Showing 66001 words to 69000 words out of 82682 words
shi sannan yace "Nagode sosai da sosai!
Duk wanda yazo wajen yaci ya sha wasu ma harda guzuri suka yi ga kuma kyautan shadda, karamin buhun shinkafa da dubu 10 aka ba ko wani namiji mata kuma atamfa, shinkafa da dubu 10!
Haka taro ya watse kowa yana cikin farin ciki da annashuwa!
Dr. Godwin yana fitowa yan jirada suka tsare shi suna mishi tambayoyi!
Wani yace shin zaka iya fada mana ya akayi ka iya yin wannan aiki me hatsari wanda baka taba yi ba?
"Ba yin kaina ba ne ikon Allah ne kawai domin da yardar shi ne na samu daman yin wannan aiki!
Zaka iya fada mana dalilin ajiye aikin ka a lokacin da mutane ke tsananin bukatar ka?
"Bana yin aiki cikin walwala kuma a cikin damuwa nake yin komai shiyasa na zabi barin aikin domin aiki na yana bukatar natsuwa da kwanciyar hankali!
Toh meke saka damuwa?
Wannan kuma personal issue na nane wanda ba zan iya fada ba!
Haka dai suka yi ta mishi tambayoyi wani ya ba su amsa wani kuma ya share su!
A can Lagos ma Momma, Dad da Annabelle suma suna kallon komai! Farin ciki mara misaltuwa suka dinga yi Momma har da kukan farin ciki, nan fa suka zube gwiwowin su kasa suna wakan godia irin na addinin su!
_Rukkybae_πππ
[12/4/2017, 10:45 PM] RukkyBaeπππβ£β£: [12/3, 2:45 PM] RukkyBaeπππβ€β£: β€π€β₯β£β₯π€β£β€π€β₯π€β£β₯β€π€β€β£β₯β£β€β£β₯β£β€π€β€π€β£β€β₯ *MATAR DOCTOR* β£β₯π€β€β£β₯π€β£β€β₯β£π€β₯β€β£π€β₯β£β€π€π€β€β₯β£π€β₯β€π€β£β₯
_Rukkybae_πππ
π *HAJOW*π
βπ»βπ» *_HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS_* βπ»βπ»
_Duk abunda hakuri be baka ba toh rashin hakuri ba zai baka ba!!!_
_Mu kasan ce masu hakuri a koda yaushe!!_
1β£1β£1β£
Washe gari da wuri ya fara shiri dan komawa Lagos ko su Momma basu san ze zo ba dan surprise yake son basu!
Yana zuwa airport ya gama komai nan da mintuna 30 zasu tashi!
π€
Yana fitowa daga jirgi ya tsare taxi, daya ke drop ya dauka har kofan gida ya ajiye shi!
Kallon gidan ya dinga yi a ran shi yace "nayi missing gidan nan da mutanen gidan! Sannan ya fara knocking kofan!
Mai gadi dake zaune yana gyangyadi yaja tsaki yana fadin "waye ne ze zo ya dame ni ina hutawa ta! Ya tashi riqe da sanda yana fadin ''waye ne a wajen?
Shiru Dr. Godwin yayi!
Mai gadin ya kara tambaya nan ma shiru! Wani dan karamin space dake jikin kofan wanda zaka iya hango mutum daga waje ya dan leqa!
Budewa yayi yana fadin "ka zo kana ta faman knocking ana tambayan ka waye kayi shiru kuma kana ji! Wa kake nema?
Cike da mamaki Dr. Godwin ke kallon shi a ran shi yace "gaskiya wannan bako ne be san da wanda yake magana ba!
''Mr. Man in ba zaka yi magana ba ka fita tun kafin raina ya baci in maka rashin mutuncin"
Kallon sama da kasa Dr. Godwin yayi mishi sannan ya raba shi ya fara tafiya!
Da gudu ya biyo shi yana fadin "kai wani irin mutum ne? Kazo ana maka magana kayi banza da mutum sannan ka wani shige ba tare da izini ba''
Shi dai be tanka shi ba ya cigaba da tafiya cikin bacin rai!
