau wani irin tausayin shi taji a ranta tana mishi kwadayin musulunta sbd ya samu rabo gobe Qiyamah...
Maganar shi ta dawo da ita daga tunanin da take yi inda yake ce mata shin wani abu ne mafi girman sabo a wajen Allah?


Kamar yanda yazo a cikin littafin Kaba'eer (wato manya manyan zunubai) akwai abubuwa masu yawa waenda suke a matsayin manyan zunubai a wajen Ubangiji but zan fada maka kadan daga cikin su..
Akwai shirka! Wato hada Allah da wani a wajen bauta kamar mutum, dabba, rana, wata, taurari, wuta da duk wani abu da mutum yayi Imani da shi wanda ba Allah ba!
Sannan saba ma iyaye
Sannan Zina, Luwadi, Madigo duk suna cikin manyan zunubai... Duk wannan abubuwan dana lissafo babu wanda ba a aikatawa a bayan kasa kuma duk da haka idan muka roki Allah gafara yana yafe mana domin shi Mai Gafara ne kuma Mai Tausayi....
Hmm lallai Ilimin addinin Musulunci akwai shi da zurfi se dai ni a ganina Islam is so complicated komai kayi se ace ba daidai ba kuma akwai hukunci akai...


Tace No no no u r mistaken! Islam is nt complicated and it will nvr be cuz it is d total way of life sbd babu abunda Musulunci be koyar da mu ba, ya koyar damu yanda za muci abinci, kamar yanda yazo a hadisin Annabi Muhammad (SAW) inda yake cema wani Yaro lokacin da zai ci abinci : _ya kai Yaro! Ka anbaci sunan Allah, kuma Kaci da daman ka, kuma Kaci abunda ke gaban ka_...
Musulunci ya koya mana zamantakewa da mutane, kula da iyalin mu, da abubuwa masu yawa wanda idan nace zan fada maka ba zan taba iya gamawa ba, kuma shi hukuncin da ake yankewa mutum se yayi laifi idan beyi laifi ba babu yanda za a zalince shi domin Allah Madaukakin Sarki yana fadin _Lallai na haramtawa kaina zalunci kuma na sanya shi haramun ne a tsakanin ku, kada kuyi zalunci_


Hmmmm! Yau na gane abubuwa masu yawa thanks a lot, ki tashi in maida ki gida... Ya dau glasses din shi ya maida ido sbd baya so taga yanda suka kada suka yi ja cake din kawai ya dakko suka fito, mota suka shiga yazo fita ya cewa masu gadi suje su kwashe sauran drinks da abincin!! Godia suka fara mishi be bi ta kansu ba yaja motar shi suka tafi.... Babu me cewa kowa komai sbd kowa da kalan tunanin shi wannan karan a hankali yake tukin ko waka ma be kunna ba...


Daidai kofar gidan su Janan ya tsaya ya bude kofa ya fito itama ta fito tana fadin "Nagode sosai Doc. Seda safe" ta juya ta fara tafiya... Da sauri ya kirata ta juyo yace ki zo mana"
Ba musu ta dawo booth ya bude ya dakko wasu ledoji guda 2 se wani karami akwati wanda be fi girman hannu ba ya bata yana fadin ga birthday gift din ki kuma bana so ki furta ko kalma dayace" shiru tayi..


ya ce bari in taya ki shiga da kayan ke kuma ki dakko cake din"
Babu yanda ta iya haka ta bude motan ta dakko cake din da kyar sbd nauyi duk tsoro ya cika ta sbd bata san me zata ce a gida ba.... Ji tayi yace take care of ur self inna kai gida I will call u" ya daga mata hannu yayi shigewar shi mota ya wuce...


Tafi minti 15 tana tarabbabin shiga gida can dai tayi adduaa ta shige.... A parlor ta tarar dasu duka tana sallama suka amsa nan parlor ya kaure da wakan happy birthday! Dadi ne ya kamata ta shiga ta ajiye cake din akan table tace Ina zuwa ta koma ta kwaso ledojin.. Mamaki suke wa ya bata kayan, nan dai ta basu lbr amma ta kasa fada musu sun je Hotel 17 sbd abun ma ba zai yi dadi ji ba... Ba su kawo komai a ransu ba suka cigaba da nasu celebration din...
Daki ta shiga ta bude karamar akwatin nan dan duk ta kosa taga miye a ciki sbd se daukan ido yake, wani zobe ta gani karami na gold me kyan gaske, ido ta zaro tana mamaki, ta bude drawer ta ajiye.....


Seda tayi wanka sannan ta tuno da wayar ta dake cikin jaka ta dakko nan taga missed calls kusan 28 duk Imran ne kafin ta kira ya ya kara kira tana mishi sallama tace "ayi min hakuri kaina bisa wuya" Duk wani bacin ranshi yaji ya kau sukayi hira sosai yayi mata adduaa na shiga wani shekaran tare da fatan samun lfya da tsawon kwana a gare ta.....




