Showing 63001 words to 66000 words out of 82682 words

Chapter 22 - MATAR DOCTOR COMPLT BY ESHAAT.txt

ESHAAT   

18 Jan 2025

4337

rawa yake yi...


Awananni goma sha biyar suka dauka suna abu daya cikin ikon Allah suka gama duk jikin ta nade da bandeji tana kwance kamar ba ta da rai...


Suna fitowa suka tarar da Iyayen ta da sauri suka karaso suna fadin "Dr. Ya akayi? Ya jikin nata? An dace?


Ku biyo ni office" abunda yace dasu kenan..


Jiki na rawa suka bi bayan shi, waje ya nuna musu suka zauna sannan ya fara musu bayani "mun gama mata aikin kuma muna fatan samun out come me kyau,


Dr. Zamu iya zuwa mu ganta?


Aa ba zaku iya ba sbd yanayin jiki ta se nan da sati daya zaku iya ganin ta.


Godia suka mishi sannan suka tafi..












_Rukkybae_😏😏😏
[11/24/2017, 9:20 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: ♥♣♥❤♣♥♣♥♣♥♣❤♥♣❤♥♣❤♥♣❤♥♣❤♥♣❤♥♣♥ *MATAR DOCTOR* ♥♣❤♥♣❤♥♣❤♣♥❤♣♥♣❤♣♥♣❤♣♥❤♣








_Rukkybae_😏😏😏






🌐 _*HAJOW*_ 🌐
*Hakuri Da Juriya Online Writers*✍🏻✍🏻✍🏻






_Duk wanda baya tausayin mutane Allah ba zai ji tausayin shi ba_






1⃣0⃣9⃣

















Abbiey ya shigo gida da sallama, a parlor ya sami Ummiey da Janan zaune yace "me ake tattauna babu ni"


Ummiey tace "Sirri ne tsakanin 'Ya da Uwa"


"Nima ai 'Ya tace kuma Mama ta kin ga ko na fiki matsayi"


Duk suka sa daria


Ummiey tace "dama magana muke yi akan ko za ta samu wani aiki ne ko kuma zata koma makaranta shine ka shigo ka ji mu muna magana"


Aiko faduwa tazo dai dai da zama dama jiya na ji an fara saida form yanzu dai bari in duba naga ina da yafi dacewa ta tafi tunda Direct Entery ne"


Ummiey tace Allah yasa a dace Allah ya zaba mafi alkhairi..


Abbiey na ngd sosai Allah ya sa a dace Allah kuma yasa albarka" inji Janan..


Ya amsa da Ameen




*****


Bayan kwana 3 se gashi da forms guda 2, daya na Base University Abuja dayan kuma na UNILAG wato University of Lagos! Ummiey tace "Nursing zaki dai saka koh?


Tace "a'a ni yanzu so nake na zama kwararriyar Likitan Mata wato Gynae Doctor sbd mata sunyi karanci a wannan fannin daga maza se waenda ba Muslmai ba, se kiga mace ta je ganin Likita kuma namiji tana fada mishi sirrin ta wanda ko gaban mace yar uwarta se ta jin kunyan fadar haka, sannan idan ma ya kai da yaga tsiraicin ta haka nan zata bude mishi ya gani in dai tana so ta samu maganin ciwon ta ni kuma wannan dalilin yasa nake jin kishin matan mu kuma shi ya sa zan karanta wannan fannin sbd muma mu samu cigaba kuma in kare mutuncin mata yan uwana"


Dadi sosai Ummiey taji tace "gaskiya wannan shawarar taki abun dubawa ce kuma da za a samu mata kaman ki dayawa za a samu ci gaba me anfani Allah yayi miki albarka ya baki ilimi me yawa"


Abbiey yace ina alfahiri dake Allah yayi miki albarka!


Ameen ya Rabbi Jazakumullahu khairan!


Ameen wa iyyaki!