Se fama masifa Mai gadin yake mishi tare da fada mishi duk maganar day yaga dama a haka har suka kai kofan parlor'n gidan!
Hayaniyar mai gadin ne ya fito da su Momma cikin sauri! Cak suka tsaya suna kallon Dr. Godwin tsaye ya yamutsa fuska da ganin shi yana cikin bacin rai! Har rige rige suke wajen karasowa in da yake, a tare suka karaso suka rungume shi, shima ya ajiye akwatin hannun shi ya rungume su yana jin wani irin natsuwa tare da jin duk wata bacin rai ya kau suka ce "we really missed u Baby!
yace "I missed u more ! There is no place like home!
Mai gadi dai kallon su kawai yake yi yana mamakin waye wannan! Yana cikin tunani ya tsinkayo muryan Dr. Godwin yana fadin "Momma I want this trash outta this house! Ya nuna mai gadi!
Kallon shi Momma tayi tace " haba Baby daga dawowan ka yau ka fara daga murya mu je ciki kada kanka yayi ciwo"
"No Momma ba zan shiga ba se naga an kore wannan abun daga cikin gidan nan kuma ba se anjima ba yanzu nake so ya bar gidan nan"
Gwiwowi biyu mai gadi yasa a kasa yana fadin ''Oga abeg, abeg u in d name of God forgive me, ban san kai dan gidan nan bane, nayi haka ne sbd kare aiki na amma ba dan komai ba ka taimake ni kayi hakuri!
Wani kallon raini ya watsa mishi kafin yace "kar ka bari in fito in sake ganin ka a gidan nan! Ya wuce su Momma ya shige ciki!
A tsakar wajen Mai Gadin ya fadin yana ta kuka kamar karamin yaro! Annabelle ta kalle su tace "Momma haka zamu bar shi ya tafi? Ji yanda yake kuka, kuma kun san wahalan da yake ciki kafin ya samu wannan aikin kuma Dad ne fa ya kawo shi!
Momma tace "toh ya kike so muyi? Kema fa kin san halin Baby in yace yana son abu in ba a mishi ba akwai matsala, ni dai bazan bata mishi rai ba daga dawowan shi!
Annabelle ta kalli Dad tace "Dad zaka iya mishi magana ya yi hakuri?
"Princess kin san halin Brother din ki I don't think ze janye daga abun da ya fadi!
A ranta tace "ohh! Gaskiya sun shagwaba Babyn Momma da yawa su basa tunanin halin da wasu zasu shiga se gudun bacin ran dan su!
A fili kuma tace "OK! OK!! Naji I will handle it my self" ta wuce su!
A bakin kofan dakin shi ta tarar da shi a tsaye ya dafa kanshi , a hankali ta karaso tare da dafa bayan shi ''Babyn Momma me ya faru?
"Lil Sis ki kalli Dakin nan duk kura! Na kasa shiga ciki sbd na san ba zan iya takawa ba kuma ina so in yi wanka amma ba zan iya ganin dattin nan ba gaskiya"
Huh! Babyn Momma ba zaka taba canzawa ba, ni ban ga wani datti ba dan ko shekaran jiya seda Momma tasa aka gyara maka amma yanzu kazo har ka fara rigiman ka!
Dariya kadan yayi duk da baya jin yin haka amma ba zai iya bata rai ba In yana tare da ita sbd yana tsananin son ta!
"Toh naji ba zan iya yi a nan ba can I use ur toilet pls! Ya hade hannayen shi waje daya alaman ro'ko!
Dariya tayi tace "Anything 4 u Babyn Momma, amma zan ro'ke ka wani abu in ba zaka damu ba!
Yace '' Uhum ina jin ki Lil Sis!
Hannu ta miko mishi alaman su kulla alkawari, shima ya mi'ka mata suka kulla!
Tace "Daman akan mai gadi ne pls kar ka kore shi, cuz in ya bar nan bazai dunga samun abinci ba pls ka taimake shi!