Tunda Dr. Godwin ya sauke Janan a gida yake ta wasu irin tunane tunane ya rasa me ke mishi dadi a haka har ya kai gida... Dakin baccin shi ya wuce ya haye gado sbd yana bukatar bacci, be dade da kwantawa ba bacci ya kwashe shi cikin baccin ya fara wasu mafarkai wanda suka haddasa mishi tashi a firgice.....










RukkyBae 😏😏😏
[11/7/2017, 11:04 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: [10/9, 8:22 PM] RukkyBae😏😏😏❤❣: ❤♣♥❤♣♥❤♣♥♣❤♣♥❤♣❤♣♥♥❤♥❤♥❤♥❤♣❤♣❤♣❤♣♥♣ *MATAR DOCTOR* ♣♥❤♣♥❤♣♣♥❤♣❤♥♣❤♥♣♣♥❤♣♥♣♣










_Rukkybae_😏😏😏












_Alhamdulillah 😘😍Baba yaji sauki sosai.. Ngd da adduo'in ku Allah ya bar zumunci.... Allah ya biya mana bukatun mu na alkhairi baki daya_








1⃣0⃣2⃣












Ji yayi kanshi na juyawa sosai a take ya fara tuno mafarkin yana so ya gane me mafarkin yake nufi....


Cikin mafarkin yaga Janan sanye da fararen kaya shi kuma gashi can da Momma, Dad, Annabelle a kulle da wasu igiyoyi ko motsin arziki basa yi a hankali take takowa har tazo gaban su ta durkusa a kasa tare da fadin "kuce ashhadu an La ilaha illallah"


Godwin da Annabelle na kokarin fadan haka Dad yace aa! karku fada! kar ku fada! kar ku karya alkawari karku karya!


Janan ta tashi tare da miko hannuwan ta biyu Annabelle da Godwin suka mika mata amma sun kasa riqe mata hannun.. Duk Iya kokarin su sun kasa se gani sukayi tana ja da baya su kuma suka fada wani rami me zurfi da tsananin duhu... . Mafarkin daya farkar dashi kenan a firgice... Jikin shi duk yayi weak gashi yana jin kan shi na wani irin yi mishi ciwo... Bayi ya wuce yayi wanka ya sauya kaya zuwa riga baka da wando 3quarter... Wayar shi ya jawo ya fara kallon hotunan da yayi ma Janan dazu a take yaji wani irin natsuwa na saukar mishi duk wani tsoron da yake ji ya fita daga ranshi.... Be kirata ba sbd be san me ze ce mata ba duk da yana missing dinta sosai, da kyar ya iya cin abinci ya zauna yana dube dube a laptop din shi...








_Bayan Sati 2_






Biki se matsowa yake yi duk wani abu daya dace su Ummiey da Abbiey sun yi jira kawai suke yi lokaci yayi...




Kamar koda yaushe yau ma Imran din ne ya kaita asibiti seda ta zo sauka sannan ya mika mata wasu envelope guda biyu yace daya naki da frnds din ki dayan kuma na Ummiey, anjima in shaa Allah zan kaima Abbiey nashi da kaina,
Murmushi tayi tare da fadin na gode sosai Nurul_Qalb Allah ya kare mun kai..
Ya ce Ameen Angel se munyi waya... Suka daga ma juna hannu ya wuce ita kuma ta shiga cikin asibitin....




Tana shiga bata ga Dr. Godwin ba cike da mamaki take tambayar kanta toh Ina ya shiga!


Bata fi minti 5 da zama ba se gashi ya shigo sanye da Navy Blue riga da Navy Blue jeans se bakin cover shoes, yayi kyau sosai
Kallon ta yake yi gani yayi ta kara kyau...
Be mata magana ba ya zauna sbd yau duk ji yake wani abu ya tokare mishi maqogoro ya rasa mene ne haka..


Kiran shi aka yi a waya da sauri ya fita..




Wajen su Eesher taje ta basu kati suna ta mata tsiya ita dai bata kula su ba nan suka yanke weekend za su raka ta rabon kati, tayi musu godia ta koma office din kafin ya dawo....


Lokacin data shigo ta tarar har ya dawo cikin office din se faman hada abubuwan bukatan shi yake yi yana juyowa ya ganta, key din shi ya dauka yace "ni nayi tafiya se bayan 3weeks zan dawo so ga office nan ki kula da shi watakila za a kaiki office din Dr. Magaji ki dinga taya shi aiki kafin in dawo"
Yana gama fadin haka ya fita da sauri sbd wayar shi se ringing take yi..
Yana fita tace "Alhamdulillah gwara ka tafi zan samu ayi biki na cikin kwanciyar hankali, in dai aka maida ni office din Dr. Magaji na huta kuma na san ze dunga daga min kafa ba kamar wannan Dr. Godwin din ba...






Duk wata old frnd din su sun kai mata kati ba suyi anko ba ance kowa tasa kayan da take so... M.Sabo tace "haka za ayi biki ba wani motsi!


Zee tace ke ma ai kin san halin mutuniyar taki bata da son bidi'a..