*****


Yau sati daya kenan da yi ma Hanan yar gidan Mataimakin Gwamnan Jihar Kaduna aiki, bakin kofan dakin cike yake da jama'a yan zuwa dubiya, Dr. Godwin ne ya karaso bayan sun gaisa yace "zaku shiga one after d other kuma pls banda hayaniya"


Maman ta da Baban ta ne suka fara shiga, a kwance suka ganta nade da bandeji babu inda ake gani hatta idanun ta an sa mata wani karafuna, a jiki ga kuma wasu na'urori jone a jikin ta.. Kallon ta suke yi duk jikin su a sanyaye dan sun fara cire rai da ita gata ita kadai ce kwal a wajen su


Hankali tashe suka fito, wajen Dr. Godwin suka nufa Maman se kuka take yi shima dai Baban karfin hali yake yi amma hankalin shi ya kai kololuwa wajen tashi, suna karasawa yace "Dr. Zata samu sauki kuwa? Kana ganin zata tashi? Dr. Kar ka bari ta mutu ita kadai kawai muke da Dr. Ka taimake mu!


Cike da tausayi yake kallon su yana mamaki wai shine yau Mataimakin Gwamna ke ronkon shi? Yau ina mulkin? Ina karfin ikon? Ina wani girma da jijji da kan yake? Hmmm lallai mu mutane ba a bakin komai muke ba, kuma mu bamu isa muyi ma kan mu komai ba dole ne se wani ya taimake mu ta wata hanya!


Dr kayi shiru baka ce komai ba kai muke sauraro, ni nayi maka alkwarin kudi masu yawan gaske da duk wani abu da kake so zan baka!


Dr. Godwin yace "kuyi hakuri kuje ku cigaba da addua'a ni ban isa in bata lfya ba, Allah ne ze bata lfya ni dai nayi iya kokari na ban isa in sa ta rayu ba ko Da zaka bani duk duniya da abunda ke cikin ta dan ranta baya hannu na se dai in zama sila wajen cigaba da rayuwar ta sannan ban san gaibu balle in san koh zata warke ko bazataba zata warke ba!


Jikin su yayi sanyi da maganganun da ya fada musu, godia suka yi sannan suka wuce!






An saki list kuma a duka Universities din sunan Janan ya fito Base Uni sun bata Biochem, UNILAG ne suka bata Gynaecology!
Nan fa ta dinga murna tayi ma Allah godia se dai ita bata so tayi nisa da gida kuma taji Ummiey da Abbiey suna tunanin barin ta tafiya can Lagos din! Ita dai ta bar ma Allah zabi! Sannan tana jiran su yanke hukunci a matsayin su na iyayen ta...


Cikin kwana 2 suka yanke hukunci kawai su barta ta tafi dan sun yarda da tarbiyan da suka bata amma za su cigaba da taya ta da addua'ar Allah ya tsare ta a duk in da take dan yanzu duk tarbiyyan Yaro seka hada da addua'a.


Da Ummiey ta fada mata abunda suka yanke a take a wajen ta fadi tayi sujjadar godia sannan ta rungume Ummiey tana farin ciki.. Itama Ummiey tayi farin ciki da ganin yarta na cikin farin ciki dan tun bayan rabuwar su da Imran ta rage walwala da farin ciki...






Kwanakin da Dr. Godwin ya diba dan bude fuskarta yau ya cika mutane sun cika ta ko ina a asibitin, yan jirida, yan gidan T.V da Radio duk suna wajen dan daukan rahoto, Dr. Godwin kawai ake jira ya karaso..


Cikin Izza da Jarumta ya shigo asibitin sanye da Bakar suit da mint blue shirt ya rufe idon shi da bakin glasses, yana zuwa yan jirada suka yo caaa a kanshi suna mishi tambayoyi!


Ku bari muga yanayin aikin kafin ku fara min tambayoyi! Abunda kawai yace dasu kenan ya wuce.. !