Ajiyar zuciya ya sauke dan dai kawai sun yi alkawari ne da ba zai janye kudurin shi akan koran mai gadin ba! Gira kawai ya daga mata ya wuce hanyar da zai kaishi dakin ta!
Dadi taji daya hakura kuma ya yarda , da sauri ta fita tace ma Mai gadi "yace ya hakura but kaima ka kiyaye ko dan nan gaba ka dena daukan mutane for granted! Godia ya dinga mata kamar ze kifa dan murna!
A takaice dai se da aka sake share dakin aka wanke mishi bayi tare da sa room freshener kafin ya iya shiga dakin!
Abinci aka shirya mishi yaci ya dan kwanta dan hutawa se bayan ya tashi suka sha hira sosai harda irin nasarorin daya samu ta fannin aikin shi amma be fada musu komai akan Janan ba dan ya barma kan shi sani! Dad ya fada mishi nan da 1 week zasu koma gidan daya gina musu a Abuja a nan se ya nema aiki kafin a gina mishi nashi asibitin!
Yaji dadi sosai!
Se can dare suka wuce dakunan su don su kwanta...!!!
π€
β₯
*Kuyi hakuri zaku dan dinga jina shiru ba zan samu daman turo muku MATAR DOCTOR a kan kari ba sbd waya ta tana da matsala..!! Da fatan zaku fahimce ni kuma za ku yi min uzuri!! Nagode sosai!! I LOVE YOU ALL!!!*
_Rukkybae_πππ
[12/9/2017, 11:14 PM] RukkyBaeπππβ£β£: [12/9, 7:25 PM] RukkyBaeπππβ€β£: β€β£β₯β β£β₯β£β β£β₯β£β₯β£β β₯β£β β₯β£β β₯β£β£β₯β β£β₯β β£ *MATAR DOCTOR* β β₯β€β£β₯β β₯β£β€β β₯β£β β€β β₯β£β₯β β€β β₯β£β₯β β€β β£β₯β€β β₯β£β€β£β₯
π *HAJOW*π
*Hakuri Da Juriya Online Writers*
_Rukkybae_πππ
_Wannan shafin naku ne Masoya na!_
_Wasu sun sanni ni ban san su ba!_
_Wasu na san su amma su basu sanni ba!_
_Wasu na san su sun sanni_!!
_A duk inda kuke ina son ku kuma ina gaida ku!! Allah ya bar soyayya_!! ππ
1β£1β£2β£
Sati na zagayowa su Momma suka koma sabon gidan su dake Maitama Abuja! Gida ne mai kyawun gaske komai ya ji! Self contain aka ware ma Dr. Godwin!
Cikin satin suka fara shirye shiryen komawan Annabelle sch, Momma tayi tayi ta bari a aiki driver ya siyo mata duk abunda take bukata amma Annabelle ta k'i yarda tace "Momma ni kam nafi so in je da kai na ba lallai bane ya siyo min duk abunda ya kamata ba'' suna cikin haka se ga Dr. Godwin ya shigo yana danna wayar shi, kujeran da suke zaune ya zauna shima amma a tsakiyar su
Yace "maganar me kuke yi baku kira ni ba?
Momma tace "wai dole Ita da kanta zata je kasuwa siyo kayan komawan ta sch, ni kuma nace ta bari Driver yaje''
Yace "toh Momma ki barta mana in dai zata iya good and fine'' ya daga kafadu!
Toh shikenan tunda haka kace, but ba za tayi driving ba se dai driver ya kaita in ta gama su dawo"
Tace ''na yarda! Thank u Momma!
Gefen Dr. Godwin ta juya tana mishi wani kallo me nuna alaman roko!
Ya gane me take nufi amma yace "ki je ki shirya mana ki tafi kin zauna kuma time yana wucewa''
Kasa tayi da ido tana lankwasa yatsun ta kafin ta d'ago tana fadin "Babyn Momma pls ka taimake ni ka raka ni''
"I can't! Ki je ke kadan ki se kin dawo! Ya cigaba da danna wayar shi! Jiki a sanyaye ta tashi, be ankara ba ta fizge wayan tana mishi gwalo, ganin ya tashi ne yasa ta fara gudu, aiko shima ya bita, haka suka dinga zagaye dakin se faman ihu suke yi kamar kananan yara
Momma na daria tace ''baku san kun girma bane?