Eesher da take gefe tace "ai an hadu ne da an dace shima Dr. Imran din baya so"
Duk suka kwashe da daria se yamma likis sannan suka koma gida...










Yau Daddy ya dawo kowa a cikin su yana farin ciki, an hada mishi abinci masu kayatarwa na gargajiya sbd shi dai be bar al'adar shi ba, seda yayi wanka ya huta can da dare bayan sun gama cin abinci Imran ya kwaso katunan biki ya ba Daddy, cike firgici yace har ka bugo kati? Ka kai musu ne?


Imran ya fara sosai keya yace eh na kai musu Daddy....


Sallati Daddy ya fara yana fadin kayi gaggawa Imrana, na so ace ka bari na dawo se a yi a tsanake, akwai abunda nake so mu tattauna da Baban ta, gobe in Allah ya kaimu da yamma in ka dawo daga office ka kaini gidan nasu sbd maganar nada muhimmanci..
Imran dai be gane inda Daddy ya daso ba babu yanda ya iya yace in shaa Allah goben se muje..


Daddy yace tashi kaje Allah ya kaimu


Yana shiga daki ya kira Janan ya fada mata gobe Daddy ze zo wajen Abbiey,


tace Allah ya kaimu da safe in Allah ya yarda zan sanar da Ummiey..
Yau dai hirar su ba wani walwala a cikin ta gaba daya Imran ya rasa me ke mishi dadi, da Janan din ta tambaye shi sai yace "Angel ban san abunda ke damu na ba kawai ji nayi gaba na yanata faduwa ban san dalili ba"


Ayya Nurul_Qalb ka yawaita fadin "innalillahi wainnailaihirrajiun.. ni ma kwata kwata bana jin dadin jiki na ji nake yi kamar zazzabi na son kamani..
Haka dai suka gama wayan suka kwanta..






Washe Gari da safe ta fada ma Ummiey ita kuma ta fadawa Abbiey, can da yamma se gasu sun zo kamar yanda sukayi alkawari, an sauke su a parlorn baki aka kayata gaban su da kayan ciyeciye da shayeshaye kala kala.. Sun dan ci sannan aka sake gaishe gaishe Imran ya tashi ya koma mota sbd ya basu dama suyi maganan su...
Daddy yayi ma Abbiey bayanin komai,
Abbiey yayi shiru yana sauraren shi bayan Daddy ya gama se Abbiey yace "gaskiya nayi farin ciki da wannan hangen nesan da kuka yi kuma haka shi yafi dacewa da ma'aurata kafin auren su sbd gudun abunda ze je ya dawo, kuma duk wani abun da zai faru toh lallai dukkan mu zai shafa ba su kadai ba, in Allah ya kaimu cikin satin nan se suje ayi gwajin Allah yasa mu ji alkhairi...

Daddy ya amsa da Ameen cike da jin dadi kuma ya yaba da dattakun Abbiey... sallama suka yi sannan suka tafi..


Da dare suna daki shida Ummiey ya bata lbrn komai, itama ta goyi bayan haka kuma taji dadin hukuncin da suka yanke.....












RukkyBae 😏😏😏
[11/8/2017, 10:15 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: [11/8, 7:28 PM] RukkyBae😏😏😏❤❣: ❤♠♥♣♥♣♥♠♣♥♣♠♣♥♣♠♥♣♠♥♣♠♥♣ *MATAR DOCTOR* ❤♠♣♥❤♥♣❤♥♣❤♥










🌐HAJOW🌐
*Hakuri Da Juriya Online Writers*✍🏻✍🏻








RukkyBae 😏😏😏








_Alhamdulillah! Na gama exams dina lfya se fatan samun result me kyau Ina matukar godia da adduo'in ku a gare ni Allah ya saka muku da alkhairi ngd, ngd kwarai dagaske_








_Wannan page din naki ne ke kadai Khadeeja Adam (Mrs Haydar) I love u so much Babe_😘










1⃣0⃣3⃣












Kamar yanda manya su ka yanke hukunci haka aka yi Imran yazo ya dauki Janan suka tafi asibiti suna tafe suna hira amma dukkan su cikin zullumi suke dan basu san me ze je ya dawo ba. A wajen ajiye motoci yayi parking sannan suka fito suna jerawa abun gwanin ban sha'awa.
Office din Family Dr din su suka nufa Imran yayi knocking aka basu izinin shigowa. Cikin girmamawa suka gaida shi shima a mutunce ya amsa musu..


Wayan dake kan table din shi ya daga ya kira Nurse nan da nan se gata dama an san da zuwan su Janan din cikin dan lokaci kadan aka gama diban jinin nasu. Bayan fitan Nurse din ne Dr yace "zaku iya tafiya in result din ya fito zan kira Daddy in fada mishi"
Jiki a salube suka ce toh tare da yin godia suka fita..


Har kofar gida ya ajiye ta sannan ya juya ya tafi. Ji take kamar kafafunta ba zasu iya motsawa ba sbd yanda take jin nauyin su da kyar dai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login