_Rukkybae_😏😏😏
[11/28/2017, 7:55 PM] RukkyBae😏😏😏❣❣: [11/27, 7:44 PM] RukkyBae😏😏😏❤❣: ❤🖤❤🖤♥❤♥❤🖤❤🖤❤🖤❤🖤❤🖤❤🖤❤♣♠♥♣♠♣♥♣♠♣ *MATAR DOCTOR* ♠♣♥♣♠♣♣♣♥♣♠♥♣♠♣♥♣♠♣♥♣♣♥♣♠♥♣♥♣♥










_Rukkybae_😏😏😏








🌐 _*HAJOW*_ 🌐
*_Hakuri Da Juriya Online Writers_* ✍🏻✍🏻✍🏻










_Wannan Shafin na sadaukar da shi ga dukkan cousins dina! Ina son ku fiye da yanda kuke zato_!! 🤝🤝👄💋😘❤










1⃣1⃣0⃣










Zuciyar shi na dokawa da karfi ya bude dakin! Kamar kullum tana kwance, gaban gadon ya karasa ya tsaya yana kallon ta kamar yana tunanin wani abu, bude kofan da akayi ne ya sa shi waigawa, Dr. Magaji, Dr. John da wasu Likitoci mata guda 2 suka shigo, suma gefen gadon suka je suka tsaya, bayan sun dan gaisa ya mika musu hand gloves, cikin kwarewa suka fara warware mata bandejin da almakashi suna yi suna yankewa sbd rage mishi tsawi! Jikin ta yayi fari tas sbd dadewan da tayi da bandeji da kuma maganin da aka shafa mata a jiki! Wani lotion da riga armless dai dai gwiwa Dr. Godwin ya dakko ya miqa ma Likita mace yace "ki shafa mata a ko ina in kin gama ki sa mata wannan rigan kafin a bude fuskan"


Abun da ya umurce ta tayi har ta gama ta sa mata rigar!


Baya duk suka koma suka bar Dr. Godwin ya bude mata fuskar da kanshi sbd aikin shi ne su dai yan kallo ne se kuma in ya ba su umurni su yi wani abun!


Sabbin hand gloves ya sanya sannan ya fara warware mata fuskan su kan su da suke tsaye sun kosa ya gama suga fuskarta, ya kai kusan mintuna 30 yana yi yana shafa mata wani abu a haka har ya kusa gamawa!


Cak ya tsaya dan ji yake kamar karya bude, zuciyar shi tana mishi waswasi, ji yayi an dafa shi yana juyowa yaga Dr. Magaji yana daga mishi kai alamar ya bude!


Motsi ya fara yi da bakin shi wanda shi kadai ya san me yake fada sannan ya ji wani karfin gwiwa ya zo mishi! Janan ta fado mishi rai ya tuno duk lokacin da suke aiki ko me za tayi se ta ambaci sunan Allah, murmushi yayi yana me tsintar kanshi da fadin "BISMILLAH! Sannan ya bude fuskan!


Ya Salaammmmmmmm! What a transformation! unbelievable! Dr. Magaji ne ke wannan maganan ya rungume Dr. Godwin cike da farin ciki!


Dr. John ya sake baki yana kallon wannan abun mamaki


Su kuma Likitoci matan nan suka ce "congratulations Sir!


Wani irin farin ciki ne mara misaltuwa ya lullube Dr. Godwin dan gaba daya be yi zaton aikin nan ze yi kyau ba! Ohhhh My God!! Thank u Lord! Ngd maka da wannan ikon naka!


Duk kallon ta suke yi cike da mamakin ganin fuskarta tas! Babu ciwo balle tabo! Tayi fari dan gaba daya fuskarta ta canza domin wancan fatan nata daya lalace ya daye gaba daya wani sabo ya fito!


Waje ya fita fuskar shi dauke da murmushi! Iyayen ta na ganin shi suka dinga kutsawa cikin tarin jama'a suka karaso gaban shi! Suna fadin "Dr. an dace? Ta tashi?


Be iya ce musu komai ba se juyawa yayi alaman su biyo shi, har rige rige suke yi wajen shiga dakin! Dai dai bakin gadon ya tsaya suma da sauri suka karaso suka tsaya! Kallon ta suke yi suna karawa, amma sun rasa bakin magana! Da kyar Baban ya bude baki yana fadin ''Dr. Yarinya ta ce wannan? Ka tabbata ita ce? Ya kalli matar shi "kin ga abun da na gani? Sweetheart din mu ce ko idona ne ke min gizo?