Da kyar ya iya kamo ta rike da kunnen ta suka karaso inda Momma take suka zube suna maida nunfashi, da sun kalla juna se su tuntsire da daria, haka Momma ta biye musu suka dinga kwasar daria mara dalili! Seda suka gaji dan kansu sannan suka yi shiru!
Tace ''Babyn Momma bari in shiriyo mu tafi'' bata tsaya jin amsar shi ba ta wuce da sauri..
Inda ta barshi ta dawo ta same shi, ta fito dauke da hand bag, tace ''are we good to go?
Ya mike ya na fadin "ni dai gaskiya kin takura ni, oya muje''
A tare suka je suka yi kissing kumatun Momma suka ce ''se mun dawo!
Tace ''a dawo lfya, ku kula da kan ku banda rough driving kuma kada kuyi dare ku dawo da wuri''
Yes MUM! Suka amsa sannan suka fice!
Murmushi tayi ita kadai tana fadin "ina matukar son ku, bani da tamkar ku, ina alfahari daku 'ya' ya na! Ta jingina a kujera tana murmushin jin dadi!
Se yamma likis suka dawo, basu samu Momma a parlor'n ba, suna shigowa suka baje a kan kujera dan ba karamin gajiya suka yi ba! A haka Momma tazo ta same su tace ''kun sha kasuwa!
Annabelle taja dan gutun tsaki tana fadin ''I'm damn tired Momma ji nake kaman ba zan iya daga yatsa na ba sbd gajiya''
Dr. Godwin yace "ke kenan da kayan ki ne ni da naje rakiya in ce me? Duk kin bani wahala yau din nan yanzu ma kaina ciwo yake min'' ya yamutsa fuska!
Momma ta tako da sauri tana taba goshin shi tare da mishi sannu!
Annabelle tace '"O! Momma abun ma yar son kai ne? Ni ba ki da mu da gajiyan da nayi ba se Babyn ki koh?
''eh mana! Ai shi rakiya yayi ke kuma fa kika ce da kanki zaki je toh yanzu miye kike korafi?
Sum_sum ta wuce dakin ta dan bata da bakin magana tunda ita tace taji kuma ta gani!
*******
Su Janan ma se shirin tafiya makaranta ake yi, duk abunda take bukata Abbiey ya siyo mata dai dai gwargwado! Gobe za a tafi kai ta!
Ummiey da Abbiey zaune a parlor suka kirata suka mata nasiha me tsuma zuciya tare da mata Addu'ar samun nasara!
β₯
Washe gari!!! Cikin shiri suka fito dukkan su harda Ya Khaleel da Ya Saleem, a motar da Abbiey ya siya musu na gida zasu tafi wacce ta sha tinted glass, Abbiey yaso suje da nashi amma da safe suna dubawa suka ga tayoyin sun yi kasa, babu yanda za su haka suka hakura!
β
Momma suma sun shirya an saka komai a bayan boot, sun so subi jirgi amma basu yi booking da wuri ba Dr. Godwin ne ze tuka su, shima dai motar tashi rufe take da tinted! Hanya suka dauka suna tafe suna jin waka Dr. Godwin yana ta sharara gudu don sun makara wajen fitowa, seda suka biya banki suka biya kudin komai harda wajen kwana inda Momma taso a kama mata off k' amma ita Annabelle din tak'i tace tafi son cikin sch yanda komai za ayi tana nan ba zata dinga makara ba.. .
Cikin lokaci kadan aka gamawa Janan komai, harda dakin kwanan ta, sun gamsu da dakin Ummiey ta tayata jera kayayyakin ta sannan suka shirya tafiya, tayi kuka kamar idon ta ze fita, suma dai duk jikin su yayi sanyi da ba karamar kewanta za suyi ba, da kyar suka lallashe ta tayi shiru sannan suka dau hanyar tafiya tana daga musu hannu har suka bace sannan ta koma ciki!