Nima dai ban tantance ba gani nake kamar mafarki! Ta bashi amsa


Yanda suke yi yasa Dr. Godwin murmushi yace "ita ce ba wata ba! Mu gode ma Allah daya dawo mata da abun da ta rasa, sannan kuma ya barta da ranta!


Dr. Yaushe zata bude ido toh? Suka tambaye shi


Nan da awa daya sbd alluran da aka mata!


Murnar da suke yi fadan shi ma bata lokaci ne..


Hayaniyar mutane yasa shi da kan shi Baban ta ya fita yace "ku dan rage murya! Nan da awa daya za a fito da ita ku ganta ku ga yanda ta koma! Be jira amsan su ba ya koma ciki!




🖤


Awa daya dai dai ta fara bude ido a hankali, dishi dishi take ganin komai, har ta fara dan gani ba sosai ba "innalilllahi wainnailaihirrajiun" abunda ya fara fitowa daga bakin ta kenan! Da azama suka karaso inda take! Hanan! Hanan! Kina ganin mu? Ina ne yake miki ciwo Darling? Maman ta ke wannan maganan!


Hannu ta daga a hankali ta mika ma Maman tace "Mum! Ta juya kalli Baban ta tayi mishi murmushi tace "Dad! Hawaye suka zubo mata!


Dr. Godwin ya karaso da sauri yana kallon ta "akwai inda yake miki ciwo ne?


Ta girgiza kai


Kina gani na?


Ta share hawayen ta tace "eh ina ganin ka amma ba sosai ba Ido na is not clear!


OK bari muga zuwa anjima maybe idanun su dawo normal!


A tare Maman ta da Baban ta suka rungume ta! Hannun ta ta daura a bayan su se hawaye ke fita daga idon ta dana Maman ta! Se sun dago sun kalle ta se su kara rungume ta!


Mum!


Dagowa tayi tace ''naam Darling!


Hannu tasa tana goge ma Maman hawayen ta tace "ki dena kuka, godiya zamu mika ma Allah daya bani lafiya!


Gaskiyar ki ne, Allah mun gode maka da wannan ni'imar..


Tace "Ya Allah na gode maka! Mum, Dad kuma nagode muku kuma ina alfahari daku a koda yaushe!


Muma muna alfahari dake! Suka manna mata peck a kumatu!


Gefen Dr. Godwin ta kalla tace "thank u very much DOC thanks 4 everything, May Allah bless u!


Ya amsa da Ameen
Tare da fadin ''ya kamata a kaita dakin hutawa sbd tana bukatar hakan!


Ba dan sun so ba suka tashi! Wata riga kamar ta shan iska me dogon hannu da hula ya miqa ma Mama ta yace "ki sa mata don za a fitar da ita kuma naga mutane dayawa a waje sannan ba a so iska ya dinga taba ta da yawa sbd skin din ta beyi kwari sosai ba,


A hankali take sa mata rigar dan gani take in tayi da karfi zata gwalje mata fatan!




A tare suka fito dukkan su ana turo ta akan gado!


Suna fitowa yan jarida suka fara turereniya wajen daukan rahoto! Kowa da abunda yake fada a haka da kyar suka ratsa su suka wuce! Special daki aka kai ta... Nan ma yan jirada seda suka biyo su! Masinja Dr. Godwin ya kira wanda Mataimakin Gwamna ne ya bukaci haka! Yana shigowa ya zube a kasa yace "gani Sir"


Dr. Godwin yace "bani nake neman ka ba"


"ni nake neman ka! Kaje ka ce ma yan jiradan nan su tafi se ranan Juma'a su zo gida na zan hada gagarumar walima tare da kyauta na musanman da zan ba Dr. Godwin, za su iya zuwa su dauki duk rahoton da suke so zan bar su dauki duk abunda suke so!
An gama ya mai girma! Ya fita da dan gudun shi!


Sakon ya fada musu, ba haka suka so ba amma duk da haka sun ji dadi dan ko ba komai ranan Juma'a za su samu daman daukan rahoto! Daya bayan daya suka fara watsewa!


Ta ko ina labarin ake watsa tare da gayyatan mutane zuwa wannan taro! Duk jaridan daka siya labarin ne a farkon shafi tare da hoton Dr. Godwin, se kuma hoton ta lokacin da baayi mata surgery din ba da hoton da aka mata! Haka gidan radio kullum se an sanar! Duk channel din TV daka sa shine a headline din su!




*Ranar Juma'a*


Tun da safe aka fara ta ruwa dan mutane ta ko ina se zuwa suke dan su ganewa idon su, duk wanda yazo mai kudi, dan kasuwa, talaka da duk wani mutum an barshi ya shiga gidan dan Mataimakin Gwamna yace a bar kowa ya shigo kar a hana kowa shigowa!


Karfe 1 dai dai Hanan da Maman ta suka fito cikin shiga ta alfarma! An ma Hanan kwalliya me kyau da kayatarwa, ta yi kyau sosai tamkar ba ita bace mara lfya wacce tasha jinya, fuskar nan kamar ba wacce ta baci ba kyan gani kwanakin baya! Wajen zaman da aka ware musu suka zauna!


Baban ma ya zo


Dr. Godwin kawai ake jira ya karaso! Se kusan 1:30 ya zo wajen cikin shigar data amshe shi, idan ka ganshi zaka dauka tamkar ba dan Nigeria ba yayi kyau sosai! Wajen zama aka bashi kusa da Mai Girma Gwamna! Seda ya zauna sannan aka fara gabatar da abunda aka zo yi!


Live gidan T.V suke nuna komai a lokacin su Janan dukkan su suna parlor Abbiey ya sa BBC.. Nan suka ga headline din! Zama suka gyara, Dr. Godwin aka nuno zaune yayi crossing kafar shi, cikin zare ido Janan take kara kallon shi dan ko daga bacci ta tashi ba zata manta fuskar shi ba!


Ya Khaleel yace "kamar wannan Dr. Din na asibitin da Little Princess tayi aiki koh"


Ya Saleem yace "ai kuwa shine!


Abbiey yace "Ikon Allah gaskiya ya burge ni gashi very young, kuma shine na farko daya fara wannan surgery din a duk fadin Nigeria!


Hoton Hanan aka nuna a alon talbijin din an hada wanda fuskan ta ya lalace da kuma wanda aka gyara!


Ummiey tace "lallai Allah ya bashi fiqrah da basira, ga kuma sa'a se dai yana da nakasu ta wajen addini, dama ya musulunta da mutane sun ji dadi!


Abbiey yace "Wallahi kuwa ni yana min yanayi da musulmai kuma ina mishi kallon sani!


Duk abunda suke fada ita dai Janan kallon su take yi ta kasa cewa komai!




Mai girma Gwamna ne ya tashi bayan ya yi jawabi tare da janjinar ban girma ga Dr. Godwin se yace "a matsayi na na Gwamnan garin nan na baka kyautar motoci guda 10 tare da kudi miliyan 20! Nan fa waje ya kaure da ihu!


Mataimakin Gwamna shima ya tashi yace "a matsayi na na maihaifin yarinya na baka kyautan filaye guda 5 da gidaje 4 sannan a madadi na da iyalai na baki daya na baka miliyan 30! Sannan kofa a bude take ka fadi duk abunda kake so zaa baka shi yanzu!


Dr. Godwin ya tashi ya fara magana cikin turanci me daukar hankali yana fadin "ina godia da duk kyautar da kuka bani duk da ban cancanci wannan kyauta me yawa ba amma ina farin ciki da matukar nuna godia a gare ku, ina son abu 2, daya ba zaku iya bani ba se dai in fadi dayan!


Ka fadi duk abunda kake so zaka same shi!


Ina so daga yau in ajiye aiki a bisa yarjejeniyar da muka yi da yan Ministry Of Health da fatan zan samu haka!


Kowa dake gurin be ji dadi ba dan in har ya bar aiki sun yi babban rashi!


Mai Girma Gwamna yace "munji bukatar ka amma ba haka muka so ba tunda mun maka alkawari zamu maka duk abun kake so toh ba zamu saba alkawari ba, mun yarda ka ajiye sannan a duk lokacin da kake bukatar dawowa toh kofa a bude take"


Wani murmushin dadi ya kubce a fuskan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login