A dai dai bakin gate suna zuwa fitowa su kuma Motar su Dr. Godwin na kokarin shigowa, da yake tinted ne glasses din nasu babu me ganin wani a haka kowa ya kama gaban shi!
Suma haka suka gama komai aka ba Annabelle dakin da Janan din take, har bakin dakin suka rakata ta Momma da Dad suka shiga shi kuma Dr. Godwin yace ba zai shiga ba yana jiran su a mota, babu irin rokon da Annabelle bata mishi ba ya shigo amma ya k'i, dan dolen ta ta kyaleshi ta shiga,..
Sallah suka tarar da Janan tana yi, su kuma suka dinga jide kayan su har ta idar, ganin su yasa gaban ta ya fadi, ga shi harda namiji ya shigo ita bata so aka hada ta da Christian ba amma babu yanda ta iya, cikin mutuntawa da girmamawa ta gaida su! Da fara'a tare da sakin fuska suka amsa mata!
Momma tace ''kina da kyau ya sunan ki?
Murmushi tayi cike da jin nauyi tace "Janan Pharouk Makarfi!
Wow nice name suka ce da ita!
Ita kuma sunan ta Annabelle, hope zaku zauna lfya!
''In shaa Allah'' tace da su!
Horn din da Dr. Godwin ke zabga musu ne yasa su fitowa da sauri tare da yima Janan sallama, har bakin mota Annabelle ta rakasu sannan ta dawo cikin dakin!!
_Rukkybae_πππ
[12/15/2017, 10:57 PM] RukkyBaeπππβ£β£: [12/13, 7:30 PM] RukkyBaeπππβ€β£: β₯π€β β€β π€β₯β€β π€β₯β€β β₯β€β β β€β₯β β€β₯β β€π€β₯β β€π€β₯β€β π€β₯β€β π€β β₯π€β₯β *MATAR DOCTOR* β₯β π€β₯β π€β€π€β₯β β₯π€β€π€β₯β π€β€π€β₯β β₯β π€β€β₯π€β β₯β€β β₯π€β€β π€
_Rukkybae_πππ
π *HAJOW* π
_*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*_βπ»βπ»βπ»
_This page is 4 u My lovely Frnd and also a Sis, Hauwa Slim Small! Happy birthday to u, i wish u long life, good health and all d good things Fidduniya wal Akhirah! Allah ya Albarkaci Rayuwar Ki_! πππππ
1β£1β£3β£
π€
Se da suka kara introducing kan su ma junan su, a yanda Janan ta lura da Annabelle tana da sakin fuska! Hira jefi jefi suke dan yi tunda ba wani sabawa suka yi balle su saki jiki sosai, Janan tace "Wani course zaki karanta?
Annabelle tace ''ai ni returning student ce ina karanta Pharmacy'' ke fa?
Janan tace ''ni sabuwar daliba ce amma through Direct Entry yanzu haka zan karanta Gynecology ne!
''Wow kice ke babba ce, gaskiya nayi sa'an roommate, congratulations Dear!
Murmushi me sanyi Janan tayi mata tana fadin thanks!
******
Haka zaman su ya kasance gwanin ban sha'awa inda Annabelle ta dinga nunawa Janan koina na makarantan! Tare suke fita lectures dan kusan komai iri daya ake musu se dan abunda ba za a rasa ba!
Kusan kullum se sun yi waya da su Ummiey, dan ba karamin kewan ta suke yi ba, ga kuma kudi da dukkan su suke turo mata harda su Yaya Khaleel wai na handouts da Assignment, kwata kwata Annabelle bata bari tayi komai da kudin ta ita take musu wani lokacin ma Janan bata san an bada abu ba tunda bata shige-shige se dai taga Annabelle tayi mata, har girki basa yi se dai Annabelle tayi musu takeaway!
Yau ma kamar kullum Janan sanye da dogon Hijjab har kasa da socks sun fito daga lectures a gajiye suna tafe suna maganan lectures din da aka musu yau, Annabelle tace ''mitchwwwww ni ban san me ya